🧑‍🍼 RABO...❣️

24

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode twenty five 

  Yau ta kama ranar weekend kuma Omar Kano yay shirin zuwa shanono tunda sanyin safiya yay sammakon tafiya shida guards din sa direct ya wuce gurin su ummah da Abbah kamar daga sama se ganin sa sukayi kowa baki sake suke kallon sa shida kansa ya shimfida dadduma a rumfa ya zauna yana ta murmushi yace " ummah kunga na muku zuwan bazata Koh" itama murmushin tayi tace " shine ay nake mamakin ganin ka umaru ai nayi tunanin kana taya maman ka fushi ne da muka jika shiru" dan zaro idanu yay yana cewa " nina isa nayi fushi da kakar guda! Itama Ammi daga yau zaku dena fushin da ita in Sha ALLAH" batare da ta tanka masaba ne ta fito jiko masa gurasa don yimasa bandasho abinda yake kauna sosai indai yazo seyaci sama sama suke fira da matar ya Haseen harta dawo da gurarsa hadadda da madaran waken soya seda ta aje masane take cewa " yanzu ay na aika a kirawo baban nasu a gurin aiki yanzu zezo tunda na ambace ka" shidai smile kawai ya iyayi hankalin sa naga gurasan data aje masa yawo nata tsinkewa ya wanke hannu a dan bowl din data aje masa yasoma ci har wani lumshe idanu yakeyi matar ya Haseen tanata tsokanar sa ko magana ma ya kasa yimata ita kuwa Ummah kallon sa kawai take komi nasa irin na diyar tane Zeetah idan tanacin dadi itama haka take lumshe eyes dinta kullum tunanin halin da take ciki take ta damu matuka akan diyar tata amma kunya ya hanata tambayar jikan nata halin da Zainab din ke ciki yana cikin ci ne Yaya Haseen din ya dawo saboda yana gurin aiki aka sanar masa zuwan Omar din be juma da zama ba sega Abbah ya shigo shima da gasasshen kifi yanata kamshi aka kuwa zauna aka baje kolin sa anata fira kamar babu wani damuwa a tare dasu hakan yasa Omar mamaki sosai dayaga duka cikin su babu wanda ya tambaya ya Ammin tashi take seda ya gama take cikin sa ya koshi ne tukunna ya zaro laptop dinsa daga cikin jakar ta yana kunna tane yasoma magana 

   " Ummah nayi mamaki da baku tanbayi ya Ammi na takeba, shin tana numfashi ne kobata raye nema kotana wani hali duka baku saniba da alamu baku damuba ma, kuma abinda yake tafe dani dama kenan akan abinda ya faru duk duniya kune wanda ya kamata ace nafara wanke laifin ta a gurin ku, idan bada ban na tsaurara bin cikeba Ammi sedai ta mutu da bakin ciki to amma dayake Allah ba azzalumin bawan sabane gaskiya ta bayyana, nayi mamaki da kuka aminta Ammi zata iya aikata wan nan abun kunyar, matar Omar din dai itace babbar sheda niya data hadda sa musu wan nan masifar so kada dai na fiya muku surutu bari na bari ku gani da kanku sheda na farko ma kenan" video din salma kawai ya kunna musu ya aje suna gani kowa cike da sanyin jiki har zuwa karshen video din sosai Ummah ke hawaye don a kusan kullum tana mafarkai marasa dadi da autar tata cikin sharar kwallah tace " Allah sarki Omar sam bakayi sa ar mataba iyayen shima fama suke da ita yadda take kyama tarsu a yanzu indai bashine ya tursasa taba bata zuwa ko kadan kuma batason suje gurin sa ashe bakin halin ta harya kai haka? Allahu sarki Auta babu wanda zega video din nan be zarge kiba dole ki shiga mawuyacin hali danake mafarkin ki kullum baiwar Allah sam batada wayau Zainab har yanzu"  katse ta Omar yay da cewa " ay lamarin Ammi ma dama nazo ne ai hadin gwiwa gurin yi mata Addu'ah don tana tsakiyan mutuwa da rayuwa  Tun a washe garin da kuka zo har a yanzu danake magana Ummah Ammi tana can gadon asibiti mara barta da gawa kawai na urori da aka saka mata, babu wanda na taba furta ma wan nan maganar a cikin family seku a yanzu shi Omar masa maganar ta a yanzu bashi da amfani don tunanin tama baya iyayi bare ya tuno ko wacece ita din ma kanta Ammin a gareshi kawar ta itace duka tayi wan nan vidio din kuma a yanzu na kusa ma na gama da babin ta alkawari ne nayi duk wani mesa hannu a wan nan lamarin bazan barshi ba, kuma na hadashi da malamin daddy na in Sha ALLAH ze masa maganin duka wani asirin da Maya ta masa dakan shi zezo neman gafarar ku ummah nina gaya miki wan nan ina masa Addu'ah sosai danaga halin da yake ciki yana cikin masifa ga yarinyar sa autah danaje na samu an nemeta an rasa sun taso daga school duka seya bani tausayi, ada kam kan naji tarihin soyayya su na tsane shi tsana me tsanani, Allah ne yasan nufin sa dayasa basu kasance a tare ba tun ada kuma a yanzu nake fata su kasance tare har abada, kakana ya bata wata daya ta fito da miji ya mata aure yau kuma duka saura kwanaki kadan time din daya diba su cika kuma basu san halin da take ciki ba indai ba Abbah Esmaeel ya sanar musuba don tare muka kaita hospital din, anawa tunanin Abbah ina ganin meze hana ayi musu auren yanzu? Sam be kamata a cigaba da tauye zuciyan masoyan nan bah"  kallon da Ummah tasoma watsa masane a yanzu yasashi daka tawa da magana yana kallon ta cikin bakin ciki tace 

