SARTSE A ZUCI....! Chapter 14
*SARTSE A ZUCI...!đź’”* *Arewabook@ayshadansabo*
*Paid book ****
©️ _Ayshat Ɗansabo Lemu_ ✍🏻
*Chapter 14*
Bayan ta saka kayan sai kuma ta rasa ina za ta nufa? Kitchen ta fara aikin girkawa Yaya Hameedah abinda take so ko kuwa zaman ɗakin za ta cigaba dayi zuciyarta na cigaba da bugawa da takaici da tsanar Yaya Zayd ɗin?Wani sashi na zuciyarta ta bata shawarar ta fita kawai zuwa kitchen domin samawa Hameedah abinda take so,jikinta a mace ta fito cikin falon tana kasa kallon ko'ina a ciki saima gaggawar wucewa da tayi ta nufi hanyar corridor ta shige kitchen ɗin zuciyarta na sake bugawa ga wasu zafafan hawayen da suka sake wanke fuskarta domin duk yadda takai ga kada ta tuna komi saida hoton fuskarsa a yanayin ya haska a cikin idanunta.Ta isa gaban cabinet ɗin da ta aje ledojin cefanen da tayi kuka mai ƙaramin sauti na ƙwace mata,tayi saurin jingina bayanta da jikin cabinet ɗin tana wa Allah godiya daya sanya ba Yaya Hameedah bane tayi wannan mugun ganin da tabbas sai bugun zuciya ya sameta musamman a halin da take ciki ɗinnan.Tana kuka tana aikin dake gabanta zuciyarta na sake cika da tsanar Yaya Zayd tare da jin daga auren har soyayya sun fice mata akai,lokacin da sunan Aman ya haska a cikin kanta da tarin ƙaunarsa da take ji a cikin zuciyarta sai tayi saurin rintse idanunta tana jin yadda zuciyarta ke sake rawa a ƙirjinta.Idan har Yaya Zayd zai iya aikatawa Yaya Hameedah wannan cin amanar a gidan aurenta ba tare da ya duba girman soyayya da ƙaunar da take masa da kuma girman ƙarfin jinin dake tsakaninta dashi ba,tabbas bata ga Namijin da zuciyarta za ta shaidi cewar bazai iya aikata abinda Yaya Zayd ɗin ya aikata ba.Tausayin Yaya Hameedah har ma dasu Momy ya sake mamaye zuciyarta domin tana da tabbacin ko a yanzu ta fasa wannan maganar babu mai aminta da ita sai Yaya Hameedah,itama ɗin sabida abinda ya taɓa shiga tsakaninta dashi a baya ne amma su Daddy tana da tabbacin cewa za su ce sharri take masa domin sun ɗauki duk wani yarda da soyayya sun damƙa masa ba za su taɓa aminta da cewa yana aikata wannan ƙazantar ba ma a waje ba har a cikin gidan aurensa.Tuna hakan da tayi kawai ya sanya kuka sake ɓalle mata wata zazzafar tsanarsa na sake lulluɓe zuciyarta,tana tsaka da yanka su carrot dasu green pepe ɗin da za ta yi amfani dasu ta jiyo alamun takun mutum na nufo cikin kitchen ɗin.Kuma tun kafin ta ɗaga kanta ta kalli ko waye ƙamshinsa data ji ta tsana shine abu na farko daya fara sanar da ita cewa shine,tayi saurin juya baya tare da rintse idanunta tana jin tamkar tayi layar zana ta ɓace domin bata ƙaunar koda jin wannan miskilar muryar tasa.Sai dai kuma a cikin sakan ɗin da bai wuce goma ba taji hucin numfashinsa daf ita,kafin kuma takai ga yin wani motsi dakakkiyar muryarsa ta ratsa kunnuwarta time ɗin daya kira sunanta,"Amal." Duk da hakan bata waiwayo ta dubesa ba saima idanunta data sake rintsewa,magiya zai fara yi mata tayi gaggawar ɗaga masa hannu tare da katsesa cikin kaushin muryar daya girgiza zuciyar Zayd Abdallah.Cike da jin tarin tsanarsa ta fara sanar dashi