🧑‍🍼 RABO...❣️

22

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode twenty three 

Gudu yay sosai ya isa gidan ko murfin mota be gama rufewa bah ya dauka kayan yay ciki yana bude kofan ya tura yaji ya daki abu hakan yasa shi saurin zura kai ya leka yaga ashe baby dince ya bige tai wan war a kasa heart dinsa na bugu ya maza ya shigo yana sakin kayan ya sunkuya yasoma girgiza ta da karfi ai kuwa itama ta bude eyes dinta a firgice tana kallon sa cikin mayen bacci sosai ya saki ajiyan zuciya dayaga ashe bacci takeyi sosai ta bashi tausayi ganin yadda idanun ta suka kumbura alamun taci kuka ta koshi bata ce dashi kalaba illah zuba masa mayun idanun ta datayi gashi sun Kara kuru kuru sunyi waje nan da nan hawaye ya cigaba da wanke mata fuska sun kuyar da kansa kawai yay don yasan be kyauta ba ledojin shopping din yajawo ya aje mata a gaban ta murya a sanyaye yace " am sorry baby wani uzuri ne ya rike ni shiyasa na juma haka amma bazan kuma fitaba kinji sorry" duka yana maganar ne yana fito mata da kayan cikin ledojin ne seda ya gama cirowa ne yace " kici shawarma din ko da ice creams din kafin kije kiyi wankan" harya kare maganar tana kallon sa kuma bata dena zubar hawaye ba seda yay shiru ne ta kalli abubuwan da ya ajiye mata kawai ta dauke kai takoma kallon daya side din seda ya dago ne yaga halin da take ciki kawai yasa hannu ya juyo da face din ta saitin kayan yana cewa " see baby ice cream din na kawo miki fah harda shawarma kalla fa harda su biscuits" kallon kayan ta kumayi jiki ba kwari ta mika hannu da dauko roban ice cream din ta bude ta kuma zuba masa idanu sam ta kasa sha jikin Farid kara yin sanyi yay ya zauna a gaban nata cikin muryan tausayi yace " kona baki da kaina?" Tun kan ya rufe baki ta aje masa ice cream dinsa tana tabe bakin kukan na shirin kwace mata, cak ya tsaya Farid yana nazar tar ta kamar wanda aka tsikara ya mike cikin wani yanayi yace " baby kinyi breakfast kuwa?" Koda taji furucin sa kukan da take danne wa ya fito tasoma kam dafe goshin sa kawai yay yana cewa " ohh God!" Sam ya manta da batun abinci don ya tuna ko kadan bataci abinci ba tunda sukazo gidan, jiki na bari kuwa ya kwashe kayan ya karasa dasu ciki yazo ya daga ta ya kaita kan cushion ya zauna kai tsaye ya shiga kitchen cikin 5 minutes ya hada mata tea me kauri ya kawo mata ya hada mata da biscuits din batare da wani bata lokaci ba ta mika hannu ta damki cup din don har hannun ta yana rawa saboda yunwa zafin da tajine a jikin cup din ta sake shi Allah yasa yay azamar rikeshi da seta kuma sashi wani wahalan hada wani, mikewa kawai yay ya je kitchen din ya fifita mata tea din ya fito duk ya hada uban gumi tana zaune tai yaushi sosai ya kuma aje mata cup din to Yanzun ma data kuma daukar cup din aje shi tayi ta cigaba da kuka abinda ya kara hassala Farid kenan cikin masifa yace 

  " Banason iskancin nan nakifa! Yanzu wan nan tea din ne yay miki zafi? Ya kike so ki shashi kenan? Sedai in ruwan sanyi dama kike sha" ya karashe maganar a kufule ita kuwa se daga masa kai take alamun eh cikin muryan kuka tace " mummy sirka min tea din takeyi da ruwa banason zafi" cikin banka mata uwar harara ya suri cup din yaje kitchen din ya tari ruwa a tap ya juye rabin tea ya zuba mata ruwan yay sanyi kalau haka ya fito a zuciyan sa yanata masifa ya kuma aje mata cup din yana mata kallon warning, seda ta taba cup din taji babu zafi yasa ta saurin kaiwa baki tasoma sha in minute baby ta shaye tea din nan cikin cup ta miko masa cikin tura baki tace ban koshi bah" 

  " Dama taya zaki koshi kin  ki hada wa da biscuits din ko shawarma din daba seki hada da itaba babu wani tea dazan kuma dafa miki na gaji ragowan naki zan Kuma zubawa ruwa na kawo mikin" batare daya jira cewar taba ya mike gamida war tar cup din yaje ya kara zuba wa ragowan ruwa ya kawo mata, to a yanzun ma dai kwan kwadar tea din take abin ta Farid ya daka tar da ita " kinga kika shanye tea din nan baki hada da biscuit din nan ba nida kene! Kalli yadda kike ta shan ruwan tea bayan kinajin yunwa" 

