SARTSE A ZUCI...!

SARTSE A ZUCI.....! Chapter 16

by @ayshadansabo

*SARTSE A ZUCI...!💔* *Arewabook@ayshadansabo*

*Paid book ****

©️ _Ayshat Ɗansabo Lemu_ ✍🏻

*Chapter 16*

Amal taso Jameelah ta zauna amma sabida tana da school basu yi hutu ba dole babu halin zamanta,Anty Mamah ita da wata neighbour ɗin Yaya Hameedah da Babah Gaje sukai hidimar gyara jariri da mai jego.Aka wankesu tas suka fito fes kai ba kace Yaya Hameedah ce ta haifo ƙaton Babyn ba sabida tayi garas alamun lafiya lau Allah ya sauketa,baby sai kyawunsa ya sake fitowa sosai daya sha wanka aka shiryashi cikin fararen suwaita abin sha'awa.A lokacin Amal ta samu damar ɗaukarsa zafafan picture's amma sai Anty Mamah tace kada ta sake tace za ta saka a Media sabida gujewa masu kambun baka kona idanu,tana iya turawa ƴan Uwa waɗanda suka kamata amma kada ta saka a kafar sadarwar da ko wani baki zai tanka.Kuma Amal ɗin itama sai taji zuciyarta ta nutsu da shawaran Anty Mamah domin tasan tabbas ko a musulunci an ambaci kambun ido dana baki shiyasa ma aka samar da addu'ar kariya daga garesu baki ɗaya,Aman Kurfi ta fara tura mawa sai kuma su Meenal.Kuma hoton na zuwa masa ya gani sai ya kasa haƙuri ya nemeta Vedio call ta whatsapp yana yaba kyawun Yaron tare da tsokanarta cewa saura ita,zaiso ace suma first born ɗinsu ta basu mai kama da ita zar amma kada Yaron ko Yarinyar su ɗakko tsiwarta domin sai a yanzu da suke sake shaƙuwa da yin sabo da juna yake fahimtar da gaske Amal ɗin tana da tsiwa da rashin barin takwana amma kuma bata da riƙo sosai.Sun jima suna hirar luv kafin suyi sallama da juna,ita ce ta shiga kitchen ta shiryawa Yaya Hameedah lafiyayyen tuwan dawa da miyar kuka da yaji daddawa da naman saniya haɗe da busasshen kifi zuƙu-zuƙu a cikinsa.Ita kuma Anty Mamah tayi mata gashin hanta da nama da yaji kayan ƙamshi na gargajiya ya gasu yadda ya kamata,kuma itace ta sanya Hameedah a gaba har saida ta tabbatar taci tuwan da naman tasha ruwan tea mai Kaurin gaske.Yaya Sulaiman Amal ya kira ya dinga mata santin kyawun baby,ta haɗashi da Yaya Hameedah yayi mata barka yana sanar da ita cewa zuwa gobe zai tsaya anan Kaduna yaga baby idan ya baro Abuja.Washegari Daddy yazo yaga baby Abdallah ya wuce Abuja daga can zai wuce Lagos,Yaya Sulaiman ma ya tsaya yaga baby kafin ya wuce Zaria kuma tare da Yaya Zayd ɗin suka wuce zashi wajen Momy.Sai dare ya dawo Kaduna ya tadda Amal ta shirya abincin dinner ya zauna ya kwashi gara kafin ya wuce side ɗinsa,kuma yana yin wanka ya fito ya nufi ɗakin da Hameedah ke jego ya tare ma su Anty Mamah yana zuba taɓararsa da rashin kunya domin sam baya kunyar idanun Anty Mamah yake sakin kalaman duk daya zo bakinsa sai dai yabar Yaya Hameedah da jin kunya.Soyayyar Uwan da ɗan yake ji sosai a cikin zuciyarsa tamkar ya haɗiyesu,shiyasa da Momy tace masa ko za a dawo dasu Zaria suyi wanka anan yayi saurin cewa bai amince ba domin yana da tabbacin idan sun koma bazai sake idan yaje dubasu ba sabida Anty