cewa ta tsanesa ta kuma tsani sake kallon koda fuskarsa ne,don haka ya fice ya bata waje domin bashi da wasu kalaman da zai yi amfani dashi ya kare kansa a wajenta.Zuciyarsa na tsalle da tafasa ya juya domin barin mata kitchen ɗin,har yakai ƙofar fita wasu irin zafafan kalaman data cigaba da furtasu suka tsayar dashi cak! Suna sake maimata kansu a cikin kansa har yana ji kamar tasirin ɗacinsu zai iya tarwatsa kwanyarsa."Na tsaneka Yaya Zayd,kuma ina so kasan cewa ka ci amanar Yaya Hameedah,ka kuma ci amanar ƙauna da soyayya da kuma yardar data baka,sannan kaci amanar Momy da Daddy domin ba kalar tarbiyyar da suka baka kenan ba,da ace ina da ikon cire soyayyarka a cikin zuciyar Yaya Hameedah da a yau saina zare soyayyarka a cikin zuciyarta na kuma kawo ƙarshen wannan ƙaddararren auren naku da tun asali bana farin ciki dashi,sannan ina sake jaddada maka cewa i hate you!"Waɗannan sune kalaman data danƙara masa tana mai jin ɗacin tsanarsa dake sake mamaye zuciyarta har a saman harshenta.Kuma kafin ƙiftawar idanu ta nemi yawan azababben ƙamshinsa dake sake rura mata wutar tsanarsa ta rasa tabbacin ya fice daga cikin kitchen ɗin baki ɗaya kenan,gane hakan da tayi ya sanya ta juyo ta cigaba da aikin gabanta tana jin ƙirjinta na sassauta irin nauyin da yayi mata sakamakon ta samu ta gaggaya masa maganganu masu zafi.Around 1:30pm ta kammala girkawa Yaya Hameedah liver soup ɗin ta haɗa mata da ganish potato,lemun coconut tayi mata domin taga tunda ta samu ciki take tsananin sonsa musamman da cikin ya fara tsufa ɗinnan.Ta haɗa komi a cikin kyakykyawar basket ɗin ta aje a saman Island,ɗaki ta koma ta sauya shiga ta saka dark brown Abaya tayi rolling ta ɗauki hand bag ta nufi wajen data sanya wayarta a chargy.Zare wayar tayi ta kunna ta fara neman line ɗin Habu driver,bugu biyu ya ɗauka ta tambayeshi inda yake ya sanar da ita cewa gashi a bakin gate tare da Mai gadi.Take ta bashi umurnin juya kan motar kafin ta fito,tana kashe wayar ta fito ta nufi kitchen ta ɗauki basket ɗin ta fice ta ƙofar kitchen ɗin ta baya domin bata buƙatar sake shiga cikin falon dake dawo da mata da ƙazantaccen memory ɗin da take ji har abada bazai gushe a cikin kanta ba matuƙar za ta cigaba da ganin wannan miskilar fuskar tasa.Suna isa asibitin tun kafin Habu driver ya faka motar ta hango motar Yaya Zayd ɗin a fake daga hannun hagu,zuciyarta ta sake yin baƙi ƙirin har tana ji kamar kada ta shiga ciki.Sai dai tunawa da tayi da Yaya Hameedah da yadda ta nace tana son cin liver soup ɗin ya sanya ta ɓalle murfin motar ta fito,Habu ne yayi saurin ɗaukar mata basket ɗin suka nufi ciki domin yana buƙatar gaida Yaya Hameedah yayi mata ya jiki.Amal da yake itace a gaba suna wuce receptionist suka nufi ciki ta hango Babah Gaje daga wajen ƙofar ɗakin ta shimfiɗa babban dadduma tana zaune alamun shi Yaya Zayd ɗin yana ciki,wani malolon baƙin ciki ya sake turnuƙe Amal ta isa suka gaisa da Babah Gaje tare da tambayarta mai jiki Babah Gaje tace da sauƙi yanzu hakama an basu sallama.Amal ta wuce zuwa ƙofar ɗakin ta danna kanta ciki bayan ta amsa basket