  " Kaga nifa bana hada tea da komai ahaka nake shan kayana mummy ma tasani bata bani komai se tea din da safe don haka ka rabu dani, mugu kawai bayan ka barni yunwa ta gama min mugun ta" galala Farid yake kallon ta harta kare shaye tea din ta ta aje masa cup din sa tayi gyatsa, cikin shan toka yace " common ruwan tea da kika sha ya baki damar yi min rashin kunya Koh! Wlh yarinya tausayi kike bani a gaba amma bari dai nayi shiru" ay koda taji haka baby mikewa tayi ta nufi bakin kofa ta saki kuka tasoma kokarin budewa zata fita tana kiran mummy ay a dari da sittin ya isa gareta Kafin yay nasarar rike tane ta zille itama a guje ta soma zaga kujerun tana aikin Kiran mummy tana kuka idan yayi tanan ta zille tai daya bari gajiya kawai yay ya zauna yana dafe kansa ta kara kwasa a guje tai gurin kofan jiki na karkar wa tana Allah Allah ta bude ta fice taji yay sama da ita ta kuwa soma cilla kafafu tana ihu ta dole seda ya sauke ta cikin gigi tat tar tsawa daya mata yace " stop!! Tunda abinda zakiyi kenan bari na tafi na kulle ki a gidan bazan kuma dawowa ba dodo ya cinye ki!" Ya karashe maganar a hasale yaname juyawa tai azamar rike shi tana juya kai tana cewa " nadena please am sorry kada ka kuma tafiya ka barni na roke ka wlh tsoro nakeji bazan kara bah na dena kada ka tafi kajee" fisge hannun sa yayi ta kara rikewa kawai yay cilli da ita kan kujera ya nufi kofa hakan yasa ta sakin gigitat tar kara jin haryana shirin bude kofan ta duro akan kujeran a guje tai gunshi sedai ashsha tin tibe tayi da kayan daya siyo mata ta naku da kasa ta kuma sakin wani kukan harda ihu kamar zararra, jitai kawai ya daga ta ta kara kankame masa hannu jikin ta rawa kawai yake Saboda tsoro don duka ta bayar fita din zeyi, shi kuma yayi hakan ne don yayi maganin ta kusa dashi ya zaunar da ita amma duk da haka taki sake masa hannu yadda heart din ta ke bugawa kadai zesa ka tabbatar da tsoron daya kamata, 

  " Relax please ni babu inda zani duk kinbi kin wani firgice ke komai ma kin hada ga tsoro ga rashin kunya Koh" bata bi takan zancen ba ta mika masa dan karamin yatsan ta murya na rawa tace " promise me bazaka kuma tafiya ka barni bah" dan guntun murmushi yay ya sagale hannun nata yace " i promise you, so share hawayen ki kinji gashi har kina shirin jima kanki ciwo, kalli yadda kika koma kinyi gumi harda majina zoki duba kayan da zaki saka kije kiyi wanka" babu musu ta bishi cikin bedroom din daya tafi da kayan yanzu tanata shafe gwiwan hannun ta daya bugu tana hawaye yana aje mata kayan ya fito sedai be rufo kofan ba don yasan tsaf zata kuma masa wani haukan, numfashi kawai yake maida wa don tabbas kam baby ta bashi wahala babu abinda yake tunani se zaman ta da Omar, Omar Abuja kam ya shaki baccin sa iya sha ka har seda Azhar tayi ya farka jiki a mace sedai dukka nin abin da ya faru kamar a cikin mafarkin sane yake gani hatta zuwan da Omar kano ya masa kamar a dream yake gani seda yay arba da goran rubutun daya kawo masa ne ya soma gasgata lamarin gashi har mamaki yake yadda yaji kansa ya rage masa nauyi sauri sauri kawai yay wanka ya shirya so yake kawai su hadu da Omar kano wani sashi na zuciyan sa tunanin autar sa baby kawai yake duk ya rasa wani kalar tunani nema zeyi, kasan cewar Maya tasan mijin nata ba isashen lpy gare saba yasa koda ta leko dakin taga yana bacci ta juya bata tashe shiba taje sukayi magana da jami an ta shaida musu sun janye binciken sun rigada sun san inda Baby take ma ta dakatar da komai harda yin signing, bayan sun tafi ne ta lallaba Fanan tadan ci wani abu itama taje ta kwanta se kuma suka bar gidan itada sadiya har Omar din ya fito daga part din sa bata dawo bah mamaki yay dayaji gidan shiru ya leka maya bata nan seda ya leka Fanan ne yaga tana bacci baiwar Allah na 'yan mintuna ya kalleta cike da tausayin ta san nan ya tafi kai tsaye shima ya bar gidan zuciyan sa fal da tunanin ina Maya ta tafi, sauri sauri ya isa hotel din da Omar Kano ya shaida masa ya sauka tun shigowan sa ciki guards suka sanar masa da Omar Abuja din ya iso, kashe kayan kallon daya tasa a gaba yay ya fito guards nata binsa gaba da baya kamar jelina bayan sun gaisa ne yake ta masa godiya don yasami afuwa tun kan suje ma ga malamin shima murmushin jin dadi kawai yay masa ya shiga nashi motan suka tafi gurin malamin duka ya zayyano masa duka wasu matsaloli sa suna zaune ya kuma masa wani rubutun sedai wan nan karon yafi wancan yawa seda ya cika masa gora uku tukunna ya bashi tamkar wanda suka saba har yamma liss suna tattauna wa kan matsaloli na rayuwa kafin su masa sallama su tafi Omar Abuja yanason yi ma Omar maganar Zainab amma yana kasawa harya fahimta akwai magana a bakin sa amma ya share shi ya koma masaukin sa shi kuma ya wuce company din sa direct.

