SARTSE A ZUCI...!

SARTSE A ZUCI.....! Chapter 12

by @ayshadansabo

*SARTSE A ZUCI...!đź’”* *Arewabook@ayshadansabo*

*Paid book ****

©️ _Ayshat Ɗansabo Lemu_ ✍🏻

*Chapter 12*

Najwa bata yarda da cewa Zayd Abdallah da brother ɗinsa Sulaiman Abdallah idanunta suke gane mata ba har saida ta tashi taje wajensu sannan ta tabbatar,suka gaisa cikin mutunta juna Zayd ya bagatar da ita a wajen Daddy a matsayin abokiyar karatunsa a UK.Lokacin da su Zayd za su wuce hotel ɗin dasu Daddy za su yi masauki ne suka keɓe da Najwa suka sake zantawa ya tambayeta abinda ya kawota Lagos ta sanar dashi cewa tare da Anty ɗinta suke gobe za su koma Kaduna,sukai exchanging number domin ta daina samunsa a line ɗin da take samunsa kwanakin baya.Sosai Zayd yaji ganin Najwa na dawo masa da irin kalar rayuwar da sukai a UK,wani abu ya ɗarsu a cikin zuciyarsa har yana jin yayi farin ciki da jin cewa Kaduna za ta wuce wajen Anty ɗinta ba Katsina ba.Kuma tun daga wannan haɗuwar babu daren da Najwa ba za ta kirashi suyi vedio call ba,kuma a mafiya yawan lokuta sai ta saka kayan bacci masu fidda sura da tada sha'awa suke yin wayar tayi ta zuba masa shagwaɓar cewa tayi missing rayuwarsu na baya.Hakan ya taimaka ƙwarai wajen sake ƙawatawa Zayd kanta da ɗarsa wani abu a cikin zuciyarsa da tayi,duk ranar duniya sukan yi waya da Hameedah fin sau biyar yana jin lafiyarta dana unborn ɗinsa.A haka su Yaya Sulaiman sukai sati guda suka koma Zayd na cike da kewar Hameedah matuƙa da gaske,a daddafe ya iya ƙara sati biyu ya biyo flight ya koma Kaduna.Hameedah tana welcoming ɗinsa ya riƙeta a cikin jikinsa tana faman zillewa da kauda face sabida ƙamshin turarensa da bata faye so ba a yanzu,hakan yasa duk iya yadda yaso ta saki jiki ta bashi haƙƙinsa bai samu yadda yake so ba domin da ƙyar ta bashi kanta abun sam babu armashi.Hakan ya janyo zuciyarsa ta ƙuntata har ya kasa sake fuska a lokacin da suka haɗu da Amal a falo ta gaidashi,tunda ya dawo Amal ta sanar da Hameedah cewa za ta koma hostel tunda ta samu lafiya,kuma duk iya magiyar da Yaya Hameedah tayi akan Amal tayi haƙuri ta sake bari ta kwana biyu Amal ɗin bata ji ba ta tattara kayanta a washegari ta koma school abinta.Hakan kuma yayi ma Yaya Zayd daɗi domin a ganinsa har da ganin idanun Amal ɗin ke sawa Hameedah na sake lanjare masa,amma kuma sai daga baya ya gane cewa ba hakan bane domin tafiyar Amal ɗin bai sauya komi ba illa ma sake nisantarsa da Hameedah tayi.Kwanansa uku da dawowa Kaduna Najwa ta nemi su haɗu a gidan Suraj Galadima bayan Magriba,kamar Zayd bazai amsa gayyatarta ba sai kuma ya tuna shine da kansa yayi mata promise ɗin cewa za su haɗu domin baya buƙatar taje gidansa kamar yadda taso yi.Kuma wannan zuwan da yayi ya sameta a gidan amininsa Suraj Galadima sai yayi silar sake jonewarsu da juna,domin bai baro gidan ba sai da suka gama romancing junansu shi da Najwa da tayi missing salonsa mai zafi.Da ƙyar ya ƙwaci kansa daga tarkonta domin kaɗan ya rage ta rinjayesa su afka cikin aikata babban aikin,kuma a ranar ne ya fahimci cewa Najwa ta jima da sanin daɗin maza ba iya soyayyar shan sweet ta tsaya ba tasan namiji ciki da wajensa.Kuma