  " Allah ya rufa mana asiri Zainab ta auri Omar a yanzu sam kada ka kara yin wan nan maganar ma, don ba mafita bace ka dubi abinda matar sa tayi matafa yanzu tun kan ya aureta san nan kace ya aure ta, haba Omaru bazan aminta a karasa kashe min Auta ba wlh, shidai data zama kaddara a rayuwar sa dole ya cigaba da zama da ita bawan Allah tunda iyayen sa ne suka zaba masa ita, sukan su basusan haka takeba, Ina magana ta domin Allah banga ta yadda ma zan aminta Auta ta auri Omar bah" tana maganar kamar kuka ze kwace mata saboda tausayin diyar tata daya gama bi mata jiki a yanzu gyara zama Abbah yay gamida da cewa " wan nan maganar taka gaskiya ce Omar Kuma dakayi wan nan shawarar a yanzu babu wanda ya dace Zainab ta aura se Omar din tunda fari ma rabon 'ya'ya ne yasa basu rayu tare bah mun riga da ay mun gama magana da Alhj inuwan akan wan nan maganar tasu shine kawai yanzu nake jiran tsumayin zuwan sa gurin mu Omar din tom ashe ma kajee matar sa abinda tayi masa kuma Allah ya fita bata isa ta hana ikon sa faruwa bah koda kuwa zatayi yawo tsirara, bare kuma zefi kyau kada tayi jayay ya akan aure hana sunnar ma aiki babban bala i ne ga mutum rayuwar sama lalace wa take karshen mutum bayayin kyau, ki kwantar da hankalin ki juhainah Allah yana tare da mu ay" suduka suka  amsa da Allah ya tsare, yaya Haseen shima cikin damuwa sosai yace " Allah sarki Zainab naci mutum cin ki a rashin sani Allah ze saka miki don matar nan taci mutum cin ki matuka" murmushin da yafi kuka ciwo Omar yay yana cewa " ay zataga karshen ta kuwa matar nan Allah baze bar ta hakaba ko alhakin Ammi seya hanata zama lpy a duniya" 

   " Allah sarki iyayen Omar din sam basusan wani hali dan nasu yake ciki bah, washe garin da aka sace masa diyar tasa ay maman tashi har gida tazo ta gaya mana hankalin ta a tashe gashi ya hana kowa zuwa" Ummah tana maganar tana kara matsar kwallah tana cewa " ai sam bamu sanar dasu abinda Omar din yawa Zainab ba don mun yi tunanin itace batada gaskiya ashe lamarin ba haka yakeba, sam bazan yi shiru da maganar nan ba anjima senaje gidan nasu munyi magana" 

