MASARAUTAR KAIZUR

MASARAUTAR KAIZUR 51

by @nusybee143

🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑 






✍️Nusy bee 
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️ 

(Under YOTA'S AMAZING PENS)





Page 51



Shiru Munaya ta yi tana sauke ajiyar zuciya, maganar É—an nata tana ratsa zuciyarta, Sahal ya sake rungumeta sosai,a hankali ya cigaba da faÉ—in 

"Komai ya faru a rayuwa sanadi ne na wani alkhairi da zai faru Ummeey, yadda komai ya wuce, komai ya faru ya wuce,ina roĆ™on ki manta da shi,ki saka a ranki tamkar bai taÉ“a faruwa ba,in sha Allah komai zai wuce Ummeey,ko ma na ce ya wuce 

Ummeey ki daina kuka don Allah"ya ƙarasa faɗa yana goge mata hawaye

Itama rungume shi ta yi, cikin sanyin murya ta ce"ina alfahari da kai É—ana, Allah ya albarkaci rayuwarka,idan kana da rabon mulkar kaizur ina roĆ™on Allah ya ba ka ikon yiwa jama'ar garin nan adalci, Allah ya tsare ka daga dukkan sharri 

YaĆ™in da za ku fita gobe Allah ya ba ku nasara"ya yi murmushi sosai yana faÉ—in "Ameen Ummeey na,ina alfahari da ke"daga nan ya fara yi mata sakalcin da ya saba don ya mantar da ita damuwar da take ciki, tuni ta biye masa, yana zuba mata shagwaÉ“ar cewa ya yi mafarki da Hayat tana cikin damuwa 

Munaya ta ce"gaskiya idan aka dawo daga yaƙin nan ko a bangon duniya iyayen yarinyar nan suke sai mun je an nemo maka aurenta,don gaskiya ba zan iya zuba idanu soyayya ta yiwa ɗana lahani ba"

Tura baki ya yi yana kwanciya akan cinyarta ya ce"Abbey baya son na ce ina son a nema min aurenta,ban san me yasa ba"

Munaya ta ce"kuma ya zama dole ba, bari zan yi masa magana "

Ya kanne ido É—aya yana murmushi ya ce"amma sai an yi naku ko?"ranĆ™washinsa ta yi tana É—an murmushi,shima ya yi saurin tashi zaune yana Ć´ar dariya, Kafin ya miĆ™e ya fice daga É—akin 

Washe gari dakaru suka fara hallara a Ć™ofar fada cikin cikakken shirin yaĆ™i, wannan yana wane wancan, sarki Mu'iz da yarima Jamal ma duk sun hallara 

Babu jumawa sai ga yarima Sahal, cikin shirin shi cif,duk da sulken yaƙi ya saka ya yi kyau sosai kamar koyaushe,ya ƙarasa inda su sarki Mu'iz yake ya rissina ya gaishe su

Suka amsa cikin sakin fuska, sarki Mu'iz ya miƙa masa takobi ya ce"ga takobin Shamal nan,tana yiwa Yarima Barka da dawowa Kaizur "yarima Sahal ya karɓa yana faɗin"na gode sosai Abeey!"

Daga nan suka hau dawakansu,aka buga gangar yaĆ™i,suka dumfari babbar Ć™ofar garin kaizur, wadda zata kai su zuwa daular Aluuz bisa jagorancin Yarima Sahal 







*DAULAR TAYAAR*


"Barka da shigowa Abeey!"

Bai amsa ba,ita kuma tunda ta ganshi jikinta yake ta tsuma saboda fargabar abin da zai biyo baya,bata ankara ba ta ji ya sauke mata mari irin wanda tunda ta zo duniya ba'a taÉ“a yi mata irinsa ba, gigicewa ta yi ta yi baya kamar zata faÉ—i,amma ta yi saurin daga bango tana kallon mahaifin nata a matuĆ™ar razane 

Shima kallonta yake yi cikin tsananin baĆ™in ciki da takaici, cikin wata iriyar murya mai É—auke da tsananin baĆ™in ciki ya fara magana 

"Da kyau Hayatul Islam!