ɗin dake hannun Habu,kuma a kallon farko data yima ɓangaren gadon da Yaya Hameedah ke kwance idanunta suka sauka a kansu ita da Yaya Zayd dake zaune nane da jikinta tamkar mai shirin shigewa ciki.Daga saman cinyarsa take away ne da bata san uban daya sayo mata yana bata a baki tana ci ba,tsabar takaici har bata san bakinta ya suɓuce yaja wani dogon tsaki ba saida ta jiyo muryar Yaya Hameedah na tambayarta ko lafiya?Ta kalli fuskar Yaya Hameedah dake cike da annuri tana jin tausayinta na sake mamaye zuciyarta,tsanar Yaya Zayd ya cigaba da cika zuciyarta domin sai yanzu take sake gasgata halin wasu mazan da ake faɗi.Yadda ya saki jikinsa yana nunawa Hameedah kulawa da ciyar da ita cikin nuna tausayi da soyayya za ka rantse da Allah bashi ne ta kama da mace haihuwar Uwarsu ba a ɗazu,tayi saurin saita kanta da gyara mood ɗinta tana ƙarisawa gaban gadon ta aje basket ɗin dake hannunta ba tare da tayi gigin kallon Yaya Zayd ɗin daya kafeta da idanunsa jin irin mugun tsakin data saki daga shigowarta.Gaida Yaya Hameedah tayi da jiki ta sanar da ita cewa Habu nason ya shigo ya gaidata,Hameedah tace a shigo dashi tana ƙoƙarin matsawa daga jikin Yaya Zayd ɗin daya kanainayeta.Bayan Habu ya gaidata ya fice ne Amal ta sake shigowa ta tambayeta ko za a zuba mata liver soup ɗin ko kuma sai sun koma gida tunda anyi sallama?Buɗan bakin Hameedah sai cewa tayi sai sun koma gida honey ya ciyar da ita farfesun kayan ciki daya tsaya a wani ƙayataccen gidan abinci ya taho mata dashi.Sabida tsabar takaici Amal bata iya cewa komi ba ta fara haɗa musu kayansu,domin duk ta ƙosa ma su wuce gida ta fara shirin barin musu garin domin tasha alwashin ba za ta wuce gobe ba za ta wuce Zaria kuma duk yadda za ta yi ta sille ma dawowa sai tayi domin ba za ta iya cigaba da zaman gidan tana kallon yadda zai cigaba da nunawa Yaya Hameedah soyayya da tarairayar da a yanzu ta tabbatar na yaudara ne tunda har soyayyar da yake mata bai hanashi rintse idanunsa daga sauran mata ba.Tana cikin haɗa kayan tana taɗin zuci taji Yaya Hameedah ta dafata ta baya tana tambayarta lafiya? Domin tun shigowar Amal ɗin data kalli cikin idanunta ta fahimci cewa tayi kuka.Amal jin hannuwan Hameedah duka biyu a saman kafaɗunta ya sanya ta waiwayowa ta zube mata idanunta da har lokacin akwai ragowar ja a cikinsu tana ƙoƙarin wadata fuskarta da murmushi,kuma cikin kwantar da murya ta sanar da Yaya Hameedah cewa lafiya ƙalau take wani film ne data gama kallo ya sanya ta rasgar kuka sabida tausayin star ɗin cikinsa da akai raping ɗinta.Ta girba wannan ƙaryar tana jan istigfari a cikin zuciyarta domin tayi hakan ne don ba za ta iya sanar da Hameedah gaskiyar lamari ba sabida yanayin da take ciki,kuma kamar yadda take ta addu'a kada Allah yasa Yaya Hameedah ta sake tuhumarta sai taji ta saki murmushi tana faɗin cewa ta cika saurin yiwa film ko novel kuka tamkar ba zama ake a tsara komi ba,kuma daga hakan sai ta shiga tayata suka kammala kayansu waje guda Babah Gaje ta shigo ta fara ɗauka domin tuni Yaya Zayd ya tafi office ɗin Doctor Rafin Daɗi.Lokacin da suka isa zuwa