🧑‍🍼 RABO...❣️

30

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode thirty one 

Yanajin kiran datake masa ne ya taso daga parlour din ya shigo bedroom cike da mamaki take cewa " Dad menene wan nan?" Zaga yowa yayi yana kallon inda layan take ajiye kasan katifan sa yayi shiru ya zuba mata Idanu gaban sa na faduwa don tabbas yasan wan nan bakar layan ba alheri bace a gurin dake wa yayi don kada Fanan ta fahimta wani abu yayi Bismillah ya dauke ta yace ta cigaba da aikin ta yana fita yasaka layan a leda direct ya nufi gurin malamin su da ita, koda isar sa as usual malam na zaune shida daliban sa suna karatu mamaki ya kamashi ganin yanayin da Omar yazo masa se bayan da suka zauna ne a sitting room dinsa ya ciro masa layan yana tambayar sa ta mecece domin a kasan katifan sa yarinyar sa ta ciro ta, cikin al ajabi malam ya ansa layin cikin yin Bismillah yasoma bude ta layan sannu a hankali seda yay mata filla fillah Omar na zaune gefen sa ya zuba masa idanu soyake kawai yaji ta bakin sa, fuskan sa ta canza sosai malamin tausayi ya mamaye sa ya dago ya kalli Omar din na wasu second tukunna yace

" wacece Zainab?" 

Kasa koda furta kalma daya Omar yayi malam kawai yake kallo da layan dake hannu sa, sosai malamin yake nazar tar sa seda ya nanata masa tambayar sau uku ya kasa furta komai ne ya mike ya dauko wani kaskon kasa ya kona layan a ciki duka Omar na zaune yana kallon sa yana kuma jin wani irin abu dake masa zarya cikin brain dinsa kamar kurma haka ya dawo malam harya gama masa rubutu ya wanke ya bashi ya sha yace ya tafi gida ya kwanta ya sami hutu, be musaba ya mike sedai ya kasa tafiya seda ya kuma tambayar sa

  " Layan ta mecece?" 

"Layan kuce kaida zainab anyi maka sihirin mantuwa akan Zainab, an danne zuciyan ka bazaka iyayin komai ba, shin wacece ita din agare kah?" 

Shiru Omar ya kuma yi masa hakan ne yasa malamin fita daga dakin ya koma gurin daliban sa shiku ma yace ya Kwan ta ya huta anan kafin ya sallami daliban sa yazo su karasa magana akai, tom rashin baccin da be komaba ne yasa yana kwanciya bacci me nauyi ya dauke shi se wajen 12 ya farka a baccin saka makon mafarkin masoyiyar sa dayayi tana cikin wani hali duk Addu'ah datazo masa baki yinta yake yi yayi gumi Sosai yana mikewa yaci karo da ragowan rubutun da malam ya masa ya kwankwade shi saboda bushe wan da bakin sa yayi, afujajan malam yaga Omar din ya fito suna karatu ya masa sallama ya tafi bayan ya sheda masa kano zeje yanzu cikin farin ciki ya masa ala kiyaye don ya tabbatar da yanzu komai ya dawo dai dai, gudu yay a motar bana wasaba harya isa gidan nasa burin sa a yanzu be wuce yagan shi gurin Zainab bah, ko shigan da mota gani yay bata lokaci ne parking yay a gefen gate din gidan nasa yay amfani da key dinsa ya bude kofan ya shiga a gaggauce ya amsa gaisuwar me gadi yay ciki,

   Maya da sadiya suna parlour a zaune sun tasa TV a gaba koda wasa basuji shigowan Omar bah saboda basuji karan bude gate ba bare shigowa da mota don bayan TV din da suka kunna hankalin su kacokan naga maganar da suke tattauna wa yana sawo kansa ciki yana shirin kwada sallama kunnen sa yajiye masa abinda ya girgiza shi matuka kamar gunki haka ya kame a haka yana sauraren Maya tana cewa 

