🧑‍🍼 RABO...❣️

23

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode twenty four 

Sukuwa suna zaune a parlour suna kallon wani Indian film aka hasko wani kyakkyawan saura yi wanda hakan yasa baby saurin mikewa Zaune cikin farin ciki tace " Wlh yana kama da guy din dana gani ran nan ya burge ni sosai cikin azabar babi ta koma kusa dashi tana sakin wani silent smile har dimples dinta na lotsa wa tace in gaya maka wani hadadden guy ne na gani ran nan a TV ya matukar burgeni over kaga idan na tuno yadda yake smile wani dadi nakeji nima har gwada wa nakeyi ina jin dadi idan na tuna shi sosai ranar da zaka dauke nima  seda nayi mafarkin sa ya goyani wlh kasan yadda yake burge ni kuwa? Kuma a ranar ban karasa ganin saba yaya ta janye ni daki saboda su mummy da suka fara fada ai naji haushi gashi ban kuma ganin saba" kura mata idanu kawai yay yana nazar tar ta harta kare zancen ta tukunna yace" to baby kenan idan na fahim ta kinason wanda kika gani a TV Koh" saurin daga masa kai tayi tana cewa " ina sonsa sosai ma" dariya kawai Farid yayi yace " kai jama a to Allah ya hadaki da wahala kuwa yanzu ta ina zaki kuma ganin sa ko shima irin wan nan fina finan yakeyi?" CIKIn tura baki gaba tace " nima ban san inda zan kuma ganin saba, bafa ba dan India bane shi amma dai yafi kama dasu wlh baka ganshiba yafi ka kyau" shiru kawai Farid ya mata jin da yay kamar an bude gate mota ta shigowa kasa kunne yay dakyau ya kara tabbatar wa cike da mamaki ya mike yaje ta window ya yaye labule yana leken wajen dai dai time din kuma Omar na fitowa cikin mota murmushi ne ya subuce wa Farid yace " uban marasa hakuri ay nasan dama bazaka hakuri ba se kazo yana ganin sa yaje suka gaisa da me gadin seda ya dawo jikin motar ya tsaya ne ya ciro waya yana shirin kira ne Farid ya juya ga Baby yace ta bashi wayan sa nan gefen ta ba musu ta dauko ta kawo masa tun kan ya gama ansa kiran Omar din ya shigo wayar daga wa yay abinsa yana shirin yin magana ne ya katse sa cikin masifa yace " can you come out and let's go?" Shirun da Farid ya masa ne yasa shi cewa "  don't Waste my time" kit ya datse kiran kawai Farid ya soma bin wayar da kallo ba zato ba tsamma ni yaji baby ta koda wani irin ihu daya sashi sakin wayar hannun sa a tsorace yana kallon ta tasoma tsalle tsalle tana tafa hannuwa " wlh shine na rantse da Allah shine!! Dama ka sanshi ashe zaka kuma yimin karya, bude min kofa naje gurin sa, wayyo yau burina ya cika zan ganshi again" sake yaye labulen Farid yay yana leken Omar yaga kodai su biyu ne bega kowaba se shikadai wanda a yanzu ya sunkuya ze dauki wayan sa da ihun baby ya daki cikin brain dinsa yazo maida wayan sam besan sanda ya sake taba shima kawai ya kurawa saitin window din daya jiyo ihun oily eyes dinsa koda ya dago daga daukar wayan nasama gurin ya kuma zuba wa Idanu, kallon ta Farid yay ya nuna Omar yace " baby kina nufin wan nan shine kike magana kin gani a TV?" Cikin farin ciki baby ta daga masa kai tana cewa" shine mana baga shican ba sedai yau baya wacan smile din" 

