2
*BAYAN AURE*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 2.
Sarac Stars R Pen...✍️
Ɗakin uwargida Fatsime suka fara shi ga, nan tayi mata nata faɗar tare da yayyin Hamida mata da suka zo bikin, bayan sun gama sai suka isa ɗakin mai bima Uwargida Inna Zainaba, itama tayi nata faɗar kafin suka fito suka shiga ɗakin kakarsu wato mahaifiyar babansu, ita kasa yi mata faɗan ma tayi sai kuka. Dama matan baba su uku ne Fatsime ita ce babba yaranta guda shida mata huɗu duk sunyi aure sai maza biyu sune suke gabanta, Inna Zainaba ita ce mata ta biyu yaranta biyar maza uku mata biyu, itama duk matan sunyi aure namiji ɗaya ma ya yi sai biyu ne ke gabanta, mama Hajjo ce amarya yaranta uku, Hamida ce babba sai Yusuf sannan auta Jafar wanda da cikinsa baba ya rasu ya bari, shiyasa da ta haihu aka saka masa sunan baba suna kiransa da Babangida.
Da suka fito daga ɗakin kaka sai suka fita zuwa gidan ƙanin baba autansu mai suna Musa, maƙota suke dan lokacin da zai yi auren farko baba ya yanka masa fili daga cikin gidansa ya sayar masa ya gina, yanzu matansa biyu da yara takwas, uwargida tana da yara biyar amaryar kuma uku, haka suma suka yi wa Hamida faɗa da fatan alheri kafin suka dawo cikin gidan a lokacin kuma aka fara kiran sallar isha'i.
Sai wajen ƙarfe takwas da kwata abokan ango suka zo ɗaukar amarya, haka jerin gwanin motoci suka yi dafifi a ƙofar gidan Marigayi Malam Jafaru, ga kuma mutane sun yi cirko-cirko suna jiran damar da zasu samu shiga cikin motocin dan kai amarya Hamida, dan kusan kowa so yake yaje yaga irin daular da ta samu. Bayan dangin ango sun gama gaisawa da mutanen cikin gidan tare da aje musu kaɓakin abincin biko, ba ɓata lokaci aka basu amarya suka fito suka shiga mota, ƙananun motoci takwas suka kawo ɗaya dangin ango suna ciki sauran kuma dangin amarya ne suka shiga, waɗanda basu samu mota ba kuma suka shigo damuwa tare da alwashin In Allah ya kaimu gobe da wuri zasu dira gidan amarya. Haka suka wuce babu wani hayani kamar ba amarya aka ɗauka ba, duk da wasu daga cikin dangin Hamida sun cewa direbobin ayi wasa dasu, amma basu kula su ba duba da su ɗin suna da dattako ba irin samarin nan ne masu rawar kai ba kuma suna da ilimi da wayewar zamani, daga nan Tudun Wada Layin ƙosai minti talatin ya kai su unguwar rimi duba da babu yawaitar abun hawa saboda dare. Motar farko ta tsaya a ƙofar gidan Hafiz ya buga hon, maigadi ya buɗe gate ɗin duka saboda yasan da zuwansu, wasu suka shiga ciki suka fara parking, wasu kuma a waje suka tsaya duba da girman farfajiyar gidan ba zai ɗauki duka motocin ba, duk mutane suka fito aka wuce babban ƙofar falo, 'yan uwan Hamida sai ƙus-ƙus suke yi duba da irin tangamemen gidan sama da aka kawota, wasu kuma suna faɗin Masha Allah cike da tsantsar murna, goggo Larai ce take riƙe da hannun Humida suka isa ƙofar falo ta kama handle ta murɗa amma ta ji a rufe, sai ta soma bugawa amma zuwa wasu mintuna shuru ba a buɗe ba, goggo ta juyo tana cewa.
Jamila ko zaki yi magana da abokan ango su bamu key kamar ba mutane a cikin gidan.
Amma kuma Hafiz ya sanar damu anty Laila tana nan.
Cewar Suhaima Ƙanwar Hafiz, Inna Jamila tace.
To abun da mamaki, amma je ki yi musu magana in da key a buɗe mana kawai mu shiga, dan an bar mutane a tsaye.
To tace ta juya gurin Jamil abokin yayanta ta sameshi ta faɗa masa cewar ƙofar falo a rufe yake Kuma an buga ba a buɗe ba, sai yace cikin mamaki.