              WASHE GARI

  Tunda wuri Omar yabi jirgin safe ya koma Kano seda ya isa gida yake shaida masa yana kano kuma kada yazo ya sameshi don  suna fitowa daga cikin airport din wan nan motar ya cigaba da bibiyar su kawai Omar murmushi yay abinsa don yasan duka shirin Maya ne,seda suka gama waya da Farid tukunna ya kashe wayan nasa, baby na gefe a zaune dama tunda ta tashi take masa kuka harya gaji da mata magana ma ya share ta ko abinci taki kulawa seda ya kammala waya da Omar din ne tana kallon sa tace " waye shidin?" A takaici ya kalle ta shima yace " shine wanda yasa na kawo ki nan" dauke kanta kawai tayi ta cigaba da zubar hawaye har yanzu bata aminta da maganar saba tabama zuciyan ta karya kawai yake mata shine ya sace ta kuma yana mata karya cigaba tayi da zubar hawaye tana share wa abin tausayi ko magana ta kiyi masa almost 15 minutes ya dauke yana kallon ta wani idea ne ya fado masa kawai ya mike yaje ya kunna wani na ura dake saman TV stand ya shige bedroom duk tana kallon sa harda tabe baki kusan 'yan mintuna ne da shigan sa taji wani irin kida yana tashi ta cikin abinda ya kunna har seda ta firgita saboda yadda wakan keda duka speakers din dake ajiye gefe suke duka tana kallon inda kidan ke tashi ne yasa batasan ya fito ba sedai voice din sa taji yana bin wakar ya sawo wani wando 3qtr ga karamin riga yasa a ciki ya dora kuma necktie da rigan suit ta wajen dan jagaliya dai zam ikon Allah kawai take kallo yadda yake rawa kamar wani dan daudu na kwai kwayen mata hakan daya keyi ne ya bata dariya sosai ta shagala da kallon sa  shi kuma ganin hakan ne yasashi wucewa kitchen yana aiki yabar kofar a bude duka wani abu dayake tana kallon sa sosai ya dauka hankalin ta tana murmushi ta bishi kitchen din tana kallon sa harda harde hannayen ta a kirji tana kallon sa, yadda yake kobare wa irin na swaggers din nan ne bata dariya kuma yanata aikin dafa indomie dinsa sosai yaji dadi ganin yadda ta saki jikin ta ganin tanata leken nonstick pan din indomie dinsa sa yasa ya jawo mata hannu ya tsaida ta gaban gas din ya bata fork din dayake amfani dashi gurin juya indomie din da kansa ya mata alamun ta cigaba da luran masa yasoma kada kwai cikin bowl haba sosai dadi ya ishi baby ganin ta tana aikin abinci abinda mummy ta bata taba bari tayiba wan nan dalilin ne yasa dadi ya cikata ta maida kaimi se cakude masa indomie din take kamar tana juya Stew dariya yaso yi ya basar ganin yadda itama tasoma rawa gaban nonstick pan din ga dukkan alamu kuma bata san ma tanayi bah daya side na gas ya kunna ya soya 🍞 dinsa da kwan seda ya gama ne ya aje mata plate bayan ya kashe gas din ta kwashe musu indomie din a ciki suka fito parlour again yana wan nan tafiyan ta bokare wa yana bin wakar A Da! don tayi masa dadi sosai akasan rug ya aje plate din bread itama ta aje na indomie duka kayan hada tea din ya kawo su nan ya ajiye ya dauko ruwa me sanyi a fridge yazo ya hada mata tea din rabin cup ya kara dana sanyin ya tura mata cup din gaban ta yana wani layi yana tafa hannu babu wani damuwa baby tasoma shan tea din harta karar dashi tass san nan ta koma kan indomie din duk abinda take yi yake kamar baya kallon ta ta kuwa ci ta koshi sosai ta kora da ruwan sanyin tana gama wa ya kunna musu game yana cin nashi abincin suna buga game har mamakin ta yake ta ware kamar wadda bata da damuwa, to nidai bansan iya adadin time din da suka bataba gurin buga game din nan har ta gaji ya kuma janye ta kitchen sukayi wanke wanke duk da yaga babu abinda ta iya tafka tafka kawai take masa sedai baya nuna wa duk abinda suka bata seda suka gyara bayan sun gama ne yaje ya hada mata ruwan wanka ba musu ta shiga tanayi Farid dadi yaji sosai ganin yasoma shawo kanta cikin zuciyan sa yana cewa 

