SARTSE A ZUCI.....! Chapter 13
*SARTSE A ZUCI...!💔* *Arewabook@ayshadansabo*
*Paid book ****
©️ _Ayshat Ɗansabo Lemu_ ✍🏻
*Chapter 13*
Kamar yadda Iyayen Nadeeya haka suka buƙata haka aka aje magana cewa da zaran ta kammala service ɗinta za a saka lokacin aurensu,Aman Kurfi shima sai ya fara shiri domin a tsarinsa shima yana buƙatar a haɗa bikin ayi gaba ɗaya tare da shi da Amal Taheer kamar yadda ya sanar mata ta kuma bashi goyan baya.Sai dai ya bar abin a cikinsa bai sanar dasu Abbansa ba ganin a kwanakin Abban bai cika wani lafiya ba cutar cancer da yake ta ɓoye musu yana da ita ta fara cin ƙarfinsa duk da cewa yana kiyaye shan magunguna da duk wata doka da aka gindaya masa,sai kawai ya cigaba da shirinsa kuma a daidai wannan tsukin aka bijiro da tsarin rage ma'aikata a babban bankin Nigeria inda yake aiki.Sai dai a cikin tsarin akwai baiwa wasu daga cikin ma'aikata damar suyi resigning a sallamesu da manyan kuɗaɗe daidai da level ɗinsu basai sai sun jira kora yazo kansu ba,kuma a cikin waɗanda suka zaɓi tsarin aje aikin gabannin sallamar har da Aman Kurfi a ciki domin a cikin shekaru huɗu da fara aikinsa yaji cewa ya gaji da aikin Banki domin ba ƙaramin wahala ne da takura dashi ba.Don haka suna cikin sahun farko da suka rubuta takardar shaidar aje aikin don radin kansu kamar yadda aka basu dama,aka kuma sallamesu da manyan kuɗaɗe domin dama shi da level mai girma aka ɗaukeshi ya kuma samu promotion ma.Bayan aje aikin nasa da sallamarsa da akai sai ya fara tunanin komawa jami'ar Robert Gordon domin haɗa PhD ɗinsa duk a fannin Accounting ɗin,sai dai kuma a son ransa baya sha'awar ya tafi ba tare daya mallaki Amal Taheer a matsayin abokiyar rayuwarsa ba.Time ɗin daya fara yima Amal maganar sai ta bashi go ahead akan ya fara processing tafiyarsa domin ita a ɓangarenta bashi da wani damuwa domin shi kaɗai ne zaɓinta,don haka ko bayan ya tafi ne zai iya dawowa suyi aurensu ya ɗauketa su koma lokacin ta kammala service ɗinta domin cika burinsa na zurfafa iliminsa.Don haka kai tsaye ya fara shirye-shirye bayan yayi shawara da Doctor Kurfi shima kuma ya bashi goyan bayan tafiya ya sake zurfafa iliminsa,don haka hankalinsa kwance ya fara processing ta online.Da yake ɗan adam na cikin tsarinsa Allah kuma yana nashi,sai jikin Doctor ya rikice masa a daidai wannan gaɓar da Aman ke daf da cimma burinsa na tafiya UK.Ciwo sosai ya kwantar dashi kuma sai a lokacin suka san cewa yana fama ne da cutar cancer ta mafitsara,hankalin Iyalansa yayi mummunar tashi musamman Aman Kurfi da shi kaɗai ne Namiji tilo da Doctor Kurfi ya mallaka.Wata guda yana jinya a National Hospital Abuja likitoci ƴan Uwansa suka bada shawarar a fita dashi waje tunda babu laifi yana da iko,nan da nan kuwa manyan likitoci suka lalubo asibitin da suke ganin ya dace a fita da shi a ƙasar Cairo Egypt.Wasu daga cikin aminansa dake riƙe da madafin ikon ƙasar sukai ta bada gudunmuwar manyan kuɗaɗe domin a fita dashi ko zai samu lafiya,don haka nan take Aman ya dakatar da shirinsa na tafiya UK domin shi kaɗai ya cancanta ya jagoranci zuwa jinyar Mahaifinsa.Ranar da sukai sallama da ƴan Uwa da dangi suka wuce da Doctor Kurfi ƙasar Cairo,ita kuma Amal a ranar Hameedah ta tashi da matsanancin zazzaɓi da yazo mata da zafin gaske gashi cikinta ya shiga watanni takwas cikin na tara.Yaya Zayd baya nan lokacin yana Lagos satinsa uku da