21
by @nanabmb
🧑🍼RABO!!❣️
*NA*
NANA BMB
Episode twenty two
Omar Abuja seda ya shiga dakin sane ya dauraye cup don komai na dakin na bukatar gyara kwana biyu Maya bata gyara masa dakin ba saboda tashin hankali da suka shiga hakan nan ya zauna gefen bed ya tsiyaya rubutun maganin yay Bismillah yasha abinsa sedai tun kan ya cire cup din daga bakin sa yasoma jin cikin sa na wani irin juyi nan danan ya rintse idanun sa gami da damke hannayen sa yadda cikin ke murde sa ko salati ya kasa bude baki ya furta se faman juya kai dayake yi yana cije lips ga wani irin tukuki dake taso masa a hankali a hankali yasoma jin kamar amai na taso masa lokaci daya kuwa ya taho gaba daya cikin zafin ciwo yay azamar shiga bathroom tunda ga bakin kofa yasoma yin vomit din bakin kirin dashi ga yawa sosai ya gala baita kuwa seda ya gama ne ya cire duka kayan jikin sa ya sakin ma kansa shower mamaki ne ya kama Omar Abuja matuka dayaga bakin aman dayayi yana kokarin tuna meya cine yasa shi haka rubutun maganin ya fado masa a rai se yake tunanin shine yasashi wanga bakin amai tass ya wanke bayin yay wanka ya fito jikin sa yayi weak sosai ga kansa dayake jin sakayau sedan abinda ba a rasa ba boxes kawai ya iya sawa ya kwanta cike da mamaki bacci ya dauke shi,
Farid yana bude kofan baby datayi wani uban tsalle ta shake masa wuya tana barza kuka tana dukan sa tako ina duk tabi ta gigice ko maganar ta kasa dukan karfin sa yasaka ya rike mata hannun nata ya zaunar da ita kan kujera cikin seriously yace " baby ki tsaya ki nutsu ki saurare ni ya kamata kicire gida a ranki yanzu Bayan zu zaki koma ba se randa Allah ya nufa school ne idan kinaso ni dakaina nayi miki alkawari zan sakaki wata anan garin so gara ki dena batawa kanki time ki nutsu kisan me kikeyi" cikin kuka baby tace " Yanzu bazan kuma ganin mummy dasu Dad ba meyasa zaka sace ni menayi maka?" Sosai ta bashi tausayi ganin yadda take kuka jiki a sanyaye yace " zaki sake ganin su mana zaki koma gida idan lokaci yayi" " to yaushe ne time din zeyi?"
" Gaskiya babu rana don kima dena saka rai"
" Wlh bazan iya rayuwa anan ba ni kadai ko yaya ce ka kawo min please koka tausa ya min ka maida ni gida bazan iyaba kaji tausayi na ni yarinya ce"
Dafa ta yayi cike da rarrashi yace " zaki iya mana idan kika sawa zuciyan ki salama Addu'ah zaki dage da ita Allah yasa mummy tazo da wuri ta tafi dake gida" kura masa idanu kawai tayi cike da mamaki da al ajabin sa tace " tell me please meyasa ka saceni" murmushi kawai yayi yace " ay bani na sace kiba kula dake ne kawai aiki nah" cikin kwalalo idanu tace " to waye ya sace ni dama ba kai bane kaje school dinmu ka tafi dani"
" Nine mana ay sani akayi na kawoki nan"
" Bazan yarda dakai bah kaine kawai ka dauke ni na fuskan ci makarya cine kai kullum Karya kake min" bata fuska yay sosai yace" yayi kyau zaki gani ay yarinya inma karya na gaya miki wan nan bakin rashin kunya taki an kusa ladaftar dashi" bata ce kala ba sema harara datake binsa da ita cikin tura baki tace " toni inason yin wanka babu kuma kayan da zan saka don kasan bazan kara saka kayan kaba" mikewa yay yace " yanzu zanje na kawo miki autar mummy ki jirani yanzu zan dawo" a firgice ta mike ta rike masa hannu jiki na bari tace " wlh bazan iya zama nan ni kadai ba ka temake ni kada ka barni a nan ni kadai, wlh ban taba zama ni kadai bah bazan iyaba tsoro nakeji ka tafi dani" duk a firgice take masa maganar hawaye na zuba zaro idanu yayi gami da cewa " inje dake Ina?" " Inda zaka nima zani, sena zabi kayan ma danake so"
" A ah indai kika bini to bazan siyo miki ice cream din ba in kika zauna kam yanzu zan dawo" tana sharar kwallah tace " ay tsoro nakeji ni!!"
