Chapter 10
*...RIGAR ƘAYA*
BY
SADIYA ABDULRAZAK
PAGE 9
Ashna ba ta fito daga ɗaki ba har dare, Muhasin ta yi tunanin gajiyar hanya ce ya sa hakan don haka ba ta shiga ɗakin ba, sai da aka yi sallar isha'i ta leƙa, ta ganta zaune tana chatting, cikin shigar ƙananun kaya riga da ɗan wandon da kaɗan ya fi pant tsayi, sai da gabanta ya faɗi, amma ta maze ta yi mata murmushi ta ce"Sannu, ko duk gajiyar ce kika ƙule a ɗaki?"
Ashna ta yamutse fuska "Wallahi kuwa duk a gajiye nake".
"Ya kamata ki fito ki ci abincin dare".
"To zan fito, Yaya ya dawo?"
"A'a yana hanya dai".
"Ok thanks".
Muhasin ta juya ta fita zuwa falon, ba ta daɗe da zama ba ya shigo gidan, a tsakar gida ya tsaya ya kira Ashna a waya, ya ce"Ga ni na dawo, yanzu ya za a yi anjima? Gara mu tsara komai".
Ta ce"Ai kai za ka faɗa ba, matarka ce kai ka san yadda za ka ɓullo mata ko?"
"Haka ne, to ina ga zan hana ta kwana a ɗakina, idan dare ya yi nisa na tabbatar ta yi bacci sai na kira ki ki zo ɗakina ko?"
"Nice! Sai ka shigo".
Ta tashi ta fito falon, daidai sanda yake shigowa, sai da gaban Muhasin ya faɗi kunya kuma ta kama ta lokaci ɗaya ganin yadda ta fito da wannan kaya na jikinta, rigar shara-shara ce komai nata ana gani, ga wannan wando da ko gajeren wando bai kai ba, nan take kuwa ta canza fuska, sai da ta ji kishi ya ɗarsu a ranta, duk da tana yi mata kallon ƙanwar shi uwa ɗaya uba ɗaya, amma a wannan zamanin ai irin haka ganganci ne ko da kuwa a gaban mahaifinka ne.
Shi ma Jawad gabansa faɗuwa ya yi, hankalinsa sai ya tashi, bai taɓa zaton haukan Ashna ya kai haka ba, ganin ta nufe shi tana washe baki da fadin "Yaya sannu da zuwa".
Ya sa kishin Muhasin ƙaruwa, ta riga ta ƙarasawa ta shiga jikinsa ta rungume ita ma tana sannu da zuwan.
"Yawwa" Ya amsa ba tare da ya karɓi rungumar tata ba.
Sannan ya fara fadin "Ke Ashna kina nan har yanzu da wannan jin zafin naki kenan, irin wannan shigar haka?"
Muhasin ta ce"Amma ƙanwata kamata ya yi ki dinga haƙuri da zafin, ko zani ne sai ki ɗaura a kai, idan kika kaɗaice sai ki cire ki sha iskar, kuma ma ga AC wane zafi mutum zai ji?"
Sai kuwa Ashna ta turo baki "Au wato Yaya don na zo gidanka shi ne matarka za ta yi min iyaka? Kayan da zan saka ma sai ta zaɓar min? Kawai dai kora da hali ake yi min bari na tafi, wallahi ba zan kwana a gidan nan ba" Ta fara kukan ƙarya ta juya ta tafi ɗaki.
Jawad ya kalli Muhasin da ɓacin rai ya ce "Ke wace irin kidahuma ce wai? Don ta fito a haka sai me? Da kike faɗin da AC ku da ba ku taso a cikinta ba ne take yi muku maganin zafi, amma mu da aka haife mu a cikinta ai mun saba da ita, idan zafi ya yi zafi ba ta hana mu ji zafi, kuma ai kin san muharramata ce dai, don haka ba na so ki ƙara yi min haka, yanzu kin sake ja wa kanki baƙinjini a wajen Ummi, ƙatuwar banza kawai!".
