TUHUMA!

Chapter 2

by @mamananalbarkace777

*⚖️TUHUMA!⚖️*

*🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️*
   

             PAGE 2️⃣ 

     *ALHAJI BATURE HAUSE.*

 Yadda ake buga ƙofar da ƙarfi kamar za'a ɓalla ta, hakan yasa  Malam isuhu mai gadi da ya zagaya bayi kama ruwa fitowa a gigice ya nufi bakin gate yana faɗin "Lahaula walak'uwwata..."bai kai ga ƙarasawa ba yaji an danna zagi ance "Za ka buɗe ƙofar ne ko sai na hauro na buɗe?."
Hannun sa na rawa ya fara kokawa da ƙaton gate ɗin ya buɗe, yana jin zuciyarsa cikin tsoro kamar zata faso ƙirjin sa ta fito, ganin wanda ke tsaye jikin mota ya zuba masa ido.

Matashin saurayi ne fari dogo kakkaura yana da faɗin ƙirji, tubarkallah kyakkyawa ne, amma da gani shaye-shaye ya masa muguwar illar, dan bakin shi har ya koma baƙi, sai manyan idanun shi da suka ƙara fitowa sosai, ga wani uban kwalli da ya ranbaɗa kamar wanda yasa da taɓarya.
Sanye ya ke cikin riga da wando irin na gayu jibga jibgan, ya zamo wandon ƙasa sosai har ana ganin rabin wandon shi na ciki, kan shi yasha wani irin aski irin na ƴan iskan nan, sai wani cije baki irin na riƙaƙƙun ƴan daban nan.

Hannun shi riƙe da makullin mota ya na kaɗawa fuskar nan a haɗe cike da fushi ya ɗaga murya irin ta ƴan daba yace "Kai Isuhu uban me kake nake ta buga ƙofa ka share ni?."

Da sauri Malam Isuhu ya ja  baya cikin rawar baki yace "Ka yi haƙuri wallahi na je kama ruwa ne."

"Dallah Malam matsa ka bani waje, ko na shiga motar nan na bi ta kan ka, daraja ɗaya ka ci kai babbane, yau da na nuna maka ɗanyen kai."

Da sauri Malam Isuhu ya matsa tare da sunkuyar da kan shi cikin ban haƙuri yace "Ka yi haƙuri hakan ba zata sake faruwa ba."
Bai ƙara bi takan Malam Isuhu ba, ya juya tare da shigewa motar shi, a guje ya sawo kai cikin gidan ya tunkari wajen parking, ko gama gyara parking ɗin bai yi da kyau ba, ya buɗe ƙofar motar ya fito cikin izza da jin kai ya tunkari Ainahin cikin gidan.

Wani irin katafaren gida ne mai ɗaukar hankali, wanda aka zuba maƙudan kuɗaɗe wajen ginin shi da ƙawata shi. Da zarar ka shiga ta ƙaramar ƙofa, daga gefen hagun ka za ka ci karo da ɗakin mai gadi, daga gefen dama kuma wani babban wajen ajiye motoci ne, cike da manyan motoci na alfarma har guda tara, duk da haka akwai sauran fili mai faɗi da zai iya ɗaukar wasu motar cin biyu zuwa uku.

In ka kalli gaban ka kuma, akwai jerin gine-gine guda shida da aka tsara iri ɗaya sashi-sashi, (part by part). Sai kuma wani katafaren gini wanda ya kasance a ƙarshe, duk yafi sauran girma da ɗaukar hankali, kasancewar yana da bene painting sa ma ya banbanta da sauran.
Baki ɗaya an kewaye harabar gidan da kyawawan fulawowi masu kayatarwa, hakan ya ƙarawa gidan wani irin kyau na musamman.
Kai tsaye saurayin ya nufi sashin dake tsakiya, wanda ya kasance na uku daga cikin gine-ginen, tura ƙofar farlon ya yi da ƙarfi ba tare da sallama ba.

Gaba ɗaya farlon sai da ya amsa ƙarar banka Ƙofar da ya yi, a tsorace ƴammatan dake zaune su uku a farlon suna ta hayaniya, sakamakon film ɗin India na faɗa da suke kallo, suka wani irin juyowa kowacce ta na faman zazzare ido.

Tsaye ya yi a bakin ƙofar, tare da sa hannu ya dafe saman Ƙyauren, yana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya.

