MASARAUTAR KAIZUR 50
by @nusybee143
🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️ Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Page 50
Wani kallo sarki Rislan ya yi masa sannan ya yi wata ƙasaitacciyar dariya yana girgiza kai,ya sake duban Sarki Iyaad da ya zuba masa idanu ya ce "abin da mamaki sarki Iyaad,sarki mai ƙima da daraja a idanun duniya ya aikata haka
A baya tabbas na kyautata maka zato, saboda nagartar ka da al'ummar ka da sauran al'ummar duniya suka gani har suka yaba,Nima na ji sha'awar haɗa zuri'a da kai,ashe da tuni na tafka kuskuren da sai na gwammace kashe kaina na yi da na aikata irin shi
Maganar da ka binne ta fita, al'ummar ka suna kallonka a banza, wannan Kazuzi ibn Murad ɗin da kake chanjawa suna ba kowa bane face wanda yake aikata alfasha da ƴarka,don asirin ta kar ya tonu shine ka kore shi daga ƙasarka don ka liƙawa ɗana!
Tunda yarinyar ta zaɓi ta yi fasiƙanci da bawa,bawan ma kuma kafiri menene ranar aurar da ita ga kamili irin ɗana? menene dalilin da ya sa ba ka aurawa bawan ba kamar yadda ita yarinyar ta so?
Ko shi bawan ya nuna ba zai aura bane?shine za'a aurawa ɗana?ko dai kwaɗayin aurar da ita ga mai mulki shine a ranka?tunda ba ka iya nemo mata daidai kai ba ko na ƙasa da kai sai inda ka san an fi ƙarfinta!!!
Kalaman sarki Rislan tamkar tafasasshen ruwa haka sarki Iyaad yake jin su a ranshi,amma bai yi magana ba sai da sarki Rislan ya kai aya, sannan ya dube shi ya ce "me kake ƙoƙarin cewa?
Ƴata mutuniyar banza ce?
Ka yi kuskure!
Kuma so kake ka ce son zuciya ce ta saka na ce zan aurar da ita ga ɗanka?
To baku da wannan wadatar!!
Kuma wai kana gadara da sarautar ku da ta ɗan ɗara ta Tayaar?
Ka tafka kuskure!!
Ni Iyaad bn Nufail ban hana Nasrullah auren Hayat don wani abu ba, sai don mutane irin ku da abubuwan da za su ce,a yau kam na yi nadamar aikata hakan
Ba kaine za ka dube ni ka yi kurin ɗanka ba,nine zan kalle ka na ce na fasa bayan samun labarin su Wanene al'ummar Kiswa!!!
Sai kuma me ka ce?ƴata fasiƙa ce,ta miƙa kanta ga bawa, wannan shaidar da hukuncin yana ga Allah madaukakin sarki,kuma abu ɗaya na sani,duk da kasancewarka sarki mai mutane da muƙami da a gaban shi wanda kake faɗar maganar akanshi kake baka isa ka yi wannan maganar ba tare da ya raba ka da numfashinka ba
Batu na aure na san ka janye ko?
Nima na janye,abin da kuka kawo za su riga ku isa Kiswa,ina yi muku fatan alkhairi "daga haka ya miƙe ya fice daga ɗakin tattaunawar cikin tsananin zafin zuciya
💫
Tun daga nesa ta gano su ta ɗauke kai, jakadiya Rubayya tana kawo shi bakin lambun ta juya ta fice daga lambun ta koma inda ta fito
Kai tsaye cikin lambun ya shigo yana aika mata wani mugun kallo,ita dai Hayat hankalinta yana kan wasu tsuntsaye da suke gefenta kaɗan suna ta waƙarsu
"Sannu uwar isassu!"ita ce kalmar farko da ya fara ambata yana watsa mata wani mugun kallo,bata tanka masa ba,sai ma cewa da ta yi"sannu da zuwa!
Ga waje zauna!"