Mamah ce zatai kane-kane tace a side ɗinta Hameedah za ta zauna.Shiyasa yafi aminta da cewa Anty Yaganah tazo ta zauna dasu tunda ana yin suna Anty Mamah za ta tafi,ga kuma su Babah Gaje dattiya data san kan komi da harkokin kulawa da jariri.Amal ma ya roƙi Momy ta lallaɓa musu ita tayi zamanta har su Hameedah su yada wanka,domin baya ƙaunar ya dawo yaci girkin kowa sai nata kona Hameedah domin ya sawa kansa koya koma bazai dinga wuce 2 week's baizo yaga baby Abdallah ba.Anty Yaganah ta iso su Hameedah nada kwanaki biyu,kuma tunda ta iso ta fara kulawa da Hameedah tana girka mata kalan abincin dake ɗauke da sirrikan gyara kala-kala a cikinsu.Suka haɗu ita da Anty Mamah suna nunawa Hameedah gata da ƙarshen kulawa,shiyasa kafin kwanaki bakwai Hameedah tayi wani irin tas da ita tamkar ba itace ta haihu ba kyawu kawai take zubawa.Ana gobe suna Anty Falmata da Anty Yakaka suka iso tare da step mother ɗinsu Momy Hajiya Yaya,tuni an kammala shirya yadda bikin sunan zai kasance gida duk ya cika da ƴan Uwa da dangi hatta su Gwaggo Abu da Sakeenah da ƙannin Marigayiya Asiya duk sun iso daga Zaria domin halartar bikin sunan.Amal sun sha ɗinkuna fitan suna na garari domin ita indai akan harkar saka suturu da gayu ne lamba ɗaya ce,gabaki ɗaya ta jingine harkokin business ɗin turarukanta dasu humras ta bikin suna kawai take.Kuma cikin hukuncin Allah aka gudanar bikin sunan da aka yishi a babban hall da aka kama akai naming decoration daya ƙayatar da duk waɗanda suka samu halartar wajen,anci an sha har an ɗauka domin Yaya Zayd ya saki kuɗi ba kaɗan ba ga kuma Daddy kansa daya turawa Amal Uwar tsara komi manyan kuɗi yace ayi komi cikin wadata.Anko yi ɗin domin har da souvenirs aka rarraba,kuma tun a ranar da yawa suka juya inda suka fito musamman ƴan Zaria dangin Asiya da wasu daga cikin ƴan Ƙaura duk a ranar suka juya Zaria.Bayan kwana biyu da yin suna kowa ya watse su Gwaggo Abu duk sun koma gida,Anty Mamah a washegarin ranan sunan ta tafi tabar Yaya Hameedah da kewa domin sai da ta zauna da Anty Mamah na kwanakin datai dasu ta sake yaba kirki da dattakonta.Hatta Anty Yagana ta yaba mata ta kuma taya Momy murnar samun abokiyar zaman data san ciwon kanta mai hankali da sanin yakamata,kai hatta friend's ɗin Yaya Hameedah su Hamdiyyah sun yaba da Anty Mamah da irin hidimar da tayi da Hameedah.Gidan ya rage daga Anty Yaganah sai Amal dasu Babah Gaje da Kulu wacce ta jima da dawowa daga zuwa ganin gida da taje yi,Yaya Zayd shima bayan kwana biyu dayin sunan ya juya Lagos.Mai jego da baby sun sama abin duniya ba kaɗan ba,domin hatta Yaya Sulaiman akwati guda yayi musu ita da baby.Amal kanta ƙaramin akwai guda ta cika da kayan baby,haka Anty Mamah itama abinka ga mai saida kayan babies trolley guda madaidaici haka ta cika da kayan baby ta kuma yima Hameedah zannuwa manya guda uku.Jameelah dake business ɗin saida dogayen riguna itama kayan baby masu tsada kala biyar tayi ma Abdallah,kuma Ummanta da Abbanta ma duk