3
by @mamuhgee
GANIN IDO 2026
Mamuhgee
3
Last free page
Madam meemah dake tsaye a dakin duk da bataji komai da Dr Mum ta fada a cikin wayar ba amma yanayinsa daya bayyanarda dukkanin mahimmanci da kamewa ya sakata fahimtar akwai abinda yake faruwa.
Numfashi ta sauke a natse tana takowa ta iso gabansa ta miqa hannunta daya akan fuskarsa ta dan shafa tana kallansa da kulawa tace
'Zanje na hada maka dining you should freshen up first'
Juyawa tayi ta nufi kofa ta fice tana jin itadai farin cikin dawowansa batareda ya kwana biyu ba yafi mata komai dadi dan kuwa bata taba gajiya da mijinta tana mutuwar son ace koyaushe yana tareda su iya su kadai daga ita sai yarsu da ita kadai Allah ya basu tak wadda basu taba hadata da komaiba duk da anasa bangaren yana tsananin son 'yar tasu amma bai hada iyayensa da kowa da komaiba dan kuwa akansu ne ya raba al'adarsa biyu dan bawa kowannensu cikakken haqqinsa dayake kansa.
Tana fitowa daga bangaren nasa qasa kai tsaye ta sauko ta nufi dining room ta fara duba komai taga ya zama set ta fito ta zauna a palo tana dan duba abu a wayarta hankali kwance tana jiran masu aiki su qarasa shirya dining din shima kuma ya fito.
Zaman kusan awa daya tayi bai saukoba daidai lokacin motar FAMMAH JEERAH ta shigo harabar gidan tayi parking tareda drivernta wanda yake sanye da uniforms dinsa na kaki ta bude motar ta ziro qafafunta masu danye da wasu irin wedges na original VC brown da suka zauna akan kafafuwanta dake farare tas suna bayyanarda asalin hutu da daular da aka haifeta cikinta ta taso cikinta ta girma cikinta.
Fitowa tayi gabaki daya motar tana nufowa cikin gida kai tsaye sanye da doguwar Moroccan gown datake rawa a jikinta mara dogayen hannu sosai sai iya silk scarf dake kanta rataye fuskarta sak ta mahaifinta daya haifota duniya babu abinda ta bari nasa dan kuwa babu abinda ta dauko ko daya na mahaifiyarta komai na fuskarta da kammaninta irin na mahaifinta da kakanta ne wato JEERAHs.
Qamshin tsadaddiyar turaren Rossa Ocean take fitarwa a duk inda ta wuce tana tafiya tamkar first class model dan kuwa komai nata ihun hutu class da wayewa kawai yakeyi duk da bata tara wasu shekaru masu yawan gaske ba sosai bata fi shekaru 21 ba a duniyar.
Tana shigowa babban palon taga Mum dinta a zaune tana waya ta qaraso a natse cikeda kulawa ta rankwafa tayi kissing gefen fuskanta batareda ta iya cewa komaiba sbd ganin tana waya.
Qamshin turaren mahaifinta ne yafara silalowa a natse yana shiga hancinta dan haka ta juyo a hankali cikeda mamaki ta kalli hanyar stairs dinsa datake jin amon takunsa yana bayyana.
Akansa idanuwanta suka sauka asalin kwarjininsa yana cike idanuwanta da wata irin tsananin kaunarsa da farin cikin ganinsa sbd itama duk duniya babu abinda bata gajiya dashi irin kasancewa da mahaifinta sbd koda ta taso ba wani zama yakeyi ba sbd yanayin aikinsa.
Murmushi ne ya sauko fuskarta yana mamayewa ta aje jakar hannunta tana nufarsa da sauri bata tsaya komaiba ta rungumesa ya rungumeta da kyau shima a natse tareda shafa kanta yana amsa gaisuwanta cikeda kulawa kafin ya kama hannunta suka nufi dining room wanda itama Madam Meemah ajiye wayarta tayi tana miqewa suka dunguma tare tana jinsa yana magana da Fammah din a natse da wani irin class da kulawansa da ita kanta a natse take.
Zaunawa sukai a dining fammah ta bude baki tace
'Dad thank you daka dawo yau'
Da kulawa ya dan kalleta yana karantar yanayinta na alaman karatu yafara bata wuya kenan.
Shugabar masu aikince datafi sauran matsayi tayi serving nasu abincin dan kuwa babu abinda madam din gidan take taba yi da kanta bayan kwanciya a dakin miji da sonsa sai kuma kulawa da kanta wanda kusan shima wasu abubuwan yi mata akeyi.
Fammah kuwa daman itace tamkar saurauniyar gidan sbd itace asalin 'ya kuma magajiya daya tak ga maigidan haka kuma mai sunan mahaifiyar maigidan dan haka gatanta na daban ne batama san kowane aiki ba a duniyar bayan na yiwa kanta wanka da shirya kanta sai kuma sakawa bakinta abinci sune kadai aikin data iya a gidan ubanta da rayuwarta sai karatunta kadai da shine abinda yake wahalarda ita.