tun daga ranar alaƙarsa da ita ta sake yin ƙarfi domin ita ke rage masa tulin sha'awar da Hameedah ke kasa biya masa buƙatunsa,ya zamana cewa da zaran abin ya motsa ya nemi Hameedah taƙi sai kawai ya kira Najwa ta samesa a gidan Suraj su jiyar da juna daɗi har ya samu biyan buƙata ta hanyar wasanni da juna.Sai dai ita Najwa burinta kullum shine ta rinjayesa ta jiyar dashi asalin ni'imarta,amma Zayd ɗin na kaucewa faruwar hakan domin yasha faɗi mata cewa yana ƙyanƙyamin shiga jikin macen da bashi da tabbacin cewa shi kaɗai zai fara saninta ba.Sosai Najwa tasha alwashin sai ta cigaba da liƙe masa har zuwa lokacin da za ta samu galaba a kansa,don haka koda yaushe suna maƙale a waya kobai nemeta ba sai ta kirashi vedio call tasan yadda akai ta tada masa sha'awa.A lokacin da Hameedah ta gano cewa Zayd ɗinta ya canza ya daina damuwa da rashin bashi kanta da take idan yazo gari sai hankalinta yayi mummunar tashi har ta fara sanya ma duk wani motsinsa idanu,kuma bata sha wani wahala mai yawa wajen gano cewa kamar ya faɗa soyayya da wata mace dake neman ɗauke hankalinsa domin ta kula duk dare sai ya fiso ya zauna a ɓangarensa ya kulle kansa baya so sam ta raɓesa.Watarana ya shiga wanka ta mamayeshi ta ɗauki wayarsa domin yin bincike,ta riga tasan password ɗinsa domin sunanta ne ya saka.Kuma koda ta saka sunan nata take wayar ta buɗe alamun har lokacin bai sauya wani password ɗin ba,cikin sauri-sauri ta fara duba chat ɗinsa idanunta ya sauka akan saƙon da bai buɗe ba sai sunan da yayi saving da N.Katsina ya ɗauki hankalinta.Kuma a lokacin da hannunta ya buɗe saƙon ta shiga duba chat ɗinsu take bugun numfashinta ya kusa tsayawa sakamakon irin kalaman da suke amfani dashi da irin vedios ɗin da Najwa ke tura masa na tsiraicinta yana gani,wani irin zufa ya shiga wanke jikinta zuciyarta na wani irin jijjiga.Hankalinta yayi wani irin tashin gauron zabi domin bata taɓa tunanin cewa Yaya Zayd zai iya komawa wannan rayuwar da yayi mata alƙawarin dainawa ba,kuka ne ya ƙwace mata daidai da fitowar Yaya Zayd daga cikin toilet ɗin.Kuma tunda ya kalleta ya hango wayarsa a hannunta ya tabbatar cewa tayi masa bincike taga chat ɗinsu da Najwa ranshi ya ɓaci,hankalinsa ya tashi domin baya buƙatar ganin damuwarta bare jin kukanta a wannan situation ɗin da take ciki.Don haka cikin sauri ya ƙarisa yakai zaune yana ƙoƙarin janta jikinsa tayi saurin dakatar dashi,domin wani irin haushinsa taji tana ji duk da cewa zuciyarta taƙi ta tsanesa.Haƙuri kawai ya fara bata yana sanar da ita cewa laifinta ne domin ya kasa mallakar kansa da wannan horon da take masa na hanashi kanta da take yi,kalamansa suka sake sanyata kuka domin take ta ɗauki duk wani laifi ta ɗaurawa kanta.Haka ya shiga rarrashinta har ya samu kanta ta bashi damar daya jima bai samu a kanta ba,sai dai suna gamawa ta fara sheƙa amai abin tausayi kuma dama abinda ke sawa taji ta tsani ya raɓeta kenan.Shi ya taimaka mata suka nufi toilet ya wanke mata jikinta ya naɗota a towel suka fito,da kansa ya taimaka mata suka shirya kansu domin akwai kayanta a cikin closet ɗinsa.A ranar gabaki ɗaya zuciyar Hameedah ta kasa nutsuwa da ganin