28
by @nanabmb
🧑🍼RABO!!❣️
*NA*
NANA BMB
Episode twenty nine
Tana zubar hawaye har suka karasa wani babban super market gashin ta yashiga maida wa cikin hulan daya dora saboda duka ya fito sosai gashi yayi dauda kan nata ya gyara zaman hulan tukunna ya gyara mata zaman rigar suit din guards din sa kuwa wasu sun tsaya bakin kofan shiga ciki wasu kuma gaban motocin su suna jiran isowan motan nan, ba kunya kam suma suka karaso zasuyi parking bodyguards din sukai kan motan wan nan dalilin ne yasa suka ja motan a mutukar sukane har tana wani kara suna tada kura suka hau kan titi a dari da hansin still kuma suka cigaba da tsaiwa anan, Omar na Ganin an war taka motan ya fito ta site din da motan Farid take kusa da tashi sedai tayi dan gaba kadan motan, kasance war sun gama tsara Komai a bude motan take ko rufe murfin beyi ba sayashi yayi, sam babu kowa gurin kuma parking da sukai basuyi wajan da CC TV camera zata dauke suba suna gefen ta Sosai gurin sedan tsallin motocin da akazo siyayya cikin super market din, kuma motan guards din sun dan masa covering batare da bata time bah ya na ciro ta cikin motan sa ya tura cikin motan Farid din zuciyan ta na kara bugawa seda ya gama turata sit din bayan tanaji tana gani ya maida kofan ya datse, sauri sauri ya shiga cikin super market din yadan dauki abinda ba a rasa ba mussam man juice suyafi dauka don nan yafi kauri shi yana musu payment ya fito suka tafi baby nata buga glass din motan tana sanyin ihu bazata iyaba don ko motsa bakin ta tayi zafi yake mata tana bugawa kozasu jiyo ta suzo su fiddo t, don ta matukar rudewa ganin su Omar sun tafi sun barta sam bata kula da dayan motan guards din dake bayan taba sunata gadin gurin Kuma suna son rabawa nacikin motan nan masu binsu hankali,se bayan tafiyan su da dan mintuna ne Farid ya fito cikin super market din niki Niki da ledoji seda ya ajesu a front sit tukunna ya zaga ya shiga ban garen driver seda ya kunna light ya kare mata kallo jikin sa ya kara yin sanyi kalau tausayin ta na kara kamashi mussam man irin kallon da take binsa dashi a yanzu duk se yakejin babu dadi har suka karasa gidan babu wanda ya iya furtawa wani kala, ita baby maganar ne bazata iya yin ta ta sauki ba saboda azabar da takeji cikin bakin ta ta konu Sosai da tea din nan hawaye ne dai kam sunki tsayawa har suka shiga cikin gidan suka zauna a parlour yana aje kayan hannun sa dama jira yake su shigo cikin gidan ya tambaye ta, yana shirin zamane yake cewa
" Baby meya sameki ne haka? Ko magana bakyay"
Hawayen tane ya karu sosai taji bazata iya jurewa ta fashe da kukan da muryan tama baya fita sosai duk da tanaji a jikin ta bude bakin da take amma takasa dena yin kukan se a time din yasami ganin yadda bakin ta yayi jajir cikin yanayin kaduwa ya karaso gareta ya mika hannu ze dafe kanta ne yag bakin dakyau ta make masa hannun ta juya masa baya ma, kyale ta yayi ya bude kofa ya fita ya debo goran ruwa a ciki boot din motan sa yaje yasaka mata daya cikin freezer minti kalilan ya ciro shi yanata tururin sanyi ya bata sam bata yi masa musuba ta amsa ruwan ta kwan kwade tana ta jan ajiyan zuciya seda tadanyi relaxing tukunna cikin kallon ta dayake yi yace
" Kinajin yunwa?"