    " Yarinya indai rayuwar shagala ce yanzu kika fara ganima sena sa kin manta dasu mummy tafi tafi dai" list din abubuwan wasa babu iyaka Farid ya bawa me gadin su yaje siyo masa bayan cefa nen daya basa yayo musu da safe, gidan su kuwa karya ya dankara wa iyayen nasa ya sheda musu ay yakoma Abuja gurin Omar kafin ta fito daga wankan ne ya daura mata wani lafiyayyan lilo harda cushion yasaka tana fito wa cikin shirin ta kamar kullum ta labto uban mai ganin yadda yake kada mata lilo din ne yana mata alamu da ido akan tazo tahau takuwa daka uban tsalle taje cikin farin ciki ta haye ya soma turata tana dawowa yana maida ita dariyar ta kawai kakeji tana tashi cikin parlour din tajin dadi, 

   Shi kuwa Omar kano seda yay bacci ya huta ya kuma yin shirrin fita office ko kadan baya kaunar zaman gidan nasu saboda damuwan Ammin shi dake masa yawa ko lunch da aka gama se a warmers yasa aka saka masa ya tafi dasu seda ya fara biyawa hospital duba Ammin tashi kullum kamar jiya iyau dai babu cigaba a lamarin ta jiki ba kwari ya fito suka dauki hanyar company yana kallon motar nan na bibiyar su again ta cikin mirror kawai baki ya tabe yace 

  " Baku da aikin yine, akwai time din dana dibar muku kuma, Maya badai kina ganin ke me wayau bace so we shall see" seda ya shiga office dinsa kafin ya fara aiki ne ya kira Farid wanda sukaci wasan su suka koshi shida baby guje guje babu kalan wanda basuyi ba shikuma da biyu ya gajiyan da ita sosai suna zama ta bingire se baccin wahala ay kuwa ya ringa dariyar mugun ta daman yasan za a rina haka kiran na shigowa wayan sa ya dauki wayan seda ya kalli baby din tukunna yay picking call din kafin yace wani abune ya katse sa da cewa

  " Anjima kaje gidan ku mu hadu a can, don nan ne privacy din da zamu  muyi magana hankali a kwance" 

  " Wai nufin ka na fita nabar yarinyar nan ita kadai a gidan nan da daddare? Gaskiya baze yiwuba bazata iya zama ita kadai ba" 

" Farid wani shirme ne kake shirin gaya min haka? Meya dameni da bazata iya zamaba so what! Ashe ma lallaba ta kakeyi Koh?" 

  " Haba Omar baby yarinya cefa koka manta ne? Kuma ba itace tayi laifi nan bah, rigimam miya yace fiyeda yadda kake tsamma ni ko kadan nasan bazata bari na fito bama anjima so kayi hakuri gaskiya" cike da mamaki Omar kebin wayar tasa da kallo takaicin daya gama cikashi shine yasa shi zabga uban tsaki ya kashe wayan nashi, kusan kwana uku kenan Omar na fama da Farid amma yaki yarda yabar Baby ita kadai a yaune rana na ukun bayan yaje office dinsa yasa aka kai masa mota ta bayan company dinsa yafice ta baya yabar shashashu masu binsa gaho cikin mota ko guards daya be dauka ba shi kadai ya shiga motan me tinted ya nufi gidan....✍️

  
IN KUNCI KARO DA MISTAKE KUYI HAKURI KAINA YANA CIWO NE BANYI WANI EDITING ME KYAU BAH, INA KUMA JIN DADI DA SHARHIN KU AKAN BOOK DIN NAN ALLAH YA BARMUN KU MASOYAN BOOK DI NAH KUNATA BANI KWARIN GWIWAN CIGABA DA SUBUR BUDO MUKU IDEAS NA GODE 🤗