#BAITA
by @ummyz
HUKUNCI!
3_4
Cikin zafin nama tajuya kai tsaye ruwan ya kware mata agadon baya tafasa ƙara saboda azaba,ita kuma Linda ta tsaya tana hararenta tace ubanme namiki zaki mareni?.
Cije baki tayi tajuyo a fusace ta cakumeta itama cafkarta tayi suka fara naushin juna saboda a tsaye Linda takusa biyunta daka kalleta kaga rainon doya duba da yadda take faskekiya kasan zatayi karfi ba amma haka sukaci gabada kokawar kafin Allah yabata Sa'a takafa mata haƙora a gefen wuya tariƙe gam taƙi saki duk yadda lindar keyimata dundu a gadon baya amma kamar ba dukanta takeba.
Saida azaba ta ishi lindar sananne tafasa ihu tana kiran Jesus Christ amma shiru babu wanda yashigo saboda babu kowa a arean sai Habib shikuma baccin shi yafara nauyi,cigaba tayida ƙoƙarin ƙwatar kanta amma yadda kasan aikin Aljannu takasa gashi tanajin azaba sosai dole sai ihun tacigaba dayi tana kiran Jesus.
Saida Ruth data fito ɗaukar wayarta data manta falon sanan taji kururuwar Linda da kukanta harta ɗauki wayar tayi tsaye takasa cigaba da tafiya kuma takasa baya saboda mugun tsoron daya ziyarce ta yadda takejin ihun Linda cikin wanan tsohon daren,cikin sauri ta matsa kusada Habib dake kwance tumbur tafara kiran sunan shi tana bugun kirjinshi cikin tsoro jikinta narawa.
Farko lalubeta yafara amma tadoke hannunshi tana faɗin Habib wake up Aljannu. Sakinta yayida sauri yana faɗin mene? Waro ido tayi tana lalubo wandon daya cire tajefa mishi tana sake maimaita mishi abinda tafaɗa cikin rawar jiki har yanzu saboda jin Muryar Ruth daya farayin ƙasa saboda wahala.
Cikin mutuwar jiki yasaka wandon yatashi yanufi hanyar kitchen ɗin dayake jiyo kukan itama ruth nabiye abayanshi sai ƙarawa idonta girma take tana kama hannunshi, yana shiga kitchen ɗin yayi mutuwar tsaye Saboda ganin yadda tahaye Linda duk girmanta kamar wata Aljana.
Ranshi wani irin ɓaci yayi afusace yakira sunanta
"KHADIJAH!"
dirar muryarshi cikin kunenta ne yasata dakata kamar wacce tadawo cikin hankalinta yanzu tafara rage ƙarfin riƙon datayiwa Linda tajuyo Ahankali tazuba musu idanunta da sukayi jawur bakinta duk alamar jini.
Riƙeshi qam Ruth tayi cikeda tsorata hannu yasaka yazare nata data qanqameshi yafara shiga kitchen ɗin daidai lokacin da Linda ta tattaro ragowar ƙarfin daya rage mata ta hankaɗota ƙasa goshinta yadoki tiles da ƙarfi.
Kamo Linda yayi yasaka jikinshi yana tambayarta "are you ok?"Kai taɗaga mishi a wahale tana kallon Deejah da tunda tafaɗa ƙasan batayi motsi ba aranta tana faɗin saita ɗauki fansar wanan cizon datayi mata bazai tafi a banza ba.
Sake Jinjina mishi kai tayi tana dafe wuyan ta sosai cikin lokaci kaɗan duk tafita daga hayyacinta,kallon Ruth yayi yace jekiyi mata dressing ina zuwa. Yana gama maganar ya tunkari Deejah dake yashe yafara zare belt ɗin dake jikin wandon yana naɗashi a hannunshi cikin fushi sosai batare da tausayawa ko makamancin shiba yafara zuba mata belt ɗin a tsakar baya saboda akife take.gwauron numfashi taja sau ɗaya tasake kifewa kunnuwanta nayin dif tadaina gane meke faruwa acikin duniya.
Saboda zuciyar tariga ta ƙeƙashe yasa bai kulada yanayin datake cikiba yaci gabada laftarta Saida yayi mata ruɗu ruɗu sanan yayi jifada belt ɗin yafice daga kitchen ɗin tana faɗin gobema kya ƙara matar ƙadara kawai!
