29
by @nanabmb
🧑🍼RABO!!❣️
*NA*
NANA BMB
Episode thirty
Ahankali ta dago idanuwansu suka kara sarqewa cikinnna juna wannan karan nawal takasa samun daman janye idanuwanta don sakon da yake turamata da Ido tasoma amsarsa gyaran murya da Maya tayine yasa shi kasada kanshi,ya juya ga tray da aka aje masa gefenshi yadauki plate yazuba shinkafar da tasha kayan lambu,sannan yabude miyar tasha hanta sai zuba kamshi take ya hada mata abincin yasa spoon ya kuma ajeshi gefen datake zaune yace " Fanan sauko kici kinji!" suduka kallon sa suke da mamaki don sam Farid be bari kansa ya kulle bah kiri kiri yake nuna zallan kaunar sa gaban maya wanda face din sa kadai zaka kallah ta shaida maka hakan,dagowa Fanan tayi tana kallon momyn ta alamu tayi mata na tasauka mana,asanyaye tasauko tadau spoon din tasoma tsakurar abincin ahankali, zaman dirshan Farid yayi yana kallonta sonta yana kara mamaye masa ruhi tuni Maya ta gama ankare inda ya nufa shiya sama tatashi tanufi daki hakan kuwa yayiwa Farid dadi anan yasamu damar aiwatar da abindake zuciyanshi,gaba daya Farid ya da baibaye fanan da kalamansa masu wuyar fassaruwa kalmansa suna sata awani yanayi wanda yasa takasacin abincin nata saijuya spoon dintake kantana duke takasa amsa maganarsa don batasanma waca amsace tadace tafa daba,karantarta Farid kawai yake yanajinshi cikin wani irin shauki da annushuwa ita kuna sam takasa koda kwakwaran motsi eyes dinsa kawai takejin na yawo a jikin ta heart din ta na tsanan ta bugawa don hatta hannun data rike spoon 🥄 din yana kakkar wa duk yabi ya rikita baiwar Allah lamarin nasa yazo mata a bazata a time din da bata taba koda tunani bah, ganin halin da tashiga ne yasa shi ansar spoon din gurin gogar hannayensu Farid har lumshe idanunsa yayi abincin ya debo yakai bakinta amma kunya ta hanata amsa sai murmushi da take kokarin yi masa saboda shakiyancin da Farid yake mata shikuwa murmushin tane yake kara nutsardashi a kogin sonta shagwaba yaketa zuba mata kamar zaiyi kuka akan saita amshi abinci har yanzun taki amsar abincin spoon ya ajiye yadora hannuwa biyu aka kamar me shirin yin kuka hakan yasa batasan time din datayi murmushi me sauti ba tadau spoon din tanacin abincin shikuwa Farid dadine yakamashi sosai taci abincin kadan tarage sannan takalleshi tace " Barina zuba maka abincin kaima" daga mata kai yayi yana kasheta da murmushi wani plate din tadauka zata zuba masa yace" A'ah zubamin anaki plate din" batai musuba tazuba masa abincin,ta ajiye agabanshi kallonta yayi yace " wato wayau kikamin kikaki amsar abincin saboda kada nace nima kibani Koh tana murmushi tana girgiza masa kai kada kai yayi yace to aishikenan yazanyi yanzun nan gaba dai in mukai aure ko ruwa ke zaki bani insha bare abinci" hannu biyu nawal tasa tarufe fuskarta,baki yabude yace lailai su kunya manya daga wannan maganar har anji kunya ashe inada aiki nan gaba amma bakomai kiyi kunyarki ai dama adon kuce" yanacin abincin yana kara janta da hira har tadan sake dashi dukda tanacikin damuwa amma Farid yasata rage damuwa sunadan hira cikin dabara yasata karanto masa number din mommyn tasu yakuma mata alkawarin gobe dasun sauka zai kirata, Maya bata kuma fitowa parlour ba har saida Fanan tahaura saman taje tasanar mata zai tafi sannan tafito hannun ta rikeda leda babba tabashi tace