ƊANƊANO.
*Friday, 10 April 2026*
*DAGA MARUBUCIYAR.*
*TA FITA ZAKKA*
*GIDANMU*
*KANA NAKA*
*TSAKA MAI WUYA*
*IDAN AN CIZA*
*TURKEN GIDA*
*JANAFTY*❤️
*AREWABOOKS:JamilaUmarJanafty*.
*WATTPAD:JamilaUmar315*
***
https://www.arewapen.com/u/jamilaumarjanafty
*ƊANƊANO DAGA LITTAFIN FARGAR JAJI.*
Sannu da zuwa Noori."
Ta faɗa tana nufarsa, bai tsaya ba amma ya amsa da yauwa a ɗakune yadda ta bar fuskar shi a cunkushe ɗazu to a yanzu ma haka ya shigo
Tana ƙoƙarin karɓan jakar hannun shi ya wuce ta da sauri zuwa cikin bedroom tana jin ƙaran yadda ya rufe ƙofar da ƙarfi. Ummu salma ta yi sansarairai a tsaye ta kasa motsi saboda mamaki da al'ajabi a wattani takwas ɗin da suka yi da aure ita da Habib ba su taɓa riskan wannan matakin ba sai yau.
Ajiyar zuciya ta sauke, komawa ta yi ta zauna tana sake karfafa ma kanta gwiwan ba komai yana fushi ne ya ɗauka ta san tana da ciki ne ba ta faɗa masa ba. Tana nan zaune sama da mintina talatin sha biyu saura na dare sannan Habib ya fito daga cikin Bedroom, ya sauya kaya zuwa wani gajeron wando da farar singlete da alamu wanka ya yi ko kallon ta bai yi ba ya wuce kitchen ya ɗauko ruwan gora ya fito da shi a hannu ita kuma ganin haka ya sa ta miƙe jikinta har yana rawa.
"Noori."
Ta faɗa cikin sanyi da karyewan murya.
Sai da ya sha ruwan rabin goran sannan ya ɗago yana kallonta cikin wani irin kallo da ya sanyaya mata jiki.
"Ga abinci."
Ta faɗa tana nuna masa Dinner ɗin da ta gama shirya masa komai tun ɗazu.
"Na ƙoshi."
Haka kawai ya faɗa lokaci ɗaya yana sauke goran hannun shi a saman dinning ɗin ya wuce ta ya koma ciki, da sauri ta bi bayan shi ta ci sa'a bai rufe ƙofar ba.
Yana zaune a gefen gado yana duba wayarsa ta shigo gefensa ta zauna tana neman kwanciya a saman kafaɗan shi ya yi saurin matsawa gefe, Ummu ta saki baki tana kallon shi.
"Noori."
Ta kira shi da mamaki a muryanta bai amsa ba ya dai kalleta a tsaye da idanuwansa fuskar nan ba fara'a.
"Me ya faru ne?
Banza ya yi da ita sai ma ya cigaba da duba wayarsa.
Sai ta yi mirmishi kafin ta ce.
"Wai akan mganar ciki ne?
Ga mamakin ta sai ya amsa mata da cewa.
"E."
Ta ɗauka tunanin ta gaskiya ne yana fushi ne akan yana tunanin ta sani ba ta faɗa masa ba, ba ta san tunanin Habib a lokacin ba.
"To ka yi haƙuri Noori na, wallahi da gaske na ke yi nima ban san ina da ciki ba."
Har ta gama mgana bai ɗago ba, yana cigaba da latsa wayarsa.
"Ka ji Allah ban sani ba ka yarda da ni."
Matsowa ta sake yi kusa da shi tana mai riƙe hannun shi guda ɗaya tana sake marairaicewa da muryan tare da shagwaɓan da ta san yana kunna shi.
"Am sorry Noori na.
Baby ce fa? Za ka iya fushi da ni?
Ta faɗa tana mai kwantar da kanta a saman kafaɗan shi.
Sai ya sake matsawa da mamaki ta sake ɗagowa tana kallon shi kafin ta samu damar mgana ya miƙe tsaye.
"Ummu-Salma ina son na yi mgana da ke."
Ya faɗa lokaci ɗaya yana mai kallonta a mganar shi da yanayin shi babu wasa ko kaɗan.
"Magana kuma? Wata mgana?
Ta faɗa cikin mamaki gabanta na faɗi kaɗan-kaɗan.
Bai amsa mata ba sai ya koma can farko gado ya zauna sannan ya juyo yana kallon Ummu-Salma da ta daskare a zaune saboda ita fa ba ta gane ma yanayin Habib ba gaskiya
"Ki natsu ki fahimci umarnin da zan ba ki."
Kallonsa kawai take yi amma ta kasa mgana sai dai ta kasa haɗiye miyau a bakinta saboda faragaba da tarardadi
"Ina sauraran ka."
Ta faɗa dakyar cikin rauni har idanuwanta sun fara cikowa da ƙwallah tun kafin ma ya faɗi mganar.
"Ummu-Salma."
Ya kira sunan ta a kausashe, sunan da ba taɓa jin ya kira ta ba tun tana gida da Baby yake kiranta har bayan auran su bai sauya mata suna ba shi ya sa jin yau yana kiran ta da sunan ta cikin kaushi ba tausasawa jikinta ya fara rawa cikin tsoro ta amsa.
"Na'am. "
A muryan ta kamar saura ƙiris ta fashe da kuka.
"Umarni na ke so na ba ki, ta wani fanni kuma ba Umarni ba ne."
Ita dai ta ƙura masa ido, ta kasa cewa komai amma ta matsu ya faɗi abin da zai faɗa kafin zullumi ya ɗauke mata numfashinta.
"Ina son a zubar da cikin jikin ki Ummu-Salma."
Ya faɗa yana mai kallonta domin ganin yanayin ta.
Ita ta ko sai ta ji kamar ba ta ji da kyau ba ya sa ta sake tambaya.
"Naam me ka ce?
Ta faɗa tana mai ƙura masa ido, kamar ta ji Habib na maganar ciki, me ya ke cewa ne?
"Na ce ina so a zubar da cikin nan."
Ido ta zaro kafin ta ce" Wa ni ci ki.?
Ta faɗa a rarrabe cikin tashin hankali.
"Wanda ke jikin ki."
Ya faɗa ba tare da ɗar ba, kuma babu nadama a mganarsa.
Sai Ummu ta fara mirmishi kafin ta ce.
" Haba Noori ka bar irin wannan wasan don Allah ba na so."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana girgiza kanta. Domin a tunanin ta wasa ya ke yi, ita kuma ba ta son irin wannan wasan, duk duniya a yanzu ba wanda ya isa ya raba ta da cikin jikinta sai wanda ya ba ta, amma ba dai wani mutum ba.