komawa suna tunanin dawowarsa a cikin satin,Amal dake koyon driving a lokacin har ma ta fara hawa titi itace tayi karanbanin ɗaukar Yaya Hameedah zuwa asibiti da gaggawa ganin yadda jikinta yayi zafi sosai.Suna isa aka turasu yin test domin sanin haƙiƙanin abinda ya kawo zazzafar zazzaɓin ga tsohon ciki,kuma result na fitowa aka ga cewa Malaria ce gashi ba a son mai ciki da yin Malaria sabida yana effecting hatta ɗan dake cikin ciki.Don haka da gaggawa aka basu gado domin bata treatment ɗin daya dace,sai da aka kammala yin komi aka basu gado sannan Amal ta samu nutsuwar kiran Yaya Zayd ta sanar masa.Kuma a yadda taji ya gigice ta tabbatar dama bazai iya wuce washegarin ranar bai iso Kaduna ba,tana gama waya dashi Momy ta kira ta sanar mawa halin da ake ciki.Kuma da yake around 11am ne ta sanar dasu zuwa 1pm na rana sai gasu Anty Mamah da Momy har da Jameelah sun iso asibitin domin duba jikin Hameedah,Momy nata jinjina yadda ba a son mai ciki da kamuwa da Malaria amma babu yadda suka iya tunda haka Allah ya hukunta.Sai yamma sosai time ɗin Hameedah ta tashi daga bacci har ta samu taci wani abu tasha magani sannan sukai sallama dasu suka juya Zaria aka bar Jameelah ta kwana ɗaya ta taya Amal da jinya,tare da Jameelah suka kwana da Yaya Hameedah a asibitin kuma washegari da safe Yaya Zayd ya biyo morning flight ya iso.Ƙarfe goma a garin Kaduna tayi masa don ma ta Abuja ya sauka ya ƙariso a mota,don haka Amal data koma gida tabar Jameelah a asibitin tana tsaka da shiryawa Yaya Hameedah lafiyayyen breakfast ɗin data san zaiyi mata daɗin ci Yaya Zayd ya shigo gidan.Kuma wanka kaɗai yayi ya wuce asibitin domin duba lafiyar Hameedah,Amal koda ta kammala girkin tayi wanka ta kintsa driver ne ya ɗauketa ya mayar da ita asibitin.Kuma ga tsananin mamakinta saita tadda Daddy da Yaya Sulaiman a asibitin sunzo duba jikin Hameedah,don haka tana aje basket ɗin hannunta wajensu ta nufa suka gaisa tana sanar da Yaya Sulaiman irin missing ɗinsa da take domin ganinsa yayi wahala Daddy baya barinsa zama kullum cikin tafiye-tafiye suke.Jameelah jin cewa Zaria su Daddy za su koma sai ta tubure za ta bisu,haka nan Amal ta barta ta tafi domin itama Jameelah ta tashi da nata zazzaɓin ne shiyasa hankalinta yayi gida.Babu laifi kuma jikin Yaya Hameedah da sauƙi domin ana bata kulawar daya dace,har bakin mota Amal da Yaya Zayd sukai ma su Daddy rakiya.Suna koma cikin ɗakin da Hameedah take Yaya Zayd ɗin yayi saurin isa bakin bed ɗin da Hameedah ke kwance ya ɗagota tare da bata wani hot kiss a saman forehead ɗinta,wani irin kyawu tayi masa a cikin simple gown ɗin dake jikinta ramar da fuskarta tayi ya sanya kumburin da fuskartata yayi ada ya sace sai fuskar tayi wani fayau kyawu da fresh ɗinta ya sake bayyana.Amal na ganin yadda yake kissing ɗinta hannuwansa na yawo a saman titsetsen cikin Hameedah tayi gaggawar ɗaukar phone ɗinta ta fice ta basu waje,shi kuwa dama haka yake so don haka ya cigaba da nunawa Hameedah soyayya yana sanar da ita cewa yayi kewarta gashi ciwo ya dawo yayi masa tsiyar da ba za a duba shi a bashi kulawa ba.Da kansa ya ciyar da ita abincin da Amal ta girka mata,kuma taci da ɗan dama shima sai ya zauna yaci nasa domin baiyi breakfast ba hot coffee kaɗai yasha a cikin jirgi.Har wajen azuhur yana asibitin nane da Hameedah yana bata kulawa kafin ya fito yayi sallama da Amal yace zai koma gida,ya