Tsit sukai suna cin abinci idanuwansu cikeda kauna da kulawa da juna musamman tinda yana nan nutsuwan da farin cikin na musamman ne.
Suna gamawa kai tsaye palon hutawansa suka dunguma suka tafi banda Fammah data wuce dakinta tai wanka tai sallah ta fito sanye da straight doguwan rigar Amienies black ta nufo gurin Dad dinta ta zauna suna maganar da kusan duka ta karatunta ce.
Ya basu time dinsa sosai sukai fira dashi sosai duk da kusan komai na firan sune masu yi yana kuma jin dadi da samun nutsuwa da hakan sbd sune basa irin wannan farin cikin kadai na family sbd bai taba sanin cikakken kauna da shaquwa da kusanci tareda nutsuwan dake cikin family ba saida ya samesu a rayuwarsa dan kuwa koda ya taso ne a tsakiyar iyayensa uwa da uba da basa tare sun rabu tin yana yaro hakama kowannensu yaqinsa akan ya nuna shine mai isa da iko dashi dan haka irin wannan sanyayyar kaunar da sanyin na ahali sai akansu yasansa bayan ya gama sadaukar da kuruciyarsa a gurin aikinsa.
Abu dayane haryanzu bai taba sani da dandana nutsuwansa da farin cikinsa ba shine kaunar ahalinsa a kammale ba cikakke wanda zaace ya samu daga iyaye da iyalinsa lokaci dayaba dan kuwa abu ne da kaman bazai taba samuwaba sbd banbanci raayi da tsayuwa cak akan raayi da karfin zuciya dan kuwa haryanzu mahaifinsa da iyalinsa babu wata shaquwa da sanayya me karfi sbd yanayin rayuwarsu da kowa yake qasa daban yana rayuwarsa da kuma kafiyar raayi dayake tsakanin iyayensa dan kuwa matarsa itama daga kabilar mahaifiyarsa ta fito,kabilar da kusan basu yadda da zama da namiji da wata matar ba dan kuwa tamkar ma hakan a gurinsu baya yiyuwa sbd tsananin zafin kishi da taurin zuciyarsu tareda kafiya tareda iya yadda subar namiji har abada akan hakan dan haka ne yasa mahaifiyarsa takeda wani zafi da kafiya mai zafi akan ikonta da kabilarta.
Tareda iyalinsa yayi sallolin daren basuyi dinner ba kawai snacks suka ci shima yaci pieces biyu sbd ba cimarsa bane,
Tinda ya shige babu wanda dama zai sake ganinsa idan ba Imran ba shima sbd aikin dake gabansa yau bai samu ganin nasa ba saida safe shima sbd isar masa wasu bayanai akan schedules nasa da akai clearing ne da tafiyar dake gabansu wanda kusan komai ya kammala dan daman tafiyarsa zuwa Nigeria kowane lokaci ba matsala bace ko aiki me tsayi dan mahaifinsa dake can koyaushe a aje tafiyar take.
Washe garin matarsa tasan da maganar tafiyarsa Nigeria kai tsaye wadda ta sakata yin shiru tana jin wani irin sanyin jiki sbd tasan dole ba lafiya ba tinda Nigeria ba gurin zuwansa bane a yanzu da tin bayan daya rasa Rabin jikinsa na farko da bayan iyayensa dasu bai hadasa da komai da kowa ba,shine rashin da bazai taba mancewaba harya mutu.
Sanin matsayin mamacin a gurinsa ya saka mahaifin nasa da kansa ya yafe masa zuwa Nigeria din kwata kwata sedai su hade a wata qasar idan yaje wani abin,
Mahaifinsa na barin Nigeria ko tafiyar kwana biyu ce duk abinda yake saiya aje yaje duk qasar dayake ya samesa yagansa wanda hakan ke qara tattabarwa duniya girma da matsayn da ubansa yakeda shi a gurinsa da rayuwarsa.
Numfashi ta sauke me sanyi da sauti sbd Nigeria gurine da suke tsananin son ringa zuwa ita da 'yarta sbd son samun shiga da shaquwa da kusanci sosai da SIR JEERAH wato mahaifin mijinta wanda sukafi kowa sanin yanda yake kaunarsa fiyeda komai to tinda ya aureta take tsananin son kasancewa akwai kusanci da shaquwa tareda kauna me karfi tsakaninta da Sir jeerah din amma bata samu hakan ba dan haka a iya gurin Dr mum takeda kauna me karfi da duka kusancin datake buqata wanda ma harta ke ganin ta gama kama komai tinda ta kasance ta Dr mum.
