Rayuwar Maraici

Chapter 01

by @teemerheart

Daga kan ta tayi tana duba lokacin Taga har Karfe bakwai da miti goma tayi Subhanallahi ta ambata tana Mikewa daga kan sallaya ta nufi bedroom ta tarar da Asmira tayi dai dai a kan gado tana baccin ta hankali kwance.



 “ke Zainabu ke zainabu, tashi kin makara fa”

Hajiya kaka nayi sallahn fa sannan na kwanta Asmira ta Fada cikin magagi bacci. 


  “Ko yau baza kaje makarantan bane”

Hajiya Kaka ta sake fadi cikin mamaki yadda Asmirah take son bacci a Rayuwa tan. 


 Cikin Fargabar kar dae ta makara ta bude idon ta tare da ambaton addu ‘ar tashe aga bacci a bakin tah. 


“Innalillahi Hajiya Kaka har lokacin yaja  haka ban sani ba” ta fada cikin mamaki 


“ To zai tsaya jiran kine maza yi sauri ki tashi ki shirya ka fin lokaci ya Karasa kurewa,Bari naje kitchen na dafa miki Dan wake tunda shine yake da sauri Kafin ki gama shiryawa” ta Fada tare da ficewa daga bedroom din.



Zainab Umar Duwa Wanda akewa lakani da Asmirah yarinya ce Mai Kimanin shekaru  sha shida   (16 years) black Beauty ce sannan kuma Tana da tsayi Amma ba sosae bah kuma tana da Kiba amma ba sosae shima. Ta Kasan ce Mai son karatu na boko da na addini sannan kuma tana da bada himma sosae akan a binda tasa a gaba. Asmirah marainiya ce tana da shekaru biyu a duniya Allah yayi wa Mahaifin ya rasuwa.Mahaifin ta Dan jihar Adamawa ne   suna zama a anguwan Modibbo sannan ma aika cin gwanna tine mutum ne shi mai son Jama’a sosae  shiyasa mutane dayawa sun shi a cikin garin.Ya Kasan ce Da na Hudu a gurin Mahaifin shi sannan kuma Da na farko a gurin Mahaifiyar shi.Shine mafi soyuwa a gurin Mahaifin shi Saboda hazakar shi da mai da hankali Akan abinda yasa a gaba yana da Kanne guda hudu daya namiji uku mata. 

Sun hadu da mahaifiyar Asmirah ne a ciki garin Gombe saka makon yaje bikin wani abokin shi ita kuma tana daya daga kawayen amarya.Ta Kasan ce mace ce ba Mae son hayaniya ba shiyasa har aka yi bikin aka gama bata San da wan zuwar shi a cikin abokanan Ango bah.A Wannan bikin ne ya ganta Bayan ya koma gida ya sannan da abokin shi kan magana ta yace ba damuwa zae bin cika mishi. Bayan yayi bin cike ya sanar da Malam Umar shi kuma ya shirya ya taho Gombe domin su gana.Daga haduwar su Allah cikin ikon sa ya sanya ya musu kwanar juna ba a dau lokaci ba iyaye suka shi cikin maganar.Bayan anyi bikin Su Mahaifin Malam Umar ya nuna wa Hafsat soyayya tamkar shi ya haife ta.Duk Bayan sati yana zuwa har gida ya duba ta sbd Mahaifin ta amana ya damka masa Kun San muntanan da da rukon Amana. Sakamakon zuwa duba ta daya keyi Duk Bayan sati a nan ne ya tarar da ita tana koyawa yaran makwaftan su karatu.Ya tambaye ta Dama tayi makaran ne tace eh. Bayan ya koma gida ya Kira Dan shi Malam Umar ya mishi baya nin abinda ya gani a gidan shi ya kuma ce ya karbo takar dun ta zae nai mamata aiki. Mahaifin Malam Umar ya mai mawa Hafsat koyarwa a wani primary dake kusa da su dake babban mutum ne shi ba dade wa ta fara fita aiki. Bayan shekara daya da Auren su Allah ya azurta su da haifun Diya mace Wanda taci Sunan mahifiyar Malam Umar wato zainab suna mata lakani da Asmirah. 

Sunyi zama na dadi sosae Tsakanin Malam Umar da iyalin shi saboda ya kasance shi mutum ne mai son iyalin shi yana kyauta ta musu dai dai karfin shi Duk da Bawani kafi ne dashi ba amma akwai wada tar zuci. Ita ma mahifiyar Asmirah mace ce mai godiyar Allah sannan tana da hakuri sosae. Asmirah na da shekara biyu a duniya Wata rana Malam Umar ya tashi da ciwon Kai mai tsanani Wanda ya daga hankalin mahaifiyar Asmirah wacce take kiran ta da Aunty tabi bakin yaran makwaftan su Haka kazalika hankalin Mahaifin Malam umar ya tashi sosae.Sun kai shi asbiti da kwana biyu Allah ya kar bin abin shi.

Bayan Anyi kwana arba’in da rasuwan shi iyayen Aunty suka zo daukar ta a nan Mahaifin Malam Umar yace wa Aunty ta dauki Asmirah ta tafi da ita saboda shi bazai Iya raba ya’ da Uwa ba. Baba tsoho da Hajiya kaka sun ji dadi sosae da abin da Mahaifin Malam umar ya su. 