"Wasa ka ke yi ko Noori?
Ta sake faɗa tana kallon shi.
Amma sai Habib ya miƙe a fusace har yana nuna ta da hannu.
"Kin ga wasa a mgana ta! Ko kin ga fuskata da alamun wasa?
Ya faɗa a fusace, jikin Ummu na rawa ta miƙe, cikin mamaki da aljabi ta ce" Cikina zan zubar Noori?
"E haka na ce"
"To saboda mene? Cikin yana da wata matsala ne?
"Ba shi da wata matsala, amma ni ne zai iya kawo ma matsala a rayuwata nan gaba."
Ummu cikin rawan baki da na murya ta ce
"Ban ga ne ba?
"Ai ba za ki gane ba. Malama ni dai ga abin da na ce. Ciki za a zubar da shi."
"Aa"
Ummu ta faɗa hawaye na zubo mata cikin kuka ta ce" Me ya sa zan zubar da cikina? Cikin sunna ne ba na shege ba."
Ta faɗa cikin zubar hawaye
"Ni haka na ce za a zubar da shi."
"Ba zan iya ba. Ba zan iya zubar da cikin nan ba, haka kawai sai ka ce na zubar da ciki kuma ba da wani ƙwaƙwaran dalili ba"
Ta faɗa tana share ƙwalla kafin ta matsa kusa da shi tana cewa" Noori ni ce fa, ka tuna lokacin da ka shiga damuwa da na rasa cikina na farko me ya sa ba za ka yi murna da samun cikina a karo na biyu?
Me ya sa ka canza? Ciki fa ka ce na zubar? Zunubi fa kake so mu aikata."
Ta ƙarishe faɗa tana ƙoƙarin riko shi da sauri ya kauce yana faɗin
"Ni ba damuwa na shiga don cikin ki ya zuɓe ba, ko bai zube ba za ki zubar da shi. Murna na yi lokacin da ya fita ba baƙin ciki ba.".
Ya faɗa yana kallon ta, cikin ɗimuwa da firgici Ummu ta zare ido, kafin ta kifta idanuwanta amma ta kasa mgana domin sai ta ji wani abu ya tokare mata maƙogwaro
"Kin ji da kyau, saboda haka na ba ki kwana uku ki yi shawara. Duk da Umarni ne ba zan miki dole ba amma ki sani zubar da cikin nan kamar makullin auran ki ne, taurin kai kuma na ƙin zubarwa dai dai ya ke da rasa komai na ki, in na ce komai ina nufin komai. Kuma wallahi sai kin yi nadaman saɓa ma umarnina."
Yana gama faɗin haka ya fice ya bar mata bedroom ɗin. Ummu ta rasa wani tunani za ta yi, sai take ganin kamar a mafarki gaskiya ne abin da ke faruwa ko ƙarya, amma kuma kamar da gaske, ganin ta kawai ta yi tana tafiya a falo ta iske Habib zaune a saman kansa ta tsaya tana kallon shi cikin mamaki, so take yi ta ga shin Habib ɗin ta ne ko sauya mata shi aka yi amma ba ta gano wani abu da zai saka Habib ɗin ta ya sha bambam da wannan dake zaune a gabanta ba.
Tashi ya yi zai bar mata falon da sauri ta sha gaban shi tana faɗin" Noori an ya kasan me kake faɗa kuwa?
Ta faɗa muryanta na rawa kaɗan ya rage ta fashe da kuka
"Kwana uku na ba ki , ki yanke ma rayuwarki hukunci. Kwana uku kacal."
Ya faɗi haka sannan ya raɓa ta gefen ta ya bar falon, nan ƙasan cafet Ummu ta durƙushe tana mai fashewa da kuka, ji take yi kamar ba ita ba zuciyarta na zafi kirjinta wani abu ya tokare mata da ya kasa wucewa kuka ya sake kece mata, tunani take yi ko Habib ya fara shaye-shaye ne yau wata ƙila ya sha wacce ta fi karfin ƙwakwalwarshi shi ne ta faɗa masa ba daidai ba, amma ta ya ya zai ce ta zubar da cikin jikinta cikin sunna ba ta taɓa jin maganar da ta ruguza zuciyarta kamar wannan mganar ba, me mganganunsa suke nuna mata! Me ya sa ta ji zuciyarta na yi mata rawa akan Habib? Me ya sa yau ya sauya mata? Me ya sa zai yi haka?
*
Tana kuka tana shessheƙa ta labartama Baffa abin da ke faruwa amma ta ɓoye maganganun Habib a kan ta na cewa ba ya son ta auren sha'awa ya yi da ita sannan ta ɓoye hanyoyin da ya bi wajen mata barazanar ta zubar da cikin, ta dai faɗa ma Baffa zaman su ya lalace domin Habib ya ce in har ba ta bi umarninsa ba, yanzu suka fara yar tsama a tsakanin su.
"Innalillahi wa'innna ilaihirraju'un"
Baffa ya dire salatinsa cikin mamaki yana kallon Ummu yadda take kuka kamar ran ta zai fita.
"Baffa don Allah ka kira Habib ka yi masa faɗa na san yana jin maganarka. Ka faɗa masa ina son cikin nan ba zan iya zubar da shi ba"
Ta sake faɗa cikin kuka Baffa ya yi shuru lamarin na ɗaure masa kai , ina aka taɓa haka? Ka yi ciki da kan ka sannan ka dawo ka ce ba ka so sai an zubar.
"Don Allah Baffa."
Ta sake roƙon shi, tausayi ta ba shi Ummu ta faɗa cikin kaddaran aure tun tana da ƙananun shekaru.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Abin da ban gane ba, me ya sa ba ya son ciki? Mene ne dalilin shi na cewa sai an zubar?
"Baffa wai ba yanzu ya tashi haihuwa ba."
"Ka ji wani shirmen banza. Da man shi ke da wannan tsarin ba na Ubangji ba ne? Habibu ya ba ni mamaki ina ɗaukan sa mai hankali ashe kallon kitse na ke yi ma rogo ban sani ba?
Baffa ya faɗa cikin bayyana mamakinsa domin abin da ya yi, aikin jahilai ne mara sa ilimi da tarbiya.
"Tun yaushe ne kuka cikin wannan yanayin?
"An fi wata fa Baffa."
Ta faɗa tana cikin dashewar murya lokaci ɗaya tana share hawayenta da gefen hijabin jikin ta.
"Me ya sa tun a lokacin ba ki zo kin faɗa mini ko Amman ku ba?
"Baffa na ɗauka za mu iya warware matsalan ne da kan mu."
Baffa ya jinjina kai kafin ya ce" Ni lamarin ne ya ɗaure mini kai. Ban taba zaton haka daga Habibu ba."