tambayeta idan tana buƙatar wani abu ta sanar dashi tace babu sai dai ya saka driver ya kawo Babah Gaje domin ta zauna ita kuma ta koma gida ta sake shiryo ma Yaya Hameedah wani abun zuwa can yamma sai ta dawo Babah Gaje ta koma tunda gidan babu kowa sai su biyu ita da Babah Gajen domin Kulu taje ganin gida bata dawo ba.Hakan ko aka yi yana komawa ya sanya Habu driver ya kawo Babah Gaje ita kuma Amal ta koma gida domin tana buƙatar rintsawa ta huta before ta sake samawa Hameedah wani abin,da yake kuma tana off ne ranar baccinta tasha sosai sai after la'asar ta tashi.Gidan tsit da alamu shima Yaya Zayd ɗin ya fice baya nan,don haka wanka kawai tayi ta faɗa kitchen domin yin girki.Ta kammala komi wajen biyar da rabi,don haka kai tsaye ta kira layin Habu ta shaida masa ya gyara parking gata nan fitowa.Tana aje wayar Yaya Zayd na shigowa cikin falon da yake tana zaune ne a cikin falon Yaya Hameedah,kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kansa ta gaidashi ya amsa ciki-ciki yana tambayarta ta gama abinda take ne ta amsa masa.Cewa yayi ta tashi su wuce asibitin zai koma,don haka data wuce zuwa room domin ɗakko jaka da mayafi saita kira Habu ta shaida masa cewa ya barshi ma tare da Yaya Zayd za su tafi.A front seat ta zauna duk ƙamshinta ya gama cika kafofin hancinsa kamar yadda shima nasa ƙamshin ya gama cika motar,satan duban Amal ɗin kawai yake yana mamakin yadda take jin kanta.Ita ko Amal wayarta ta zaro ta kunna data ta hau online har suka isa asibitin babu wanda ya tanka ɗan Uwansa,kuma abin sai ya baiwa Yaya Zayd haushi domin yasan da tare suke da Yaya Sulaiman da tuni ta cika musu kunni da surutunta amma shi da yake ta tsanesa ta maidashi dodonta shiyasa bata sakin jiki dashi suyi hira.A ranar sosai yaji zuciyarsa ta sosu domin yana ƙaunar dukkansu a cikin zuciyarsa don dai kawai shaƙuwarsu da Hameedah na daban ne shiyasa ake kallon kamar baya son Amal ɗin ne,shi kuma Allah ya sani shegen tsiwarta da rakaɗinta ne baya so duk da cewa ya kula tunda ta zama cikakkiyar budurwa tayi aji ta koma miskila babu wannan rawar kan irin na Yarinta ada.Koda suka isa hospital ɗin sun tadda Hameedah ta samu bacci don haka bai wani jima ba yace zai je ya dawo zuwa anjima sai ya tafi da Babah Gaje idan zai koma gida,kuma hakan akai domin yana dawowa bayan sallar Isha'i ya gama duba jikin Hameedah dake samun sauƙi sosai ya wuce tare da Babah Gaje.Kuma tun suna hanya kiran Suraj Galadima ya damesa har saida ya ɗaga wayar tukunna,kuma abinda Suraj ɗin ya sanar masa a cikin wayar ne ya sanya ya dinga sakin tsaki domin sanar dashi yayi wai ga Najwa nan a gidansa yau ta shigo Kaduna daga Katsina shine tazo gidan take masa magiyar ya sasanta tsakaninta da Zayd ɗin domin ta sanar dashi komi daya faru a tsakaninsu a Lagos da irin yadda Zayd yayi blocking line's ɗinta ta daina samunsa a waya.Shi kuma Suraj Galadima da yasan sunyi waya Zayd ya sanar dashi shigowarsa gari shine ya kira domin sanar da Zayd ɗin komi,har suka isa gida tsaki yake ja domin baya son tuna abinda ya shiga tsakaninsu da Najwa a Lagos wanda har yau idan ya tuna abin na damunsa don baisan ya Hameedah za ta ji ba duk randa tasan cewa bayan ita ya taɓa kwanciya da wata mace kuma bata hanyar aure ba.Babah Gaje tana bayan Mota tana jiyo yadda ogan keta jan tsaki har ya faka motar ta fice tana masa sannu da gajiya,koda ya isa