Batace komaiba akan tafiyar kaman yanda bata tambaya dalilin yinta ba ko tambayar lafiya ita dai muradinta kawai yaje ya dawo garesu dan shine kadai abinda takeso take buqata,
Fammah dataji tafiyar tasa jin tayi tana tsananin son binsa dan kuwa tinda take so daya ta taba zuwa Nigeria din kuma ita a gurinta taji dadinta da har take marmarin sake zuwa harma da fatar ta dan zauna acan dan haka kai tsaye ta roko mahaifin nata tana son zuwa.
Da farko bai yadda ba amma yanda ta sake marairaicewa da fidda kaunarta da kaiwa mahaifinsa ziyara saiya amince musamman dayake bawai dadewa zaiyiba tafiyar kwanaki ce kadan dan haka zuwan da ita ba illa bane dan haka take akai shirin tafiyar da ita wadda ta saka Zuciyar Mum dinta damuwan kadaici da kewansu su biyun tin yanzu dan haka ta marairaicewa Fleet da narke masa gabaki daya akan kewansu da zatai.
*****Kwanaki kadan akai aka gama shirin tafiyar FLEET ADMIRAL RAHEEM JEERAH zuwa Asalin qasar mahaifinsa Nigeria wadda haqqoqa masu girman gaske da dama ke jiransa dan haka a ranar da jirginsa ya daga a ranar can Nigeria aka tanada duk wani tsaro da shirin tarbansa da zaman da zaiyi na lokacin da kuma tanadar da duk wata rayuwar da akasan itace rayuwarsa daya saba da ita.
NIGERIA
Saukar bayan Asuba jirginsu yayi dan haka ko kafin su baro airport gari yayi haske sosai mutane sun fito sosai sun fara kaida kawo,
Motocin securities biyar ne suka daukosa na alfarma sai lafiyayyar BMWi7 ce ta daukosa wadda ba kowane yake tuqata da kansaba face SAMAD JEERAH wato Qaninsa da suke uba daya,
Qaninsa da iya su kadai rak mahaifinsu ya haifa a duniyarsa,
Qaninsa da duk duniya shikuma Yayansa ne wanda yafi masa komai bayan iyayansa,
Qaninsa daya daukesa matsayin uba,dan uwa,madubi,abin koyi,wanda zai iya ajiye masa ransa gabaki daya kuma duniya tasan da hakan dan kuwa hakanne yasaka shine GODFATHER dinsa dayaxo karshen magana akan komai na rayuwarsa.
ABDULSAMAD HAKEEM JEERAH bai taba taka rawa dakowace matsayi da dukiya da komai na mahaifinsa ba sai na dan uwansa kuma godfather dinsa FLEET RAHEEM JEERAH dan hakanne ko mahaifinsa yasan duk duniyarsa babu wani mai girma da matsayin Raheem jeerah duk da tsananin girma da tsayuwar dayake da ita akansu a matsayinsa na mahaifinsu ya sheda girma da matsayin RAHEEM a gurin Samad daban ne hakama ko mahaifiyarsa ta yadda ta karbi hakan dan hakanne ta kwantar da kai ta karbi FLEET din tamkar godfather dinsu itada danta dan a yanzu suna da matsayi da power me karfin da danta ke juyawa a hannunsa cikin qasar Nigeria duka ta FLEET RAHEEM JEERAH ce dan haka suka bi Allah suka bisa duk da baimasan da wannan mutuwar dataiba akansa qaninsa kadai ya sani kuma shima yana kaunarsa kauna me karfi da tsafta dan shine kadai dan uwansa a duniya bayan rasa rabin jikinsa da yayi wanda shine dan uwanda harya mutu bazai dena radadi da kewansa ba.
Motocin a jere kai tsaye daga airport ba hanyar gida suka kama imran ne dayake cikin motar dake gaban ta Admiral din yasa aka juyata zuwa maqabarta da zasu fara kaiwa ziyara kafin isa gida dan kuwa ya gama sanin daman duk ranar da Admiral ya fara sauka Nigeria can ne zai fara isa yakai ziyara.
Samad ma daya san can din dole daman zasu fara zuwa take ya dafe bayan motar gaban suka nufi can din.
Isarsu maqabarta take securities suka tsaya waje suna bude masa hanya tareda tabbatarda tsaro daga waje dan kuwa daga shi sai imran da Samad ne suka saka kai a maqabartar bakinsa da yayi wani irin nauyi dauke da adduar ziyara idanuwansa na sauka akan daidai kabarin da suka tsaya wanda bazai taba manta gurin dayake ba take suka sauya ya sauke su akan sunan dayake kan kabarin..MUHAMMAD NASIR IBRAHIM.
Shekarun baya..........
#MAMUH
#BEST STORY
#FLEET ADMIRAL RAHEEM JEERAH
#MUHAMMAD NASIR IBRAHIM
#LOYALTY
#JEERAHs
#AGE GAP LOVE
#HOT+HOT+ROMANCE
GANIN IDO 2026
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummi