Chapter 4
***
IMAM ZAID 🔬🥼
Pending Amarya ce🎭
JAJIRTATTU WRITERS ASSO………………✍️
The Odogwu Writer ✍️
Chapter1: THE BEGINNING 🙌🏻
An Empty barrel makes the loudest noise 🙌🏻🎭
IMAM ZAID 🔬🥼🧪
Paid book ne.
At a low fee za ku samu 500 naira kacal.
***😢
Opay Farida Aliyu Ibrahim
shaidar biya via what’s app🙌🏻
***
When Allah tests you, it is because He wants to hear your voice🥺💕
Pending Amarya 004🥰
Not edited 😩
“Fattumah.” Ta ji saukar muryarsa a sanyaye kamar ko da yaushe, ɗago kanta ta yi wanda hakan ya sanya idanunsu hadewa cikin na juna, wanda hakan ya ƙara karyar da zuciyarta ta ƙara fashewa da wani sabon kukan.
“Toh yanzu mai ye na kukan?, wani ya bata miki rai ne?.” Ya yi maganar tare da dan kwanto da kanta a kan kafadar sa.
“Toh ba kaine ka min tsawa ba, kuma gashi babu wani feedback a hospital din da kuka kai cousin din ku, and wallahi babu abin da na mata, a kasari ma ni naje kitchen daukan abincin da zan ci ne.” Ta yi maganar wani hawayen ma sauka a idanunta.
“Kin ji na ce wani abu ne Cutie, I trust you , na san ba za ki taba yin hakan ba .” Ya fada tare da janyota jikinsa.
“Amma fa har tsawa ka min?.”
“Toh yi hakuri ba zan Kara ba.”
She just nodded, sannan ta fara wasa da hannunta a jikinsa.
“Ta haifi tagwaye, buh unfortunately they’re no more sun koma ga mahalliccinsu.” Ya yi maganar with soo much sadness.
Ba ta ce komai ba illa ajiye kanta da ta qara yi kwalla na zuba a idanunta.
“Shirya muje hospital din, and don’t say a word to anyone kin ji ko?.”
Nan ma gyada kai kawai ta yi sannan ta shirya cikin wani Abaya mai kyau sannan ta dauki leather bag dinta ta bar dakin tare da nufar Compound din gidan, duk wasu habaici da facalolinta ke mata yi ta yi kamar ba ta ji ba.
Har suka karaso asibitin murtala ba ta yiwa kowa magana ba ko Dadah ba ta gaida ba har ya dawo da ita gida.
Sakinat kam ban da kuka babu abin da take, da ta ga Fattumah ma cewa ta yi ita ala dole ta fita daga dakin.
A bangaren Fattumah kam har aka sallamesu ba ta sake zuwa hospital din ba, kuma gaba daya kowa na gidan ya kullace ta dan Dadah har mayya ta kan kirata wasu lokutan.
Yau ma kamar kullum zaune take a waje daya hannunta rike da telephone da ta gama waya da Appahnta da yake sanar da ita zuwansu Nigeria, sun zo yin wani gaisuwa a gidan cousin dinsa da matarsa ta rasu.
Tsagala wayar ta yi a ma’ajiyyar shi sannan ta tashi a wurin ta nufi bandaki domin watsa ruwa sannan ta wuce can gidan Uncle Abdallah cousin din mahaifinta.
Cikin wani atamfa mai kyau ta shirya, sannan ta dauki Jakarta mai gashi ta tsagala shi a kafadarta, tare da nufar kofa ta fice daga side dinta.
A babban falon gidan ta tarar da yan Uwan mijin nata gaba daya, su Sakinat da su Shema’u na ganinta suka fara yada mata habaici.
Ba ta musu magana ba ta gaida Dadah dake zaune da facalolinta duk da ba ta amsa mata ba amma ta sanya kanta ta fuce daga cikin gidan ba tare da ta juyo ta kalli Dadah dake zaginta hade da kusheta ba.
Taxi driver ta tsayar tare da barin kofar gidan mijin nata, cikin mintina kalilan ta iso giginyu quartz daidai kofar gidan Uncle dinta.
Ta yi farincikin ganin yan gidan nasu gabadaya har da step sister dinta wacce mahaifiyyarta ke riketa dalilin Ana haihuwarta maman ta ta rasu.
“Aunty dubi yadda kika yi kyau ma shaa Allah, wallahi Kina Jin dadin ki a gidan Yaya Jalal.” Ta yi maganar tare da rugumeta.
Murmushi kawai Fattumah ta yi sannan ta ce “Ya Tanzania, da su Uncle Rafiq, kuma kin cigaba da zuwa Islam iya?.”
Kyalkyalewa da dariya Sabila ta yi tare da fadin “Timmy!, ba dole na koma islamiyya ba ai Uncle Rafiq ya ban hakuri kuma an kore shi daga Islamiyyar, Imam Yazid dai ya mutu since last month wallah.” Sabila ta karashe maganar da jimami.
“Allah ya jikansa, amma gidana za ki kwana yau ko?.”
“Waii nii Yaya?, wannan Maman mijin naki da bakin halin tsiya, ta min dai kinsan ba zan kyale ba wallahi.”
Fattumah ba tace komai ba suka ci gaba da hira har lokacin komawar ta gida ya yi, ta sadakar da Sabila za ta bita kawai sai ta ganta itama ta shirya har da akwatinta.
Ta yi murna sosai sannan suka fice daga gidan AMMUH na musu a dawo lafiya.
Har suka karaso gidan bakin Sabila bai yi shiru ba sai har suka karaso gidan.
Dake drop suka dauka naira biyar ta ciro ta mikawa driver din, yana mata godiya ta wuce shi suka shige gidan.
A babban falon ma kamar yadda ta yi expecting hakan ce ta faru, dan gabadayansu suna zaune suna dinner, har da qanin Jalal da dawowarsa kenan daga Zanzibar can gida.
Sai da ta bi mutanen falon da kallo, sannan ta wuce ba tare da ta ce dasu kala ba, Sabila ce kadai ta gaida su ita ma ta bi Yayarta a baya.
Tsame hannunsa ya yi daga cin abincin ya fara tafiya da niyyar bin su shima.
“Dan uwarka wa zai ci maka wannan abincin daka jagwalgwala?, ko zuwa za kai ka mace mata yadda ka saba?.” Dadah ta yi maganar cikin zafi.
“Aa Maama, ba wajen ta zan je ba akwai abin da zan dauka a bangarena na can side din nata ne.” Jalal ya fadi hakan ba tare da ya juyo ba.
“Kaje din ma mana wannan Ayy matsalar ka ce, tun da ka rantse sai ka yi mu’amula da mayya.”
Bai ce mata komai ba ya wuce ya shige side din nata.
Zaune suke a falon dakin nata suna ta hira har da dariya.
“Assalamu alaikum.” Cikin muryarsa mai sanyi ya yi sallamar tare da kutso kansa cikin falon da su biyu ke zaune.
Amsa sallamar suka yi sannan Sabila ta ce “ Yaya ina wuni.”
“Lafiya lau yar gidan AMMUH, ya school?.” Ya amsa mata gaisuwarta tare da zama a kan kujerar falon.
“lafiya lau Ya Jalal.” Ta fada a dan kunyace, tare da sauke kanta kasa.
“Ma shaa Allah.”
Fattumah kam gaishesa ta yi a takaice sannan ta maida hankalinta a kan wani Nollywood movie da take kallo.
Daga haka suka ci gaba da hira dan har 12 na dare ya yi ba su sani ba.
Bubbuga kofar da aka fara yi shi ya fargar da su da sauri ya mike tare da fadin “sai da safe Sabila zamuyi magana da safe.” Bai jira cewarsu ba ya fice daga dakin.