Yana barin kitchen ɗin yakoma ɗakin shi acen yatarar dasu har Ruth dagama yimata dressing sauke numfashi mai zafi yayi batare dako sake kallonsu yayiba yazare dogon wandon yafice daga jikinshi yazama dagashi sai hallitar jikinshi yayi jifada wandon tsakar ɗaki yawuce Bathroom yana tafiya cikeda taƙama da izza,duk da kallo suka bishi tunba linda ba da duk lahin datake ciki Saidata matse ƙafa gam saboda kallonshi data shagala wajen yi.
Hararenta Ruth tayi a fakaice ta ɗauke kai, bai daɗeba yafito saidai yanzu yaɗan saƙala ƙamarami towel a iya ƙugunshi ya tsaya gaban closet ɗin yaɗauki 3qtr yazura bayan yazame towel ɗin yana tsane ruwan gashin shi.
Linda mancewa tayida wani ciwon wuya ta taso tana karairaya da jijjiga nono tashige jikinshi tabaya tana kiran sunan shi,baki sake Ruth tariga Binta da kallo kamar sakarya, dayake shima a wuya take dama kuma bai iya fushi ba juyowa yayi ya hankaɗata gefe yana huci yafara nunata da yatsa kamar zaikai mata hannu yace “kefa jarabar tsiya ke gareki idan ba iskanci ba aikinsan idan na kwanta da mace biyu adare ɗaya bana buƙatar ƙari ko?
Badan kan sopa tafaɗa ba dasai jikinta yakuma faɗa mata,wani guntun dariya Ruth tayi tana gyara kwanciyar ta saman hadaɗɗen gadon ɗakin shi tana danna waya.
Deejah kuwa ahaka ta kwana itaba mai raiba itaba matacciya ba,babu wanda yakuma bi takanta Saida Asuba Allah ya taimaketa ta farka da azababben ciwon kai mai tsanani tana buɗe idonta da ɗayan yaɗan kumbura suka sauka akan belt ɗinshi dake kusada ita da sauri ta ɗauke ido jikinta na ɗaukar karkarwa tafara jan jiki tafar kitchen ɗin tanajin inama zata iyayin kuka amma babu hali hawayen ma nata kamar sun ƙafene jkinta babu inda baya ciwo ga kumburi da hanunta ɗaya yayi, adaddafe tawuce bathroom ta haɗa ruwan ɗumi tashiga ko rigar jikinta bata cireba jitakeyi jikinta yazama kamar banata ba.
Adaddafe tayi wanka da Alwollah tafito tana haɗa hanya da ƙyal ta iya janyo Abaya tasaka batare data saka inner ko ɗaya ajikinta ba saboda saboda koyaya abu yashafi jikinta ciwo, azaune tayi sallar asuba sai lokacin tasamu kuka yazo mata tahaɗe kanta da gwuiwa tasha kukanta sosai kukan da batada mai lallashinta ko rungumeta tayi ajikinshi wani irin kewar Ammaah takeyi sosai saidai inda zata ganta shine babban aiki.
Bayan tagama kukan tashi tayi taje tarufe ƙofar ɗakin tabar key ajiki saboda tasan babu jimawa habeeb zai iya zuwa yasakata yimusu breakfast ita kuma yadda takejin jikinta koda wasa bazata iya motsashi sosai ba.
Kamar yadda tayi zato wajen 9 lokacin har bacci yajima da kwasheta tajiyo bugun ƙofar da ƙarfi yana kwalla kiran sunan DEEJAH, "Ya rab" shine abinda ta iya faɗa tana tashi zaune akan gadon.
"Deejah" kamar bazata amsaba tayi shiru amma kuma jin yadda yake kiranta yasa tace na'am tana saukowa daga saman gadon ahankali ta isa gaban ƙofan batare data buɗeba tace mishi gani.
Wanan time ɗin Muryar tashi babu hayaniya ko ɓacin rai aciki yace “Deejah Am felling hungry sosai rabona da abincin Tun jiya kifito kisamamin abinda zanci kinji beb.
Jitayi kamar tadoka mishi tsaki saboda ganin shi damuwar shima ta abinci ne harya manta dukan dayayi mata kamar wata jaka itaduk ba wanan yafi ɓata mata raiba kamar yadda yake shigo matada karuwai a cikin gidanta na Aure. dannar zuciya da harshenta tayi tace “Habeeb banada lafiya kuma kaima kasani tunda kaine sanadi bazan iya shiga kitchen ba after all banada gas kuma bakayo reffiling ba”.
Ɗan jim yayi cikin rashin jindaɗi yace jikin naki nayin ciwo sosai ne?,kukan datake riƙewa tasake mishi saboda jin tambayar dayake mata.
“ Deejah” kasa Amsawa tayi taci gabada kukanta tana jingina jikin ƙofa.