"Nima ban yi zato ba Baffa."
Ta faɗa cikin sanyin murya.
"Ki yi hakuri Auta. Amma ba ni ne zan yi ma Habib mgana ba. Ta in da aka hau ta nan za a sauka."
Ya faɗa yana kallon ta, kafin ta yi mgana ya rigata da cewa." maganar ki zubar da ciki ma bai taso ba tun da lafiyan ki lau, saboda haka waliyin shi wanda ya karɓan masa auran ki za a yi ma mgana su za su kira shi su yi masa magana."
"Baffa me ya sa kai ba za ka yi masa da kan ka ba?
Kai tsaye Baffa ya ce" Maganar ba ta ni kaɗai ba ne, dole a sako waliyin shi a ciki "
Ummu ta yi shuru kanta na ƙasa Baffa bai fahimci abin da take tsoro ba. Kamar ya san abin da take tunani ya kalle ta yana faɗin" Ki kwantar da hankalin ki, Baffan ki Umaru zan yi ma waya shi zai kira waliyin na shi mu ji me zai ce."
"Baffa ina son Habib, ba na so a raba mu "
Ummu ta faɗa cikin karyewan sauti kamar za ta sake fashewa da kuka.
Baffa na shirin mgana su ka ji sallama, gaban Ummu ya amsa domin ta ji muryan Hamma Abdurrahaman.
"Ammah ko ba ta nan ne?
Ya faɗa daga tsakar gida, kafin kuma ya kariso ɗakin Baffa tun da ya ga motarsa ya san yana gida, balle ma ya yi waya da Ammah da safe ta ce ya fita tare da Abdullahi amma ba za su daɗe ba.
Jikin Ummu ya fara rawa lokacin da Hamma Abdulrrahaman ya shigo ɗakin Baffa da sallama ta kasa iya ɗago idanuwana ma ta kalle shi, fatan ta ka da Baffa ya sanar da shi abin da ke faruwa.
"Abdulrrahman lale sannu da zuwa."
Baffa ya faɗa cikin mirmishi, shima Hamma Abdulrrahaman ɗin cikin fara'a ya amsa yana mai zama kusa da Baffa a saman darduman da ya ke zaune sai a lokacin ya kula da Ummu.
"Ke lafiya?
Ya faɗa yana kallonta kafin ya juya yana kallon Baffa.
"Baffa me ke faruwa ne?
Saboda irin zaman da ta yi ne ya sa ya ji kamar jikinsa bai ba shi ba.
"Lafiya lau. Ya aiki da wajen iyalan naka?
Baffa ya faɗa yana mirmishi, ya amsa da duk suna lafiya yana sake nazarin Ummu da ke dukar da kai kamar munafuka.
"Na zo nan kusa ne kan wata sharia da na kai ne a yanzu."
"Allah ya ba ka nasara."
Ya amsa da Amin.
"Ke jira kike ni na fara gaishe ki?
Hamma Abdurrahaman ya fada a ɗan zafafe.
Baffa ya yi saurin tare shi da faɗin". To sarkin ƙorafi yaushe mu ka gama gaisawar ballanta ma ta samu damar gaishe ka?
"Baffa kar ka kare mata, mintina na nawa da shigowa ɗakin nan?
"A yi haƙuri."
Baffa ya faɗa yana ɗan mirmishi.
"Hamma ina yini."
Ummu ta faɗa muryanta na rawa, lafiya lau ya amsa sannan yana sake kallon ta.
"Kin yi ciwo ne?
Ya faɗa daidai da ta tashi za ta bar ɗakin na Baffa.
Sai ta juyo tana kallon shi duk da ya ɗan kwana biyu bai gan ta amma ta lalace da yawa.
"Ta yi zazzaɓi kwana biyu."
Baffa ya amsa mishi, kallon shi ya yi kafin ya sake kallonta ya ce" Baffa wannan ya wuce zazzaɓi, idanuwanta da fuskarta sun nuna tana cikin damuwa."
Baffa na dariya ya ce" To lauya."
Shima sai da ya yi dariyan da haka Ummu ta so ta sulale Hamma Abdulrrhaman ya tsare ta da cewa ta dawo ta zauna jikinta na rawa gabanta na faɗi ta koma ta zauna a in da ta tashi.
"Ke kina da wata damuwa ne?
Ya faɗa yana mai tsare ta da ido, har yana sauke jakar hannunsa a ƙasa, sanye yake da suit ya tsuke, da man Hamma Abdulrrahaman in ya ta saka ka gaba ba ka iya ƙwatan kan ka, aikin lauyancin har a gida yana yi, in yafara jefa maka uban tambayoyi sai ka fara zufa ma ba ka sani ba.
"Ko mijin na ki ne ke ba ki wahala! Kin rame sannan fuskarki ba ta cikin walwala."
Ya sake tambaya kanta na kasa ta kasa mgana sai rawan hannu take fama da shi duk yana lura da ita.
Baffa na so ya yi mgana ya katse shi da cewa" Baffa da wani abu ko! Wani abu na damun yarinyar nan kamar mai depression kalli yadda hannayenta ke rawa?
Baffa na dariya ya ce" Kai ne ka saka ta rawan hannu. Daga zuwan ka, ka fara mata tambayoyi sai ka ce a kotu."
Baffa na so ya ɗan shashantar da maganar amma Hamma ya ƙi yarda saboda ya fahimci akwai wani abu.
"Baffa wani abu na faruwa, kai ma fuskar ka ta bayyana damuwa."
Baffa ya kasa mgana, da gaske ne tun da Ummu ta faɗa masa abin da ke faruwa ya rasa abin da ke yi masa daɗi.
"Ya kamata na sani Baffa?
Ya tambayana yana kallon shi, Ummu kuma Baffa take kallo tana girgiza masa kai, karaf ko ya ganta da sauri ta mai da kanta ƙasa tana jin hancin jikinta na ƙalawa saboda tsoro.
"Baffa me ke faruwa?
Ya faɗa cikin muryan da ba wasa a cikin ta.
Baffa ya yi gyaran murya sannan ya shiga sanar da shi abin da Ummu ta gama faɗa masa.
"Yanzu nan da ka gan mu, nima ta gama faɗa mini abin da ke faruwa kenan."
Hamma Abdulrrahaman ya yi shuru kafin ya ce.
" No wonder na ga yarinyar nan duk ta lalace, ba ma za ta rasa depression ba."
Baffa ya yi shuru bai yi mgana Hamma Abdulrahaman ya kalli Ummu ya fara faɗin" Shi don uban shi bai shirya haihuwa ba yanzu ya zo ya aure ki? Ya san bai shirya haihuwa ba ya yi aure? Ji wani rashi tunani don uban shi ba a haihuwa shi aka haife shi?