bakin motar Yaya Zayd ɗin Hameedah ce ta shiga front seat,Amal da Babah Gaje kuma suka shiga back seat tunda Amal ta riga ta sallami Habu driver.Ko a hanya Amal takaici ne ya cika zuciyarta na ganin yadda Yaya Zayd ke nuna ma Yaya Hameedah rawar ƙafa shi a dole yayi missing ɗinta,ta dinga jan tsaki a cikin zuciyarta tana tsinewa halin maza.Suna isa gidan da sassarfa ta wuce falon ta isa ɗakin Yaya Hameedah tunda ƙarfi da Yaji Hameedah ta daina zuwa side ɗinsa sun maida mata ɗakin zamanta wajen kwanansu suna morewa rayuwarsu,tunda ta shige kuma bata sake marmarin fita zuwa falon ba duk irin kiran da Hameedah ta dinga yi mata akan ta fito ta sama musu abinda za su ci for dinner haka Amal tayi biris tace Kanta na ciwo Yaya Zayd ɗin yayo musu take away ita za ta sha ko tea ne ya isheta da daren.Yaya Hameedah bata kawo komi a cikin zuciyarta ba domin tasan Amal akwai daru idan ƴan hutsancinta suka motsa,kuma tuni ta daɗe da gane cewa matuƙar Yaya Zayd na gidan kuma ya fito zuwa falonta to Amal ba za ta taɓa so su zauna inuwa ɗaya dashi ba.Shi kuma Yaya Zayd sai ya kasa ya tsare ya hana Hameedah dukkanin damar da za su keɓe ita da Amal domin zuciyarsa cike take da tsoron kada Amal ta tona masa asiri,domin yasan halin rashin kan gadonta idan ranta ya ɓaci.Musamman da yake sake tuna irin baƙaken kalaman da tayi masa a ɗazu ya kuma ga tsanarsa a cikin ƙwayar idanunta ƙarara,shiyasa koda Hameedah ta sanar dashi cewa Amal najin daru sai dai ya fita ya yayo musu take away sai cewa yayi ta daure su fita tare ko za ta ga wani abu da take son ci.Hakanan ya tasata a gaba ita da titsetsen cikinta suka bar gidan,kuma koda suka dawo ɗauke da tarin kayan ciye-ciyen da suka shigo dashi Amal taƙi yarda ta fito bare ta amsa nata sai cewa tayi Hameedah ta bar mata nata idan ta tashi ci za ta fito ta ɗauka.Suna kammala cin abubuwan da suka shigo dashi ya tasa ƙeyar Yaya Hameedah zuwa room domin su kwanta,kuma a cikin daren yasan yadda ya lallaɓata ta samar masa da nutsuwa.Washegari da wuri Amal ta tashi ta shirya musu abin breakfast,tana kammalawa ta wuce tayi wanka ta shirya cikin simple gown na atamfar batik mara nauyi.Tana tsaka da fesa turare wayarta ya fara ringing,koda ta isa wajen wayar taga Momy ce mai kira sai tayi gaggawar ɗauka.Momy cikin muryar kuka take sanar da Amal mutuwar Mahaifiyarta Hajiya Safiyyah da aka bugo aka sanar mata bada jimawa ba,ta kuma gargaɗeta akan kada ta sanar da Hameedah ta shirya kawai gobe da sassafe za su tsaya su ɗauketa su wuce Borno tunda morning flight za su bi ta Abuja su wuce Maiduguri.Amal sosai mutuwar Kakar tasu ya taɓata domin Kakarsu mutumiyar arziƙi ce,taci kuka sosai ta share hawayenta kuma koda Yaya Hameedah ta fito bata sanar da ita mutuwar ba tadai ce mata gobe su Momy za su tsaya su dauketa za su tafi Borno.Tunda Yaya Hameedah taji hakan haka kawai taji bata nutsu ba sai ta ɗaga waya ta kira Anty Falmata,jin muryarta tana kuka ya bata tabbacin ba lafiya ba kuma Anty Falmatan saita ɗauka cewa Hameedah ta kira ne ta jajanta musu mutuwar Hajiya Babba don haka ta fara furta mata