Ya isa daina kukan bari naje nasama mana abinda zamuci Nasan kema kinajin yunwa ko?.
Banza tayi dashi taci gabada kukanta kawai,shima jin bazatayi maganar ba yasa yajuya ɗakinshi yaɗauko car keys yajawo ƙofan saboda tunda safe yakaɗasu Linda bayan yasake ƙwaƙulesu tas.
Bata fito ɗakin ba Saida taji yadaɗe da fita sanan tafito jikinta yayiɗan dama dama kunne tafara kasawa taji idan zataji motsin kwaratan nashi amma taji alamar basu gidan,haurawa tayi tabuɗe ɗakin shi ahankali ta leqa nanma taga basunan sanan ta shiga cikida kyau idonta na sauke kan farin bedsheet ɗin da sukayiwa kaca kaca, ga gefen gadon duk ledojin condom da kayan habeeb yashe awajen baki ɗaya ɗakin a hargitse yake dafe stoll tayi gamgam tana maimaita “La'ilaha illallahul Azimul Halim,
La'ilaha illallahu Rabbul arshil Azim
La'ilaha illallahu Rabbus samawati wa Rabbul ardi wa Rabbul Arshil Karim” haka tacigaba da maimaitawa har Saida nutsuwarta tafara dawowa amma jitayi wallahi bazata iya ɗauke ko tsinke a wajen ba damata lallaɓane tashigo idan basunan ta lallaɓa ko sharane tayi mishi tunda tasan itace maiyi dole.
Saukowa tayi ƙasa tanajan jiki tanufi kitchen tahaɗa tea, a kitchen ɗinta zauna tasha sanan tafito tana neman wayarta datun jiya rabonta da'ita da ƙyal taganota gefen Center table ta tarar da miss call ɗin Surayya kusan guda 4.
Wucewa tayi ɗakinta ta zauna sanan tayi flashing ɗinta saboda batada isasshen credit,bugu ɗaya ana biyun tayi picking tana faɗin smolly ina kika ajiye waya tun ɗazu nake nemanki kwana biyu banji motsin kiba?.
Cikin raunin murya tace “surayyah"
"na'am"
kidaina cemin smollyn nan kinji gabana faɗuwa yake sosai kamar zuciyana zaifito.
Cikin ƙoƙarin kwantar matada hankali tace to shikenan yawuce yanzu yakike? Ina fatan komai yafara daidaita kamar yadda aka fara?.
Duk yadda tayi ƙoƙarin dannewa kasawa tayi saboda Surayya bata layin mutanen dazata iya ɓoyewa damuwarta take suka kashewa su binne asiri rufe basa ɓoyewa juna damuwar datafi ƙarfin zuciya. Cikin rawar murya tace “Surayya dan Allah yaushe zakizo wallahi zuciya tana neman bugawa narasa mekemin daɗi yanzu haka jikina babu inda baya ciwo saboda dukan da habeeb yayimin” tayi maganar hawaye na sauko mata sosai kukan datake ƙoƙarin dannewa na bayyana.
“DEEJAH”
Bata amsaba taci gabada kukanta Saida Surayya tasake kiran sunanta cikin sanyi sanan taja hanci ta amsa. Kinsan abinda nakeso dake DEEJAH kiyi haquri yanzu dai kidaina wanan kukan babu abinda zai ƙaramiki sai damuwa da ciwon kai kiyi haquri babu auren da bayada ƙalubale duk ma'auratan dazaki gani dakwai matsalar dasuke fuskanta a zamantakewar su.
Amma tawa ƙaddarar tayi zafi dayawa Surayya, wallahi nafara gajiya da rayuwar duniyar nan wallahi duk soyayyar danakewa habeeb da kishin shi zanyi farin ciki ace Aure yaƙaro yakawomin mace agidan nan da'ace yana shigowa da ƙaruwai koba komai nima zanfi samun salama da kwanciyar hankali, ban saniba kodan yaga banada kowa banada gata yasa yakemin hakaba ko kuwa soyayyar dayakemin ce tarikiɗa Takoma ƙiyayya.
" DEEJAH karki kuma faɗin bakida gata kinji ko kece kikeda gata tako ina, kalmar haƙuri nada tsananin girma da ɗaci amma ki daure komai zai wuce da izinin ubangiji, Allah bazaibar haqurin ki ya wulaƙanta ba! Idan Allah yakaimu anjima Abbansu khairi yadawo zan lallaɓashi yakawoni gidanki kicire damuwa daga zuciyar ki kinji.