Ya faɗi kalaman ƙarshen ne don su ɓata ranta yadda za ta ƙi zuwa ɗakinsa yau ɗin, ya wuce ɗakin da Ashna take yana cigaba da ƙunƙuni.
Muhasin kan mutuwar tsaye ta yi cike da baƙinciki, a kan ƙanwar shi zai faɗa mata wannan maganganun har da su gorin AC? Wata zuciyar ta ce ita ta ja wa kanta, wata kuma ta ce wulaƙancin Jawad ne kawai, amma gaskiya ta fadawa ƙanwar shi, kuma ita ba ta san ba ta da kunya ba da ba za ta fara ba ma saboda su rabu lafiya.
Yana shiga ɗakin ya haye katifar da take ya janyo ta jikinsa ya rungume, ita ma ta lafe tana cewa "Lallai Jawad kana da ƙarfin hali, wato ba na son zafi ko?"
"To kin gigita ni, anya zan jira daren ya yi nisa? Jikinki yana na da kyaunsa my Ash".
Ya ɗago ta yana kallonta, "Kalle ki yar caras komai daidai, kin dai ga matata over size, ina zan kai ta don Allah?"
Ta kwashe da dariya "Kana cikin alheri mutumina, ai ta fi komai baja-baja".
"Hmm ina fa, ni dai sam mai ƙiba ba ta yi wallahi".
Ta ce"Amma kai Jawad ka san da haka me yasa za ka aure ta?"
Ya yi tsaki yana shafa cinyarta "Ke dai bari ai ban san cikakken ra'ayina ba sai da na yi auren, wallahi na ji sam gara marasa ƙiba, duk da yanzu wai ta fara sleeming amma idan na samu 'yar caras ɗin da ta kwanta min aure ta zan yi, ba zan iya ba".
Ta yi masa wani kallo kafin ta ce"Wai kana nufin ka rabu da Hasina ka daina sonta?"
Ya taɓe baki "Yaushe rabona da wannan yarinyar? Wacce ta ce ba ta sona ba za ta aure ni ba? Few days fa ya rage aurenmu ta watsa min ƙasa a ido".
Ashna ta jinjina munafurcin namiji, don har chart ɗinsu Hasina ta nuna mata, amma ta maze ta ce"Haka ne kuma, to ni fa? Me yasa ba za ka aure ni ba?"
Ya yi dariya "Ai Ashna tsoronki nake ji wallahi, tsaf za ki yi aure ki cigaba da rayuwar nan".
Ta ce"Idan ka daina ni ma zan iya dainawa, idan ba ka daina ba mu yi one-one, kai ni fa akwai wani da ya suffanta min wata da yake so, ya ce idan na samo masa zai ban dubu ɗari biyar, wallahi sak matarka, yadda ka san ya ganta ne ya suffanta, da za ka yarda ai sai na haɗa su".
Nan take ya canza fuska "Ke ya ishe ki haka, matar tawa ce za ta yi zina? Kina da hankali kuwa? Kin ga tashi ki tafi idan abin da ya kawo ki kenan, ok kin zo ne dama don ki zauna da ita ki yaudare ta ta amince ko? Tashi ki bar min gida, ko ni maye ne na haƙura da ke".
Ta ɗan rikice don ba ta ga ta tafiya ba idan ba ta yi aikin Hasina ba, ta ce"Haba Jawad wasa fa nake yi maka, har yanzu kana nan da wannan zuciyar taka kenan, wallahi da wasa nake yi, yaushe zan fara zuga matar aure alhalin a matsayin ƙanwarka na zo gidan? Allah ya ba ka haƙuri".
Ya tsaya yana yi mata mugun kallo, ta faɗa jikinsa ta fara kissing ɗinsa, nan take ya fara mayar mata da martani, sai da ta tuna masa da Muhasin za ta ji shirun ya yi yawa samun ya tashi ya fita.