Nan fa suka shige laluben ɗan kwali, suna rige-rige wajen ɗaurawa, kasancewar dukan su kan su ba ɗankwali kuma sun san halin shi, yanzu zai kai duka.

 "Sannu da zuwa Ya Sa'id."
Suka haɗa baki wajen faɗar hakan a tare.

Ko kallo basu ishe shi ba, ya fara takowa cikin farlon, kai tsaye ya doshi inda TV take ya ɗauke remote ya kashe kallon, ya juya ba tare da ya yi magana ba ya sa kai bedroom ɗin dake can ƙarshe.

Haɗe kai ƴammatan suka yi ƙasa-ƙasa ɗayar tace "Hamida mun shiga uku ya dawo."

"Ke dai Na'ima ki yi addu'ar Allah yasa ya tattara ya koma inda ya fito."
Cewar Hamida kenan.

Ɗayar na ƙoƙarin magana suka ji Muryar shi cikin tsawa yace "Ku ina Momcy?."
Miƙewa tsaye wadda aka kira da Hamida ta yi tace "Tana baya ta je shanya kaya, bari na kira maka ita." Ta yi  hanyar barin farlon tana addu'a a ranta akan Allah yasa kar ya dakatar da ita, dan daga nan sashin Hajiya Kaka zata gudu, dan ba za ta iya da masifar shi ba.
Sai dai addu'ar ta bata amsu ba.

"Kee dawo, ko na aike ki ne? bayan nan kuna me ku ke, ku ka bari Momcyna na wanki da kanta?."

Jiki na rawa Hamida ta dawo ta sunkuyar da kanta, sauran ma duk sai jikin su ya fara rawa aka rasa mai magana a cikin su.

Takawa ya yi ya tsaya a tsakiyar farlon yana wani irin ciccijewa yace "Na rantse da mai busa min numfashi, duk ranar da ku ka bari na dawo na tarda Momcy na aiki, ku kuna zaune sai na ɓalla ƙafar yarinya, wannan ɗin doka ta ce." Yana gama faɗar hakan ya sa kai ya fice.

Wata irin ajiyar zuciya Hamida ta sauke ganin ya fita, ta kalli su Na'ima tace "Mun godewa Allah bamu shiga hannun wannan mugun ba."

Da sauri Na'ima ta miƙe ta kalli ɗayar tace "Ke Salama ki tashi muje mu ɗora girki, kafin Mom ta faɗa masa ba mu yi ba, kin dai san abinda zai aikata."
A guje suka tashi suka yi hanyar kitchen.

Hamida ta bisu a baya tana jan tsaki, ganin yadda suke rawar jiki yasa tace "Haka kawai mutum duk ya bi ya uzzura mana, shikenan kowa a gidannan yana da masu aiki mu mun zama kamar jakai, ya kori masu aiki saboda tsabar mugunta."

Na'ima da ta kunna gas tana ƙoƙarin ɗora tukunya ne, ta kalli Hamida cike da takaici tace "Ai ni babban baƙin ciki na, shine yadda ya dage sai ya maida mu kamar waɗan can jakan yaran, da uwar su ta maida marasa gata kamar yayan talakawa."

Tsaki Salama ta ja tace "Ni dai ku daina maganar nan, kun san shi da kunne kamar na maciji, kar ku je ku ja mana duka a banza."

"Dallah rufe mana baki, mara zuciya ke kullum bakya so ki ga ana maganar wannan annamimiyar matar."
Hamida ta faɗi hakan cikin dakawa Salama tsawa.

Ficewa Salama ta yi a kitchen ɗin, ganin sun rufar mata suna zagin ta, nan suka cigaba da maganganu suna aikin ransu a ɓace.

A baya ya tarda mahaifiyar tashi tana shanya kaya, babbar mace ce doguwa baƙa kakkaura, tana da ɗan kyanta gwargwado sai dai ba za'a kira ta da kyakykyawa ba kai tsaye.

Tana ganin shi ta ajiye botikin hannun ta tare da buɗe hannayen ta, ta washe baki fuskar ta ɗauke da fara'a tace  "Oyoyo ɗan gidan Momcyn sa, daga ina haka rana tsaka Allah yasa lafiya?."

Yana wata irin tafiya ta gayu ya ƙarasa kusa da ita, tare da rungume ta ya kwantar da kan shi a kafaɗar ta yace "Momcyna komai lafiya, kawai dai na dawo a gajiye ne, kuma babban dalilin Dawowar tawa ma shine kuɗin hannuna ya yi ƙasa sosai."