DZ CARE HOSPITAL
(Your Health,Our Priority)
Babban private hospital ne dakeda 3 floor dasuka sake faɗaɗa ginin dawani iri kyau da tsari mai ɗaukar hankali babu hayani ko kaɗan sai nurse's dake gudanar da Aikinsu cikin tsari da kwarewa duk da darene amma ko'ina fes yakeda hasken fitulu daya sake ƙawata hospital ɗin kamar rana
Ƙarfe 8:12 PM yashiga hospital ɗin kuma tunda yashiga babu wanda zaice yaga fitowar shi tunda yashiga.
Cikin nutsuwa yayi parking a parking lot sanan yafito cikin nutsuwa lokaci zuwa lokaci yanaɗan gaisawa da jefi jefin nurse's dayakan haɗu dasu kafin yashiga Elevator lokaci zuwa lokaci yakan duba wayarshi kafin ta tsaya yabuɗe yafito floor 3 gaban office ɗin dake ɗauke da tambarin d sunan DR ZAYD BAITA.
Hannu yasaka yatura glass door ɗin yashiga yana mayarda wayar Aljihu ya kalli wajen dake Kamar ƙaramin falo mara hayaniya sanan ya isa gaban ainafin ƙofan office ɗin yashiga da siririyar sallama batare dayayi yadda zai takurawa na ciki ba.
Ɗagowa ɗaya yayi ya amsa mishi sallamar batare daya bashi second look ba yamayar da hankalin shi wajen sarrafa system dayake cikin ƙorewa lokaci zuwa lokaci yana buso numfashi mai ɗumi daga bakin shi ta hanyar fitar sautin shi.
Zama yayi kujeran dake facing dinshi yaɓata fuska yana faɗin “BAITA”ganin yadda yaƙi kulashi kamar bashine yatakura mishi sai yazoba.
Sake ɗago dara daran fararen idanunshi da launinsu yaɗan koma jaja yayi yaɗora mishi yana ɗaga gira ɗaya alamar mene?.
Ɗauke kai yayi daga kallon dayake mishi yace kiran me kakemin ZAYD, haka kawai ina zaune gida cikin iyalina ka tasoni ka katsemin jindaɗi kuma kaƙi kayi magana kodai natashi nakoma.
A ɗan ƙufule ya kalleshi yanuna mishi ƙofar daya shigo da hannu, ɗayan hanun kuma yaɗora saman soft lips ɗinshi yana shafawa hankali yana yimishi kallo mai kamada harara.
Ƙin tashi yayi yace BAITA meke damunka?ciwon kan ne?. Ahankali ya jinjina mishi kai sanan yace kazo ka kaini gida I’m unable to drive myself.
A rikice HAYAT yatashi tsaye sai kuma yakoma ya zauna cikin rauni yace Innnalilahi Did you take the medicine ZAYD? This time harara ta gaske yayi mishi yana ɓata fuska yace miye kakemin kamar wani baby Haa'aan Look at me carefully ƙato dani kakeyiwa wanan silly questions ɗin kamar wani Affan bayan da inada rabo da yanzu nadaɗe da zama Papa. Yayi Maganar ƙarshe cikin wani sanyi da ɗaci dan Muryar shi harta soma canjawa ta hanyar yin rauni sosai.
Tashi hayat yayi batare dayabi takan maganar ƙarshe dayayi ba yazagayo wajen kujeran dayake zaune yarufe system ɗin yana ɓata fuska yace “BAITA Kanada damuwa wallahi you’re a doctor, right? Amma sam baka damu d lafiyarka ba gakada raki kamar mace ciwo kaɗan yasaka narke, tashi muje na ajiyeka gida karkabar Farida cikin tunani, kuma wallahi kasani saina haɗaka da Ammaah indai baka natsu kasha magani ba, haaba.
Murmushi mai taushi daya bayyana jerarun fararen haƙoran shi tas tas yayi yanaɗan cije lips ɗinshi na ƙasa kaɗan yamiƙe yana tattara kayan wajen gefe yace“to Baba hayatu za'a gyara nidai muje kaina ciwo sosai”.
Yayi maganar lokacin dayake fitowa tsakiyar office ɗin yana zame rigar suit ɗin dake jikin shi light Ash yariƙe a hannu yayi saura dagashi sai wandon suit ɗin da farar long sleeve ta ciki tattara kayan wajen hayat yayi yamiƙa mishi wayarshi daya bari wajen yana faɗin we shall go kosaina kamaka?.
Bai kulashi ba kawai yafice cikin tafiyar shi marar garaje ƙaƙƙarfan jikinshi na buɗewa.