chat ɗin Najwa da Yaya Zayd,ta ɗauki laifi ta ɗaurawa kanta domin tabbas tasan yanayin halittarsa mai yawan buƙata da son a kula dashi ne.Sai ta sanyawa kanta cewa za ta jure duk wani halin da za ta shiga ta daure ta riƙa biya masa buƙatarsa,ta tuna shawarar da Amal ta bata tunda fari akan ta daure ta riƙa bashi haƙƙinsa.Kwanakin da suka biyo baya komi na tafiya normal Hameedah na matuƙar ƙoƙarin bashi haƙƙinsa har ya koma Lagos,Yaya Hameedah ce ta kira Momy ta roƙeta akan ta sanya Amal ta dawo wajenta da zama domin ɗebe mata kewa.Momy da dama tayi tunanin hakan take ta kira Amal ta sanar da cewa ta bar hostel ta koma wajen Yaya Hameedah ta tayata zama tunda Zayd ba mazauni bane,dole Hameedah na buƙatar mai ɗebe mata kewa.Don haka a cikin week ɗin Amal ta kwaso kominta ta koma gidan Yaya Hameedah kamar yadda Momy ta buƙata domin har Daddy ta sanar mawa shima kuma ya aminta da hakan.Sannan Momy ta sanya Babah Salame ta samowa Hameedah masu aiki har guda biyu,dattijiya ɗaya sai budurwa guda ɗaya wacce za ta riƙa mata hidimar shara dasu mopping ita kuma Babah Gaje ta tayasu zaman gidan da yin wasu aikace-aikacen.Amal Taheer ta koma gidan Yaya Hameedah ne badon zuciyarta naso ba,sai don babu yadda za ta yi kuma itama tasan dole Yaya Hameedah tana buƙatarta a kusa da ita tunda ita kaɗai ke gareta.Duk weekend anan gidan Yaya Hameedah Aman Kurfi yake zuwa susha hirar luv ɗinsu,a ranakun wasu weekend ɗin kuma takan je Zaria ta dawo.Momy tazo ta duba jikin Hameedah har sau biyu ita da Anty Mamah shima Daddy haka,kowanne a cikinsu ya ɗaura buri akan wannan ciki da Hameedah ke ɗauke dashi suna kuma yi mata fatan sauka lafiya idan lokaci yayi.Sosai Yaya Zayd yake kulawa dasu kullum suna maƙale a waya suna vedio call,yana kulawa da ita sosai domin da gaske ba ƙaramar soyayyar Hameedah da urborn ɗinsa yake ji a cikin zuciyarsa ba.Satinsa uku da tafiya yazo domin dubasu da kuma sauke babbar buƙatar daya tara,da ƙyar Yaya Hameedah ta bashi haɗin kai domin ɗan nesa da ita da yayi sai taji tamkar an sake zare mata sha'awar son abin ne.Tunda ya dawo dariyar Amal a gidan ta ɗauke ta koma zaman ɗaki,sam idan yana falo bata fitowa saita tabbatar ya koma side ɗinsa take fitowa tayi sabgar gabanta.Sati ɗaya yayi ya juya Lagos cikin matuƙar takaicin yadda ya kasa samun cikakken gamsuwa domin Hameedah taƙi ta saki jiki ta bashi kanta yadda yake da buƙata,shiyasa bayan komawarsa yayi ta fama da ciwon ciki har sai da ya yankewa kansa hukuncin fara yin azumin litini da alhamis.Satinsa biyu da komawa Najwa ta kirashi tace gata a garin Ikko,yasha mamakin mai kuma ta dawo yi a garin Lagos domin sanin kansa ne bata daɗe da zuwa ba time ɗin da suka haɗu tace tare da Anty ɗinta suke,sai dai abinda bai sani ba shine babu wata Anty ɗinta tare da saurayinta Kasheem take.Kuma a wannan zuwan ma shi ta rako domin a zahiri yawonta kawai take tana buga barikinta,amma shi Kasheem ɗin aurenta yake da burin yi har ma Iyaye sun shiga cikin maganar amma kuma basu fasa yawon holewa da junansu ba.Koda Zayd ya tambayeta sai ta tsarashi akan cewa Anty ɗinta ta sake rakowa za ta shiga Cotonou domin sarin kaya,don