yakaiwa Farida ansa yayi cikin girmama wa yay mata sallama har ya tafi yadawo yace " mummyn mu zandinga kira kullum inaji in fanan takarya alkawari tace kullum zataringa cin abincin duk randa nakira akace daman bakiciba to nida kene" yacca yay maganarne yasa Fanan yin murmushi ita kuwa Maya dadi taji harcikin ranta ta tabbatar da nufin Farid yanzun akan Fanan takumaji dadin hakan saboda taji Farid din ya kwanta mata arai gashi kuma dan kwalisa san kowa kin wanda ya rasa ga wayewa katse tunanin da takeyi tayi tace " To shikenan duk randa bataci bama zan zane maka ita" kwalalo ido Farid yayi sannan yace a'ah mummyn mu banda duka ayi hakuri ai zamata dingaci ko my fanan" itadai tana murmushi ta daga masa kai," yawwa to zoki dan takamin koh" kallon momyn nata tayi alamun tana neman izini aikuwa ta kada mata kai, jiki ba kwari tabi bayansa Fanan suna tafe yana mata hira har suka fito wajan gate, Maya dakinta takoma tana lekensu ta window tana murmushi dadine yakamata ganin yar tata tana dariya jinjina Kai tayi tace " lallai Farid kaciri tuta ji yacca yar nan take dariya rabona dana ganta haka tun ana gobe baby zata bata in wannan abun yadore Fanan kin samu miji wayayye kamar yadda nake miki Addu'ah a kullum kuma ga nera zaki huta yar nan Allah dai tabbatar da alkhairi" (taf nikuwa nace digimi dagani sarkin fawa se miya tai zaki) tana kallonsu har sukai sallama yau Farid jiyake kamar anmai bushara da gidan aljannah harya isa kano yana zuba murmushi koda ya isa gidan tararwa yayi baby na bacci kura mata Ido yayi yana kallonta yace " Allah sarki autar mommy sunaji dake musamman sister dinki tana matukar sonk" wucewa yayi ya shiga toilet yay wanka da alwala yafito yana zura kaya ya fice masallaci dawowarshi babu jimawa baby ta tashi tasoma kalle kalle tasoma kallonshi murmushi yamata gami da daga gira yace
"lafiya?"
" kanshin mommy nakeji adakinnan"
Ai Farid cikin sane yabada wata kara kuuuu!!! Jin furucin autar mommy "Allah kamshinta nakeji adakinnan tana Ina?" idonshi ne yasauka akan ledar kayan daya ajiye kan kujera wacca Maya tabada akawowa farida saurin mikewa yayi yace " kawaidai hancin kine yake Miki gizo" ledar ya dauka yashige daki da ita ita kuwa tarakashi da kallo sosai ranar tabirkice masa dakyar da sidin goshi tayi bacci ga haushin Omar datakeji shikuwa Farid ga kira anata kiranshi agida akan yadawo gida ya kwana tunda gobene tafiyarshi amma dole yay musu karyar cewa Omar ne bayajin dadi dole shizai zauna dashi ,kwana Farid yayi yana tunanin masoyiyar sa ta bangaren tama Fanan haka take tunanin Farid yahanata sakat don bata taba ganin simple man irin saba me bar kwanci, Omar burinshi yanzu baiwuce yaga su Farid sunbar kasarba shiyasa ya kasa zaune yakasa tsaye komai ya kammala wa Baby na tafiya a cikin sirri.
WASHE GARI
tunda wuri Farid yatashi ya karasa hada mata kayanta tsaf ajaka na tafiya tanata bacci ma har ya hada mata break fast yay wanka sannan yatasheta yana parlour har tai wankan tashirya cikin kayan daya fito mata dashi saida tafara yin break fast din sannan ya fita,kai tsaye gidansu ya wuce karfe daya jirginsu zai tashi gidan sai soye soye ake yimasa auntie Basma yayarsa ta tasashi agaba sai surutu take masa tana zolayarsa Mommy dinsace tace "Farid jikin omar yayi tsanani baze iya rakaka airport bah?"