Bai tarar da Muhasin a falo ba, ya san ta yi fushi ne, ya wuce dining ya zauna ya ci abincinsa, yana ci yana waya da Ashna, ƙarshe ta ce ya zubo abincin ya kawo mata, da ya gama ya zuba ya kai mata, bai bar ɗakin ba sai da ya ƙara tattaɓa ta, ita ma sosai ta ƙosa su kasance, ta ma jinjinawa Hasina da ta ba ta wannan damar, a dai yadda ta ga tana kishin matarsa duk da ta kasance 'yar'uwarta, amma ba don haka ba ba abin da zai hana ta ja ra'ayin Jawad ya aure ta, to idan ta yi hakan ɗayan biyu ne zai faru, nasara ko asara, saboda Jawad yana son Hasina zai iya ƙin amincewa, daga nan kuma idan Hasina ta ji ta san ta rabu da ita kenan, ba za ta so hakan ma tun da duk rabin mazan da take taƙama da su suke buɗe mata aljihu Hasina ce ta haɗa su, ta san za ta janye wannan tallafin, amma ta saka a ranta sai ta more shi tass kafin ta yarda asirinsu ya tona a yi plan ɗin da aka turo ta domin shi.
Muhasin kuwa da ta koma ɗakinta zama ta yi tana hawaye da ba ta yi mata wuya, ta nemi waje ta kwanta tana tunanin wane irin raini mijinta ya yi mata haka, kuma ƙanwar tashi wace irin mara kunya ce haka? Indai haka wayewa ce to Allah Ya wadaran irin wannan wayewar, a ce ki zauna a inda ba gidanki ba kusan tsirara, kuma shi har yana ba ta goyon baya?
Wayarta ta fara kawo haske don tana silent ne, a haka take barinta tun da suka fara waya da Khalid, yanzu ma da ta janyo wayar shi ne me kira, a yanzu tana kasa banza da kiran shi ne idan ta tuna shi ne wanda ya cece mahaifiyarta, idan ta daina kula shi kamar zai ga ta ci moriyar ganga ne ta ya da koranta.
"Assalamu alaikum".
"Wa alaikumussalam, babyna ya daren?"
"Alhamdulillah".
"Me kike yi ne?"
"Ba komai ina kwance kawai".
"Ji nake kamar na zo na taya ki fira, inda ni ne mijinki ba zan dinga firar dare a waje ba, ina liƙe a wajenki wallahi, amma wannan mijin naki da yake shashasha ne wai ba ya kusa da ke".
"Hmm shi ma ya dawo yana gidan ai".
"Shi ne kuma kuke waje da ban da ban? Ko live yake yi?"
Ta sauke numfashi kafin ta ce"A'a fa, wata ƙanwar shi ce ta zo" Ta tsinci kanta da kwashe komai ta ba shi labari
Cikin kuka ta kare da faɗin "Ya kamata ya ci min mutunci daga ɗan wannan?"
Khalid ya yi shiru yana nazari kafin ya ce "Kika ce sunanta Ashna? Ya kamanninta suke?"
"E Ashna, siririya ce doguwa haka, ba wata kyakkyawa ba".
Ya yi 'yar dariya "Ke dama ai ba za ki ga kyaun ba, kuma ba wannan ne ya kamata ta kasance a gaban ki ba, ke yanzu kin yarda ƙanwar tasa ce da gaske?"
Ta ce"E mana, me zai zaka ya yi ƙarya?"
"Son zuciyarsa mana, ni ban yarda ƙanwar shi ba ce, yadda kika suffanta ta ma sai na ji kamar na santa, kuma abin da ya sa na yi wannan tunanin shi ne ma san wata ƙawar shi mai irin sunan, tana yin tiktok ko yanzu ki yi searching sunan indai ita ce tabbas za ki ganta, amma Ash Baby za ki saka".
Zuciyar Muhasin ta dinga bugu, ta ce"To bari na duba"
Da sauri ta kashe wayar ta tafi tiktok.