Saurin daga masa kai tayi, cikin ledojin daya shigo dasu ne ya bude ya dauko mata kayan snacks ya aje mata ya kuma saka mata lemu a freezer don yayi sanyi, duk cikin kayan 🍰 ne kawai ta iyaci saboda zafin da bakin ke mata, se lemun me sanyi ta kora dashi yana zaune kallon ta kawai yake ta cire rigar sama ta suit din tai wurgi da ita haka hulan da takalman kafan ta duka tai cilli dasu ta kuma komawa ta kwanta kan cushion ta cigaba da kuka duk da muryan baya fita sosai yanajin yadda take kiran su mummyn ta har baccin wahala yay gaba da ita, cike da tausaya wa yace
" Haba ay gara ma dazaki bar kasar nan kyafi samun nutsuwa don muddin kina nan a gaba ban san wani irin mugun ta kuma Omar ze miki bah, gara kiyi nisa dashi ina gani bazan bari a illata rayuwar yarinyar da batada hakki akan komai"
Gobe alhamis ta kuma kama ranar tafiyan su New York komai na tafiyan baby an gama matashi cikin kan kanin lokaci, a yaudinne kuma Farid ya cala Abuja don ya dauki aniyar seya dasa fadan sa cikin zuciyan Fanan zebar kasar, da Azhar jirgin su ya isa Abuja wanda ko Omar besan ya tafi bah shida Madam Farida kadai sukai maganar su, yadau wanka iya wanka Farid yay matukar kyau cikin wani dakakken shadda daketa kyalli maroon color yanata zuba uban kamshi koda ya isa gidan knocking yay gate man ya bude masa bayan sun gaisa ne ya shaida masa yaje ya masa iso gurin matar gidan a gaya mata kanin Farida ne yazo, babu bata lokaci me gadi yaje ya sanar ma Maya cikin zagwadi tace ashigo dashi ciki, murmushin samun nasara Farid yake tayi harya shiga cikin main parlour din gidan yay arba da Maya din dakyar ya iya rike dariyar sa ganin yadda ta koma din kana ganin ta kasan bata cikin nutsuwa idanu sun kumbure fuska tai jajir, bata sauke idanun ta akan saba har seda ya rusuna yana gaishe ta, cikin dan sakin fuskan da ta mance rabon ta dashi ta amsa gaisuwa tana tambayar sa meke faruwa da aminiyar tata Farida ne, tom cikin damuwa Farid yadan yi shiru kamar gaske ya soma cewa
" Farida elder sister di nace kuma zaman aure ya kawo ta nan a maganar da mukayi da ita tace makociyan tace ke, maman baby Koh"
" Tabbas nice makociyan ta kuma aminiya ta kamar 'yar uwata na dauke ta nima" Maya tana masa maganar cikin zakuwa da sonjin meke faruwa ne da Farida haka,
" Tom dama ta turo ni gurin kine na shaida miki, abinda yasa ta tafi kwatsam bata miki salla maba, ta tafi cikin dare nema saboda rashin jituwa da suke samu da mijin nata ya saketa abun dai babu dadin ji don ba rabuwan dadi akayi ba, tana koma wa gida kuma ta kwanta ciwo saka makon kuncin da mijin nata yasata a ciki ko magana ma bata iyayi a halin yanzu saboda paralyzed dake shirin ma jikin ta lahani bakin na shirin shanye wa shima, wan nan dalilin ne yasa muka kaita can kasan waje New York acan take jinya yanzu kuma canne nake karatu na tom nasami hutu nema zanzo ganin iyayen mu ta rokeni alfarmar nazo na gaya miki halin da take ciki ki sakata a Addu'ah, ban sami zuwan miki dai da wuri bah don gobe in Sha ALLAH zan dauki hanya komawa"
Tunda Farid ya fara magana Maya ke jimami da salati tana sharar kwallah seda yay shiru ne tace " Allah sarki 'yar uwa ashe kema kina cikin jarabawa rayuwa Allah ubangiji ya baki LPY Farida yasa miki dan gana ya tashi kafadun ki, hakika mijin ki ya cika azzalumi kuma in Sha ALLAH baze gama da duniya LPY bah, zan ta tayata da Addu'ah Farid Allah ya sauwake kajee! Nima ka sanar da ita tashin hankalin dakazo ka riskeni a ciki yau sati nawa kenan an nemi autata baby an rasa daga zuwa school har yanzu babu ita ba labarin ta!"
