🧑‍🍼 RABO...❣️

26

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode twenty seven 

Jin abinda securities din suka sheda masane yasa mamaki kamashi yana tunanin taya ma yay sakaci ya kyale masu motar nan dake bibiyar sa, ya tabbatar da sunga time din da Farid ya kawo baby ne a jiya, cikin takaici kawai Omar ya shaida musu bari ya shirya ya fito kit ya dace kiran cikin wani irin sauri ya duro akan bed din ya bude kofan abin takaici yaga har yanzu tana nan a kwance a gurin baby tana cikin bacci seji tai anyi sama da ita direct ya wuce da ita part din Daddyn sa har cikin master bedroom tukunna ya ajeta idanun ta kuru kuru kamar zasu fito saboda tsoro voice din ta kuma ya dishe da yawa saboda bacci koda tadanyi kara  muryan be fitoba cike da al ajabin abinda yakeyi yanzu take kallon sa shi kam bebi takan taba seda ya gama janye katon dressing mirror din dake manne ikin bango ya dauko wani dan mitsitsin remote ya danna tiles guda hudu dake bangon sukayi sama, mamakin ta be kare ba seda taga yayo kanta nan da nan ido kam yay rau rau da hawaye a yanzun ma kuma daukar ta yayi ya isa gun da ita, koda taga yana shirin turata cikin wan nan surkukin duhun tasoma girgiza masa Kai hawaye na ambaliya kiris take jira ta fashe da kuka heart dinta na wani irin bugu sosai, seda yaga yadda ta tsorata ne ya sunkuya ya rike mata hannun wa cikin yanayin tsorata ta dayake sonyi ne yace 

  " Kinga sojoji ne sukazo mana gidan nan kuma yanka mutane sukeyi shiyasa zan boyeki anan kada su ganki gurin babu wani zurfi sosai babu jumawa zanzo na fito dake a ciki kinji Koh! Ko kinaso nabari su yanka ki?" Saurin girgiza masa kai tayi jikin ta har tsuma yake Saboda kuma tsorata ta dayayi, cikin gamsuwa yace " good to kada kiyi ihu ko kuka su jiyoki kiyi shiru ki toshe bakin ki kada kiji tsoro babu abinda ze sameki a ciki kima rufe eyes dinki kinji Koh!"  Cikin sallama wa da maganar sa ta daga masa kai har yanzu tana hawaye, cak ya dagata yasoma zura ta ciki kanta ya soma turawa da hannayen ta seda yasa karfi gurin turata donkam neman hanyar dawowa wajen takeyi seda yazo kan West dinta ne babu zato yaji heart dinsa tayi wani harbawa saka makon idanun sa dasuka sauka kan kugun nata yaga iyayen hips malam ga mazaunai kamar na uwar mata, sosai mamaki ya kamashi ganin yadda Allah yay halitta a jikin tatsitsiyan yarinya, saurin kauda idanun sa yayi domin wan nan kam shine weakness dinsa tun farkon tasowar sa ya fahimta hakan tunkan yasan ma me ake nufi da wani feelings kuma dake miskili ne ko Farid be taba sanin wan nan bah, seda ya gama tura tane ta zauna daram acikin ma ajiyan kudin da batasan ko meye ta zauna akai bah jikin ta nawani irin mazari ne tai saurin riko masa hannuwa ganin yana shirin rufeta cikin wan nan bakin duhun yanajin yadda jikin ta ke rawa amma cikin kwalo mayun idanun sa ya dora finger dinsa kan lips din sa babu shiri ta hadiye kukan data fara don sosai idanun sa suka bata tsoro 

  " Kinason ki mutune?" 

Saurin girgiza masa Kai tayi yace " tom karki kara yimin kuka anan su jiyoki ko wani motsi me karfi suna tafiya zanzo na fito dake kinjee!" Cikin sarewa ta sakin masa hannun sa ta maida kanta ciki tana jin heart dinta kamar ze fito waje " close your eyes" yace da ita ai kuwa ruf ta kama idanun ta matse tanajin sa ya maida tiles din nan ya rufeta ya maida mirror din inda yake sedai yana dubawa yaga sahun kafan sa duk ya bayyana don dakin yadanyi kura saboda babu me zowa nan din, mayafin da aka rufe mirror din ya fisgo ya share kasan tiles din daya taka tukunna ya hau kan carpet din dake gefe a hankali yake kakkabe dan mayafin harya kai bakin kofa ya sake goge sahun kafan sa na gun ya dan kakkabe abin cikin hanzari ya maida kofan yasa wa key again yana tafe yana goge sahun kafan sa harya kare sauka a steps seda yaje ya wulla abin cikin store tukunna ya wuce daki ruwa yasa yadan wan wanke jikin sa ya fito ya zura jallabiya ya sauka kasan hannun sa dauke da wayan sa seda ya duba su Lisa dake aiki a kitchen ya musu bayanin abinda ke faruwa ya fice, kamar yadda yake tsamma nin kuwa jami ay ne da Maya fuskan nan tata babu alamun rahama basar wa yay abinsa ya karasa garesu suka shaida masa binciken yarinyar Maya sukazo yi cikin gidan nasa saboda shedun da suka samu mamaki sosai akan fuskan Omar ya kalli Maya din yana cewa 

" Yarinyar ki a gidana?" 

Tsaki maya tayi cikin masa kaskan taccen kallo tace " bakada wayau yaro! Sam bakasan 'yar Maya ka sataba naga alama, to ayau Allah ya toni asirin ku kaida uwar taka! Wani abu kuma ya sami yarinya ta Wlh bazan taba yardaba!" 