sunzo sunyi barka sun kuma kawo kayan barka masu kyau da tsada daidai ƙarfinsu.Daddy ya siyawa Hameedah ƙaramar Motar hawa mai tsadar gaske,dama ya jima da burin yi mata wannan kyautar tun lokacin da akai aurensu amma bai samu hali ba sai a wannan karon.Yaya Zayd kuma set ɗin gwal ya siya mata na manyan kuɗaɗe bayan akwatinan kayan fitan sunan da yayi mata ita da baby Abdallah,komi dai anyi shi cike da harkar girma domin itama a ɓangaren Momy su Anty Falmata suma sunyi kayan suna na garari sosai.Bayan suna da sati biyu Amal ta samu ta sille ta gudu Zaria,tun ranar da Momy tazo ganin baby Abdallah anyi suna da sati ɗaya Amal taso ta bita Momyn taƙi.Sai yanzu da taji Hameedah na faɗin cewa Yaya Zayd zai dawo Friday ta haɗa kayanta ta wuce Zaria ranan Thursday,Anty Yaganah ta dinga roƙonta cewa kada ta wuce kwana biyu bata dawo ba amma Amal jinta kawai tayi domin da shirin yin sati guda ta wuce Zaria.Kuma tana isa ta cidda zancen auren Jameelah daya taso,za a haɗata da Cousine ɗinta Muhammad Yaron Yayar Ummansu Uwa ɗaya Uba ɗaya.Jameelah sam bata son haɗin amma shi kuma Muhammad ɗin ya mato a kanta yana ƙaunarta sosai,hakanan dai aka bata baki ta amince za a tsaida lokaci bada jimawa ba domin yace bazai iya jira har ta ƙare school ba tunda a lokacin nema ta shiga level 3.Amal tayi murna da farin ciki sosai da jin zancen auren,duk da cewa ta tausayawa Muhsin domin shi Jameelah keso yake sonta kamar yayi hauka shima.Daga ƙarshe dai itama ta ƙarfafa Jameelah akan ta amshi zaɓin Iyayenta tunda dai Muhammad ɗin yana ƙaunarta sosai,don haka a cikin sati ɗaya da Amal ɗin tayi duk hirarsu a ɓangaren Anty Mamah akan tsaren-tsaren yadda bikin Jameelah zai kasance ne idan an sanya lokaci.Amal na yini a ɓangaren Momy susha hira da yin shawarwarinsu da juna ita da Yaya Sulaiman idan yana gari,domin shima ya maida hankali sosai akan fara shirin aurensa gini yake a Millenium city Kaduna har kuma an kusa kammalawa domin yace da Daddy shima yafi sha'awar zaman Kaduna.Shi kuma Yaya Zayd anan Zaria ya sayi wani uncompleted building a cikin gonan ganye ana ƙarisa aikin ginin,yace za su riƙa sauka idan sunzo Zaria yin sha'ani ko wani abin idan ya taso.Burinsa bai wuce ya ɗauki Hameedah su koma Lagos da zama da zarar ta kammala service ɗinta da za su gama a ƙarshen watan da za a shiga,amma ita Hameedah tana yawan faɗi masa cewa bata sha'awar zaman kudu domin ta tsani zama cikin ƙabilu ko sabida tarbiyyar Yaranta da bata son ya gauraya dana yaren da ba nata ba.Yakan jita ne kawai domin shi a tsarin halittarsa bazai taɓa iya cigaba da zama shi kaɗai babu mace a kusa dashi koda yaushe ba,musamman ma a wannan gari na Lagos da yake zuwa wajen hutawa kala-kala yana ganin mata kala daban-daban masu yin shiga na rashin tarbiyya da kunna wutar fitina a zukatan maza.Ba domin ya ɗaukarwa kansa yin azumi da kauce ma yawan zuwa wuraren da yasan hankalinsa zai dinga tashi ba da baisan halin da zai dinga shiga ba kafin yazo ga