Wannan shine sakamakon da za ki iya biya na da shi na rainonki da na yi bayan rasuwar mahaifiyarki da É—an'uwanki,kin ja ni a Ć™asa, kin saka na ji kunya a bainar jama'a, kin janyo min dariyar maĆ™iya 

Hayat me na yi miki da na cancanci wannan baƙar sakayyar?

Saboda na haife ki?ko saboda na raine ki,na janyo ki a jikina,na nuna miki ƙauna?

A yau na yi nadamar hakan,a yau na gwammace dama ke ce kika mutu kafin ki janyo min wannan abin kunyar ba Nashwaar ba,a yau na yi nadamar haifarki, tabbas na kasance mara sa'a saboda samunki,ina ma na buɗe idanu na ganki ba kya raye?da sai hakan ya fi min sauƙi fiye da tuna yadda kika wulaƙanta ni a idanun duniya Hayat!!

Amma ba ki cuce ni ba,kanki kika cuta!!!"yana kai wa nan ya juya a tsananin fusace ya bar É—akin, Hayat da take zube a Ć™asa dafe da kunci ta bi shi da kallo, hawayen ma sun Ć™afe Ć™af,sun daina zuba 

Sai da ya fice gaba É—aya sannan ta miĆ™e ta zauna a gefen gadonta tana sauke ajiyar zuciya, maganganun mahaifin nata suna dawowa kanta tiryan tiryan 

"Hayat me nayi miki na cancanci wannan baƙar sakayyar?

Saboda na haife ki?ko saboda na raine ki?na janyo ki a jikina?na nuna miki Ć™auna?"wadannan kalamai ne suka yi ta yi mata yawo a kai,kuma a gare ta sun fi saukar aradu taratsi da muni 

Lokaci guda kuka mai tsanani ya Ć™wace mata,ta sani ko raba É—ayan biyu bata yi,akan batun aurensu ne da yarima Zohran 

Ya aka yi maganarsu da Nasrullah ta je har Kiswa? Wanene ya canja ta daga soyayya zuwa wani abu dabam?

Ta yi burin a fasa aurenta da Yarima Zohran,a tunaninta duk lokacin da hakan ya samu zata yi farin ciki irin wanda bata taÉ“a yi ba,amma sai gashi akasin hakan take yi saboda abin da mahaifinta ya yi mata,take ta fashe da matsanancin kuka cikin karayar zuciya 

Ta rasa mahaifiyarta tun tana yar ƙaramar yarinya, Nasrullah shine ya ceci rayuwarta daga sharrin matar ubanta da ɗanta,shine ya tseratar da ita daga sharrin Amjad har sau uku,shine mutum na farko da ya shayar da ita madarar soyayya,ya damu da damuwar ta,yake gane tana cikin damuwa ko da bata faɗa ba,shine mutum na farko wanda ya tsaya mata,yake jurar cin mutunci daga gare ta ba don yana tsoron ta ba, wanda yake yi mata uzuri a kowanne lokaci,a wanne dalilin za'a hana zuciyarta ta so shi?

Ko ita ba zata iya hana zuciyarta son Nasrullah ba,kuma ta san da yana nan da bata kasance cikin baƙin ciki haka ba

Cikin kuka mai gunji ta É—aga hannunta sama tana faÉ—in "ya Ubangijin al'arshi mai girma!

Ya mai kun fayakuun!ya shugaban halitta!!!kai ne mai iko akan komai,mai juya komai a lokacin da ka so kuma a yadda ka so,ya hayyu ya Ć™ayyum!! Allah ka juya damuwa ta zuwa walwala,ka juya baĆ™in ciki na zuwa farin ciki,ka juya fargaba ta zuwa annashuwa,idan Nasrullah alkhairi ne a gare ni Allah ka gaggauta juyo min da hankalinsa ka dawo min da shi lafiya, idan ba alkhairi bane shi Allah ka kawo min abin da zai zame min farin ciki a rayuwa ta,ya Allah ba zan iya ba, Allah ka iya min,ya Allah ni mai gazawa ce Allah ka dube ni,ya rabbul alameen Allah ka kawo min dauki!!!"ta zube a wajen tana kuka sosai, zuciyarta kamar ta fashe saboda tsabar baĆ™in ciki 





*DAULAR ALUUZ*


A kusa da ganuwar Daular Aluuz dakarun kaizur suka yada zango,don zuwa lokacin sun fara hango dakarun daular kafirci ta Majrah da suke ƙara kusanto su

Sarki Mu'iz ya kama hannun Sahal wanda yake zaune cif a kan dokinshi yana kallon dakarun Majrah yana nazartarsu,ya É—ago yana kallon Mahaifin nashi,sarki Mu'iz ya ce

"ĆŠana ka kalli dakarun mutanen nan,ina jin tsoron kar wani abu ya same ka "

Murmushi Sahal ya yi yana girgiza kai,ya ce"abbey ka gansu fa,wasu ƙwari ma,ka daina kokwanto,yau za ka tabbatar da Wanene ɗanka Sahal "

Sarki Mu'iz ya yi É—an murmushi ya dafa kafaÉ—arshi ya ce"fatan nasara mai É—orewa É—ana, Allah ya shiga lamarinka "Sahal ya yi É—an murmushi, sannan ya zare takobin Shamal daga cikin kubenta, kafin Kowa ya ankara ya zabura da gudun tsiya akan dokin shi ya tunkari maharan mayaĆ™an Majrah 

A cikin ƴan daƙiƙu ƙazamin yaƙi ya ɓarke tsakanin Sahal da mayaƙan Majrah, saboda tsananin mamaki sarki Mu'iz da yarima Jamal kasa taɓuka komai suka yi,suka tsaya suna kallon yadda Sahal yake kai farmaki cikin tsananin zafin nama mai cike da ƙwarewa,kuma a lokaci guda yake kare farmakin da ake kai masa

Cikin É—an Ć™aramin lokaci ya fara yiwa dakarun Majrah É“arna ta ban mamaki,gaba É—aya yaĆ™in hankalinsu ya koma kan Sahal wanda ba ya jiran a Ć™are masa hari,kuma baya barin damar kai hari, cikin É—an Ć™anĆ™anin lokaci dakarun Majrah suka fara razana,don su ma dakarun Kaizur da na Aluuz da suka haÉ—u dukkansu ba su yi musu da wasa ba 

A Ć™asa da yini guda dakarun Majrah sun tsiyaye sosai, babu shiri Sarkin yaĆ™insu ya busa wani Ć™aho, ba tare da É“ata lokaci ba dakarun Majrah suka juya da tsananin gudu, kafin wani lokaci tuni sun tsere 

Da kallo Sahal ya bi su yana mamakin wannan gudun,tuni dakarun su suka fara kabbara cikin tsananin farin cikin wannan nasara,ya yi tsaki ya kaɗa dokinshi ya dawo inda su sarki Mu'iz suke tsaye suna kallonshi cikin farin ciki da alfahari,shi abin ma haushi ya ba shi,sai ya ji kamar ba yaƙi suka yi ba, yaƙin Kamar wasan yara ma

Yana ƙarasowa sarki Mu'iz ya sauko daga dokinsa,shima ya sauka ya ƙarasa inda yake, sarki Mu'iz ya rungume shi cikin tsananin alfahari da farin ciki,yana faɗin "lallai yau na ga sadaukin nan da ake faɗa amma ban taɓa gani ba! tabbas yau na ga ɗaya tamkar dubu,ina alfahari da kai Muhammad Sahal!"

Yatsina fuska ya yi,ya ce"sun san ba za su iya ba shine har da takalar faÉ—a?

Kamar wasu zomaye ji yadda suke gudu, abin takaici"

Yarima Jamal da ya kasa magana saboda mamakin Sahal,duk da cewa ya samu labarin shi,ya yi Ć´ar dariya ya ce"banda abinka ai duk yawan kuraye suna tsoron Zaki 

Ballantana wannan Zakin mai cikar sadaukantaka da jarumta, Kaizur tana alfahari da yariman ta"murmushi Sahal ya yi ba tare da ya ce komai ba, don shi bai ga abin yabo a nan ba,don ya kara da waÉ—annan matsoratan 

A ranar suka koma Kaizur tun kafin su isa labari ya isa Kaizur na nasarar da suka yi a wannan yaƙin,ba nasarar tasu ba ce abar dubawa da yabawa ba ma,sai mamakin da yariman Kaizur ya ba wa masu yi masa wani kallo a wannan yaƙin

Da gudu Munaya ta zo ta tari É—an nata,ta rungume shi cikin jin alfahari da shi,ya goge mata hawayen idanunta yana kallonta, cikin sanyin murya ya ce"Ummeey murna ya kamata ki taya ni,ki daina kuka haka Ummeey "

Munaya ta yi murmushi ta ce"kukan farin ciki ne É—ana,ina alfahari da haihuwar wannan lu'ulu'un,kai É—in alkhairi ne a gare mu, kuma É—aya tamkar dubu,ina alfahari da Sadauki na"ya yi murmushi,ta ja hannunsa suka wuce,suka bar su sarki Mu'iz da bin su da kallo suna murmushi 

A ranar tare suka kwana da sarki Mu'iz,yana ta ba shi labarin irin yaĆ™e -yaĆ™en da ya yi a baya,da irin gagarumar nasarar da ya samu a rayuwarsa,da irin Ć™alubalen da ya fuskanta kafin ya zo wannan gaÉ“ar 

Sarki Mu'iz ya yi mamaki sosai,kuma ya tausaya masa sosai jin yadda ya yi rayuwa cikin wahala,a hankali ya gangaro kan labarin Hayat 

Daga yadda yake magana sarki Mu'iz ya fuskanci tsananin zafin da yake ji na raba shi da ita da aka yi,ya dube shi ya ce"yanzu idan na ce zan nema maka aurenta kana so?"

Da sauri ya jinjina kanshi,a take rauninsa da ya saba bayyana duk lokacin da aka yi batun gimbiya Hayat ya bayyana,sarki Mu'iz ya dafa kafaÉ—arshi ya ce"khairan in sha Allah É—ana!

Ka ba ni lokaci,in sha Allah zan je har can Tayaar É—in na nema maka aurenta,ka kwantar da hankalin ka"

Da farin ciki yarima Sahal ya fara yi wa sarki Mu'iz godiya, lokaci guda kuma fara'ar fuskar shi ta ɓace,a hankali ya ce"to idan kuma an aura mata wani fa?"

Cikin son Ć™ara masa Ć™arfin gwiwa sarki Mu'iz ya ce "ba'a yi mata ba ma in sha Allah 

Allah ba ya jarabtar bawa da abin da ba zai iya ba,in sha Allah ba za ka ga jarrabawa ta ɓangaren Hayatul Islam ba bayan wadda ka gani a baya "

Shiru Sahal ya yi,kafin ya yi magana cikin sanyin murya 

"Abbey sarkin su fa ya kore ni,ina shakkar sake shiga garin ko don halaccin shi a gare ni"

Sarki Mu'iz ya ce"za ka shiga garin ne a matsayin yarima Sahal É—an sarki Mu'iz na garin kaizur,ba a matsayin Kazuzi ibn Murad É—an asalin garin Baruda,ko kuma Nasrullah wanda ya koma Tayaar da rayuwa ba

Fatana É—aya ne kawai, Allah ya sa ba kai É—in bane ba zai ba wa auren ba,nasabar Ć´aĆ´an Ć´arshi yake dubawa"

Yarima Sahal ya lumshe idanunshi ya buɗe ya ce"to Allah ya sa hakan, Allah ya sauƙaƙa komai"sarki Mu'iz ya yi ɗan murmushi yana faɗin"Ameen ɗan umminshi"






#Nusy_bee
***