"Ba zama na zo yi ba, tambaya nake da ita, kuma ina buƙatar amsa a take!
Wanene Kazuzi?"
Ƙirjin gimbiya Hayat ya buga da ƙarfi,ta kalli Yarima Zohran da sauri, yarima Zohran ya yi wata dariya ya ce"na taɓo miki inda yake yi miki kaiƙayi ko?
Wato dai da gaske ke ragowar wani ƙato ce za'a kai min saboda tsabar rashin tunani irin naki da na mayaudarin ubanki!
To ina yi miki rantsuwa da Allah da a ce an kai ki ɗakina kuma na gano hakan to tabbas da sai na kashe ki da hannu na,kuma mutuwar wulaƙanci a bainar jama'a, yadda hakan zai zama izina ga makwaɗaitan sarakai irin ubanki,ko......"
"Ya isa!ya ishe ka haka!!ya isa!!!"Hayat ta faɗa cikin wani irin kuka zuciyarta tana tafasa
Shiru ya yi da mamaki yana kallonta, tunda yake bai taɓa lamuncewa mace ya faɗa ta faɗa ba, ballantana kuma har ta katse shi har ta kai ga yana magana ta katse shi a tsawace,ba ta jira amsarshi ba ta cigaba da faɗin
"Wanene kai! ɗan Sarkin daular kiswa
Ina ne kiswa?wata daula ce wadda mutanenta sam ba su san darajar aure ba,ba su san darajar mace ba,abin duniya kawai suke girmamawa ba tare da tunanin su ma watarana za su mutu ba
Kana tunanin da hankali na zan yarda na yi aure a daularku?kana tunanin yadda mahaifina ya so ni fiye da kanshi zai yarda ya kai ni cikin Waɗannan ƙasƙantattun mutanen waɗanda ba su san darajar kansu ba ballantana su san darajar wani?
Me ka ɗauki kanka ne? wulaƙantacce ne kai,don wallahi duk mai wulaƙanta wani akan abin duniya shima wulaƙantacce ne
Sannan batun Kazuzi, Nasrullah ya fi ƙarfinka,ya fi karfin tunaninka,shine namiji,kai baka kai a kalle ba ma muddin yana waje,ba zan san cewa ka fi ƙarfin abin da ya shafe shi ba sai ka gwabza yaƙi da shi ka yi nasara,ko ka yi kwalliya da shi kun fito ka ga Wanene za'a kalla, Wanene kashi ya fi shi ƙima, sannan kuma......."marin da ya sauke mata ne ya hana ta cigaba da maganar da take yi cikin ɓacin rai da fitar hayyaci,ta dafe kuncinta a firgice yana kallonshi, cikin tsananin ɓacin rai,wai yau shi mace,mace dai,macen ma wadda bawa ya aikata baɗala da ita ita ce take gaggaya masa magana,me ya janyo masa wannan wulaƙancewar ne?
