🧑‍🍼 RABO...❣️

25

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode twenty six

       BAYAN WASU KWANAKI

Baby tasoma sabawa da Farid tayi kukan ta ta gaji ta bari data ga babu maceci dole ta hakura sedai rashin kunya datake masa ita kullum cikin masa maganar su yaya take da Omar beauty dinta sunan da take kiran sa kenan yace ze kawo mata shi be kawo shiba ya mata karya kullum cikin masa mita take,shi kuma tana bashi tausayi don gurin Omar din ze maida ta  komai na tafiyan sa karatu daddy sa ya gama masa komai se tafiya New York ko kadan baya kaunar tafiyan dai saboda Omar bayason bari sa shi kadai, dukda hakan kuma Omar ke danne damuwan sa yana lallaba Farid akan tafiyan da nusar dashi amfanin ta, gidan su Farid kam duka sunyi tunanin yana zaune ne tare da Omar yana tayashi aiki da debe masa kewa saboda yawan cin idan zasu hadu gidan su Farid din ne suke haduwa suyi maganar da zasuyi da rana wan nan dalilin ne yasa iyayen sa basu taba cewa ya dawo gidaba coz sun san yadda suke da juna, saura 2 Days tafiyan Farid kuma a yau ne ya shirya  kayan ta don maida ta gurin Omar din ya tafi gida ya karasa shirin tafiyan sa dukda komai yasan an gama masa a gidan nasu, murna sosai yau baby takeyi saboda Farid ya shaida mata anjima da dare ze kaita gurin beauty,

  Zuwa yanzu Maya tazama abar tausayi tayi wani irin rama saboda tunani ya mata yawa ko bacci bata iyawa a yanzu seta sha maganin sa bacci me karfi tukunna shine zata samu tayi Fanan kam kullum taje school din su setayi kuka saboda gani take kamar zataga baby sam ta dena wal wala kullum cikin damuwa take da kuka itama Omar Abuja ya rarrashe su harya gaji ya zuba musu Idanu shima yana jinyar tashi zuciyan a Yanzu kan batun batan ta ya dena bashi mamaki sedai tsoro koda sau daya an kasa jin koda labarin diyar tasa sam baya gajiya wa dayi mata Addu'ah haka gurin malamai ma anata Addu'ah, batun zuwan sa gurin malam sam Maya batada labari daga gurin aiki can yake zarce wa yana shan rubutu iri iri da malamin ke masa kuma Alhmdlh sosai yasamu sauki, tashin hankali da Maya ke ciki ne yasa bata fahimta mijin nata ya dawo dai dai ba sedai Zainab ce har yanzu be tuna taba sedai dreams nata dayake akai akai, wan nan kenan.

     Bayan sallan ishah ne Omar Kano yana hospital gurin Ammin shi Farid ya kirashi a waya yana shaida masa sunzo gidan baya nan ina ya tafi? Batare daya tanka ba ya kashe wayan sa seda ya dauka time sosai tukunna ya fito suka nufi gidan zuciyan sa a cunkushe, baby tana kwance ta kifa ta cikin ta  kan sofa da wayar Farid a hannun ta tanata buga game ga earpiece tasaka abinta wan nan dalilin ne yasa koda Omar ya shigo cikin parlour din sam bata saniba  shi Farid TV ya kunna yana kallon news ganin yanayin da Omar ya shigo dashi ne yasa ya maida hankalin sa duka kansa cikin kulawa ya rike hand dinsa yace

  " Omar what's wrong with you?" 

Seda yaja time yana sauke ajiyan zuciya tukunna yace " Farid naje gurin Ammi ne" Ya karashe maganar kamar zeyi kuka se yanzu ya fahimta abinda yake damun sa sake rike hannun sa yay dakyau yana cewa " in Sha ALLAH bazamu sare bah Ammi zata tashi zata samu lafiya kamar da zamu cigaba da rayuwa in Sha ALLAH Addu'ah zamu cigaba dayi mata kajee am sorry please banason kana shiga damuwa haka dayawa" dayan hannun sa ya dora kan na Omar din Farid yana cewa " har se yaushe Ammi zata farka? Kewar ta yana mun yawa ina rasa yadda zanyi da life dina Farid gashi sam ban kyau ta mataba nakasa fahimtar tar ta koda kowa be aminta da itaba a time din nan ya kamata ni na fahimce ta, nima kamar kowa fita nayi daga harkan ta sam bazan taba samun nutsuwa ba har seta tashi na nemi gafarar ta!" 

   Farid ganin yadda aminin nashi ya birkice ne daya ga eyes dinsa tuni sun rikide yana daf da fara kuka yace " haba my hero ka rage damuwa nan haka kada Wani abu ya sameka, Ammi bazata iya fushi dakai bah koda ta farka sedai tayi alfahari dakai saboda ka fitar da ita daga cikin mugun kulli da aka mata hakika zatayi matukar farin ciki da saka ma albarka" 

  " Farid ka tabbatar Ammi bazatayi fushi dani bah?" Yadda yay maganar kamar karamin yaro yasa yay masa murmushi yana daga masa kai ya dauko masa ruwa me sanyi a fridge ya tsiyaya masa a cup ya bashi seda yasha sosai tukunna yaji sanyi cikin ransa tukunna yace " jibi ne tafiyan ka koh?" 