A tsaye ya tarar da Dadah ita da Sakinat a tsaye suna jiran firowarsa.
“Wai dan Gidanku ba na ce ka daina shigowa nan ba ko sai ranar da zan saɓa maka za ka san ko ni wace?.” In ji cewar Dadah dake ta wuci.
Bai mata magana ba ya bangaje Sakinat dake gabansa sannan ya kara gaba.
Tun safiyar ranar zazzabi ya lullubeta gabobin jikinta baki daya ciwo suke mata.
Sabila ce a kusa da ita da cup din kunun gyada a hannunta wanda yayarta ta dan sha kadan ta rage.
“Oh mine Timmy, ki kara sha kadan mana?, na yi waya da su AMMUH suna hanyan zuwa and you’re not taking anything, dan Allah ki taimaka ki sha ko kadan ne.”
“Sabila kamshin kunun nan nashigar min kai, dan Allah ki fitar da shi zai sanya ni amai.” Ta fada tare da fara yunkurawa dan har ga Allah aman take ji.
Ta na cikin kakarin aman ya shigo cikin dakin hannunsa dauke da wani briefcase.
“Mai ke damunta Sabila?.” Ya fada tare da yin cilli da briefcase dinsa tare da nufar wajen da take, ganin haka ya sanya Sabila barin wajen da sauri ta nufi hanyar living room din gidan gabadaya.
Falon shiru yake babu kowa sai karar wakar _Baby one more time._ na babban mawakiyyar nan Britney Spears, wadda ke tashe a wancan lokacin.
Zaune yake a hakimce a babban falon gidan nasu ya na controlling TV din da remote din hannunsa, Jin takun kafar mutum shi ya sanya shi fadin “Shamsiyya get me some water.” ya fada ba tare da ya dago ya ga wacece ba.
Jin shiru kuma babu alamun za a shiga kitchen din ne ya sanya shi dago kansa tare da kallon kyakkyawar budurwar dake gabansa.
Ita ma kallonsa take babu ko kiftawa, ganin sun hada ido ne ya sanya ta dauke kanta tare da juyawa ta bar wajen.
Shi kam tun da ya kalleta ya ji yana son samunta a matsayin mallakinsa dan babu ruwan sa da wata Shema’u.
Ko da ta gama aman bai bi ta tata da ta ke cewa lafiyarta kalau ba ya shiryata tare da tattara ta suka wuce hospital.
Sai da suka yi zaman jiran awanni biyu sannan results ya fito ta na dauke da cikin wata biyu.
Wanda hakan ya yi daidai da last intercourse dinsu.
Sai da ya yi sujjadul shukr amma still bai yadda da hakan ba sai da suka biya hospitals har biyu aka tabbatar da hakan.
Bai kudurci zai fadawa kowa ba, hakan ya sanya shi direct gidan Yaya Shattimah ya yi da ita.
Sai da ya yiwa Auntyn bayani, ta nuna farincikinta sosai ba kadan ba sannan ta ce ya kawo mata Sabilar nan ita ma tun da ba kowa a gidan wanda ta sani.
A kwana a ta shi har cikin Fattumah ya yi wata biyar kuma babu ranar da zai zo ya wuce ba tare da Jalal shi da kaninsa Jamal sun zo dubata ba.
Wasa wasa haka soyayya mai karfi ta shiga tsakanin Jamal da Sabila, da ya dauki son duniya ya daura mata .
Bangaren su Dadah kuwa ko Sakinat ta samu ciki sai ya bi ta makwarara, abin duk ba a cewa komai.
Kuma har yau ko da wasa Jalal bai sanar da su cikin dake jikin Fattumah ba, kuma suma basu damu su ji inda take ba……
> IMAM ZAID ONLY ON PENDING AMARYA’S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY 🥰
~///Soft Noorah///~
> PENDING AMARYA😘
> FARIDATOOL NOOR🥰🙌🏻
> THE ODOGWU WRITER ✍️