Hameedah,domin tun daga ranar da Amal ta kamasu shi da Najwa bai sake haɗuwa da ita ba yakan dai yi picking call ɗinta time to time idan yana Lagos ta kira.Amma idan yana Kaduna ne yana kiyayewa domin baya ƙaunar Hameedah ta kamashi kota sake binciken wayarsa ta gano suna tare har yanzu,domin kullum addu'a yake kada Allah yaba Amal damar da za ta tona asirinsa a wajen Hameedah.Amal bata koma Kaduna ba saida sukai waya da Yaya Hameedah ta sanar da ita cewa ta dawo dodon nata ya tafi,a lokacin Amal dariya tayi tana mamakin yadda Yaya Hameedah tayi saurin gane cewa shi take guje mawa.Ranar data koma Kaduna a ranar da dare Aman Kurfi ya kirata vedio call ta whatsapp call kamar yadda suka saba,kuma tun daga ganin yanayinsa tasan cewa baya cikin nutsuwarsa.Koda ta tambayesa abinda ke damunsa sai ya sanar da ita cewa jikin Abbansa ne ya rikice,domin tunda akai masa aikinnan maimakon a samu sauƙi sai kuma jikin nasa ya sake tsananta.Amal ta tausayawa Aman Kurfi domin ta kula sun fara fidda rai da Abban nasu,haka ta dinga rarrashinsa da kalamai na ƙarfafa zuciya da imani domin zafin cuta ba shine mutuwa ba duk da cewa cutar cancer kowa na tsoronsa musamman idan akace ya kama maƙarfafa irin na Doctor Kurfi.Kuma cikin hukuncin Allah bayan kwanaki biyu da sukai waya Aman ke sanar da ita cewa Abban ya samu sauƙi sosai suna saka ran zuwa next month ma su dawo gida Nigeria ya cigaba da yin jinya a gida,Amal tayi farin ciki sosai kuma a ranar ya haɗata da Momynsa Hajiya Hauwa suka gaisa tayi mata ya jikin Abban ta bata tabbacin samun sauƙinsa sosai.Satin Yaya Zayd biyu da komawa ya sake zuwa ganin masu jego,a lokacin suna da kwanaki kusan talatin.Yayi mamakin girman da Abdallah yayi domin Yaron yayi tulele dashi abin sha'awa,da alamu kafan nononsa mai kyau ne ita kanta Yaya Hameedah tayi shar da ita sai glowing da fresh kawai take sabida gyara da hutun da take samu.Shiyasa tunda gogan nata ya iso ya rasa dukkanin nutsuwarsa sai faman shige mata yake ko kunyar idanun Anty Yaganah baya ji,hakan da Anty Yaganah ta gani ne kuma ya sanya ta saka Hameedah a gaba taja mata a kunni akan tayi hankali dai kada tayi saurin bashi kanta ta jira su yada wanka duk da cewa taga jini bai ɗauke mata bama har lokacin.Kunya ya rufe Yaya Hameedah da Amal wacce tana wajen Anty Yagana ke jawa Hameedah kunne,kuma sai Amal ɗin ta kalli Yaya Hameedah da wani irin kallo mai cike da tausayi a lokacin da zuciyarta ta waiwaya baya ta tuno mata da ƙazantaccen yanayin data taɓa samun Yaya Zayd ɗin a ciki.Kuma idan har za ta yi tunani daidai to tabbas ba maza irinsu bane za su juri rashin mace har na tsayin wani lokaci ba tare da sun saɓi Allah ba,zuciyarta tayi baƙi tana ji a cikin zuciyarta cewa tabbas dole za ta baiwa ƴar Uwarta shawarar ta kula da mijinta domin akwai hanyoyi da dama da za ta samar masa da nutsuwa ba dole saiya kwanta da ita ba tunda tana a halin jinin biƙi.Kuma a daren bayan Anty Yaganah ta fita daga ɗakin Amal ta sanya