🧑‍🍼 RABO...❣️

21

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode twenty one 

               WASHE GARI

10 da wani abu Omar Kano ya isa gidan Omar Abuja, dukda baya cikin yanayi me dadi haka ya masa masauki a garden, yana daga zaune ne ya zubawa Omar Abuja idanu cike da tausaya wa harya karaso inda yake din shima ya zauna kan daya daga cikin kujerun gurin yana waya ya baza kunnuwan sa Omar Kano tsaf yagama nade abunda suka tattauna shida jami ay seda ya gama wayar suka gaisa yake tambayar sa ya maganar yarinyar tasa kuwa,jujjuya kai kawai yay cike da damuwa yace 

" Omar batun Baby a yanzu yagama daure min kai da mamaki, koda sheda daya an gagara samu akan lamarin nan, kawo yanzu bansan iya ina aka baza hotunan taba gidan radio stations television babu inda ba akai bah, muna cikin tashin hankali gaskiya canma gidan mu sun tashi hankalin su dondai na hana kowa zuwa da yanzu sun cika gidan nan anata koke koke ni kuma banason wan nan ko kadan hayaniyar banaso saboda matsala ta nima abinda nake fama dashi" 

  " Tabbas dole hankalin ku ze tashi zamu dage da Addu'ah Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu, in Sha ALLAH daga yau ciwon da kake fama dashi zaka samu afuwa, ajiya naje gurin malamin mu na masa bayanin matsalan ka yabada rubutu ka fara sha kafin kaje yasan meya kamata ya maka, so ina ganin tunda abin yana damunka haka meze hana muje gurin malamin a yau daga nan semuyi masa bayanin baby ayi mana Addu'ah harda sauka duka ayi akan ta wan nan ma hanya ne me kyau dukda jami ay na aikin su se an dage da Addu'ah don bawan da yasan hannun da ta fada a yanzu" 

  Seda yaja dogon numfashi ne tukunna yace" Eh Omar ko acan gida shanono ma sunata yi har saukar ma amma duk da haka bazan kibin shawaran kaba zan iya yin komai akan baby kota lpy din tawama banayi baby yarinya ce taya hankalin mu ze kwanta? Komai nawa na ajiye shi a gefe meze hana bazamu je can gurin malamin ba idan rana tayi sanyi semuje tun da ka riga ka sanar masa gara muje din Allah yasa dai mu dace" 

" Ameen summa Ameen" shine kawai abinda Omar kano yace yana me kafe Fanan da kallo ta kasan ido tana tafe garesu cikin nutsuwar ta hannun ta dauke da tray me dauke da coffee tasha abayan ta me kyau tayi rolling sedai kana kallon face din ta zata baka tausayi yadda tadan tasa da eyes dinta sunyi jah kamar batason taka kasa har ta karaso da sallamar ta daddyn nata ya amsa yana kallon ta cike da damuwa shima, " morning Daddy" shine abinda tace dashi ta ajiye tray din tana zuba musu coffee din, " Fanan kukan kike har yanzu ko?" Dad din nata yay magana ita kam kasa rike hawayen ta tayi suka soma sauko wa ta girgiza masa Kai alamun a ah seda ta gama zuba musu coffee din ne ta tsugunna ta gaishe da Omar Kano Sosai Fanan ta birge shi don shidai kam yanason yaga mace me nutsuwa da ladabi cikin dan guntun smile yace,

  " Fanan how are you? And our concerns?" 

Kan Fanan a kasa batare da ta dagoba tace " ALHMDLH!" Sosai yaji tausayin Fanan din ya kamashi ya zaro handkerchief ya sunkuya saitin face din ta yana mika mata yace, " please stop crying" se a wan nan time din ne Fanan ta dago ta kalle shi heart dinta yay wani irin bugu arba datayi da kyakkyawan halitta sa me cike da haiba da kwarjini yadda ya zuba mata oily eyes dinsa ne yasa tai saurin sunkuyar da kanta  kasa jikin ta daya karayin sanyi tasa hannu ta amsa handkerchief, " thank you" shine tace dashi tana mikewa harta juya zata tafi yace " ki gaida min da mummy din taku kice ina mata jaje kinjee!" Jinjina masa kai tayi batare da ta juyo ba tayi gaba tana share hawayen kamshin handkerchief din na sanyaya mata zuciya sam barka Fanan na shiga ta hadu da mummy din tata da sadiya a parlour wanda shima mutan company dinsu ne sukazo musu jaje ta fito parlour din zama kusa da ita tayi gamida da cewa " mummy bakon Dad yace a gaishe ki yana miki jaje" jajayen Idanun ta ta dago tana kallon ta dasu tace " waye bakon nasa?" " Ban taba ganin saba mummy, yaro nema saurayi!" Hakan nan Maya taji faduwan gaba ya sameta wanda ta rasa dalili seda ta gyara zama tana fuskan tarta tace " to waye wan nan kenan?" " To kije mana ki gani ko waye tunda kin damu" sadiya tace da ita, ba musu kam ta haura upstairs seda ta shiga cikin bedroom dinta ta bude window ta hangosu kuwa sedai ta kasa tantance fuskan Omar din kuma faduwan gaban ta yana kara hawa wan nan dalilin ne yasa ta gaza hakuri ta sauko ta fice ko su sadiya bata kalla bah, 