Ba a buɗe ba kuma.? amma ai Laila tana nan. Bari na kira Hafiz nasan ma sun kusa ƙaraso wa dan yace yanzu zai zo ayi siyan baki a sallami kowa.
Ya ƙare maganar yana ɗaga wayarsa ya dannawa Hafiz kira, bugun farko ya ɗauka yana cewa.
Yaa Jamil kun ƙaraso ko.?
Eh muna cikin gidan yanzu haka, amma kuma Laila bata buɗewa mutane ƙofar falo ba, kuma a nata bugawa shuru, idan kuma bata nan ka ƙaraso ka buɗe ƙofar nasan ba zaka rasa key a hannunka.
OK bari na kirata naji, muna hanya yanzu haka gamu nan zuwa.
OK Jamil ya faɗa ya kashe wayar sai ya sanar da Suhaima ga Hafiz nan zuwa, haka ta koma ta sanar da su goggo Hafiz yana zuwa, sai kuma kowa ya yi jugum ana jiran tsammani waɗanda suka fara gajiya da tsayuwa suka samawa kansu gurin zama a gajerun dakalin da aka zagaye furannin cikin gidan, Hamida ma a dakalin corridor Inna ta ce ta zauna su jira.
******
HAFIZ.
Yayi matuƙar cika da mamaki akan wai ba a buɗe ƙofa ba, kuma ya san Laila tana gidan bata ce masa zata fita ba, sannan duk yinin yau suna maƙale da juna a waya yana ta kiranta dan ya kwantar mata da hankali, sannan ɗazun ya dawo gidan yayi wanka ya sauya kaya har ya same ta da baƙi a gidan, da zai tafi take tambayarsa da yaushe za a kawo amarya.? ya faɗa mata, suka rabu tana yi masa tsiyar ya ƙara kyau saboda shi ango ne, sai dai yayi murmushi bai ce mata komai ba ya fice dan lallaɓa ta yake yi kar ya faɗi wani abu yayi mata laifi. Ya sauke numfashi ya kira layinta amma a kashe, sai ya kira number Ƙanwarta Zahida, bugu biyu ta ɗaga tana cewa.
Yayanmu ango kasha ƙamshi.
Zahida wai bakwa ji anata buga ƙofar falo ne, ki je ki buɗewa mutane ƙofa suna jira, sannan ina Laila ta shiga.? na kirata waya a kashe.
Laaa yaya Hafiz wani gidan kake magana.? Ai tun kafin sallar magrib muka tarkato zuwa gidanmu saboda anty Laila ta kasa kwantar da hankalinta.
Kina nufin yanzu bakwa cikin gidan kenan.? Ina Laila, bata wayar.
Anty ai bata nan ta fita wani park ita da yara wai ko zata ji sauƙi a ranta, nima zanyi baƙo ne shiyasa ban bisu ba.
Shi ne kuma zata kashe wayarta, wai meyasa Laila zata yi min haka.?
Hafiz ya faɗa cikin gajiyawa ransa a ɓace, Zahida tace cikin ko in kula.
Yaya wayoyinta ba chargy a gida ta barsu har da power bank ɗinta.
Bai ce mata komai ba ya kashe wayar dan yasan wani iskanci Laila ta shirya masa, amma babu yadda za ayi ace wayarta ba chagy su da suke da wuta 24hrs, in nepa sun ɗauke akwai solar, sannan ko fita tayi tana tare da power bank ɗinta da yake kullun a cike, Hafiz ya kalli abokinsa Musa yace.
Kaji wai bata gidan tun ɗazu suka fita.
To saboda Allah shi ne ba zata bar ƙofar a buɗe ba, hakan bai yi ba gaskiya.
Dama tun ɗazu na kula da dariyar da take yi na yaƙe ne, sai dai ban kawo zata aikata wani abu ba, muyi sauri mu ƙarasa ni akwai key a hannuna.
Ya faɗa yana duba keys ɗin motarsa da ya haɗasu dana gidan, sai dai abun mamaki babu key ɗin ƙofar falo a ciki ya zare daga inda yake ya shiga dubawa amma babu, sai ya mayar ya duba Musa ya ce cikin murmushin takaici.
Laila ta ƙulla mini tsiya kaga babu key ɗin anan ta cire shi wlh, to amma ya ban gane abunda take shiryawa ba tuntuni.?