Ya ƙarishe faɗa cikin ɗaga murya jikin Ummu ya fara rawa kafin ma ta samu damar magana Ammah ta faɗo ɗakin tana faɗin" Waye kuma ba ya son haihuwa?
Ta yi turus ganin Ummu zaune tana rawan jiki ga Hamma Abdulrrahaman na ta bala'i Baffa na zaune a gefe bai yi mgana ba.
Ta ji zuwan shi lokacin tana salla ne amma yanayin da ta gan su a ciki ya sa jikin ta ya yi san yi.
"Baffa me ke faruwa,?
Ta faɗa tana mai zama a gefen Ummu.
"Me aka yi ma wannan ta ke rawan jiki?
Ammah ta sake tambaya tana mai kallon Ummu da har ta fara hawaye.
"Au kema ba ki sani ba?
Hamma Abdurrahaman ya tambaya yana kallon Amma.
"Mene ne? Ban sani ba"
Ta faɗa cikin mamaki, Hamma Abdurrahaman bai tsaya ba ya kwashe komai ya faɗa ma Ammah yana fada mata tana sake kallon Ummu cikin mamaki.
"Na zo na same ta durkushe a gaban Baffa kamar wata marainiya, ba ta so na ji mganar ba ne. Raina ya ɓaci sai da lokacin nan Kabiru ya yi ta cewa an yi gaggawa Baffa ko fa bincikan shi yaron ba a yi ba sosai in da an yi bincike sosai ta ina za a aura mata ɗan iska wanda ba ya son haihuwa. ? Wato in ma wajen zubar da cikin wani abu ya same ta shi ba shi da asara kenan ko?
Ya sake faɗa har yana ta yar da jijiyan wuya.
"Duk binciken da ya kamata a yi an yi Abdurrahaman kuma ba a same shi da wani abu na ashha ba."
"To Baffa wannan dai abin assha ne, jahilci tsantsan da rashin tunani. Tunda cikin ya shiga sai ya bar shi ta haihu can tsakaninsu za su iya tsayar da haihuwa da fahimtar junan su duk ana haka ba matsala ba ne. Amma kawai ya ce sai ta zubar da ciki da karfin tsiya wannan ya saɓa ma doka. In muka yi ƙaran shi sai ya gane ba shi da wayau"
"A'a ba za a yi haka ba."
"To Baffa me ye amfanin zama da mara mutumci? A raba auren kawai."
Da sauri Baffa ya ce" Na ce aa ko, shi ya sa ban faɗa maka da farko ba sanin halin ka na saurin yanke hukunci."
"To Baffa me kake so a yi?
Hamma Abdurrahaman ya faɗa cikin sarander
Ammah mamaki ne ya sa ta kasa mgana tunani take yi lokacin da Ummu ta yi ɓarin cikinta na farko yadda Ummin ikki ta ce ya damu, to yanzu kuma da ya kamata ya yi murna me ya sa zai ce ba ya so?
"Baffan ku Umaru zan kira, shi zai kira waliyin shi ya faɗa masa sai mu ji abin da ya kamata mu yi nan gaba."
"Baffa ya fa san da waliyin na shi ya ce sai ta zubar da ciki. Ni ina ganin a biyo da shi ta hanyar da ya biyo, ka ji fa ta ce yana azabtar da yarinya yana so ya yi mata dole."
Baffa ya tare shi da cewa" Duk da haka dai a fara sanar da su, a bi komai a hankali."
Amma ta jinjina kai kafin ta ce" Baffa ya yi gaskiya a fara sanar da su a ji su kuma na su hukuncin. Amma dai Habibu ya ba ni mamaki ban zaci haka daga wajen shi ba."
"Nima haka wallahi."
Baffa ya faɗa shima cikin ɗan damuwa Ummu kuma hawaye ta ke sharewa ta kasa mgana.
"Ni da man na san za a yi haka. Yaro ne fa ƙarami Baffa yarinyar nan da karatunta ta cigaba amma ta na ce ta ce aure za ta yi ai ga shi nan kin fara ganin uwar da ke cikin auren."
Baffa sai da ya yi dariya Amma ta kauda kai ba ta yi magana ba.
"Ba yadda ba mu yi da ke ki cigaba da karatu ba kika ƙi, kika ce ke aure ke yar soyayya to yau duk ina soyayyar! Tun da kin samu ciki ya ce dole sai kin zubar? Kin ga wawancin da muke faɗa miki kin yi ko a wancan lokacin ko? Auran ki ko shekara bai yi a ce su Baffa sun fara sulhu tsakanin ku? Da yau karatun ki kike yi da ba ki yi kuka ba"
Ya sake faɗa yana kallon Ummu yadda take kuka har yana fidda sauti.
"Na so ki cigaba da karatu, na so ki yi karatu. Nawa kike Ummu? Just 24 to 25 kina da sauran damarmaki masu yawa amma kika ƙin jin maganar mu, Baffa da Hamma Jibo suka mara miki baya. Yanzu don Allah ina amfanin a fara kiran su Baffa Umru da magarnar ki? Yaron ma ba shi da mutumci in har ba zai sauke kudirinsa ba ya sake ki kawai "
Ummu ta sake jin kuka ya taso mata, domin ta san ko giwar wake ta sha ba ta isa ta ce ma Hamma Abdulrrahaman tana son Habib ba ta son rabuwa da shi ba, ta tabbata sai ya yi ball da ita shi ya sa ta yi shuru tana ta kuka shi ko yana ta faɗa da masifa Baffa ne ke tausan shi amma bai haƙura ba.
"Kaddara ta riga fata fa, Abdulrrahaman. Fatan mu dai Allah ya sa lamarin ya zo da sauƙi."
Ammah ta faɗa, ita tausayin Ummu ta ke ji. Ita mace ce sannan ƙarin tausayin ta da fatan ta kar Ummu ta fara fuskanta kaddaran aure da ƙananun shekarunta. Ita ta zauna da Fatima lokacin da kaddaran aure ta faɗa mata da shekarunta sha bakwai a duniya ita kaɗai ta san siraɗan da fatima ta tsallake kafin ta iya tsayuwa da kafafunta. Fatan ta Ubangiji ya zaunar da Ummu a ɗakin auren ta na har abada ya kuma sassauto da zuciyar Habib a kan ta. Kar Allah ya sa ta ɗanɗana zafin zawarci har abada a rayuwarta.
"Fatan da za mu yi kenan tun da mai afkuwa ta faru. Kuma bawa bai isa ya sauya zanen kaddaran sa ba."
Baffa ya faɗa, amma shi fa Hamma Abdulrrahaman bai yarda ba faɗi yake yi har da kuskuran su Baffa.