 Wannan ke nan 




Ta shirya tsaf cikin uniform nata tare da goya school bag din ta a baya.Ta fito tsakar gidan su Wanda yake a share babu alaman datti ko daya yayi dai dai da fitowar kaka daga kitchen hannun ta rike da kwanon abinci.



“Hajiya kaka tah na shirya” Asmirah ta fada cikin fara 


“Masha Allah,karbi nan ki zauna ki cinye shi duk bayawa bane dashi na sanki da kin son cin abinci”ta fada tare da mika mata kwanon Dan waken.Ta karba tana dan tura baki abin ka da goyon kaka. 


Parlo ta koma ta zauna ta fara cin dan waken kadan taci taji ta koshi, tashi tayi ta nufi tsakar gida ta ajiye kwanon a gurin wan kewan ke. 


“Hajiya kaka tah na gama cin abinci zan wuce makara ta” 

 

“ To zainabu nah Allah Ubangiji ya kiyaye ya bada sa’a ya kare ku, ga kudin a daidai ta maza kiye sauri akar su rufe gata kuma kar ki manta da yin addua” 


“ insha Allah sai na dawo “ 


Tana fita ba dade wa ta samu abin hawa ba a dau lokaci bah suka isa makaranta  tayi sa’a kuwa saura minti biyar a rufe gate.Tana shiga Aji ta tarar da kawarta aminiyar ta wato Aisha•S  wanda suke Kira da Eshert a bench su tana jiran isowarta.


“Bestie yau kin yi latti”Eshert ta Fada 


“Kibari Kawae Bestie bacci nayi badan Hajiya kaka ta tashi ni ba  da yau kam sae dae na hakuri da zuwa school din” 

 

“ Yar gatan Hajiya kaka, kin samu ko kinyi assignment din English teacher kin San fa yau zae karba”


“ Tab ae ko banyi bah na dauka sae next week fa zae kar ba yanzu ya zanyi kuma fa shine first period namu” 


Tana rufe bakin ta sae Gashi ya shigo class,gaba daya hankalin ta ya tashi saboda malamin baya wasa ko kadan da student,ta fara addua a zuciyan. 


Sir Alfa ya musu darasin ya fita ba tare da ya tambayi assignment nashi bah.Ajiyan zuciya tayi mai karfi bayan ya fita tare da kallon side din Eshert  Tana fadin 


“ Allah ya tai make ni Besty yau da na fadi Yaren garin mu” 


“ Wlh fa may be ya manta ne fa “


“ Wa ya Fada miki mutum nan yana man tuwa da wuri Kawae da ya shirya yin mugunta ne, Sae an manta daya bada assignment sannan yace zai kar ba”


“Haka fa to mudai insha Allah zamu na zuwa da namu”


Yinin ranan Sunyi shi cikin farin ciki tare da bada himma a duka darusan  da aka musu. Karfe biyu dai dai aka tashi daga makaran ta, sallama sukayi da class mate nasu kowa ya kaman hanyan gida.


Da Sallama Asmirah ta shiga gida ta tarar da Baki a gidan su.Mahaifiyar tace wato Aunty tare da kanan ta mata goda biyu Aunty Fateemah wacce take da yara goda biyu a duniya Aliyu da kuma Hasenah sae kuma Aunty Zulaihat wacce take da yara goda uku Sadeeq,Ummi da kuma Nana. Sannan Aunty tana da yayu maza guda Uku babban yayan su Shine Yaya Muhammad Wanda suke Kira da Abba yana aiki a kaduna yana da yara guda biyar Khadeeja,Haroon,zainab,Nusaibah da Abdul yana aiki ne a garin kaduna.sai Yaya Usman Wanda yake aiki a kano yana da yara guda uku duka mata Ammie,Meeenat da Husna.Yaya bukar shi kuma Dan kasuwa ne yana nan a garin Gombe yana da yara uku shima Hafsat mai sunan Aunty,Haroon da Maryam.


“ yan makaran ta an dawo kenan” Aunty Fateema ta fada cikin fara a 


“ Eh Maman Haidar,Ina yinin ku,kunzo lafiya”


“Lafiya qlau ya karatu” 


“Alhamdulillah “ 


“Maman Haidar Ina Alkawari na da kika ce zaki kawo min in zaki ko “Asmira ta fada cikin shagwaba 


“ To Sarkin Surutu maza tashi kije ki cire Kayan nan kızo ki ci abinci ki wuce Islamiyya” Aunty ta fada da Dan fada fada.


Tashi tayi ta shiga bedroom tana Dan tura Baki ita ba tasan me yasa Aunty take ya wan mata Fada ba.


“Wlh Hajiya duk kin bata yarinyan na ace Kina da kamar ta a gida sae kin nai mi mai aiki ba abin da ta Iya sae shiriri ta sa’annun ta duk sun Iya girki Amma ita ko kitchen bata shiga”Aunty ta Fada cikin baci rai


“ Ina ruwan ki a gidan ki take daza ki damu bata iya girki ba Zata koya ae anan gaba” Hajiya kaka ta Fada 


Maman Haidar dai Dariya tayi saboda ita Asmirah yar dakin tane,Aunty zulaihat ne ta daura da fadin 


“Ni ae shiyasa bata son zuwa gida na saboda Ina sata aiki yarinya duk ta zama wani iri kannen bayan ta ma sun iya aiki amma banda ita daga ka taba ta kadan sae tace maka ita karatu takeyi sai kace a kan ta aka fara kara tun” 


“ nifa kar ku ta kura min yarinya daga zuwan ku,ku barta ta sha iska