Yaya Hameedah a gaba ta bata shawarar tayi watsi da maganan Anty Yaganah ta kula da mijinta idan har ya nemi hakan,ta rufe idanunta tare da cire kunya ta haska mata wasu hanyoyin da take karantawa a litattafan soyayya na irin yadda mace za ta kula da mijinta koda tana cikin halin da bazai iya kusantarta ba.Kuma a take taga yadda fuskar Hameedah ta washe da wani irin murmushin farin ciki kafin ta shiga zuba mata godiya,kunya sai ya lulluɓe Amal lokacin da Hameedah ke tsokanarta da cewa ashe Aman Kurfi zai sha gata da tarairaya.Ƙarfe goma na dare Amal suna tare da Yaya Hameedah Yaya Zayd ya shigo cikin ɗakin cikin shigar kayan bacci masu taushi da sukai masa azabar kyau,ya nufi saman gadon da Yaya Hameedah ke zaune tana shayar da Abdallah ya zauna tare da zube musu manyan idanunsa dake cike da fitina.Wani irin azababben kyawu yaga Hameedah tayi masa a cikin kayan baccin data saka,Amal ita kaɗai ce bata riga tayi shirin kwanciya ba tana sanye da simple gown na material a jikinta.Babu kunyar idanun Amal yake sanar da Hameedah cewa yana buƙatarta yayi missing kulawarta alot,don haka ta biyoshi yanzu suje side ɗinsa yana buƙatar jinta a jikinsa.Kalaman suka daki kunnuwar Amal suka jefata cikin jin matsananciyar kunya,ta miƙe da sauri ta nufi ƙofar fita tana sakin tsakin da bata san ma ya fito fili ba.Tana fita kuma Yaya Zayd ya raka bayanta da harara yana raɗawa Yaya Hameedah cewa wai Amal bata da kunya ta tsani taga yana nuna mata kulawa,ita dai Yaya Hameedah data gama sanin dama can ba shiri suke da juna ba saita share zancensa tana lallaɓashi da cewa ya bari zuwa can anjima idan Anty Yaganah ta kwanta gaba ɗaya za ta je ta sameshi a ɓangarensa.Ransa ya ɓaci domin shi a lokacin yaso ta bishi amma saita tubure masa har hakan ya fusatashi ya bar musu ɗakin a zuciye yana sanar da ita cewa kada ma taje inda yake baya buƙatarta,Hameedah dariya kawai ta bishi dashi ƙaunarsa na sake rikita zuciyarta domin tasan duk wannan fishin daya ɗauka da zaran taje gareshi ta fara rikitashi da hot kisses zai sakko.Kuma fitarshi bada daɗewa ba Anty Yaganah ta shigo ɗakin,suka fara hira bayan ta amshi Abdallah daya buɗe idanunsa yana hirar dare sai can cikin dare ya hanasu barci da kukan dare.Amal ma jiyo dariyarsu Anty Yaganah daga cikin bedroom ɗin Yaya Hameedah ya bata tabbacin cewa Yaya Zayd ya wuce side ɗinsa,sai ta bar cikin falo ta nufi ɗakin Yaya Hameedah suka cigaba da hirarsu suna kwasan dariya har 11pm yayi sannan Amal ta wuce zuwa room ɗinta domin shirin kwanciya bacci.Itama Anty Yaganah da bacci ya fara kama idanunta sai kawai ta goya Abdallah da baida alamun bacci ta kwanta tayi ruf da ciki dashi a bayanta,Yaya Hameedah ta shige toilet domin yin fitsari zuciyarta naga mijinta Yaya Zayd tana son zuwa ta faranta ransa kamar yadda yake da buƙata.Shiyasa time ɗin data fito ta tadda har Anty Yaganah ta fara bacci sai kawai ta zari ƙaramin veil ta rufe kanta ta fito ta wuce zuwa ɓangaren Yaya Zayd ɗin.....✍🏻