cewa ai Hajiya ta samu rana tunda Friday ta mutu.Jin hakan ya sanya Hameedah sakin wayarta ta fashe da kuka,cikin sauri Amal ta riƙeta tana sakin kukan da take ta riƙewa.A haka Yaya Zayd ya fito ya samesu kuma cikin sauri ya ƙarisa ya janye Hameedah daga jikin Amal ƙirjinsa na tsananta masa bugu,domin duk a tunaninsa Amal ta sanar da Hameedah abinda idanunta suka gani ne jiya.Jin Hameedah na kiran sunan Hajiyarsu Momy tana roƙa mata gafara cikin muryar kuka ya sanya ya gane cewa Hajiya Babba ce ta rasu kamar yadda ake kiranta acan gida Borno,ya shiga salati yana rarrashin Hameedah da tausasan kalamai idanunsa akan Amal yana jifanta da wani mugun kallo.Daga ƙarshe ma ɗaukar Hameedah yayi ita da cikin jikinta suka nufi side ɗinsa domin ya sake cusawa Amal dake jifansa da kallon tsana haushi,yako cusa matan domin suna ɓacewa ganinta ta ja wani dogon tsaki idanunta na kaiwa kan inda komi ya faru a jiya.Ta rintse idanunta da sauri hoton surarsa dana girman mazantansa da idanunta suka gane mata ya haska a cikin kanta,tayi saurin sake rintse idanun tana jin wani irin ɗaci har a saman harshenta.Gabaki ɗaya ji tayi ya gama fice mata aka ko kaɗan bata ganin girmansa a cikin idanunta yanzu,Yaya Sulaiman dama shine nata kuma har a yanzu shi kaɗai take ji a cikin zuciyarta domin wannan abin da ya faru ya tsiyayar da ɓurɓushin ƙaunar jini da ganin ƙimarsa da take baki ɗaya.Shiyasa ko kaɗan bata yi nadama ko danasanin kallon idanunsa da tayi ta sanar dashi zafafan kalaman data furta masa a jiya ba,kuma bata jin cewa har abada za ta taɓa yin nadama.Kamar yadda Momy ta faɗi ƙarfe takwas na safe motarsu ta faka a ƙofar gidan Zayd Abdallah ta kira wayar Amal da tun 7:30am dama ta gama shirinta,domin dama tamkar akan ƙaya take haka take jinta duk ta ƙosa ta bar wa Yaya Zayd gidansa.Tana ɗaga call ɗin Momy taji cewa suna waje taja ƙaramin luggage ɗinta ta fito,kuma cikin sa a Yaya Hameedah itama ta fito kenan daga side ɗin Yaya Zayd domin itama Momy ta kira wayarta.Kafin kuma Amal tace komi shima Yaya Zayd sai gashi ya fito sanye da brown jallabiya a jikinsa,kallo ɗaya Amal tayi masa ta ɗauke kanta tana gaidashi a daƙile.Baibi takan gaisuwarta ba ya kama hannun Hameedah suka nufi ƙofar fita domin already sanye da ƙaramin hijab Hameedah ta fito,itama Amal saita rufa musu baya suka nufi bakin gate ɗin wajen su Momy dake cikin mota tana faman share hawayen da suka kasa daina zuba a idanunta tun daga sanda aka kira aka sanar da ita mutuwar Hajiyarta.Zayd Abdallah ya duƙa ya riƙe hannuwan Momy yana rarrashinta bayan yayi mata ta'aziyya,Yaya Sulaiman ke Jaye da motar daga gefensa kuma Daddy ne sai Anty Mamah dake tare da Momy a back seat dukkaninsu tare za su wuce Borno domin yin ta'aziyya tunda tun a yammacin jiya aka riga a birne gawarta domin ta samu ranar da bai kamata ayi mata jikirin tsayawa jiran sai wasu sunzo kan gawar kafin a rufeta ba.Amal ta shiga back seat suka kama hanya Hameedah na kuka sosai,haka Yaya Zayd ya janyeta suka koma ciki bayan ya sanar da Momy cewa shima zuwa gobe zai bi flight ya samesu acan......✍🏻