Janye jikin ta ta yi, ta riƙe hannun sa suka fara tafiya tana faɗin "Mu je na baka abinda ya samu, amma fa sai dai ka yi haƙuri da abinda ka gani dan jiya na tura kuɗi China akan kayan da za'a kawo min.

Zame hannun sa ya yi ya ɓata fuska yana kallon Mom ɗin nasa yace "Gaskiya Mom kuɗin da nake buƙata suna da yawa, in baki dasu kawai ki faɗa min sai na je wajen Mamy na amsa."

Wani irin kallo ta watsa masa nan da nan fara'ar fuskar ta ta ɗauke, jin ya kira sunan maƙiyiyar ta wadda tafi kowa tsana a duniya, cikin nuna ɓacin ranta a fili ta nuna shi da hannu tace "Wato Sa'id kai ba zamu iya magana tsakanina da kai  lafiya mu ƙare ba, sai ka sako min maganar wannan shegiyar matar ko?."

Ɓata fuska ya yi shima tare da ɗaga mata hannu yace "A'a fa Momcy, kar ki zagi Mamy a gabana hakan na ɓata min rai, in za ku yi faɗan ku, ku yi a tsakanin ku amma ni dukan ku iyayena ne."

Kamar wadda ya watsawa wuta haka ta taso tana nuna shi da yatsa cikin faɗa tace "Ahir ɗin ka Sa'id, akan wannan maganar taka zan iya rufe ido na cima mutumci, saboda kai ɗin ɗana ne da na sha wahala na haifa, babu ta inda ta zama uwar ka har abada kuma ba za ta zama ba."
Ta ƙarasa maganar tana sakin huci.

Nan da nan idanun Sa'id suka birkice alamar ɓacin rai, wani .wahalallen numfashi ya fara saukewa kamar tsohon zaki.

Nan fa ta cigaba da zagin shi cikin ɗaga murya, tana aibata shi tana kiran sunan Hajiya Bilkisu tana zagi.

Hajiya A'isha ce da sashin ta ke kusa da su, jin hayaniyar Mom ɗin yasa ta fito tana faɗin"A'a Hajiya Habiba wai ke da wa ye  na ji kina ta faɗ.."
Maganar ce ta maƙale ganin wanda ke tsaye, nan tasa hannu ta dafe ƙirji tare da zaro ido, da tasan da wanda Hajiyar ke magana da ba ta yi gigin fitowa ba, dan ba za ta manta haɗuwar su ta ƙarshe ba, da uban marin da ya sauke mata wanda har yanzu kumatun ta, bai gama dawowa daidai ba, ji take kamar yanzu ya mare ta.

Kuma a dalilin irin haka ne, ta zo ta tarda Mom ɗin na zagin shi ta sa baki, harda ɗaga hannu ita a dole uwa ta sauke masa mari, ƙarshe ya rufe idon shi ya sauke mata lafiyayyun maruka guda biyu.

Kuma haka ta haƙura, bata da yadda za ta yi dan duk gidan shakkar shi ake, koda ta sanarwa mijin ta cewa ya yi me ya kaita wajen su, ai ta san Sa'id bai da mutumci baya ganin girman kowa ta mare shi.

Shi kam yana ganin Hajiya A'isha ta juya, shima ya juya a fusace ya bar wajen.
Yana jin takaici akan zagi da albatawar da mahaifiyar tashi ke yi gare shi, bata san illar da hakan ke yi a gare shi ba, duk da ya san shi ɗin ba mutumin kirki bane, amma ya san daraja da girma na iyayen shi.

Tana ganin wucewar shi ta ja tsaki, saboda ɓacin rai ko botikin bata ɗauka ba ta nufi ciki tana banbamin faɗa.

Su Hamida ta tarda a kitchen ta daka mu su tsawa tace "Duk ku fito daga kitchen ɗin nan, babu ƴar da zata ƙara shiga kitchen ko yin wani aiki, yanzu zan kira Zainabu mai aiki ta dawo bakin aikin ta."

Wani irin ihu Na'ima ta buga, ta yarda albasar dake hannun ta ta rugo ta rungume Mom ɗin nata tana faɗin "Wayyo daɗi Mom Allah ya bar mana ke, wallahi mun ji daɗi ni dama ba son shiga kitchen ɗin nan nake ba."

Ita ma Hamida rungume Mom ɗin nasu ta yi tana faɗin "Mom kin cecemu, hala Ya Sa'id ya yarda a dawo da mai aikin ne?."