side ɗinsa wanka ya faɗa ya fito ya nufi kitchen domin duba ko Amal ta aje masa abinda zaici.Kuma cikin sa a ya tadda ta shirya masa komi bisa ƙaramin dining ɗin dake cikin kitchen,zama yayi yaci abincin yana yaba yadda ta gado Momy wajen iya abinci mai mugun daɗi.Yana kammalawa ya wuce part ɗinsa yayi shirin kwanciya kafin ya sake kiran Hameedah domin jin ya jikin nata,vedio call ya kira suka jima suna magana kafin suyi sallama yana jin wani irin kewar rashinta na lulluɓe zuciyarsa.Sosai yake jinsa cikin wani yanayi domin ɗumin jikinta kawai yake da buƙatar ji a daidai wannan time ɗin,haka ya kwanta yana juyi kafin ya kasa haƙuri ya sake komawa kitchen ya haɗa tea da yaji lemon a ciki yasha kozai samu sassauci.Har yayi tunanin yin unblocking line ɗin Najwa sai kuma ya fasa ya kwanta ya cigaba da juyi har zuwa lokacin da barci ya sacesa,washegari da safe yana tashi around 9am ya kira Amal domin jin ya jikin Hmaeedah domin ya kira yaji line ɗinta a kashe.Amal ta shaida masa cewa chargyn Hameedah ne ya ƙare kuma sun manta da charger a gida ita kanta chagyn wayarta ya kusa ƙarewa,ita ta baiwa Hameedah wayarta sukai magana bayan sun kammala Habu driver Amal ta kira tace ya ɗakko Babah Gaje suzo ya sanar mata cewa ta dafo ruwan zafi ta haɗa da simple breakfast da za ta iya dafawa su taho dashi tunda wayayyace ta iya girki bakin gwargwado.Tana gama waya dashi kiran Daddy ya shigo mata kuma suna cikin magana wayarta ta mutu domin chargyn ya ƙare,don haka sai tayi zaman jiran isowar Babah Gaje domin ita kuma ta samu damar komawa gida tayi wanka ta dafowa Hameedah farfesun liver da tace tana son ci.Babah Gaje sun iso asibitin around 11:30am na safe,Amal bata ɓata lokaci ba ta ɗauki abinda za ta ɗauka ta wuce domin tana son biyawa ta kasuwa tasai veggies da babu a gidan.Shi kuma a ɓangaren Zayd Abdallah yayi wanka kenan ya saka Three Quarter wando da ƙaramar shirt ya wuce zuwa kitchen domin nemawa kansa abinda zaici,toasting bread yayi ya soya egg sai ya dafa ruwan tea daya zuba tea spices a ciki tunda yasan duk inda Hameedah ke ajewa.Anan cikin falon Hameedah ya zauna yayi breakfast ɗinsa,bayan ya kammala ya kira Momy vedio call suka gaisa ta tambayeshi jikin Hameedah yace da sauƙi domin ta kira line ɗinta a kashe shine yake sanar mata cewa wayarta ta mutu babu chargy shima yanzu zai gama kintsawa ya wuce asibitin.Sun gama waya da Momy kenan ya jiyo ana danna door bell don haka ya miƙe ya nufi ƙofar domin ganin ko waye,ta circle ɗin wajen ya leƙa ƙirjinsa ya buga da ƙarfi sakamakon wacce ya gani tsaye a bakin ƙofar.Ya buɗe ƙofar yana haɗe annurin face ɗinsa tamkar bai taɓa sanin miye dariya ba,Najwa wacce ke tsaye ta zuba masa idanu tana jin tsananin kewarsa na sake mamaye zuciyarta domin tun daga randa ta ɗanɗani zumarsa soyayyarsa ya sake girma a cikin zuciyarta ita kaɗai tasan azabar da take sha dalilin yadda yayi watsi da ita.Tambayar daya fara jefa mata shine mai ya kawota gidansa kuma Uban waye ya bata address ɗin gidan ma tukunna? Buɗan bakinta kuma ta sanar dashi cewa Suraj ne domin shi ya yana jin tausayinta tunda shi Zayd ɗin baisan irin halin da zuciyarta ke ciki ba tun bayan rabuwarsu dashi a Lagos.Hanya ya bata ta shiga cikin falon tana ƙarewa tsaruwarsa kallo,wani irin ni'imtaccen ƙamshi daya gama kama gidan ta shaƙa tana sake tabbatarwa kanta da cewa tabbas ta shigo gidan