Amma ta ga Autar ta nata kuka ya sa ta shigar mata.
"Don Allah ka kyale ta Abdurrahaman ba ta ko da cikakkiyar lafiya!. Ke ta shi ki je ki ci abinci"
Ammah ta cece ta, ta samu ta bar ɗakin Baffa tana kuka zuwa falon Ammah ta faɗa saman kujera ta saki kukan ta shike nan abin da take gudu ya faru ya za ta yi ma Hamma bayanin yadda take son Habibu ta ke kuma son cikin jikinta da aurenta. Ta tabbata ba zai taɓa ganewa ba gwara Baffa shi ne zai fahimce ta da halin da ta ke ciki ba amma ba su Hamma Abdulrrahaman ba da daman yana cikin yan adawa da auran ta da Habib.
*
Kamar a mafarki ta ji bugun ƙofar domin har ta fara barci kanta ke ciwo saboda kukan da ta sha, sai ta sha pracetamol tana idar da sallar isha'i ta kwanta cikin ikon Allah barci ya kwashe ta da man wani lokacin tana samun yin barci a farkon dare amma in ta farka ne yake da matukar wahala ta samu nasaran komawa, wata rana ta tashi ta yi salla wata rana kuma ta yi karatun Qur'ani wata rana kuma ta yi kuka. Yau ma da wuri ta samu barcin amma bugun ƙofar da Habib yake yi ya katse mata barcin nata kuma a daidai lokacin daman mafarkin Habib ɗin take yi wai ya kira ta yana yi mata mgana ita kuma ta ɗuka har ƙasa tana bashi haƙuri har ya tashi zai tafi ta riƙo kafarsa amma ya juya ya ture ta a cikinta ta faɗi, sai ga jini na bin ƙafarta shi ya sa bugun ƙofar da mafarkin da ta yi suka samar mata da tashi a firgice tare da fargaba mai tsanani.
"Ba za ki buɗe ba! Ke Ummu Salma."
Ta ji muryan Habib yana magana, ta sake figicewa cikin gigita ta sauko daga kan gadon da take kwance, ta ma manta da hulan kanta da ya saɓule bayan ta kwanta sai da ta nufi ƙofar sannan ta shafa kanta ta ji ba ɗankwali ga shi kan ya yi datti goron kitso har ya ɓace saboda daɗewa, saboda ba ta kitso take yi ba.
"Wai ba za ki buɗe ba? Na san fa kina jina."
Habib ya sake faɗa kuma yana cigaba da buga ƙofar, yadda jikinta ke rawa haka zuciyarta ke rawa domin ba ta san da abin da Habib ya zo a daran nan ba amma dai tafi tunanin abin da ke kawo shi wajenta ya zo nema jikinta, in shi ne kuma ya zo ga shi nan har sai ya gaji.
Saboda saurin ta buɗe kofar har tana neman faɗuwa rigar jikinta ce ta harɗeta ta kusa kaiwa ƙasa sai da ta riƙe gefen wardrope ɗin dake ɗakin. Hannnunta na rawa ta murza key ɗin dake jikin ƙofar ta buɗe ɗakin, Habib ya tsaya yana kallon ta cikin bacin rai.
"Ni za ki mayar ɗan iska kina ji ina kiran ki kina yi mini shuru?
Kanta na ƙasa ta ce" Ka yi haƙuri ban ji ba ne"
Ta ɗauka abin da ya saba kawo shi yau ma shi ya kawo shi ya sa tana gama bashi haƙuri ta juya za ta koma ciki.
"Ki same ni a falo."
Ta ji ya faɗa ta juya cikin mamaki shi kuma tuni ya bar wajen, zuciyar ta amsa na rashin sanin dalilin kiran Habib amma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta bi bayan shi zuwa falon, jikinta ya yi wani irin sanyi ne lokacin da ta ga Habib zaune kan kujera mai zaman mutum biyu ya harɗe kafafunsa kamar wani basarake ga littafi da takarda a hannun shi har da biron rubutu.
Kasa ƙarisowa ta yi ta tsaya cak daga nesa tana kallon shi cikin bugawar zuciya, me Habib zai yi da takarda da biro? Allah ya sa ba abin da zuciyarta ke saƙa mata ba ne, in ko haka ne da ta ce ita yau Ummu Salma ta shiga uku ta lalace rayuwarta ta faɗa cikin mawuyacin garari, gararin da har abada ba za ta iya fita daga cikin sa ba.
"Malama ki ƙariso kin tsaya mini a saman kaina "
Salau-salau haka ta ƙarisa gaban shi, ta zauna a kasan cafet tana mai ƙura ma kwalliyan cafet ɗin idanuwanta, amma hankalinta ba ya wajen in da zai lura ma kafafunta da hannayenta ma rawa suke yi tsabar firgici.
"Kin gama na ki aikin saura nawa aikin kuma Ummu Salma."
Sai ta ɗago tana kallon shi amma ba ta yi magana ba.
"Kin je kin haɗa ni da iyayena, kin yi ƙoƙarin ɓata mini gobe na sai dai burin ki bai cika ba."
Ya sake fada yana mai kallon ta fuskar nan ba fara'a kamar bai taɓa dariya ba.
"Me kuma na yi?
Ummu ta faɗa muryanta na karyewa kamar ta fashe da kuka.
"Ni kike tambaya abin da kika yi! Kin manta kin sake kai ƙarana wajen iyayen ki? Ke a tunanin ki za su iya sauya komai ne?
Ta ma kasa mgana bakinta na rawa, shi ya sa kawai ta yi shuru amma har hawaye sun kece mata maganarsa ya ba ta tabbacin Baffa ya ji labarin halin da take ciki, magana ta kai kunnen iyayen Habib.
"Ummu Salma ba ke kaɗai ne ba ki da tunani ba har da iyayenki ma."
Da sauri ta ɗago ta kalle shi cikin mamakin kalaman shi, iyayenta ne marasa tunani? Yau ita Habib ke faɗa ma iyayenta ne ba su da tunani?
"E haka na ce ba su da tunani, in har suna da tunani ai ya ci ace zuwa yanzu sun fahimci bana ra'ayin ki, na nuna bana son ki a aikace duk domin su fahimta su sauƙaƙa mini aiki amma sun kasa fahimta ban sani ba ko a wajen su ne kika gado wannan kidahumancin na ki ba"
Habib ya gama faɗa har yana nuna kanta cikin izgili.
Ummu Salma ta yi ma Habib ƙuru da ido ta kasa mgana, domin sai ta ji kamar an zare mata duka lakkan jikinta.