  " Ai sam bana wani tantama baby tana gurin sa shi yasan inda yakai mun ita hakan bakaramin barazana bane a gareni sam banida kwanciya hankali sadiya ban san meze aikata wa baby taba saboda badon kudi ya sace min itaba sedon daukar fansa ada ina tunanin uwar sace ta dauke min ita ashe ma sedaga baya naga yadda take a hospital mutuwa ko yau ko gobe, wlh zuciya ta tacika da tsoro bansan meze aikata wa baby ba duk don akan abinda mukai wa Zainab, idan fansar ze dauka aini dake ya kamata ace zewa ina ruwan 'yata a wan nan lamarin! Sam banida ikon kai karar sa don ko sheda daya nagaza samu akan sa shi Dad din su Fanan yana nan yasa a cigaba da bincike nace yabar min komai a hannu na yakiji se bulayin iska da suke tayi kullum, Wlh danasan wan nan abun da mukai wa matar nan ze shafi autata da bamu aikata shiba da bari zanyi ko auro ta zeyi ya auro in yaso inta shigo gidan nan ko kiyama ina iya turata wlh domin babu wadda nafi tsana a duniya sama da ita komai ina iya aikata mata don itace silar lalace war farin cikina, sheda ko dayace naketa fafutukar nema wadda zan iya yaki dashi akan autata amma na gaza sami abu ya gagara har yanzu"

  Gyara zama sadiya tayi tana cewa " lallai wan nan shi ake kira anyi ba aiba, gaskiya yaron nan Omar yacika dan iska tanan kuma ze bullo mana Tab! Aikuwa indai hakane akwai matsala don adazu nabiya gurin malamin nan zemin wani aiki ya shaida min mijin naki yanzu wan nan asirin baya jikin sa abinda yasama kenan kiga ganni nazo miki ba shiri inji garin ya kikai wan nan sakacin ke kuwa?" 

  Wani irin zabura Maya tayi cikin kwalo idanu tace " nashiga ukuna! Garinya hakan ya kasance? Kai anya kuwa yaga dai dai malamin nan nifa bana ganin alamun ya dawo dai dai duk da bana wani bi takansa yanzu saboda tashin hankalin da nake cik" 

  Katse ta sadiya tayi tace " to yau ki gwada shi ki gani indai be tuno komai bah dole asake yin wani shirin don duka zata kwabe mana kinsan yadawo hankalin sa ya tuno abinda ya faru" 

  " Amma sadiya wan nan layar fah tana nan kasan katifan sa har yanzu ban cire taba taya ze dawo normal?" Maya ta tambaye sadiyan cikin wani irin mamaki, dan yake ta mata kawai tace " Maya layar nan bata cikin gidan nan, idan kina musu kuma kije ki duba" 

  Da gudu Maya ta mike ta haura upstairs Omar ya bita da wani irin kallon al ajabi tsoro da firgici duka a lokaci daya, jikin sa a matukar san yaye ya maida kofan parlour din ya rufe karan rufe kofan ne yasa sadiya saurin waigowa koda ta ganshi heart dinta ne yay wani irin harbawa ta risina zata gaishe shine ya daga mata hannu cikin wani irin birki taccen yanayi yace " tashi ki fitar min daga gida! Sadiya Allah ya isa tsaka nina dake, duk ranar da kika kara tako min gida wlh sena sa an daureki bin bokaye ban hana kiba keda Allah amma kisani abinda kukai min bazan taba yafe muku bah Wlh, kuma koda matata na sake ganin ki sekinyi nadamar zuwan ki duniya wlh kinji na rantse miki!!" Tuni sadiya jikin ta yana tsuma ta dauki jakar ta sim sim sim tai bakin kofar tana son bashi hakuri amma daya buga mata uwar tsawa bata san time din data rarumi kofa tai wajeva tsaf tasan a wan nan yanayin Omar yana iya babba lata, tana fita ya nemi kan cushion ya zauna da hannu biyu ya dafe kansa hawaye masu zafi na kwaran ya a idanun sa jijiyoyin sa sun wani mimmike sun fito saboda tsananin bacin rai har wani vibration yakeyi, "INNA LILLAHI WA INNA LILLAHI WA INNA LILLAHI RAJI UN!! Shine kawai abinda kawai yake iya nana tawa harta sauko kasan ta sameshi koda tayi arba dashi a haka jikin ta seyay sanyi kalau tsoro da fargaba suka dirar mata a yayin daya dago kuwa saurin jada baya tayi tadafe kirjin ta tana fiddo idanu saboda yadda taga mijin nata ya koma mussam man irin kallon dayake mata cikin Zubar hawaye yace