wanɗanda suka san sirrikan ƙamshi da gyara.Da kanta ta samawa kanta wajen zama tana sauke idanunta akan kayan da Zayd ya gama yin kalaci bai kaiga mayarwa kitchen ba,ta saki lallausar murmushi tana tsareshi da wani mayen kallo kafin ta tambayeshi jikin matarsa domin Suraj ya sanar da ita cewa suna asibiti shiyasa ma ta samu ƙwarin guiwar biyoshi har gida domin ta bashi haƙuri su koma kamar da su cigaba da more junansu koda kuwa bazai sake kwanciya da ita ba.Banza yayi mata lokacin da take tambayar lafiyar Hameedah,hakan yasa Najwa tashi tsam ta isa kujerar daya harɗe ƙafafunsa ɗaya kan ɗaya yana watsa mata wani irin kallo.Bata jira komi ba ta faɗa jikinsa tare da fara shafar saman ƙirjinsa tana bashi haƙuri,cikin gaggawa ya tureta daga jikinsa domin baya buƙatar ta sake loda masa wata damuwar bayan wanda yake ciki na rashin samun biyan buƙatar sha'awarsa.Sai dai tana barin jikin nasa ta sake komawa kuma bata jira komi ba ta haɗe bakinsu waje guda,bata barshi haka ba domin hannunta tayi saurin kaiwa wajen data san dole jikinsa ya magantu ya kuma barta tayi yadda take so da gangar jikin nasa.Kuma kafin wani lokaci ta hargitsa nutsuwarsa domin dama a sama yake ƙiris kawai yake jira ya bada kai,cikin zafi-zafi ya fara maida mata da martani ko'ina na jikinsa na sake ɗaukar ɗumi.Time ɗin da yayi nasarar sauke zip ɗin dake jikin pitted gown ɗin dake jikinta bai jira komi ba ya zare rigar yayi wurgi dashi,bra ɗin ma jifa da ita yayi ya fara huce haushinsa akan na shanunta.Ganin hakan ya sanya Najwa saurin rabashi da nashi rigar tana wasa da ƙirjinsa hannunta guda kuma yana can wani wajen daban.Kan kace kwabo sun lula can wata duniya har sun manta a muhallin da suke ma,tuni Najwa ta samu nasarar sauke wandon dake jikinsa zuwa ƙasa tana cigaba da bashi wuta da dukkanin salon data san zai sake kunna wutar fitina a cikin zuciyarsa.A kuma daidai lokacin motar dake ɗauke da Amal ya shigo cikin gate ɗin gidan,kuma tana fitowa daga cikin motar ta nufi hanyar shiga cikin gidan ta ƙofar kitchen ta baya sabida kayan cefanen dake hannunta tafi buƙatar ta fara isa ta aje a kitchen ɗin kafin ta nufi ɗaki.Kuma cikin sa a ƙofar a buɗe yake domin ba a cika rufeshi da key ba tunda ba kowa yasan ana shiga ta wajen bama,kayan hannunta ta aje a saman cabinet ɗin kitchen ɗin tana faɗin cewa ta gaji a bayyane.Kuma batai tsayuwar mintuna biyar a cikin kitchen ɗin tana ware kayan cefanen ba ta fice ta nufi hanyar zuwa room ɗinta,sai dai wani abin daya bata mamaki shine tana dosar hanyar corridor ɗin da zai fitar da ita zuwa falo ta nufi hanyar bedroom's ɗin Yaya Hameedah taji gabanta ya yanke ya faɗi.Bata kawo komi a ranta ba ta cigaba da takawa har ta sanya kanta a cikin falon,a kuma daidai lokacin Najwa ta samu nasara akan Zayd ya fara ƙoƙarin maimaita abinda ya faru a Lagos domin har ya kwantar da ita ta yadda yake buƙata Amal ta danno kanta cikin falon kuma a lokaci guda ƙamshin turarukan da suka haɗu biyu na Najwa dana Yaya Zayd ɗin ya bada wani kalar ƙamshi na daban ya cika kafofin hancinta.Kuma ƙamshin data shaƙa ne ya sanya tayi saurin kai idanunta direction ɗin ba tare da tasan cewa za ta yi mummunar ganin da tasirinsa bazai taɓa gushewa a cikin kanta ba har abada,idanunta na sauka a kansu ta ƙwalla wani irin ihun da yayi saurin maido su Yaya Zayd cikin hayyacinsu har yayi nasarar zare jikinsa daga na Najwa