Zamewa Mom ta yi daga riƙon da suka mata, tana tuna maganganun Sa'id waɗan da tuna su ke ƙara mata zafi a zuciya, ta zauna a kujera tana faɗin "Wai ni Sa'id zai kalla yace na daina zagin Bilkisu, saboda ta riga da ta shanye shi." Nan ta kwashe komai ta faɗa musu.

Dukan su sun yi mamakin maganar da aka ce Yayan nasu ya yi, dan sun san yana daraja Mom ɗin nasu, duk da yana shiri da Hajiya Bilkisu matar Yayan mahaifin su, amma basu zaci haka daga gare shi ba."

Zama suka yi, suka shiga zuga mahaifiyar tasu akan daga yanzu kar ta ƙara bashi kuɗi, ta bar shi da Hajiya Bilkisun zai gane darajar ta.

Haka suka dinga ƙullawa suna kwancewa, nan Mom ɗin ta ɗauki waya ta kira ƴar aikin ta ta da, wadda Sa'id ya kora a cewar shi tunda su Hamida sun zama ƴammatan, to su za su dinga aikin gidan, kamar yadda ƴaƴan hajiya Bilkisu ƴammatan ke yi, bata taɓa yarda da ƴan aiki komai su su ke yi duk da suna zuwa makaranta.

 Su huɗu ne zaune akan Dining ɗin, kowanne gaban shi da abinci  suna ci cikin nutsuwa, Babbar mace ce  kyakykyawar gaske fara tas kamar ka taɓa ta jini ya fito, sanye take cikin ɗinkin riga da zani na atamfa, ta yi irin ɗaurin nan wanda ake sokewa a ƙeya me kama da ture kaga tsiya, abincin take ci tana danna wayar ta da alamar tana wani abu mai muhimmanci.
Hajiya bilkisu kenan, mata guda tilo a wajen Alhaji Abubakar Bature gwani.

Gefen ta kuwa Yaranta ne su uku, biyu mata ɗaya namiji, wadda ke kusa da ita ta kasance kyakykyawa kamar mahaifiyarta, sai dai ita fatar ta baƙa ce, kuma bata da jiki sam irin ƙaramin jikin nan ne da ita, sai ka mata kallon tsaf za ka fahimci ba yarinya bace, a ƙalla za ta kai shekara ashirin da takwas."
Kubra Abubakar Bature gwani kenan, cikakkiyar lauya mai zaman kanta, wadda a kullum take yaƙi da zalunci dan ganin ta bayyana gaskiya, ta ƙwatarwa talaka hak'k'in sa.

Sai wadda ke gefen ta, ita kuma bata ɗauko kyan Hajiya bilkisu ba da alama mahaifinsu ta biyo, sai dai fatar ta fara ce tas ita ma tana da nata kyan daban.
Autar Hajiya Bilkisu kenan, mai suna Sayyada Abubakar Bature gwani. Zata kai shekara sha tara, a yanzu haka tana karatun Medicine ne domin cika burinta na zama babbar likita.”

Sai namijin shi kuma dama babu ta inda ya ɗauko Hajiya Bilkisu, sai dai kama irin ta jini, dogo ne kyakykyawa amma bai kai Kubra kyau ba.
Sayyid Abubakar Bature gwani kenan, shekarar shi ashirin da biyar, a yanzu haka yana karantar Journalism a Bayero University Kano.

Sallamar da suka ji yasa suka juya dukan su a tare suka amsa, Sa'id ne ya shigo ya zube akan kujerar farlon yana kallon su ganin duk sun zubo masa ido.

Hajiya Bilkisu na ganin ya kwanta a kujera, ta dangwarar da wayar hannun ta, ta miƙe tana faɗin "Subhanallahi Sa'id lafiya ka shigo ka kwanta haka?." Ta Ƙaraso fuskar ta cike da tausayin shi, ta kai hannun ta taɓa wuyan shi ta ji ko da zafi.

Duka yaran suka taso suka nufo inda Sa'id ke kwance, kamar haɗin baki suka ce "Sannu Ya Sa'id.

Ɗagowa ya yi a hankali yana bin su da kallo da idanun sa da suka kaɗa suka yi jawur, ganin yadda fuskokin su suka nuna tsantsar tausayi shi, hakan yasa ya yi ƙoƙarin ɓoye damuwar shi yace "Babu abinda ya same ni Mamy, kaina ne ke min ciwo kawai.