Khalid ya sauke numfashi ya ce "In sha Allah yau wannan auren zai mutu, domin Hasina ce ta tsara masa hakan shi ma, ta faɗa masa ga halin da ake ciki ta tura wata gidan, ya ƙara da wannan idea don abun ya tafi daidai, shi ma kuma ya so haka ɗin, yana son aurenta ya mutu, amma ba ya so ya kasance laifinta ne ya zama sila, shiyasa da ya ga wannan laifin mijin za a gani ya yarda ya aiwatar.
Muhasin tana searching sunan da ya faɗa mata ta ga vedios sun bayyana, nan take ta miƙe zaune don ganin ƙanwar Jawad ta bayyana, ta shiga account ɗin nata ta ga sam ba ma abun arziƙi take yi ba, ta kashe data ta kira Khalid, ya katse ya kira ta, ta ɗauka ya ce"Babyna ya ake ciki?"
Da sauri ta ce "Ita ce, wallahi ita ce".
Ya ce"Na sani ai, tun da Jawad ba shi da ƙanwa mace da suke uwa ɗaya uba ɗaya ai, kuma wannan yarinyar na san shi da ita dama da daɗewa, ƙawar shi ce, ko na ce karuwarsa".
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ta furta tana dafe ƙirji
Ta ce"Kenan yanzu kana nufin raina min hankali za su yi? Zuwa suka yi su yi a cikin gidan?"
Ya ce"Ƙwarai kuwa, ita ai tsarinta ba ta zuwa hotel sai dai namiji ya kai ta gidansa, ina ga shi kuma ya matsu da ita shi ne ya miki wannan ƙaryar".
Kamar za ta yi kuka ta ce"Wai kana nufin zina za su aikata a gidana?"
"To Muhasin ba kin zauna ba kin nace sai kin rayu da shi? Nan gaba ƙaryar ma ba zai yi miki ba, ai nan ana sakaya miki hali ne tun da ke amarya ce, nan gaba a falo za su kwantaa idan ya kawo mace, tun da ya gama raina ki, kuma sannan ba sonki yake ba".
Ta fara hawaye "Khalid wannan wane irin cin mutunci ne Jawad ya min? Wa nake aure? Duk rashin zuciyata ba zan ɗauki wannan ba wallahi, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un".
Cike da zuga ya ce"A to idan kin zauna ya yi ɗaya ya ji daɗi gobe idan ya kawo wata sai ya ce yayar shi ce, wataran ma ƙanwar babar shi, ke kuma kina nan sake da baki".
"Ya zan yi yanzu?"
"Ya za ki yi kuwa? Akwai abin da za ki yi wanda ya wuce ki bi dare ki je ɗakin nasa ki kama su ido da ido?"
"Kenan ma sai na ba su damar da zai taɓa ta ɗin, ba zan jure ko hannun wata ya taɓa ba, duk da na san yana yi amma wannan a cikin gidan nan fa, ba zan jure ba wallahi".
"Za ki jure mana, idan ba ki ita kama ɓarawo ba sai ɓarawo ya kama ki, yanzu idan kika yi kare su ina hujja? Please ki bari kamar ƙarfe biyu na dare haka sai ki je ki gani, na yi miki alƙawarin zan taya ki fira har lokacin".
"Har kana tunanin zan iya wata fira da wannan tashin hankalin da nake ciki? Sai anjima Khalid na gode, zan ɗauki matakin da ya dace".
Ta katse wayar ta sauka daga gadon, tana tunanin ta bi shawarar zuciyarta ko ta Khalid?
FIRDAUSI
Washegari duk samarin da suka nuna suna sonta sai da suka kira ta a waya, duka sun ce za su zo a ranar, KB ne ya zaɓi wanda zai zo, don yana tunanin ya fi sauran gwaɓi-gwaɓi, ya kalli yadda take bata rai ya ce"Sis ya dai? Ko ba shi kike so ya zo ba ne?"