Ta karashe maganar kamar zata fashe masa da kuka cikin kaduwa shima yake yo Addu'ah da sallallami tashin hankali kiri kiri a fuskan sa kamar gaske 😂 ( gaskiya Farid dan Air ne yagama rainawa maya hankali) cikin kaduwa yace " kuma ba a hada dayi mata Addu'ah cikin masalla taiba da malamai don na san jami ay suna kokarin su akai Koh? Gaskiya kuna cikin tashin hankali kuma Allah ya baiyyana ta"
Cikin sarewa da lamarin tace " Farid lamarin baby a yanzu tsoro yake bani, duk sati se anyi sauka da sadaka Addu'ah babu irin wadda bamuyi bah amma shiru kullum tunani nake baby tana cikin wani hali ne? Ga 'yar uwar tacan tana cikin wani yanayin da ciwo ze iya kamata itama"
Tunda ta fara maganar a zuci Farid ke cewa " hakkin Ammi ne zesa kome kukayi baby bazata dawoba a yanzu" tom maganar ta ta karshe ce ta dakeshi datayi masa zancen abar kaunar sa har cikin zuciyan sa seda yaji mugun ba dadi da tausayin ta cikin nuna damuwa yace " Allah sarki ashe tanada sister ma baby din dole ne zata shiga wani hali, but hakuri zatayi babu irin jarabawar da bawa baya shiga a rayuwar sa kuma a gaba komai yazo ya wuce, kuyi ta hakuri in Sha ALLAH zata bayyana Addu'ah ta amsu dayar Allah sedai ajira time ta daure ta kara hakuri taita mata Addu'ah kada ta gaji"
" Doguwan ajiyan zuciya Maya ta sauke cikin damuwa tace " Fanan tana cikin matsanan ciyan damuwan dake daga min hankali sam batacin abinci ma sedai tea kullum cikin kuka nayi rarrashin harna gaji nabar ta sam batajin magana"
" Eyyah dole ne yanzu se an mata uzuri sun taso tare lokaci daya kuma ace babu dayan su ay dole akwai damuwa, idan babu damuwa kiyi min magana da ita don Allah"
" Cikin jin dadin yadda yake tausaya musu maya tace " meze hana bari nasa a kira ta mana" idanun sa ya maida kan abubuwan da aka aje masa na abinci da abin sha yanajin ta kira me aikin su aikata dakin su Fanan din ta kirata, shiru dakin yay nadan lokaci tukunna yace " wai baby din shekarar ta nawa ne Kam?" Cikin jimami maya tace " Hmmmm! Duka fa 12years take se a yanzu ne ta shiga na 13 sam batada wani wayau"
" Ashsha!! Ashe ma yarinya ce, Baby din baiwar Allah ya tsera tar da ita aduk inda take ya dawo mana da ita LPY"
" Ameen ya Allah, shiyasa hankali nah a matukar tashe yake baby yarinya ce babu wuyan an mata wayau" sam hankalin Farid yabar gunta Fanan kawai yasa wa idanu tana tafiyan ta cikin nutsuwar ta me abin burgewa kan ta a sunkuye ta karasa kusa da mummyn tata ta zauna, tom gurin zaman ne Idanun ta ya sauka kan Farid dake mata wani irin narkakken kallo ba karamin bugawa heart dinta tayiba tai maza ta janye nata idanun cikin wani yanayi ta gaishe shi be iya amsawa ba saboda ajiyan zuciya daya sauke dayaji muryan ta ya daki kunnen sa har yana lumshe eyes dinsa batare da ya amsa gaisuwa ba yace
" Fanan kinasa damuwa aranki dayawa Ko! Kalli face din ki yadda ta koma, kinci abinci kuwa?" Jikin Fanan a sanyaye zuciyan ta fal da tunanin waye wan nan, kanta a sunkuye ta girgiza masa kai,
" Sauko plz kici abinci banason damuwa yana hanaki cin abinci Kuma, kinason samu a damuwa bayan na sister din ki kada ki kara zama da yunwa da Allah kada ki jama ma kanki ciwon yunwa Addu'ah zaki tama sister din taki har Allah ya baiyyana ta ki dena kukan tunda kinga kina kara dagama mummy ki hankali kinjee!"
Cikin sigar rarrashi yake mata magana sedai ya makaro tuni hawaye ya cigaba da wanke mata fuska jan hancin data farane yasa ya gane ta cugaba da kukan kai tsaye ya mike zuwa inda take ga Maya a gefe tana kallon ikon Allah....✍️