haka ita za ta jira Anty ɗin nata a gidan friend ɗinta har ta gama da Cotonou ta dawo Lagos ɗin.Suka rabu dashi akan cewa za su haɗu a wani beach a ranakun weekend,kuma kamar yadda ta buƙata Zayd ɗin da kansa yaje har inda ta sanar dashi ya ɗauketa suka tafi beach ɗin da itace tayi masa directing domin tafi shi zuwa garin Lagos da sanin wuraren hutawa kala-kala.Fitan yayi masa daɗi domin sun samu nishaɗi sosai,kuma koda ya ɗauketa domin maidata gidan friend ɗinta datai masaukin ƙarya saida suka sha luv ɗinsu a cikin mota ya yamutsata son ransa.Kuma abinda bai sani ba shine yana ajeta a gidan friend ɗinta Nanah badajimawa ba ta kira Kasheem suka wuce Hotel ɗin da suke kwana,kuma a washegarin ranar daya kasance Sunday ta ishi Zayd da magiyar ya sanar da ita inda yake za ta je ta samesa.Shi kuma da yake tunda suka rabu yake cikin tsananin buƙatuwa sai kawai ya tura mata address domin yana son tazo ya rage ƙarfin sha'awarsa,don haka ba tare da yasan ƙarfin ƙaddarar dake shirin afka masa ba ya kintsa yayi zaman jiran ƙarisowarta gidansa da yake renting yana zama anan cikin Apapa.Kuma wannan ziyarar da Najwa ta kawo masa shine mafarin buɗe wata ƙofar ɓarnar a cikin rayuwarsa,domin basu rabu ba saida tayi nasara a kansa har ya santa a ɗiya mace abinda yayi ta gujewa afkuwarsa tun shekaru da dama.Sai gashi rana tsaka ta rusa komi ta ɗanɗana masa zumarta wanda sheɗan ya ƙawata masa garɗinsa sosai da sosai,sai bayan lafawar komi ne yaji tsanar kansa da abinda ya aikata na lulluɓe zuciyarsa har hakan yayi sanadin da yayi mata koran kare daga gidansa.Kuma tun daga lokacin bai kuma saurarenta koda a waya ba,daga ƙarshe ma blocking ɗinta yayi domin da gaske ya shiga tsananin nadamar kusantarta da yayi.A can gida Kaduna kuwa Amal kullum driver ke kaita school ya ɗakkota idan ta gama lactures,sosai su Zulaiha ke kewar rashin Amal Taheer a hostel ɗinsu domin Amal akwaita da daɗin zama.Sukan je gidan Yaya Hameedah a ranakun weekend su yini suna hira da dabdalarsu sai yamma su koma skull,a haka har lokacin exam ɗinsu ya fara ƙaratowa.Kuma tunda Amal suka kusa fara exam ɗinsu na final year ta tattara hankalinta ta mayar kan karatu bata da lokacin kowa sai na karatunta,hatta Aman Kurfi ya rage samun time ɗinta a rana sau biyu kawai suke waya safe da kuma dare kafin su kwanta bacci.Cikin Hameedah ya shiga watanni biyar Amal suka fara exam ɗinsu,Hameedah cikin ba ƙaramin kyawu ya ƙara mata ba ta sake fresh da cika abin sha'awa.Taje Zaria kusan sau uku bayan aurenta,kuma duk zuwa sai taji tausayin yadda Anty Mamah ke hidima da ita sabida cikin jikinta.Anty Mamahn zuwansu ƙasar waje sau biyu akan maganar rashin haihuwarta amma duk ƙasashen guda biyu da aka je Cairo da India duk abu guda sakamakon suka nuna shine itace mai matsalar,last zuwan da sukai ƙasar India ne wani Likita ta basu shawarar su gwada yin IVF watakila a dace.Sai dai Anty Mamah sam taƙi aminta da wannan shawarar tace da Daddy su barwa Allah ikonsa idan har sai tayi IVF ne za ta iya samun haihuwa itakam ta haƙura ta barwa Ubangiji ikonsa.Kuma tun da suka dawo gida 9ja ta tattar maganar haihuwa ta ajesa a gefe domin