Zama ta yi a kujerar dake gefen shi ta riƙe hannun shi, ta ɗago ta kalli Sayyada fuskar na nuna alhini tace "Sayyada ki zubo masa abincin ki haɗo da maganin ciwom kai ki kawo."

Cikin hanzari Sayyada ta juya ta nufi Dining dan cika umarni Mamyn, ita kuma Kubra sai ta zauna akan kujerar dake kallon wadda Sa'id ɗin ya kwanta, a hankali ta shiga danna wayar ta tana ɗan Ɗagowa tana kallon shi.

Shi kam Sayyid tunda ya masa sannu da farko, bai ƙara magana ba kai tsaye ya koma Dining dan ƙarasa cin abincin nashi, yana gamawa ya yiwa Mamyn sallama ya fita.

Bayan Sayyada ta kawo abincin, Hajiya Bilkisu da kanta ta taimakawa Sa'id ya tashi, ta ɗora filet ɗin abincin a gefen shi tace "Maza ka ci abincin kasha magani."

A hankali ya ɗauki cokalin yana kai lomar abincin kamar baya son ci, yana kallon Mamyn da yanayin yadda take nuna tsantsar damuwa akan shi, har ma da ƴaƴan ta waɗan da sun ma fi ƴan uwan shi waɗan da suka fito ciki ɗaya nuna masa kulawa.

Ita kanta Mamy yadda take nuna masa soyayya, ko Momcy da ta kawo shi duniya iyaka cin abinda za ta masa kenan, sai dai ina sam Momcy bata son gaskiya a rayuwar ta, zata iya bashi ko nawa ne ya je ya kashe ba tare da ta tambaye shi me zai yi da su ba, babu ruwan ta da abinda ya ke aikatawa duk da tasan shi ɗin ɗan daba ne, haka bata taɓa masa faɗa ko nasiha ba, kullum sai zagi da albatawa musamman in ya yi magana akan Mamy.

Wadda Mamy ta kasance facalar ta ce, wato matar Yayan mijin ta.

Kaɗan ya ci, ya ture filet ɗin yace "Mamy na ƙoshi."
Kallon shi ta yi ta girgiza kai tace "Ka ƙara abincin Sa'id, yau kwanan ka nawa baka kawo mana ziyara ba?."

Hannu yasa ya shafa cikin shi da ya ke a shafe kamar babu ƴaƴan hanji ya narke fuska yace "Allah na ƙoshi sosai Mamy."

Shafa kan shi ta yi tana murmushi tace "Ka ƙara cokalin ɗaya dai."
Babu musu ya ƙara kamar yadda tace, ta Ɓalla maganin ciwon kan ta buɗe masa ruwan gorar da Sayyada ta ɗauko, sai da ta ga yasha maganin ta ji hankalin ta ya kwanta.

Miƙewa tsaye ta yi ta kalli su Sayyada dake hira ƙasa-ƙasa a gefe, dan sun san baya son hayaniya tace "Ku tashi mu wuce ƙaramin farlo mu barshi ya huta."

Riƙo hannun Hajiya Bilkisu Sa'id ya yi, ya watsa mata idanun shi da suka ƙara yin ja yace "Mamy kar ki tafi, dan Allah ki zauna ina son magana dake."

Tana ganin hakan ta koma ta zauna, ta kalli su Sayyada tace "To ku tashi ku shiga ciki ku bamu wuri."

Yana ganin sun tafi ya warware ya fuskanci Hajiya Bilkisu fuskar shi cikin nuna damuwa yace "Mamy kuɗi nake buƙata."

Kallon shi take tana jiran ya cigaba da magana, shima ya san abinda take nufi da shirun nata, so take ya faɗa mata abinda zai yi dasu Sannan.

"Mamy ina son taimakawa Dauda ƙaura ne, a yanzu haka an kai mahaifiyar shi asibiti dalilin wasu ƴan iskan gari, da suka haura gidan su jiya suka mata mugun sara a ƙafa, har ta kai an ce sai an yanke ƙafar ta ta baki ɗaya, saboda yadda suka daddaƙa ta."

Da sauri Mamy ta runtse idon ta jin abinda ya ce tace "Subhanallahi, Sa'id kaga illar abinda nake faɗa maka ko?."
Ta ƙarasa maganar fuskarta cike da tausayi, kamar za ta yi kuka.