" No mommy ay munyi sallama tun dare yasamu bacci ne shiyasa ban tashe shiba tunda yay kwanan ciwo jiya kinga" Addu'ah mummy sukai ma Omar din yana amsawa cikin zuciyan sa yana cewa " yaushe kuwa zakuga Omar ay komin rintsi baze zoba saboda tsaro" karfe 12 ya sulale yabar gidan ya koma gurin baby tana kallon sa harya gama hada kayan ta cikin boot ya dawo cikin gidan cikin lallami yace taho mu tafi baby Koh! In Sha ALLAH daga yau zaki masa nisa baze kara ganin kiba nan kusa bare ya miki mugun ta" sam baby jiya duk irin bayanin daya mata kasar dazasu je jinshi kawai tai don bata yadda bah a makarya ci ta dauke shi se a yanzu mamakin sa ke kara kamata batare datayi masa musuba ta bishi bayan ya kashe komai na electric tukunna ya rufe gidan yakaima gate man key din suka tafi se a waya ya shaida ma mutan gidan su ya wuce airport su sameshi acan da kayan nasa time ya kure baze iya dawowa gidan bah, time din da suka isa airport ya zaunar da ita gurin da ake musu screening yana kara lallamin ta akan cewa yanzu zasu shiga cikin jirgi wata inya murace gefen su taga yadda yake ta fama da baby taki yadda ya fita gurin 'yan gidan su guduwa zeyi ya barta harta soma zubar hawaye cike da mamaki take tambayar Farid meke faruwa da sister din tashine ganin color din skin din tasu kusan iri daya tayi tunanin yayan tane cikin iya siyasa yake mata bayanin bata taba shiga cikin jirgi bane shiyasa takejin tsoro Kuma ga sako zeje ya amso gurin abokin sa tace seta bishi, murmushi kawai tayi ta dawo kusa da Baby din tajata a jiki tana lallami da bata bakin tabari yaje mana ya dawo kamar yadda baby ke tsoro haka shima yake jin tsoron kada ta tona masa asiri baby, cikin sauri yaje gurin su mummy din suna dan masa nasihohi da Addu'ah Basma harda kuka na kewan sa dazasu yi daddy ne yake dan rarrashin ta shima Farid duka jikin sa yay sanyi ya dauki kayan sa ya koma ciki,
Me karatu zakaci dariya time din da jirgi yazo tashi kuka wur jan jan Baby se kallon su ake ana musu dariya ahaka suka lula aka soma keta hazo Omar na gida ya tura daya daga cikin guards din sa suka gane masa tafiyan su Farid din koda ya kira ya shaida masa tafiyan nasu murmushi mugun ta ya dinga Omar yana kara tsara yadda ze muzguna wa Maya sam bashida wani fargaba yanzu se fatan su sauka New York lpy kawai, wasai yake jinsa yay wanka ya nufi hospital gurin Ammi,yana shiga kamar kullum tana nan a kwance na urori sunata mata aiki gefe ya zauna yana kallon ta cike da tausaya wa ya rike hannun ta kamar zeyi kuka yace " Ammi ya kamata ki tashi please ki tausaya wa dan lelen naki! Yanzu banida abokin hira Farid ya tafi Ammi ina cikin matsanan cin kewarki ks se kadaici ya dameni, kince bazaki yi nisa daniba Ammi meyasa bazaki tashiba sam rayuwa ta babu dadi a yanzu" hawayen daya farane yasa shi kai hannun ta kan hawayen ya share yana cigaba da cewa " kinji fah Ammi hawaye nakeyi Sam bakyason ganin kuka nah ki tashi ki rarrasheni, nariga na fara daukar miki fansa Ammi an zalunce ki an bata ki har abada bazamu taba dena yiwa Maya Allah ya isaba don tariga ta gama cutarmu sedai Allah ya saka mana" hawaye sosai yake da jan hanci tunowa da abubuwan da akawa Ammin tashi sam besan iya adadin time din daya diba ba a gunta seda ya mata Addu'ah sosai tukunna ya bar hospital din direct suka nufi gidan kanwar daddy sa Eshaal takuwa yi matukar mamakin ganin sa don