Yau iyayenta ne kidahumai a bakin Habib? Iyayenta fa? In ita ya zageta ta shanye, to ai bai kama ta ya taɓo bangaren iyayenta ba, domin ya san duk ɗa na gari ba zai zura ido ana cikin zarafin iyayenshi kuma ya yi shuru ba.
"Na gaji da ke, na gaji da auren ki wallahi, ke kika fara cutar da iyayen ki tun da kika ɓoye musu gaskiyan manufata akan ki, su kuma rashin tunanin su da lissafin su yasa suke tunanin ina son ki, sannan iyayena suna da ikon sarrafa rayuwata ne? Ina, rayuwata ce ni ke da ikon zaɓa ma kaina yau n da gobe na ba wani ba, ba kuma wanda ya isa ya saka ni na zauna da abin da bana so, a farko ni ne na yi ra'ayin zama dake saboda ina son cimma burina, yanzu kuma na gama amfana dake, na cimma burina akan ki me kuma ya yi saura a tsakanina da ke?
Ya faɗa yana zare mata ido.
Ummu na hawaye har da majina, ta ce" Iyayena ba su yi maka komai ba Habib ka daina zagin su don Allah."
Ta faɗa kukanta har yana fitar da sauti.
Sai ya kwashe da dariya kafin ya ce"Oh kina jin zafi ne? To na dai na cewa basu da tunani suna da shi, amma dai ba zan fasa faɗa miki kin turo bagidajen tsohon ki wajen iyayena ba kuma ya zo, sannan kuma har ya bar mini saƙo "
"Haba Habib."
Ummu ta sake faɗa cikin kuka tana sakin shessheka domin ji take yi kamar ta shiɗe yadda maganganun Habib suke kassra tunaninta da sauran kuzarinta gabaɗaya.
"Na faɗa wannan bagidajen uban naki ne, wai shi ne yake da zarran zuwa ya faɗa ma Abba cewa in na gaji dake ne na dawo masa dake gida"
Ya gama faɗa yana wata dariya ta reni da wulakanci.
"Shi yana ɗauka ya yi gwanin ta ne, ko kuma me ya ke takama da shi? Lauyan yayanki? Ko mai aikin filin jirgi? Ko mai fama da gwajin kashi da fitsari ko mai aiki da hukumar ruwa? Ko wannan yayan na ki mai bin tsohon ku saro tsoffin injina? Ko kuma wannan yayan naki mai karatun jami'a? Ko wanda ya tafi ƙasar waje da kuɗin tallafi?
"Habibb.."
Ta faɗa muryanta baya fita saboda kuka.
Bai saurareta ba ya cigaba da faɗin.
"Oh na tuna ko yana takama da wannan ɗan da bai haifa ba ne? Lamiɗon da dangin ku ke ji dashi, Yariman Daura ko? Wanda uwarki ke zuwa maula gidan sarki ko? Da shi yake taƙama da har zai zo wajen ƙanin mahaifina ya bar mini wannan saƙon? To in ma gatse yake yi ya yi kuskure, a yau ba sai gobe ba zan cika umarninsa zan mayar masa dake kamar yadda na ɗauko ki daga gidan shi."
"Habib ka bari, ka daina zagin iyayena."
Ummu Salma ta faɗa tana kuka zuciyarta na ƙuna tana wani irin soya da irin wannan cin mutumcin da Habib ya zaunar da ita yana yi ma iyayenta da yan'uwanta.
"Na faɗa ko za ki rama musu ne?
Ya faɗa yana taso mata kamar zai dake ta sai ta yi shuru ban da kuka ba abin da take yi, yi take yi kamar zuciyarta zai fita, wani ɗaci na taso mata ɗacin an ci zarafin iyayenka a gaban idanuwanka amma ba ka da hurumin da za ka hana faruwan haka, miyan bakinta har kafewa ya yi saboda yadda zuciyarta ke tafarfasa.
"Ni ce na yi maka laifi ba iyayena ba. Ni ce baka so ba su ba, to kuma su me suka yi maka da za ka ci zarafin su?
Ummu ta faɗa cikin kuka mai ƙarfin da sautin shi yake fita sosai.
"Ka yi mini abin da za ka yi mini zan jure Habib, ka tozartani iya tozartawa ba zan taba mgana ba, amma ba zan jure jin maganganun cin fuska ko na ɓatanci ga iyayena ba, kar ka sake ban zagi naka iyayen ba kai ma ba ka da hurumin da za ka zagi nawa iyayen."
Tana magana yana mata dariya kamar ya ga wata mahaukaciya.
"Me suka yi mini kike tambaya na?
Tasowa ya yi zuwa gabanta ya durƙusa saitin kunnuwanta ya yi magana.
"Saboda sun haife ki, laifin su kenan a wajena."
Ya faɗa yana yi mata dariya, Ummu na tsiyayan hawaye tana kallon Habib tana jin son ta ji ta tsane shi, tana so ta daina jin ko da ɓurɓushin son shi a cikin zuciyarta amma ina, tunda ba ita ke da alhalin sarrafa zuciyarta ba har yau ba ta daina jin son Habib a ƙasan zuciyarta ba.
Miƙewa ya yi ya koma in da ya tashi ya zauna lokaci ɗaya yana faɗin" Tunda har tsohon ki ya bar mini sallahun in na gaji dake ne na dawo masa dake shi bai gaji dake ba, to a matsayin shi na Surukina mahaifin matar da na aura na more albarkatun jikinta ya zame mini kamar wajibi na cika umarninsa."
Kallon ban fahimce ka ba Ummu ke yi masa kamar idanuwanta za su faɗo kasa, ga shi suna masu zubar da hawaye.
Takardan ya jawo a gefen shi ya ɗora saman cinyarsa ya ɗora biron a kai lokaci ɗaya yana faɗin" Zan sake ki kamar yadda mahaifinki ya ɓukata, duk da ya ɗan yi gaggawa, da a ce ya jira da ni da kaina zan sako masa ke ba sai ya wahalar da kansa wajen zuwa ya bar mini saƙo ba."
Ummu Salma ta ji kanta ya sara, har ɗan dake cikinta sai da ta ji ya motsa saboda firgici da tashin hankali.
"Yanzu Habib sakina za ka yi?
Ummu ta tambaya muryanta cikin kuka kamar za ta shiɗe.
"Kina tantama ne? Bari na rubuta na ba ki ki karanta sai ki samu tabbaci "
Kawai sai ta ga ya fara rubutu da sauri ta rarrafa gaban shi cikin kuka tana faɗin" Don Allah Habib ka yi hakuri kar ka sake ni, don Allah ka taimaka mini ka rufa mini asiri ka da ka sake ni."
Take faɗa tana wani irin gunjin kuka, ga ta duke kan gwiyoyinta tana mai zubar da hawaye tana haɗa shi da Allah akan kar ya sake ta.