tasha alwashin babu inda za ta sake zuwa da sunan binciken lafiyarta akan rashin haihuwa,tace da Daddy ta rungumi Amal da Jameelah a matsayin ƴaƴan da za su share mata hawayen rashin haihuwa domin tana musu ƙaunar da bazai misaltu ba.Momy kanta tausayi Anty Mamah take bata,domin tana tuna lokacin data ɗanɗanin ɗacin rashin sake samun haihuwa akan lokaci har zuwa lokacin da aka haifi Zayd aka kuma jarabi zuciyarta da tsananin ƙaunarsa.Shiyasa Momy taga dacewar zaman Amal a hannun Anty Mamah domin ta kore mata kewa duk da cewa ba jimawa za ta yi ba da zarar ta kammala skull maganar aurenta za a fara itama,amma duk da hakan dai tana ganin dole tayi ma Anty Mamah kara wajen sallama mata Amal da dukkanin abinda ya shafeta.Shiyasa a wani zuwa da Amal ɗin tayi weekend ta tadda Momy da kanta ta kwashe dukkanin sauran kayanta dake ɓangarenta ta mayar ɓangaren Anty Mamah,hakan kuma ba ƙaramin daɗi yayi ma Anty Mamah da ita kanta Amal ɗin ba har ma da Daddy da kullum yake sake alfahari da kyawawan halaye irin na Momy Hajiya Aysha.Cikin nasara Amal suka kammala zana exam ɗinsu na final year,a kuma daidai lokacin aka tura Aman Kurfi wani course na wata guda zuwa ƙasar Canada.Bayan yayi wata guda ya dawo ne Amal ta bashi damar da ya tunkari Daddy domin neman izinin fara zuwa zance,kuma lokacin da Daddy ya tambayi Amal game da Aman Kurfi bata yi nauyin baki ba ta sanar da Daddy cewa da yarda da amincewarta yazo.Don haka bayan Daddy yayi bincike a kansa sai ya bashi damar fara zuwa zance gida,hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma Aman Kurfi ba nan da nan labarin soyayyarsu ya karaɗe kunnuwar dangi.Hameedah sosai ta maida hankali akan rainon cikinta da kulawa da mijinta Zayd wanda ke zuwa musu weekend duk bayan sati uku ko wata guda yayi kwanaki biyu zuwa uku ya juya,zuwa lokacin babu laifi Hameedah na bashi kulawa domin laulayin yayi mata sauƙi sosai.Shiyasa Zayd ɗin ya samu yadda yake so har ya manta wani abu ya shiga tsakaninsu da Najwa,domin har lokacin yaƙi buɗeta daga blocking ɗinta da yayi.Amal taso wucewa Zaria tun ranar da suka kammala exam amma Yaya Hameedah ta roƙeta akan tayi haƙuri tayi zamanta anan har ta haihu,duk yadda Amal taso ta tsaida hankalinta waje ɗaya a KD ta kasa domin kullum cikin zarya take a hanyar Kaduna to Zaria,kuma ko taje ba wani abu take yi ba kawai ƙawazucin su Momy da Anty Mamah ke kaita.Daddy basa zama shida Yaya Sulaiman domin ko'ina tare suke tafiya yana sake horar dashi akan harkokin business domin Yaya Sulaiman ya nuna kamar bashi da sha'awar yin aikin Gwabnati,amma Daddy tuni ya bada takardunsa yace masa da zaran yana da rabo an samu aikin zai fara aikinsa domin aikin shima wani kariya ne.Don haka shi dai burinsa kada su dogara da aikin shi kaɗai,su riƙi kasuwanci da sana'ar noma da kiwo da suka gada tun Iyaye da kakanni domin akwai tarin alkhairi a cikin sana'ar matuƙa da gaske.An tura su Baba Musa zuwa nemawa Yaya Sulaiman auren Nadeeya a garin Gombe,kuma sun samu kyakykyawar tarba daga wajen wakilanta har ma sunce sun bashi dama idan ya shirya ya turo da zaran ta kammala bautar ƙasa sai kawai a tsaida lokaci.....✍🏻