kowa yasan dama tasu batazo dayaba tunda ya taso yaga yadda take mu Amala da Ammin shi baya sonta baya son zuwa inda take hakan ne yasa a yanzu ma se tsalli tsalli suke dan magana TV kawai yasawa idanu sam Eshaal ta kasa tambayar sa Ammi sa kota zageta gaban sa saboda kwarjini daya mata, shikuw yazone koze dan sami saukin damuwan dayake ciki be gaya mata halin da Ammi ke cikiba don yasan itama ba kaunar ta takeba, yana gidan har yaranta suka dawo daga skull, Batool da Batina sauri sauri sukayo wanka akaci ado aka fito don taya dan uwan nasu fira duk da sun san bame yawan magana bane sedai inda shakikan sa, to amma dake tamkar parrot suke babu laifi ya saki jiki dasu sunyi matukar jin dadi don se dare yabar gidan duk dan kada ya koma gida kadaici ya dame shi koda ya koma gidan kam har yay bacci yana son jin kiran Farid awaya amma yaji Shiru,
Shikuwa Farid yana can bayan sun sauka a gidan su da aka kama masa haya ba acikin school tasu yakeba kuma saboda baby dinne yasa shi kin zama cikin school din sosai ya tashi hankalin sa yana neman wayan sa be gansaba Kuma yana da tabbacin gidan da suka zauna shida baby ya manto wayan bakin cikin duniya ya isheshi ba komai yake tunani bah se ina ze kuma sami number din su Fanan ya kirasu harara kawai yake zabgawa baby wadda tunda suka sauka a jirgi take tai masa hauka da shirme kala kala se kallon su akeyi har suka isa masauki nasu gaba daya ta manta da Wani abu damuwa murna ya cikata, idanun sa sunyi jajir da bacin rai cushion kawai yake duka yana cije lips yana cewa
" Yanzu bazan ji muryan kiba har sena koma Nigeria! Gaskiya impossible dole na nemi number din madam Farida gurin Omar tabani number din Maya donna san bazata rasataba" shi kadai yay ta sunbatun sa don haushi ko dakin ta be nuna mataba yabar ta anan parlour ta kwanta, babu yadda ya iya cikin kwana biyu ya kammala komai ya canza waya da sabon Sim.
Bangaren mutan Abuja kuwa jikin Omar Abuja sedai ace Alhmdlh yayi garas sedai Zainab daya gaza tunanin ta har yanzu tashin hankalin da suke cikine yasa bata fahimta mijin nata ya dawo dai dai ba kullum ya dawo daga aiki seya biya gurin malamin nasu wata rana ma se dare yake komawa gida don shima zaman gida bason sa yakeyi bah saboda Kara daga masa hankali da iyalan nasa keyi mussam man Fanan abar tausayi ta dole yasa aka cigaba da bincike akan autar tasa, kamar ko yaushe da safe Fanan ta shiga gurin Dad din nasu don kaima masa abin karin kummalo ta sameshi a parlour yayi shiru yana tunani yana sanye da jallabiya dagani tun asuba be koma bacci bah bayan sun gaisa ne yake tambayar ta me mummy tata takeyi tashaida masa tana wanka batare da bata time bah yace ta gyara masa dakin nasa don yana bukatar gyara yaushe rabon da maya tabi takan dakin mah, cikin dan kan kanin lokaci ta gama gyaran dakin ta goge komai na kyalli tasa room freshener dakin ya dauka kamshi me dadi seda ta gama komai ta soma cire rigunan pillows din dake kan bed din Dad din nasu don canza wasu seda ta gama da pillows dinne ta soma kokarin cire bedsheet din kasan cewar an cusa shi can kasan katifa yasa dole seda ta daga ta, ta janye bedsheet din kafin ta maida katifar ne Idanun ta ya sauka kan wan nan bakar laya da Maya ta ajiye sosai tsoro ya kamata don zuciyan ta sam bata aminta da layan bah bata saki katifan ba duk da hannun ta ya gaji tasoma kwala wa Dad din nasu kira .....✍️