Ya dube ta ya ce"ke ba ki da darajar da za ki tsaya a gaba na kina gaya min magana,ke ba ke ba ko ubanki Iyaad, wanda ya kasa ba ki tarbiyya ya bar ki a wulaƙance, ƙarshe kika ƙare da fasikanci da bawa saboda taɓewa da asara,na gode wa Allah da bai bani ikon aurenki ba,tsinanniya kawai"ya sa ƙafa ya hamɓare ta sannan ya fice daga lambun a fusace
Abubuwa masu yawan gaske suka tararwa Hayat,ta tabbatar ko lokacin da Nasrullah yake Kazuzi ba zai taɓa bari a dake ta ba ballantana yanzu da suka fara son juna,ga cin mutuncin da ya yi mata,ga wanda ya yiwa mahaifinta,ga ƙazafin zina da ya yi mata
Miƙewa ta yi cikin kuka ta wuce sashenta,ji take yi a duniya babu wanda ya kai ta shiga baƙin ciki
💫
A harabar masarautar Yarima Zohran ya samu mahaifinsa, cikin ɓacin rai ya karanta masa yadda suka yi da yarinyar,shima sarki Rislan ya gaya masa yadda suka yi da uban yarinyar, Yarima Zohran ya ja tsaki ya ce"wannan ba wajen neman aure bane,don ban ga alamun tarbiyya a tare da wannan ahalin ba Abeey,mu gaggauta barin masarautar nan kafin zuciya ta ɗebe ni na yaƙe ta"murmushi sarki Rislan ya yi,ya ce "mu bar su da abin kunyar da suka janyowa kansu ma,ba sai mun ƙara musu da wani ba,maza mu tafi"babu musu suka shiga keken dokinsu,masu raka su suka hau dawakansu suka fice zuwa Kiswa
*DAULAR KAIZUR*
Gobe ne za'a fita zuwa yaƙin Aluuz da daular kafirai ta Majrah,dakarun da za su fita zuwa yaƙin sun gama shiri cif, maimakon sarkin yaƙin Kaizur Nauwas ya jagoranci yaƙin Kamar yadda ya saba, wannan karon yarima Sahal ne zai jagoranta,duk da cewa ba haka sarki Mu'iz ya so ba, kawai babu yadda zai yi ne
A yau ne za'a yankewa yarima Zaffar da sarauniya Amna hukuncin kora daga kaizur,kuma kamar yadda aka saba a gaban dubban al'ummar kaizur aka fito da su kawunansu a ƙasa
Su ma iyalan yarima Zaffar ba'a bar su a baya ba,su ma suka fito zuwa bakin fadar don jin dalilin da ya sa aka kama shi, abin da har yanzu wani mahaluki a cikin daular kaizur bai sani ba,banda su ahalin da sarki Laimus ya ba wa labarin
Sarki Mu'iz, yarima Jamal tare da Yarima Sahal suka fito zuwa wajen da aka tanada don zamansu,ba su juma da fitowa ba Munaya ta fito ita ma, wadda a dalilin fitowar tata ya sa kallo ya koma kanta,don ba kowa bane ya san da sauyin rayuwar da take ciki, musamman yanzu da aka mayar da ita wani ɓangare a cikin masarautar,ta zamo tamkar sarauniya
Itama waje ta samu kusa da ɗanta ta zauna bayan ta gaida sarki, Sahal ya gaishe ta yana murmushi,ta shafa kanshi cikin kulawa tana amsawa, sannan ta samu waje ta zauna
Bayan an nutsu sarki Mu'iz ya dubi al'ummar shi ya yi musu sallama,suka amsa, sannan ya fara da faɗin
"MASARAUTAR KAIZUR tana yiwa al'ummar ta fatan alkhairi
Na san kuna cike da mamaki,ko na ce kun ƙosa ku ji abin da yake faruwa game da kama ɗan'uwa na da ba ni da kamarshi da na yi,da kuma matata, sannan kuma da zuwan baƙon saurayi wajena
Wannan saurayin ba kowa bane face jaririna SAHAL IBN MU'IZ, wanda na rasa shekaru da yawa a baya, cikin hukuncin Allah gashi nan ya sake dawowa gare mu cikin aminci,duk da cewa jarabawa da kaddarar rayuwa ta faɗa masa da yawa,amma Allah mai kowa mai komai ya ƙaddari zai dawo mahaifarshi,kuma gashi alhamdulillahi ya dawo"ya ba da tarihin yadda Sahal ya rayu a taƙaice,da yawan mutane sai da suka zubar masa da ƙwalla,sarki Mu'iz ya ɗora da faɗin"ba Kowa bane ya janyo wannan abu sai matata Amna da ɗan'uwa na