Taya zaka gano bayan baka yi zaton zata yi haka ba, ai dama na faɗa maka wannan shuru-shuru ɗin da tayi ba yana nufin ta haƙuri bane dan tana da zafin kishi. Gashi nan duk ƙoƙarin ka na son kyautata mata bai sa ta haƙura ba, ƙiri-ƙiri saboda ita kaƙi yarda a yi shagalin dinner da muka shirya maka.
Wlh kuwa, kaga saboda ita naki zuwa gidansu Hamida muyi hoton biki saboda yana cikin sharuɗɗan data gindaya mini, kuma na biye mata duk dan a zauna lafiya na faranta mata. Ina son Laila shiyasa nake yi mata komai saboda ta amince dana ƙara auren.
Hafiz ya faɗa zuciyarsa a cunkushe da damuwa, basu sake magana ba har suka isa gidan, a waje suka yi parking suka shigo ciki dan gate ɗin har lokacin a wangale yake, abokansa da suke jiran zuwansa suka nufoshi ya kalle su yana cewa.
Ina zuwa.
Sai ya wuce cikin gidan ya tsaya, 'yan rakiyar amarya suka taso zuwa gurin Hafiz, yace cikin dauriya.
Dan Allah kuyi haƙuri lalura ce ta taso na gaggawa shiyasa Laila ta fita cikin sauri ta manta ta rufe gidan, yarona ne ya ɓarke da gudawa sun tafi asibiti, yanzu zan je na amso key ɗin dan nawa na barshi a ɗakina ban fita da shi ba.
Nan ya ƙare maganar yana jan fasali, matan dake gurin suka shiga salallami da addu'ar Allah ya kyauta na gaba ya kawowa yaro sauƙi, sai dai ɓangaren danginsa sun san wannan magana da Hafiz ya yi ƙanzon kurege ne dan babu abunda ya samu ɗansa Khalil kawai dai zurfin wulaƙancin Laila ne da ta shirya, amma sai suka zaɓi yin shiru dan karsu ƙaryata ɗan uwansu, kuma ma a wannan gaɓar dole ne yayi abunda zai kare masa mutunci sannan kar su zargi da matsala a gurin matarsa. Hafiz ya amsa da Amin kafin yace.
Ina ganin zaku iya raguwa a mayar wasu gida dan kar kuyi ta jira, in ya so gobe In Allah ya kaimu sai ku dawo.
Nan take hayaniya ya tashi ga matan suna cewa zasu jira, ba haka Haifz ya so ba amma sai yace ba damuwa, amma su Suhaima suka ce ba zasu jira ba, nan suka yi sallama da dangin amarya suka fito suka shiga motar data kawo su suka wuce, abokan Hafiz kuma suka raka shi waje tare da tsayawa suna tattauna maganar, Musa yace cikin ɓacin rai.
Kun ga ɓata lokaci muke yi anan gwara mu san abun yi dare yana yi.
Haka ne bari naje gidansu Lailan na amso key.
Cewar Hafiz ya faɗa rai ɓace, sai ya nufi motarsa ya shiga Musa ya biyo bayansa ya zauna gefensa suka wuce gidansu Laila da yake Barnawa. Tafiya ce miƙaƙƙa dan akwai nisa, sauƙinsu ma dare ne ba cikowar abun hawa a titi shiyasa Hafiz ya shiga yin gudu dan suje su dawo kan lokaci.
Sai wajen ƙarfe tara da rabi suka isa unguwarsu Laila, bayan sun isa gate ɗin suka buga hon, sai ga wasu security sun fito su huɗu da bindigogi dan ganin waye ya zo, suna ganin Hafiz ne suka koma gefe suna kawo masa gaisuwa cikin ɗaga hannu, shima ya ɗaga musu hannu cikin murmushin yaƙe, a lokacin maigadi ya buɗe gate suka shiga yayi parking, sai Hafiz ya fito shi kuma Musa ya cigaba da zama a cikin motar, Hafiz ya wuce cikin gidan ya danna door bell, ba jimawa aka buɗe masa sai yaga ƙaninta Deeni yana washe baki, sai ya gaishe shi Hafiz ya amsa fuska sake.
Ina Laila.? suna ciki kuwa.?
Anty Laila bata dawo ba sun fita da yara.
Dumm Zuciyar Hafiz ta buga amma sai ya dake yace.
OK ina momy.?
Tana ɓangaren daddy dan har tayi mana sai da safe.
OK kira mini Zahida.
Itama bata daɗe da fita ba tare da saurayi ta zasu siyo ice cream.