wacce ta gama shiga cikin shauƙin samunsa a ƙaro na biyu.Amal ta sake ƙwalla wani irin ihu tana saurin rintse idanunta sakamakon idanunta da suka sauka akan fuskar Yaya Zayd da kuma gangar jikinsa da babu komi domin Najwa ta rabashi komi na jikinsa,ta ruga a guje zuwa room ɗin Yaya Hameedah wani irin gigitaccen kuka na ƙwace mata jikinta babu inda baya ɓari sabida tsananin shiga tashin hankali.A can falo kuwa Yaya Zayd ne yayi saurin maida wandonsa yana ji gabaki ɗaya duniyar na juya masa,wani irin firgici da tashin hankali na mamayeshi tare da nadamar biyewa Najwa domin sai a yanzu yaga wautarsa na barinta har ta raɓi jikinsa ta sake kunna wutar fitina a cikin zuciyarsa.Ita ko Najwa tsabar takaicin ga ƙoshi ga kwanan yunwa ya sanya ta rushe da kuka,Zayd Abdallah ya ɗaga idanunsa da sukai masifar kaɗawa ya zube a kanta kafin ya daka mata wani gigitaccen tsawar da yayi saurin maidota cikin asalin hayyacinta.Cikin matsanancin ɓacin rai ya saita mata hanyar barin falon yana gaggauta bata umurnin ficewa a cikin gidansa,jikinta na ɓari ta mayar da kayan jikinta ta saitawa kanta hanya tana rayawa a cikin zuciyarta cewa koma wace ce ta katse musu jin daɗinsu bata yafe ba koda kuwa ace itace matar gidan.Har Najwa ta fice ta banko masa ƙofar Zayd ya kasa motsawa,hannuwansa duka biyu tallafe suke da fuskarsa idanunsa sunyi masifar kaɗawa.Kuma daga nan inda yake zaune a cikin falon yana iya jiyo sautin kukan da Amal ke rusawa tamkar anyi mata albishir da mutuwar Momy ko Daddy,hakan ya sake jefa zuciyarsa cikin tashin hankali da nadama.Ga wani irin firgici na sake mamayeshi,Ya miƙe da ƙyar yana jin wani jiri-jiri na ɗibarsa ya nufi hanyar bedroom ɗin Hameedah.Koda ya isa bakin ƙofar shiga bedroom ɗin sai ya samu kansa da kasa kama handle ɗin ƙofar bare ya murɗa ya shiga ciki,yayi tsaye yana cigaba da jiyo sautin kukan da Amal ke rusawa tamkar ta rasa su Momy.Ahankali kuma yabar wajen ba tare da ya shiga ba domin baisan da wani idanu zai kalleta ba domin yasan daga ranar tabbas girmansa ya gama faɗuwa a idanun Amal,haka ya juya ya nufi part ɗinsa yana jin wani irin zazzaɓi na neman kamashi domin ƙasusuwan jikinsa gabaki ɗaya hucin zafi suke fitarwa.Ita ko Amal kuka take mai asalin tayar da hankali akan gadon baccin Hameedah tana ji ina ma mafarki take yi ba gaske bane idanunta suka gane mata abinda ta gani,ta rintse idanunta tana sake jin yadda zuciyarta ke cika da tsanar Yayan nasu ga kuma tausayin ƴar Uwarta daya gama illata zuciyarta.Ta rasa a wani aji za ta aje Yaya Zayd a cikin mazan da basa tsoron Allah da gujewa saɓa masa,ta rasa da wani suna za ta kirashi idan ta tuna irin soyayya da kulawar da Hameedah ke bashi amma duk da hakan bai tseratar dashi daga kula wasu matan har ya shigo mata dasu cikin gidan aurensu yana ƙoƙarin aikata zina a cikin falonsu ba.Wani kukan baƙin ciki ya sake sarƙeta har numfashinta na shaking,bata san iyakan lokacin data ɗauka tana rasgar kuka ba kafin ta fahimci cewa kukan babu wani abu da zai sauya ta tashi ta jona wayarta a chargy domin akwai wuta.Bayan ta jona wayar ne kuma ta faɗa toilet domin yin wanka,idanunta sun kaɗa sunyi jajir sun kuma tasa sabida kuka.Time ɗin data fito sai ta samu kanta da zama a bakin bed ta zuba uban tagumi tana rasa ma wani irin tunani zatai,duk yadda ta rufe idanunta hoton fuskarsa da surar jikinsa tsirara take gani freshly.....