   " ALLAH ya isa tsakani na dake Maya! Bazan taba yafe miki bah in Sha ALLAH kuma zakiga yadda karshen zeyi baze kyauba!" 

   Muryan sace take rawa kamar ze fashe da kuka ya mike kawai ya nufi dakin Fanan tana ta bacci ya tasheta sedai itama tana bude idanun ta tasauke shi kan mahaifin nata tashin hankali ya dirar mata da mugun tsoro saboda hawayen dayake yi, tunkan tayi magana ya tari numfashi ta yace. 

   " Fanan tashi kiyi maza ki hada kayan ki mubar garin nan duka wani abu da kikasan kina bukata kisaka shi a jaka yanzu zan fito mu tafi" 

Tun kan ya karasa magana itama tasoma hawayen kirjin ta na dukan uku uku tana tunanin meya faru haka ganin babu me bata amsane yasata mikewa ta shiga bathroom tana kara wai wayen kofan da Dad din nata ya fita, yana jiyo kukan Maya a kasa yay wucewa sa zuciyan sa na tsanan ta tafasa da harzuka harya fito wanka yana hawaye cikin mintuna 20 ya gama komai ya shirya kayan sa cikin trolley ya fito ya sawa kofan sa key, koda ya sauko kukan na Maya karuwa yay dataga abinda yake shirin aikata wa kamar zeci da wuta ya fice yasaka trolley din cikin booth din motan sa san nan ya koma gurin Fanan itama tafito wankan tagama shirya wa kayan ta take karasa sakawa cikin jaka batare da bata Time bah ya karasa zuba mata kayan ya zuge sam bata samu damar tambayar sa abinda yake faruwa bah sukai sukai ta biyo bayan sa yana rike da jakar tata Maya tana hango su ta ruga ta rike shi cikin tashin hankali tana kuka kamar zata shide tace 

   " Don Muhammadar rasulil lahi! Daddyn Fanan kar kai min haka ka rufa min asiri kayi hakuri Wlh tallahi sharrin shedan ne kada kayi min wan nan hukunci ina zan tsoma rayuwa ta!" 

   Cin cin karfin sa yasa ya kwada mata marin dayasa ta kifewa a gurin, Fanan ta kada uban ihu tana kokarin isa gareta ai dayay mata wata figa itama seda ta kusan kifewa yadda yake jan trolley din haka yake janta suna kaiwa bakin kofa ya juyo cikin karaji yace " Maya muddin kuma kika saka kafar ki kika fita a gidan nan to wlh a bakin auren ki! Idan ma mutuwa zakiyi sedai ki mutu a cikin gidan nan!"  Fuuu yakarasa jan Fanan din sukai waje tana rafka salati da kuka jin irin furucin da Dad din nata keyi seda suka kai bakin motan ne taja ta tsaya cikin kuka tace 

   " Kayi hakuri Dad bazan iya barin mummy acikin wan nan halin ba kabar ni na koma gunta!"

  Tasssss!! Kuwa itama ya dauke ta da marin dayasa ta kifawa kan motan ta bige goshi kukan ta ya kara tsanan ta kota kanta be biba ya saka jakan nata a booth itama ya rufe san nan ya bude  motan ya cillata ciki ya rufe.....✍️