" Baby wan can fah!" Ya kuma nuna Omar dake tsaye yana kallon saitin su kamar wanda shima yake kallon su,. Bata fuska tayi tace shidin fah ko ban san shibane a ka gaya ma" labulen kawai ya saki ya soma sosa haba yana kallon ta cike da tausaya wa sedai kuma kome ya tuna ne wata irin dariya ta kwace masa harda kwallah kallon sa kawai take tana tura baki yaki bude mata kofa taje gurin Omar dakyar ya iya tsaida dariyar sa ya sunkuya ya dafa mata shoulder din ta cikin seriously kamar bashi yay dariya ba yanzu yace " Tom shikenan naji kinason ganin sa Kiyi masa magana?" Daga masa kai tayi yace " Tom shikenan zauna ki jirani zanje na rakashi gida in muka dawo se yazo ya tayamu hira Koh" tuni idon ta yay kwal kwal  da hawaye murya na rawa tace" please zan biku! Bakace bazaka kuma bari naba" " nasani kinga ai tunda yazo ya tsaya din nan baze tafi ba sena rakashi kada ki wani damu yanzu fa zamu dawo kinga ga TV ma kiyi ta kallon ki harmu dawo zan sashi ma ya siyo miki kaza a hanya Koh" shiru tayi kawai tana ta kallon sa ganin tana shirin karyar masa da zuciya ne yay gaba yana cewa " Haba ke kam don't embarrass me mana we will gate back soon, keda zakiyi murna ma yau zakiyi magana da masoyin ki" be jira cewar taba yay waje ya kulle kofan seda suka shiga motan ne yake cewa " Allah baka kyauta wa mutumin nan am sure kafin na dawo tayi kuka harta gajee" murmushi kawai yay yana tada mota yace " inta kwantar da hankalin ta Farid kuka ma ai bata fara shiba Waits for time " tabe baki Farid yay yace" to babu kyau dai kuntata zuciyan masoyi wlh gara ka sani tun yanzu" Omar besan time din da yasoma zabga ma Farid harara ba yana cewa " menene yake damun kane? Wani irin magana ne haka" " Zaka fahimta me nake nufi very soon" yana maganar yana masa dariya ganin ya maida shi abin tsokanar sane yasa shi kawai tada motan suka tafi direct ya wuce gidan su Farid din acan sukai lunch abinsu kamar dawowan su kenan daga Abuja seda suka gama ne suka zauna a general parlour anata shan fira dasu da Mama da Basma yayar Farid din, tana cema Omar din

   " Wai farouk a wani makarantar zaka cigaba da karatun ka? Kaga shi aminin naka kasar ze ketare daddy nata processing akan tafiyan nashi zefi kyau ma ace tare zaku tafi kada dayan ku yabar daya" farouk shine abinda Basma ke kiran sa don sunan saurayin tane yake dashi, murmushin karfin hali kawai Omar yay yace " Ayyuka na sunyi min yawa auntie Basma baze yiwu naje wani kasa karatu bah ko grandpa ma baze yadda bah in bishi kuma ga Ammi tana karkashin kulawa ta yanzu ga company a gabana, shi Farid bashi da Wani damuwa akan sa zeje duk inda yake so, burin mu kenan ada mu kare karatun mu a tare amma yanzu kinga yadda ta Allah ta kasance a kaina dole sedai nayi karatu na kusa da gida" cike da tausaya wa Mama tace 

    " Allah sarki Omar kayi gaskiya wlh kuna cikin jarabawa rayuwa kunga abu kala kala Allah dai ya tashi kafadun Ammin taka kayi hakuri kajee babu abinda yake tabbata a rayuwa in Sha Allah wata rana se labari karga ringa sawa kanka damuwa dayawa Addu'ah tafi karfin komai" 

  " ALLAH yasa Mama na gode" Omar yay maganar cikin wani yanayi hakan ne yasa Farid cewa" Nima fa hakuri zan bawa daddy my Man kada ka wani damu akan wan nan nima ba kasar da zan bari muna tare anan in dai na maida hankali zan samu ilimi me kyau harna kaiga cimma burina nazama Dr ay bawani abune na tada hankali bah" Omar yace " aikuwa tafiya ya kamaka dole don acan zakafi samun iliman tuwa me kyau kaga kafin ka dawo ne zamu ma gina maka hospital yadda zaka mori iliman ka hankali kwance koba haka ba auntie Basma?" " Gaya masa dai farouk mu ay ko sauraren mu ba yayi akan maganar yace ba inda zashi" 

  " Ki barshi ay tunda daddy yay magana sefa ya tafin zeyi ya gama ma" harara kawai Farid yake antawa Omar daman yasani shiyasa yana juyowa suka hada idanu ya kanne ido yana masa gwalo ganin kamar idanun sa ze fado ne yasa Omar din yin murmushi yace " wani kasar kakeson tafiya ne" 

  " Oho maka!"