  " Gaskiya kam ya kamata kije din" Abbah ya gaya mata, sosai Omar ke farin ciki ganin yadda suka fahimta lamarin cikin sauki batare da yasha wahala ba, bayan sunyi sallah ne ta Azhar ya musu sallama ya tafi bayan ya aje musu garar azzikin daya musu, kai tsaye gidan auntie Hashmat ya wuce wadda tayi farin ciki sosai na ganin sa datai mussam gaskiya daya nuna mata ta bayyana harda sujudush shukur tayi kullum 'yar uwar tata tana cikin zuciyan ta tausayin ta ya kara kamata itama harda kuka ganin zata kuma rikita masa lissafi ne ya mata sallama ya tafi itama harda nata abin azzuka ya aje mata, tom daga nan ne ya tafi gidan su grandpa din nasa se akayi rashin sa a be sameshiba kakan nasa baya garin kuma dama besa a kaba dasu hajiya ya zauna ana dan firan har Esmaeel ya dawo aiki, koda suka gaisa da Omar din hararar sa yake be kuma tanka saba seda yaje ya kintsa ya nutsu tukunna ya kirashi suka zauna kan sofas din dake compound dinsu cikin daure fuska yake kallo sa yana cewa 

  " Naji dadin zuwan kan nan Omar da a gobe nake tunanin zuwa gidan naku, ya jikin Ammin taka kuwa? Har yanzu babu labari me dadi Koh?"  Cikin tausayi yake tambayar Omar din, shi kuwa yasan abinda ze biyo bayane cikin basar wa Omar yace " Abba Ammi har yanzu shiru munata Addu'ah ay Allah yana tare damu, Abbah na na kaina ai gashi ma na kawo kaina, kaga na hutashe ka" seda yadanyi shiru Esmaeel tukunna yace " Omar baka taba yimin karya bah wan nan dalilin ne yasa nake fatan bazaka faraba daga yau, tambayar ka  zanyi ka fadamin tsakanin ka da Allah kada kayi min karya" murmushin iya lips Omar yay don sarai ya fahimta ko ina ya dosa tun hararar sa daya farama masa daya dawo" in Sha ALLAH Abbah Esmaeel ina jinka" 

  " Omar" 
ya kira sunan sa seda ya dago yana kallon sane yace " Kaine ka sace 'yar gidan Omar na abuja koba kai bane?" Mamaki karara ne ya bayyana akan fuskan sa irin cikin shock din nan yace " 'yarsa kuma! Nikuwa meya hadani da 'yar sa! Haba Abbah Esmaeel dan kidnapping ka maida ni kuma? Wani irin tunani ne wan nan zakayi min, common saboda wani dan hatsa niya ya hadamu sena kama sace masa yarinya nayi mata me kenan! Wan nan ba hali na bane gaskiya, kaima sheda ne" seda ya gama nazar tarsa tukunna ysauke ajiyan zuciya yana cewa " Tom idan ba kai bane wanene? Inafa sane da batun zuwan ka Abuja! Babu abinda zaka layan cemin nikuwa nasan ka Omar abinda kawai zance ma shine wan nan ba dai dai bane tun da wuri ma ka maida ta gurin iyayen ta, yin hakan na iya haifar maka da matsala ba dayaba kabar ganin kudi ze maka abinda kake so" 

  " Naje Abuja akan business dina mana, kuma har gurin Omar din naje na sameshi akan maganar abinda yawa Ammi karewa har gidan sa naje kuma naga yarinyar a gidan taya yanzu kuma zaka dora min laifi meyasa ma kake tunanin zan iya aikata hakan?" Shiru kawai yay Esmaeel nadan lokaci tukunna yace" Omar yaran sa biyu ne ay mata karamar ce ake nema suna matukar kaunar yarinyar nan zasu iya yin komai akan ta rokon ka nakeyi dai har idan kasan yarinyar su tana gurin ka to ka maida musu ita ko kadan banason abinda kaima ze saka a matsala nan gaba" 

  " Abbah Esmaeel wai taya ne zan kama sace musu yarinya yazanyi da ita nema idan na dauke ta?" 

" Ay sanin halin ka danayi ne Omar zaka iya daukar fansa ta hakan kuma ina me jan hankalin ka daka fawwa lawa Allah komai" 

" Ina naga nutsuwar wani bin maganar daukar fansa sam bana cikin nutsuwa da kwanciyan hankali babban burina a yanzu be wuce naga Ammi Allah ya tashe taba ga business din nan ina ma naga lokacin dazan bata akan wasu banzaye can" 

Girgiza kai kawai Esmaeel din yay yana cewa" Allah yasa wan nan kalaman bakin naka su kasance gaskiya" cikin jin haushi yace masa ameen, hirar azzikin da basu yiba kenan ya musu sallama suka dauki hanyar Kano....✍️


KUYI HAKURI DA WAN NAN, SHIMA NA DAURE NE NAYI MUKU BANAJIN DADI 😔