"Ai abin da tsohon ki ya bukata ne, duk da nima ina da niyyar yin haka amma ba yau ba."
Ya faɗa yana nuna halin ko in kula, yana ma ƙoƙarin cigaba da rubuta abin da ya fara.
Da sauri Ummu ta faɗa kan kafafun Habib ta riƙe shi gam tana wani gunjin kuka.
"Ke miye haka?
Ya faɗa yana fizge kafarsa har tana yin gefe amma ba ta haƙura ba sai da ta sake riƙo kafafunsa da karfi ta rumgume a ƙirjinta lokaci ɗaya tana faɗin.
"Na tuba, don Allah ka yi haƙuri Habib kar ka sake ni."
"Wallahi sai na sake ki, mutuwa ce kawai za ta hana na sake ki, itama sai in yanzu ta zo ta ɗau raina amma in dai ina raye a yau zan yada ƙwallon mangwaro na huta da guda."
Ya gama faɗa yana sake fizge kafafuwanshi ya ɗora saman kujera ya bar Ummu duƙe a gaban shi tana wani irin kuka kamar za ta shiɗe.
"Habib in ka sake ni ina zan je? Wa zai sake kwasa ta? Wa ye zai iya aurena bayan ba ni da komai. Don Allah ka rufa mini asiri kar ka sake ni, kar ka manta da gudan jinin mu dake rayuwa yanzu haka a cikin jikina, kar ka bari ɗan mu ya rayu ba tare da kai ba, ka yi haƙuri don Allah ka rufa mini asiri "
Majina har zuba take yi a ƙasan cafet saboda kukan da Ummu ke rusawa amma ina Habib ba ya sauraranta rubutu kawai yake yi.
"To na ji , wallahi zan yi duk abin da kake so. Na ji zan. Zan zubar da cikin."
Ta faɗa cikin fitan hayyaci, har muryanta na dishewa saboda kuka.
Ganin ya ɗago yana kallon ta, ya sa da sauri ta sake rarrafawa gaban shi tana rawan bakin faɗin " Da gaske na ji zan zubar da cikin in har zan tsira da aurena."
Take faɗa cikin fitan hayyaci, domin ba ta ji ba ta gani, tunanin ta hangenta shi ne in Habib ya sake ta ya gama lalata mata goben ta, ya cuceta ya mai da ita ƙaramar bazawara, sannan tana son shi tana son aurenta za ta yi komai domin ta ga ta tsira da aurenta.
"Kika ce me?
Ya tambaya yana mata wani kallo
"Na ce, e zan zubar da cikin wallahi na yarda."
Ta faɗa hawaye na kwaranyo mata yadda ya ga ta ruɗe ne tana roƙon shi har tana cewa ta yarda za ta zubar da ciki ya sanya shi nishaɗi ya kwashe da wata dariyan jin daɗi.
"Na yarda ko yanzu ne ma mu je a zubar amma don Allah kar ka sake ni "
Ta sake faɗa tana haɗe hannayenta waje ɗaya alamun roƙo.
"Yarinya kin makara."
Ya faɗa yana dariya sannan ya cigaba da rubutun sa.
"Wataƙila da wata ɗaya kafin yanzu ne kika ce mini haka da zan iya sauraran ki, amma yanzu lokaci ya kure miki, da man ai na sha faɗa miki sai kin yi nadama, a ranar da nadamar ba za ta yi miki amfani ba lokacin da na ke bin ki, kina mini yadda kike so ai ba ki yi tunanin rana irin ta yau za ta zo ba, duk ɗaukan maganganuna kike yi a wasa?
Ummu ta kasa magana ban da kuka ba ta komai.
Ɗagowa ya yi yana kallon ta kafin ya cigaba da faɗin" Ni yanzu ban damu da ki zubar da cikin jikin ki , ko ki zubar ba ko ki haife shi duk wannan ya rage na ki, dake da cikin duka bana so, ba na kuma buƙatar ku a cikin rayuwata "
Ya ƙarishe faɗa yana nuna ta da yatsa daga sama har ƙasa cikin ƙyama.
Ummu ta gigice ta sake fashewa da kuka tana faɗin" To ba ka ce jikina kake so ba? To ai ga jikin nawa ai ba na hana ko?
Ta faɗa tana yi kamar za ta haura a saman kujeran da yake zaune.
"Ke kar ki hauro mini nan"
Ya faɗa yana zare mata ido.
"To to na zauna "
Ta faɗa lokaci ɗaya tana zaman dirshan a gaban shi yanayinta kawai za ka gani ka fahimci ta rasa natsuwarta ba ta ma san abin da take yi ba, ballantana abin da take furtawa.
Ganin ta cikin wannan yanayin yafi masa komai daɗi, nishaɗi da farinciki yake ji da man ya ce sai ta yi nadama to kaɗan ta gani.
"Ai ni gama moran duk wani albarkatun jikin ki, babu wani sauran maiƙon da ya rage da ban gama lashewa ba."
Ya faɗa yana dariya ƙasa-ƙasa har yana kashe mata ido ɗaya.
Ummu na kuka tana kallon Habib kamar zai yi mata gafara tana rokon shi Allah da Annabinsa kar ya sake ta, amma ina bai ƙara sauraran ta sai da ya gama rubuta abin da ya yi niyya sannan ya miƙa mata , ta kasa karɓa lokaci ɗaya tana girgiza kanta cikin kuka.
"Karɓi mana "
Ya faɗa yana mai sake miƙa mata takardan.
"Don Allah Habib. Kar ka. Sa ke ni."
Ta ƙarishe faɗa kamar za ta shiɗe domin har numfashinta ya fara ɗaukewa.
"Ai na ma riga na sake ki Ummu Salma."
Zuciyarta ta tsinke, idanuwanta suka fara rawa, hannaunta ɗaya ya kama ya tusa mata takardan lokaci ɗaya yana faɗin" Tunda dare ya yi na yi miki alfarman ki kwana amma gobe da safe ki tattara kayanki ki koma gidan ku, kayan ɗaki kuma suma ki zo ki kwashe kafin masu gidan su bukaci dakin su."
Yana gama faɗin haka ya kwashi takardansa da biron sa ya wuce yana sake faɗin" Alhamdulillah."
Har yana wani harba ƙafafuwansa, Ummu ta bi shi da kallo cikin zubar ƙwalla takardan ta matse a hannunta tana sakin kuka da ƙarfin iyawanta, kuka ta fashe da shi da duka muryanta da ubangiji ya ba ta, kanta a ƙasa kamar tana sujudda take rusa kuka kamar ranta zai fita Habib ya gama tozarta, irin tozarcin da bata taɓa jin labarin an yi ma wata mace ba, Habib ya sake ta da ƙaramin ciki bayan ya gama lalata mata rayuwa ya mayar da ita ƙaramar bazawara, ya kunya ta iyayenta ya cutar da ita sannan ya cutar da zuciyan ta.