Yanzu ba kowa kenan a gidan? To ɗauko mini jakar Laila wanda ta zo da shi.
Ayya bata bar shi a gida ba dashi ta fita.
Deeni ya faɗa yana yamutse fuska, Hafiz yayi shuru ya rasa me zai ce sai kawai ya juya rai a ɓace ya koma gurin Musa, Deeni ko da harara ya bishi ya rufe ƙofar yana murmushin mugunta, a lokacin Zahida ta fito daga kitchen in da ta ɓuya tana cewa cikin murmushi.
Ya wuce kenan.
Ya tafi amma wlh ya damu sosai dan a hargitse yake, amma me yasa anty Laila zata yi haka.?
Rabu da shi. Bari na faɗa mata ya zo.
Tayi maganar ta nufar saman bene zuwa ɗakinsu.
Hafiz daya ƙarasa gurin Musa cire hular kansa yayi domin gumi ne ya cika shi, sai yaji gabaɗaya babban rigar da yake jikinsa nauyi ya yi masa, dan haka nan take ya cire ya buɗe bayan mota ya aje su a seat, Musa ya fahimci komai dan haka yace.
Mu je mu san abun yi, imma ɓalle ƙofar za a yi sai a ɓalleta kawai.
Tafɗi! Ai wlh babu ɓalle kofar da za ayi haka kurum a jawo mini asarar kashe wani kuɗin gyara, kawai ina ganin ka kira Jamil ka faɗa masa su lallaɓa 'yan kawo amarya su mayar dasu gida, in ya so sai naje na kama hotel mu kwana da amayar zuwa safiya nasan Laila ta sauko sai na amsa key ɗin.
Hafiz ya ƙare maganar cikin damuwa, Musa ya ja guntun tsaki.
Wai sai yaushe zaka zama tsayayyen namiji ne a gidan ka.?Haba Hafiz kai ne kake auren Laila ba ita ce take auren ka, to taya ma zaka yi adalci a tsakaninsu kana shakkar ɓacin ranta, wannan maganar da kake yi ba mafita bace dan da ka kwana da amarya a hotel gwara a mayar da ita gidansu tunda ga uzurin daka bayar na rashin lafiya, babu wanda zai fahimci meke faruwa.
Musa ya ƙare maganar yana tsura masa ido, Hafiz ya nisa bai ce komai ba ya kira layin Jamil bugu ɗaya ya ɗaga yace.
Ango ya ake ciki ne.? mutanen nan fa da alama sun gaji dan har sun fara ƙananun magana.
Jamil ka sanar dasu jikin yaro yayi tsanani nima ina nan bazan iya zuwa yanzu ba, a mayar dasu gida ita kuma Hamida kace musu zaka kaita gidan Ummana, in ya so bayan sun tafi zamu zo yanzu sai na ɗauke ta da kaina na kaita gidan umma ta kwana a can.
Hmmm Allah ya kyauta.
Cewar Jamil rai a ɓace ya kashe wayar, sai ya juya zuwa ga sauran abokansu yayi musu bayanin abunda Hafiz yace, suma ransu ya ɓaci sosai suka shiga mayar da magana, Jamil ya wuce su zuwa cikin gida ya isar da saƙon Hafiz, kuma har ga Allah sun yarda da zancensa kuma sun tausaya sosai, dan haka dole suka amince a mayar da su, duk suka shiga mota sai Hamida ta miƙe tare da yaye mayafin fuskarta ta shiga rare kuka akan zata bisu, amma Inna Jamila ta shiga bata baki, da kyar ta haƙuri zuciyarta ba daɗi, tana kallo suka tafi suka barta ita kaɗai sai Jamil da yake tare da maigadi da ya rufe gate, ta koma jiki a sanyaye ta zauna a dakalin corridor cikin damuwa.
Rahma ce.
*Nasan akwai matan da zasu iya aikata irin abunda Laila tayi, to amma ku sani ba ko wani namiji bane zai ɗauki wannan iskancin domin maza a gabar zumudin zuwan amarya zasu iya yin komai, madadin ki musguna masa sai ki ƙare da amsar tikitin zawarci. Nasan wasu matan suna dauriya wasu kuma sai a hankali, amma abunda ke tsakanin haƙuri da rashinsa tazararsu kaɗan ne. Ku cigaba da bibiyana dan labarin nan zai tabo ko wani ɓangare cikin tsage gaskiyar abunda ke faruwa.*
Rahma ce.