" Karki ji tsoron komai kinji! Ki rufe idanun ki yanzu zan dawo kafin ki counting 10 na dawo" hannun ta ya kama ya zaunar da ita kan kujera ya soma smile yana cewa " yawwa baby wai ya sunan yayar kine?" " Mezaka yi da sunan ta? Ko itama wani mugun tar zakayi mata?" Zama dirshan yay a gaban ta yana zuba smile kamar a gaban Fanan din yake yace " sonta nake Baby hope ba tada saurayi dai Koh! Don tun time din dana ganta heart dina takeson rayuwa da ita inason na aure ta"
" Yaya Fanan din kake son aure?" Ta tambaye sa cike da mamaki" WOW!!! Sunan ta Fanan masha Allah Farid da Fanan forever in Sha ALLAH!! Sunan ma kanshi yasani shauki haka!" Batasan time din da baby tayi dariya ba tace " ay ita kuma bata sonka kuma ma tsoron maza takeyi yaya, uncle Abdullahi dayace yana sonta duk inda ta ganshi guduwa takeyi a school"
" That's good! kinga wan nan alamu ne dayake nuna Fanan tawace ni kadai" " ta ina ta zama takan a inama zakagan ta?" Ta karashe maganar ta tana tabe masa baki shikuwa cikin murmushin jin dadi yace " kedai rufe eyes dinki yanzu zanje in dawo yau zan siya miki ice cream harse kin barshi" murmushin jin dadi baby tayi cike da yarin ta ta rufe eyes dinta tasoma kirga ya daka tar da ita yace" not now sena fita zaki fara" kawai ta jinjina masa kai seda taji fitan sa yasawa kofa key ta waje tasoma kirga abinta shiku ma cike da jin dadi ya shige mota yabar gidan, be tsaya ko inaba se a gidan su bayan ya shiga da moto din sane yay parking yaje kai tsaye yay amfani da key ya bude kofan ya shiga cikin tan ga memen parlour din ya wuce direct part din maman tashi tana ganin shi ta saki wani irin lallau san murmushi najin dadin ganin autan nata datayi cikin farin ciki tace
" Auta saukar yaushe? Ina aminin naka nagan ka kai kadai?"
Bayan sun gaisa ne cikin shagwaba yake cewa " nifa Mama dawowa nayi abuna ayyuka ne suka rikeshi a can so bazan iya jiran saba gaskiya don nayi missing mama na na dawo in ganki" tunda ya fara maganar tasoma sallal lami tana tafa hannuwa da salati har taso bashi dariya ma, " Kai jama a Auta se a yaushe zaka canza halin nan naka? Se yaushe zakasan ka girma ne? Saboda tsiya taku irin naka shine ka taho ka barshi bayan tare kuka tafi" dan dariya yayi yace " To mama ba yadda zeyi dani ay, bemafa ce komai ba abinda gobe ze dawo ma" yayi maganar yana tura baki gaba harara sa tayi tace" kadai ji kunya wlh Auta son gidan nan naka yayi yawa ya kamata kasan me kakeyi don kasan kudirin Daddy ka dai ko kasan wajen nan dai seka jeta karatun likitan cinka yace bazakayi shi a nan ba kaima kuma ka sani" kamar yay kuka yace
" Mama ki tausaya mana keda Daddy please wlh banason tafiya nabar Omar anan shi kadai idan na tafi ban kyauta masaba na barshi shi kadai kinsan baya kula wasu abokai inba nibafa kema kin sani fah Mama ki fahimtar dashi"
" Aww! Da kana damuwa dashi haka ka taho kabar shi acan?" Mikewa yay fuska ba fara ah yace " ay kama wa tayi na taho nabar sa acan hakan baze kuma faruwa ba in Sha ALLAH" be kara cewa komai ba ya wuce nasa part din ta bishi da kallo tana murmushi tace " ja irin yaro bari idan daddy ya dawo seka fada masa dakan ka"
Sauri sauri Farid yay wanka ya shirya cikin kananun kaya yanata zuba kamshi yaci abinci sama sama yatafi abinsa don sauri yakeyi ya isa gurin shopping din sedai yama rasa wani kaya ze daukar wa baby don besan size dinta ba hakan ne yasa shi daukar duk wanda hannun sa yakai kai harda mayukan shafa kayan kamshi abubuwa na bukatu dai ya hada mata, hadi dasu ice creams din nata iyayen kaya jibgi ya diba tukunna ya nufi gidan....✍️