  " In Sha ALLAH wan nan dalilin ne ma yasa na kawo maka baby ay" se a yanzu ne ma Omar ya tuna daya shigo ya hange ta a kwance juya wa yay inda take yana kallo bayan ta don ta kifa a kwance gashi gown din rigan ta da kadan ya zo kasan gwiwan ta gashi gashin ta tuni ta ware 2 babies din da mummy ta tayi mata sedai tadan daure shi da soso din da ta cire karshen jelen gashin ta koma ba kallabi shiyasa Omar yaga yadda tama gashin kuma bandana kadai tasaka Sosai takaici ya kule Omar cikin haushi yace " Haba Farid wani irin shiga ne wan nan ka bari yarinyar nan tanayi haka? Kallar ta kamar diyar kafirai meyasa ma zaka siya mata irin wan nan kayan?" 

  Dafashi Farid yay yace" Haba kai kuwa my man! Kalle tafa kaga wlh she is too young dole bazan ringa matsa mataba bakomai tasani ba a rayuwar tama bare kuma world din baki daya, shawara kaima nake baka ka lallaba ta kawai ku rabu lpy don idan zaka biyewa halin ta wata rana zaka iya nakasta rayuwar ta da wan nan bakar zuciyan naka, so gara yadda muka dauke diyar su lpy mu maida ta kalau" 

" Tunda Farid yaga yana tabe masa baki daya fara magana yasan beyi na am da maganar tashi bah ilai kuwa cikin tsare gida yace " batun ni in lallaba yarinyar nan be tasoba Allah ya sauwake ni da wan nan asarar ran zuciyan" shima tabe bakin sa Farid din yay yana cewa " what ever dai ku kuka sani kome kayi mata dai dai take dakai don ba mutum ci gareta ba yarinyar nan" 

  " Fyn and good! Haka nakeso ta kasance ay dama zatayi bayani kam" kallon ta Farid din yay yaga har yanzu bata san me sukeyi bama hankalin ta naga waya kacikan murmushi yasaki yana cewa " ayna ma manta kaida kake masoyin ta ay kaine zata lallaba tasamu mazauni cikin zuciyan ka, zata yiwu kafin na dawo kunyi zurfi cikin kaunar junan ku" ay sufar da Omar yay ze damko Farid din ne yasa shi hantsila wa kasa yana dariya sosai ya mike yanufi gurin baby din shi kuwa takaici ya gama isar Omar bakaramin takaicin Farid din yake jiba uwar harara kawai yake binsa da ita be tsinke da lamarin Farid ba seda yaji maganar shi yana cewa " dalla can ga beauty dinki can yazo tun dazu kin tsaya shirme taso ku gaisa" 

  Omar besan time din daya mike ba cikin wani azabab ben sauri yay sama haka shima Farid cikin sauri ya dagota ya saita mata hanya yana cewa " maza kinga yayi fushi baki kulashi ba ya tashi maza ki bishi ki bashi hakuri" ay baby jiki har bari yake ta tafi har da gudun ta ganin Omar din datai ya kusa hayewa ya barta, dariyar mugun ta Kawai Farid yay ya maida wayan sa aljihu ya tafi yana cewa " to yau Omar taka ta sameka ka ansheni yau don haka seku karke" yanata dariya kasa kasa harya shiga motan sa yabar gidan, saura kadan baby ta kifa kan steps din Allah ya temake ta duk iya kokarin ta kuwa bata cimma Omar din ba tana karasa wa bakin kofan nashi yana banko kofar yasa key ba bata lokaci ya cire kayan sa yashige bathroom yana jin yadda take buga masa kofa yay lumei abinsa cikin bathtub din shi kansa besan time din daya bataba aciki don yanajin dadin ruwan sosai seda yaji bacci na kama idonsa ne yafito time din ya denajin bugun kofan nata shirin sa yay tsaf ya haye gado se barci, don itama baby din gajiya tayi da bugu ta silale kasa tun tana gyan gyadi har tayi flat a gun baccin ta yay nisa, 

   Sam Omar be farka da wuriba seda ana gabda tada sallan asuba ne Allah ya farkar dashi cikin sauri kawai yay brush ya dauro alwala gamida zura jallabiya ya bude kofa a hanzar ce ya fita harga Allah ya mance da wata baby se a yanzu dayaci karo da ita tasoma bashi tsoro saura kadan ya take mata ruwan ciki yay baya ya zabga uban tsaki ya tsalla keta yay gaba abinsa  ya fita masallaci dake gefen su bayan an idar ya juma yana azkar tukunna ya dawo again ya sake Ganin baby a kwance bata tashi ba ta dai takure yanzu ga sanyin asuba dana tiles sun hade mata light kawai ya kunna ya zuba mata idanu yana mata kallon Sunnah har gari yadan soma haske Omar na tsaye yana kare mata kallo ya tabe bakin sa cikin jin haushi yace " aikin banza kamar ki daya da mahaifin ki sedai sam bakiyo halin saba bakin halin uwarki duka kece kika kwashe shi" (wani karfin hali gurin Omar! Taya akayi ma yasan ya halin nata yake daze yanke hukun ci 😀 )

    Tsalla keta yay yakoma ciki abinsa yaci gaba da baccin sa hankali kwance karfe 7 da wani abu yasoma jin vibration din wayan sa cikin mayen bacci ya lalubi wayan kam ganin securities ne masu kiran nashi ne yasashi ware idanun sa akan wayan saurin daga wa yay cikin ladabi suke shaida masa ay jami an tsaro ne sukazo bincike gidan suda wata mata....✍️