Shine abinda kawai Farid yace masa a kufule, shi kuma yasa hannu cikin suman sa yana wasa da ita yace " ok ay ba damuwa daddy ze zaba maka kasan daya  dace dakai" kamar yay kuka Farid yace " wlh Mama babu inda nakeson zuwa ni gaskiya abarni anan tunda banason tafiyan" girgiza masa Kai kawai maman tayi tana cewa" Eyyah Auta Saidai fa kayi hakuri hukunci da Daddyn ka ya yanke kenan sedai muyita binka da Addu'ah ni kaina banida tacewa bazan so ba a rabaka da aminin ka mussam man yadda yakeda bukatar ka a yanzu" bekuma tanka waba Farid donya shaka har suka tafi ya maida shi gidan,su Mama suna tunanin gurin Omar din yake zaune, babu me cewa Wani kala har aka bude musu gate suka shiga kowa da tunanin da yakeyi mussam man Omar da daurewa kawai yay ya boye damuwan sa akan maganar tafiyan na Farid seda ya fito ne daga motan ya leka yana cema Omar din " Ya kamata kazo mushiga gidan nan koba komai kaga yarinyar" dauke kansa kawai yay dayaji abinda Farid din ke fada cikin yanayin damuwan dayake kokarin boye wane yace " me zanyi mata idan na ganta" 

  " Duk da haka dai kazo mushiga seda nayi mata alkawarin in mun dawo zaka shiga gurin ta" sosai kalaman Farid suka daure masa kai ya zuba masa mayun idanun sa ya kasa cewa kala, har seda yaga yana kokarin fito dashi cikin motar ne yasashi kwace wa yace " stop please, Farid kana bani mamaki ma idan kana min maganar waccar yarinyar ko kadan banida time koda 1 second dazan bata agurin ta Allah ya kiyaye saboda common ingan waccan banzar zan wani kama fita a motana! Koka manta ma aiki nakeyi ne na ajiye na taho gurin naka inta kwantar da hankalin ta ay zan gantan lokaci ya kusa ay badai tafiya zakayi bah zamu hadu ay haduwan da baze mata kyau ba muddin uwarta ta cigaba da shiga gonata, kaima dazaka iya da katafi ka barta a cikin gidan nan kome zatayi tayi amma naga se wani lalla bawa kakeyi da ita! Ta isane ma ni nabi takanta bare nasan me take cikima, Wlh kana bana haushi Farid akan yarinyar nan kaje kaidai kaita riritata kamar egg ni bada niba" bamm ya bame murfin motar sa yaja ya tafi a kufule ga bacin rai ga damuwa duka sun hadar masa, wan nan dalilin ne yasa Farid kasa yi masa magana har ya tafi duka halin daya shiga yagama fahimtar sa a tare da voice din sa ga idanun sa dasuka taro da ruwa yanata kyalli murya nata cracking duk time din dayaji aminin nashi na irin wan nan maganar yasan yana cikin matsanan cin hali ne ahaka yana a tsaye yay kusan 5 minutes yana tunanin san nan ya wuce ya shiga ciki tabbas yasan dole Omar baze taba jin Dadi ba idan ya tafi ya barshi shine komai nashi a yanzu ga daddy na shirin rabasu Kuma, duka nashi ranne yaji ya kara dagula haka ya shige ya tarar da baby tana bacci a kudun dune saboda tsoro ta dunkule kanta ahaka baccin ya saceta ba karamin tausayin tane ya kama shiba yarinya bataji ba bata ganiba maman ta tasaka ta a masifa....✍️