Cikin kakkaurar murya yace "Ki kwantar da hankalin ki Mamy, in dai mu ne wallahi sai mun ɗauki fansar abinda aka aikata mata, ai rai bai fi rai ba, jiki kuma bai fi jiki ba."
Yanayin yadda ya ƙarasa maganar har wani ɗaga hannu ya ke, yana sarawa irin na riƙaƙƙun ƴan daba ɗin nan.

Nan da nan Fuskar Mamy ta canja ta riƙe shi cikin nuna ba ta ji daɗin abinda yake ba tace "Sa'id ka nutsu ka saurareni, a kullum ina faɗa maka ka nutsu ka watsar da harkar daba, ka fita a cikin ƙungiyar yaran nan kai ba irin su bane, ba matsayin ku ɗaya ba. Kai da ka taso cikin babban family irin na Alhaji Bature gwani, bai kamata ace ka lalata rayuwar ka wajen biyewa ƴan iskan gari kuna aikata ɓarna ba."

Tunda ya ji ta fara magana, ya sunkuyar da kanshi jiki a sanyaye yana sauraren ta.

Ta riga da ta san ba zai taɓa cewa komai ba, har ta gama faɗan nata, dan haka ta cigaba da masa faɗan  kamar haka "Yanzu ga shi kun jawa tsohuwar mutane, haka kawai saboda rigimar ku ta banza da wofi."

Sai da ya gama jin faɗan nata tsaf, dama haka ya ke yi in tana masa faɗa ba zai taɓa magana ba.
Yana jin ta dasa aya yace "Ki yi haƙuri Mamy, lokaci ne watarana zan dawo yadda ku ke so, Ku cigaba da min addu'a in sha Allahu zan canja." 

Wani irin tausayin shi ta ji ya ratsa zuciyar ta, a gefe ɗaya  tana jin zafi akan lalacewar tarbiyyar yaron, bayan da ba haka ya ke ba. A da Sa'id yafi kowanne yaro nutsuwa da hankali da ƙoƙarin karatu a gidan, tunda ya  shiga jami'a gaba ɗaya ya canja ɗabi'un sa, rana tsaka suka gan shi cikin wannan rayuwa ta shaye-shaye da harkar daba, inda babu wanda zai ce ga inda ya samo waɗan nan abokan nashi, duba da yadda ya taso cikin wadata da kulawa ya samu ingantaccen ilimi na addini dana boko.

Taɓa tan da ya yi, shi yasa ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, nan ta dawo da hankalin ta kan shi a sanyaye tace "Nawa ne kuɗin aikin?."

Ɗan shafa kan shi ya yi yace "Dubu ɗari uku ne Mamynmu."

Zuba masa ido ta yi kamar me nazari, ta san ba zai mata ƙarya ba kasancewar Sa'id mutum mai gaskiya, duk lalacewar shi baya taɓa yarda ya yi ƙarya, koda gaskiyar da zai furta za ta haifar da rikici.

"Zan tura maka sai ka je ka biya."
Ta faɗi hakan tana shirin miƙewa.

Da sauri yace "Mamy kar ki tura kuɗin, ki dai bani cash ɗin in akwai."

Komawa ta yi ta zauna tana kallon shi tace "Ka ƙara bari sun sace wayar ko?."

Sunkuyar da kan shi ya yi yace "Mamy a mota na sa charge, kuma na kulle ko'ina a motar na tafi ɗakin Gwaska da makullin, da safe na tashi na tarda motar a kulle kuma an cire wayar."

Girgiza kai ta yi tace " Ba ka da kula Sa'id, duka-duka yaushe aka canja maka wayar, ka ƙara salwantar da ita."

"A yi haƙuri Mamy." Shine abinda yace mata kawa.

"Shkenan zan baka cash ɗin, amma sai ka min alƙawarin a satin nan duka za ka zauna tare damu a gida."

Ɗan jim ya yi kamar mai tunani, daga can ya jinjina kai yace "In sha Allahu zan zauna kodan saboda farin cikin ki Mamy."

Tashi ta yi tace "Ina zuwa."

*WAI SHIN SU WAYE FAMILYN ALHAJI BATURE GWANI?*

*WANNE IRIN SIRRRI NE A ƘULLE  A CIKIN FAMILYN?  ME YE SILAR RIKICIN HAJIYA HABIBA DA HAJIYA BILKISU, SU WAYE SAURAN MUTANEN DA KE CIKIN GIDAN?.*

KU BIYO NI DAN NA WARWARE MUKU WANNAN RIKICIN😃

*Ga mai buƙatar wannan littafin ya yi magana ta wannan number ****

🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️