  Murmushi kawai Omar yay yabawa securities umar nin su bude musu ko ina a gidan suyi binci kensu harda sawa a kawo musu kujeru shida Maya cikin kallo me ma ana yace Mrs Omar ki zauna koh kafin a fito miki da 'yar taki"   "kana jin tsoro ne? Ko kuma harka karaya ne?" Jinjina mata kai Omar yay yana cewa " maybe tsoro ne gaskiya ya kamani don seriously ke abar tsoro ce kuma me cutar wa kinfi shedan hatsari! Tunda ga makircin da kika shirya wa mahaifiya ta nasan hakan Kinga kuwa dole mutum yaji tsoron ki ya ringa neman tsarin Allah daga makircin ki" 

Se a yanzu tasamu yin murmushi taja kujeran ta zauna tana cewa " duk da haka ka dauka abinda nayi ba komai bane in dai akan mijina ne, haka zalika duk wan da ya taba min auta bana yafiya so kaga akwai sauran aiki kenan a gaban ku seku kiyaye koda wasa kada ku kara shiga gonata da iyali na, mijina nane kuwa har indai uwarka bata bar bibiyar min shiba" shiru tadanyi ta sukuyo kusa dashi tana me harde hannayen ta takuma cewa " ay kasan me ake nufi da gardawa Koh? To irin su sunfi mutum goma zansa sumata cinda seta tashi a matsayin mace ta koma bara gurbi tazama yawa bakin rijiya kuma dukan su masu dauke da nau ikan ciwo iri iri so kaga daga nan se mutuwa kawai don bazata kara moruwaba a duniya" ganin yadda ya rintse eyes dinsa saboda bacin rai sosai jijiyoyin kansa suka soma fitowa murmushin mugun ta tasaki tana cewa " ina gaya maka hakane don kasan tabbas nidin fa abar tsoron ce kuma ba kanwar lasaba har idan kana gudun faruwar hakan  to kajama uwarka kunne" sosai heart din sa ke tiririn azaba amma yay kokarin ya danne ya bude jajayen eyes dinsa yana kallon ta yace 

  " Hakan yayi indai kin samu dama to kiyi abinda yafi hakama, so amma ki sani yarinyar ki bakida masaniyar suwaye zasu fara lalata da ita ko rayuwar karnuka setafi ta 'yarki tsafta kisa ido kiyi kallo Maya sam a yanzu tashin hankali baki shiga irin wanda nake soba shiyasa kika samu damar yin kuka ma zan tabbatar miki da family din Alhj inuwa ba tsaran kibane cikin nidake za aga me nasara" 

  Murmushi me sauti Maya tayi kana tace " a ina kenan zaka kuma ganin 'yar tawa? Ay anyi nafarko anyi na karshe so wani fiffikan iska ma ka denashi" kallon bakida wayau ya mata yace " Mrs Omar kina bani tausayi ne tun yanzu agaba bansan ya life din ze kasance bah" 

  " Tabbas anan gaba zamu ga waye ze koma Abin tausayi" tace dashi shi kuma yace.

" Kece zaki gani ay koma waye ke dakan ki zaki sheda" 

  " Dama zan gani mana yadda uwar ka zata cigaba da wulakanta anan gaba" 

Cikin shafa haban sa dayakeyi ne yace " Maya zefi miki kyau kada ki kuma zagin mahaifiya ta" 

" Idan na kumafa! Uwarme zaka isa ka yimin?" 

" Ay ban hanaki ba ki kuma zagin ta abin akanki ze kare" 

Cikin jin haushi tace " kai yanzu har wani tutiya kakeyi da wacar shasha Shan uwar taka" mugun kallon da yake watsa mata ne yasata saurin dauke kanta cikin wani kalan voice yace " hakika kinyi kuskure Maya! Zan kuma tabbatar miki da kinyin  banida time din dazan kuma batawa a tare dake sedai kiga abinda zeje ya dawo miki" mikewa kawai yay daga inda take ya nufi gurin da yaga wani daga cikin securities din nasu yayo kanshi ya sanar masa akwai part din daya rage ba a budeba, bangaren daddyn sa kenan, ba musu kam yaje har ciki ya bude musu kofan yana fitowa yaga Maya ta shigo itama yay kamar be ganta ba ciki da waje seda aka duba gidan nan ko ina gurin 'yan aiki ne ban garen baki ne ko ina hadda gurin securities din seda aka duba babu wani alamu daya nuna masu baby na cikin gidan nan ganin babu alamun nasara ne yasa Maya ta birkice musu cikin rudu tana cewa 

  " Ku nemo uwar tashi ai ban ganta ba duk inda take tana tare da yarinya ta an tabbatar min da jiya an kawo ta cikin gidan nan" sam batasan time din da ta isa gaban Omar ba tashaki jallabiyan sa cikin fitan hankali take cewa " Wlh baka isaba seka fito min da 'yata kaida uwarka kune kuka sace min ita" 

  " Dakata hajiya ki nutsu kada kuma ki kumayi abinda zesaki a matsala" saurin sakin sa Maya tayi tana huci koda suka tambaye shi inda Ammin takene ya ciro waya yana me sanbada ma Dr din Ammin tashi waya sam barka yana office dinsa baya aiki shiyasa Koda yaga kiran nasa vidio call ya daga bakin Maya sororo take bin wayar da kallo harsu ka gama magana da Dr din ya nufi dakin da Ammin tashi take kwance ya aje wayan a saitin face din ta seda ya bama jami an wayan ne suna kallo ya kora musu halin da Ammin tashi take ciki koda basu yadda bama yace zemusu jagora har hospital din donsu tabbatar....✍️