*
Yana shirin barin ɗakin a karon farko Ummu ta yi magana.
"Ba z.. zan sha ba."
Ta faɗa cikin dashewar murya.
"Ko kaɗan ki sha Ummu"
Baɗɗo ta faɗa tana kallon ta.
"E ko kaɗan kin ji?
Hamma Saddam ya sake faɗa domin a yadda bakin ta ya bushe ya tabbata ma cikin ta a bushe yake.
"Na ce ba zan sha ba. Ba zan sha ba don Allah ku ƙyale ni."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana kecewa da wani irin kukan, muryanta ma baya fita sosai.
"Zan mutu, ina ji kamar zan mutu zuciyata ke zafi ciwo take yi.."
Haka ta faɗa tana nuna saitin zuciyarta cikin kuka.
"Zuciyata na zafi, ji nake yi kamar na kashe kaina."
Ta faɗa cikin kuka kafin ta fara buga saitin zuciyanta da hannu tana wani irin kuka da gudu Baɗɗo da Hamma Saddam suka yi kanta suna riƙe ta amma kamar an ƙara mata karfi tana fizge kanta tana kuka tana faɗin su bari ta kashe kanta, hayaniyarsu ya kawo su Ammah ɗakin ganin abin da ke faruwa ya sa ke raunana Ummin ikki ta fara kuka ita kuma Ammah ta fita tsakar gida da sauri domin ta kira Baffa sai suka ci karo da juna
"Me ke faruwa ne! Na ji kuka?
Ya faɗa cikin tashin hankali.
"Ummu ce ke kuka tana faɗin za ta kashe kanta."
Ammah ta faɗa cikin rawan murya.
"Innalillahi wa'inna alaihirraju'un."
Ya faɗa da gudu yana faɗawa falon Ammah. Daidai lokacin da Hamma Abdulrrahman ya shigo tsakar gidan da sallama. Lokacin da ya ga saƙon Hamma Jibo fitowar shi kenan daga wata sharia da ya jagoranta. Shi da man ya san sai an zo wannan matakin.
"Ammah"
Ya kira sunanta ganin ta cikin wani yanayi.
Tana ganin shi ta nufe shi da sauri.
"Abdulrrahman."
"Ammah"
Ya amsa yana kallon ta cikin mamakin ganin yanayin ta.
"Ummu Salma ce."
Ido kawai ya sakar mata yana kallon ta.
"Tana ciki tana kuka wai za ta kashe kan ta."
"Za ta kashe kanta?
Ya maimaita cikin mamaki.
Sai Ammah ta gyaɗa masa kai, goshinta har yana tara zufa saboda damuwa da firgici.
"Mu je na ganta. In ta fasa kashe kanta saboda wani banza ta ci ubanta."
Ya faɗa yana yin gaba zuwa cikin falon Ammah cikin fushi da fusata. Saboda wani banza sakarai ne za ta zo tana yi ma mutane sakarci in ta fasa kashe kanta ta ci bura uban ta in ji shi Abdulrrahman Hadi Baba, in ba ta kashe kanta ba ta ci uban ta.
*
So take yi ta daina jin zafin da ke ji a cikin zuciyanta.
So take yi duk wani damuwarta da take ji ta daina jin su, so take yi ta bar duniyan nan ko za ta samu yar salama.
Amsar kuwwan Kalaman Shamsiya sun kasa barinta ta huta, sun saka ta jin gwara kawai ta ji shuru gwara ta sama ma kanta natsuwan zuciya.
Miƙewa ta yi tana layi ta isa gaban madubi ta ɗauki reza sabuwa a cikin kwalinta ta buɗe. Rezan ba na ta ba ne na Ammah ne kwali ɗaya take siyab itama shekaranjiya cizgiya ne ya fito mata a gefen hannunta sai ta yi ma Ammah magana ta bata, bayan ta cire sai ba ta mayar mata ba sai ajiye a saman madubin ɗakin.
kallon kanta take yi a madubi tana tunanin yanzu rayuwarta ba ta da amfani hijabin jikinta ta cire ta na kallon cikin jikinta.
Ba amfanin ta haifa ma Habib yaro ko yarinyar dake cikinta domin bai cancanta ba, yadda zuciyanta ke zafi ne take son kawai ta hutar da kanta.
Ba tare da tunanin komai ba ta ciro rezan ta daidaita tsitsiyan hannunta na hagu za ta yanka lokaci ɗaya tana mai runtse idanuwanta hawaye na wanke mata fuska, sai ƙaran vibration ɗin wayarta ya dakatar da ita wayar na kan madubin ne, idanuwanta na ganin duhu amma sai da ta ga sunan mai kira, Sisna Baɗɗo ce take kiranta a lokacin da ba za ta saurare ta ba, a lokacin da ba za ta iya amsa wayarta ba.
Tana mai zubar ƙwallah wasu na fitowa wasu na ƙoran wasu ta sake daidaita hannunta
ta yanka sai ga jini ya tsartsu, ta runtse ido tana jin wani irin zafin azaba na ratsa ta daga ƙafafunta har saman ƙwaƙwalwarta.
Sake yanka hannun nata ta yi a karo na biyu jini ya sake tartsuwa, ta sake runtse ido sabo da azaba mai raɗaɗin da ya dabaibaye jinta da ganinta tana gani jininta na zuba a kan madubi yana gangarawa a kasan cafet da gudu kamar an buɗe famfo.
Azaba take ji amma kuma tana jin daɗi yanzu za ta daina jin abin da take ji a cikin zuciyanta. Gwara ta mutu in ta mutu za ta huta.
Tana mai kallon kanta a madubi tana hawaye ta fara ganin kanta biyu biyu kafin ta ji jiri ya kwashe ta, ta yi baya ta dafa gado amma ina ya rinjayeta, tuni idanuwanta suka hau lumshewa jikinta ya saki da ta kasa iya riƙe kanta
nan ta sulale ta faɗi kasa ta gefen hagu.
Hannunta kuma har a lokacin bai daina zubar da jini ba, ga rezan da ta yanka kanta nan a yashe a gefen ta
Ta ji daɗi domin jinta da ganinta ya tsaya cak zuciyarta ta daina aiki ta daina jin komai ta samu salaman da ta ke fata.
Ta ji ɗif, ta samu natsuwa ta samu hutun da zuciyarta yake muradi.
*#Labarin Soyayya*
*#Zamantakewar Aure*
*#Zalunci*
*#Cin Amana*
*#Zumunci*
*#Kishi*
*#Sarauta*
*#10/04/2026*