Tabbas na yi kuskure,na tuhumi mutane da yawa a baya, na zargi mutane da yawa,na hukunta wasu ma,ina neman afuwar dukkan wanda hakan ya shafa,ga waɗanda na yi silar mutuwar wani nasu kuma bayan hukuncin kisa bai hau kansu to in sha Allah zan biya su diyya
Yarima Sahal,a matsayin shi na wanda aka yi wa laifi, hukunci ɗaya ya ce zai yi musu shine hukuncin kora, saboda cin amana da suka aikata, kamar yadda za kuji yanzu "a take ya bayar da labarin abin da suka aikata a taƙaice,har zuwa lokacin yana jin ɗacin abin da suka aikata ɗin
Take mutane suka fara salati suna yi musu tofin Allah tsine,shi dai sarki Mu'iz ya ba wa dakaru izinin su fitar da su daga cikin kaizur baki ɗaya
Haka kuwa aka yi,hatta iyalan yarima Zaffar kuka suke yi suna zaginshi saboda wannan tabo da ya janyo musu
Ita kanta Amna kuka take yi tana tsine masa, shine ya cuce ta tun daga farko,da tuni ta yi zamanta lafiya a gidan aurenta,kuma ko da ace bata haihu ba zata riƙe ɗanta Sahal kamar ita ta haife shi
Jiki a sanyaye Munaya ta shiga gida, tana shiga ɗakinta ta rufe ta fashe da kuka,ta kasa jin zata yafewa waɗannan azzaluman mutanen,sun cutar da rayuwarta,sun kassara ta, kuma ko da ace komai ya wuce ta san sun cutar da ita na har abada
Ƙwankwasa ƙofar da ta ji ne ya sa ta miƙe tana goge hawayenta tana kallon ƙofar, ƙasa-ƙasa ta ji Sahal yana faɗin "nine Ummeey!
Ki buɗe ƙofar"
Bata yi musu ba ya buɗe tana ɗauke kanta,ya bi ta da kallo yana shiga ɗakin
A bakin lallausan gadonta ya zauna yana kallonta,a hankali ya ce "Ummeey kuka kika yi?"
Girgiza kai Munaya ta yi, cikin sanyin murya ta ce "sun cutar da ni Sahal,sun kassara rayuwa ta,sun raba ni da ɗana sanyin idaniyata,sun jefa ni a cikin musiba tsawon shekaru
Ni baiwa ce, bani da ikon komai, ban isa yin komai ba,bani da wanda zai yi min komai,an siyo ni daga wani wajen an kawo ni wani ba don komai ba sai don a zalunce ni a ci zarafi na, laifin me na yi haka?"ta ƙarasa faɗa tana kuka sosai
Shiru ya yi na wasu daƙiƙu, kafin ya taso cikin sanyin jiki ya zauna kusa da ita,a hankali ya rungume ta yana faɗin
"Ummeey meyasa wani lokacin kike mantawa cewa a rayuwa kowa da yanayin jarrabawarshi?
Ummeey duk abin da Allah ya yi daidai ne, kuma hakan alkhairi ne, fatan mu kawai shine kar hakan ya yi silar raba mu da imaninmu don mu samu gwagwgwaɓan lada daga wajen Allah
Ummeey na taso a matsayin ɗa a Baruda,amma na yi rayuwa mara daɗi,duk da kasancewa ta mai ƴanci,na koma Tayaar a matsayin bawa bayan an kashe min wadda nake jin ita ce farin ciki na baki ɗaya,amma a Tayaar ne na san yadda ake farin ciki, duk da cewa na je can a matsayin bawa,a ƙarshe Allah ya ba ni fiye da abin da nake da shi a Baruda
Daga baya aka kore ni daga Tayaar saboda rashin asali,sai gashi Allah ya ba ni asalin da ban taɓa tunanin zan samu kaina a ciki ba
Kamar dai ke Ummeey,kin taso a rayuwar ki a matsayin baiwa,aka kawo ki nan,kika haifi abin da suke alfahari da shi,duk da zaluncin da kika fuskanta shekaru masu yawa a ƙarshe komai ya wuce,kin hau wani matsayi wanda ba ki taɓa tunanin hawa ba,shin hakan bai ishe ki godewa Allah ba?"
#Nusy_bee
***