Ta ce"Bro ni ai ba na gane abin da kake nufi, a ce maza wajen nawa kuma ka ce suka na amince da su, To wa zan aura kenan?"
Ya yi tsaki "Ke ta aure ma kike yi kenan? Haba dai sweety, nawa kike ma da har za ki fara zancen aure? How old are you? Just twenty two fa, ina ke ina aure yanzu? To ni wallahi har yanzu ban ga kalar namijin da zan iya amincewa ki aura ba, don haka ki ma ajiye wannan batun a gefe, ai yanzu ki saka a ranki ke wani hannun jari ce, aka zuba ki a kamfanoni masu yawa, za mu nutsu ne mu yi kallon kasuwancin muna yin gefe da riba, idan ribar ta isa muka fi ƙarfin talauci, muka ci mutuncin talauci sannan sai mu fara tunanin wane company ne ya fi kawo riba? Kin ga kenan sai mu tattara duka mu tafi can, ma'ana sai ki aure shi kuma, wannan riba kuma kin ga sai na dinga juya mana ita, ke ma kina ciki kina ƙara warto wani abun, don gaskiya kafin ki yi aure sai mun siya danƙara-danƙaran gidajen guda biyu, mun zuba 'yan haya, sannan a siya filaye a unguwa masu daraja a ƙalla guda goma, a kuma siya motoci a ba da haya ko guda biyar ne".
Da tsoro a fuskarta ta ce"Yaya amma wannan burin bai yi yawa ba kuwa? Wannan ai ba zai yiwu ba, ina da kyau amma bai kai wanda kake nufi ba fa".
Ya yi dariya"Ai zai kai ne, aff na manta".
Ya karkace ya fito da magani a aljihunsa"Ga wannan na kara ƙiba ne, duk da za su saka ki bacci da cin abinci, amma dole sai da haka, na ga kamar sabayar ba ta sauri mu kuwa kin ga sauri muke yi ko? Ki fara da su, sannan an ce akwai wasu ƙwayoyi ma da suke ƙara haske da kyau, su ma zan siyo idan wasu kuɗi sun samu, ina sha Allah komai zai tafi normal my sister".
Ta karɓa tana cewa "Allah Ya sa".
Ya ce"Good girl, yawwa wanda zai zo ɗin nan ki ce ya taho miki da kaza mana, na ga yau tuwo Kaka take yi ko?"
Ta ce"To bari na faɗa masa".
Tun daga wannan lokacin Firdausi ta saba da kula samari kala-kala, kuma kowanne tatsar shi suke yi, ana haka me Mukhtar ya yi zancen aure don tsakaninsa da Allah yake sonta, kuma a shirye yake, nan take KB ya yi tsalle ya dire ya ce aure ba yanzu ba, Kaka kar haɗa shi ta yi da danginsu, ma ya ce shi bai yarda da nagartarsa ba, kuma ya hurewa Firdausi kunne ita ma ta ce ba ta son shi, saboda tana ganin yayanta shi ne gatanta, kuma komai yana yi ne saboda ƙaunarta bai kamata ta bijire masa ba, haka tana ji tana gani Mukhtar ya daina zuwa.
Babu jimawa kuma Kb ya zo mata da wani zancen, wai abokinsa ne ya nema mata aiki a wani waje, maza ne suke taruwa 'yan'mata suna yi musu tausa, suna biyan dubu hamsin kullum, KB ya lissafa ya ga idan fa dubu hamsin tana shigowa kullum ba ƙaramin kuɗi za a tara ba a shekara ɗaya, don haka komai zai faru dole ne Firdausi ta amince da zuwa tausar nan har na tsayin shekara ɗaya.
*LAST FREE PAGES*
*LITTAFIN KUƊI NE A KAN NAIRA 700, DAGA WANNAN PAGE ƊIN AN GAMA FREE PAGES, KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI*
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
***