   Omar kano na cikin sipping coffee din sa ya hango ta aikuwa yasaki wani almurin smile sam Omar Abuja be kula da itaba yanata magana da jami ay din dai a waya sedai yaji maganar ta akan su ya dago yana kallon ta wanda ita kuma Omar Kano din take kallo cikin wani yanayi me wuyan fassara wa tabbas kam ta shaida shi yanzu fuskan Zainab kawai take gani saboda kaman da suke sosai ta shaida shi tun ranar da ta gansu a TV shida Ammin tashi, " kaine bakon namu dama?" Se a yanzu datayi magana ya dago yana kallon ta kallon da duk wani me hankali akaiwa shi yasan akwai wata a kasa be dena sipping coffee dinba be dena kallon nataba yace " yesss! Nine kinyi mamakin ganina Koh?" Nannauyen ajiyan zuciya ta sauke taja daya daga cikin kujerun ta zauna tana cewa " lallai kam nayi mamaki kwarai da gaske wan nan shine ake kira da ana zaton wuta a makera se gata a masaka"  " Wlh ay kinsan haka Allah yake lamuran sa mummyn Baby" dauke kanta tayi ta kalli mijin nata daya gama wayar yanzu jikin sa duk ya kuma yin sanyi tace " Daddyn Fanan ba wani labari har yanzu" kamar yay kuka ya girgiza mata kai yana cewa " Lamarin baby na daure min kai da mamaki Maya" murmushin dayafi kuka ciwo tayi wanda ta gama karance Omar kano tsaf tace " lamarin baby yadena daurema kai daga yanzu ina ganin komai ma yazo karshe tunda an gagara ganin ta kawai kabar min komai a hannu na zanji da komai dayar dar Allah sena dawo da ita cikin gidan nan" sosai Omar Abuja ke mata kallon mamaki don be kula da al amarin daya kasance ba tsakanin su,sedai a yanzu sam baya iya musu da ita kanshi ya kada gami da cewa " duk yadda kikace, tunda kina ganin zaki iya" bata tanka masaba se harara da take makawa Omar kano kamar idanun ta zasu fado san nan ta maida idanun ta kan coffee din dake ajiye tace " yaro man kaza yaro besan wutaba seya taka, dan gidan Zainab tun yaushe kake a garin namu ne?" A zuciyan sa yake murmushi ganin Maya na so ta bige cikin sa beko kalle taba yace " nayi kwanaki anan ay yanzu ma jaje nazo yi miku gobe in Sha ALLAH zan koma" seda ta jinjina Kai tace " kagama abinda ya kawoka kenan gobe kuma zaka koma" 

  " Gaskiya na gama komai aikin danazo yi kuma nayi nasara Alhmdlh, kinsan harka ta kasuwan ci babu sanya kamar dai wanda akawa kullal len makirci yana fafutukar nema wa kansa mafita, muma haka muke aiki tukuru kamar yadda mijin ki shima keyi babu abinda zance se Allah ya mana jagora" Omar Abuja ya amsa da Ameen yaname Nazar tar kalaman nasa ita kuwa Maya sosai gumi ke tsatstsafo mata tana jin heart dinta na shirin karaya tana kin bata dama batare data kuma tanka waba ta mike ta koma ciki zuciyan ta fall da tunani da rudu tashin hankali duka sun sameta a wan nan lokaci, shikuwa Omar Kano bashi yabar gidan ba se wajan 12 saura seda sukazo sallama ne yabawa Omar Abuja rubutun da malam ya masa ya shaida masa ze fito da yamma kuma suje gidan nasa da haka sukayi sallama ya koma ciki, suna fara tafiya Omar ya shaida ma guards din nasa cewa su saka ido ko zasuga mota na bibiyar su, ko 3 minutes ba ayiba kuwa suka sanar masa a waya wani bakin moto na binsu kawai yasaki almurin smile ya shaida musu da su kyale motar kawai, seda ya kashe wayan tukunna yace " WOW Maya basirar ki is so excited,bari muga kuma ina zata tsaya"

                 KANO

Tunda garin Allah ya waye Farid yake fama da baby domin tubure masa tayi seya kaita school koya kaita gida koya kira mata mummy, gajiya yayi kawai da rigimar tata ya kulle ta a bedroom tun tana bugun kofan da karfin tsiya tana kuka harta koma rarumar komai tana bugawa a kofan Sosai Farid ya gaji kansa harya fara ciwo ya daga waya ya kira Omar beyi picking ba cilla wayan yay gefen sa ya mike ya isa bakin kofan....✍️