BAYAN AURE

3

by @rahmakabir13

*BAYAN AURE*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 3.

Sarac Stars R Pen...✍️

Hawaye ne ya sauka kuncin Hamida sai ta share da hannu, sai take jin wani irin kewar gida yana denne mata zuciya taji dama ta dage sai ta bisu Inna zuwa gidan, in ya so gobe a kawota bayan hankali ya kwanta, amma taya zata jure zama ita kaɗai a baƙon wurin da bata taɓa kasancewa ba, lamarin yayi mata tsaurin da take ganin an ƙasƙantar da ƙimarta ne kawai, duk da abun ya zo da lalura amma kuma barin ta ita kaɗai kamar rashin galihu ne a gareta, sai ta soma zancen zucci. 

Wannan wace irin ƙaddara ce dana fara yin sallama da ita a ranar farko a gidan aurena, ko da yake rashin lafiya baya sallama, kamar mutuwa ce nan take sai ayi a gama rai yayi halinsa, Allah ya bashi lafiya. 

Ta ƙare zancen cikin sauke numfashi tana matsar yatsun hannunta. 

Jamil ne ya ƙaraso in da take zaune ya tsaya nesa kaɗan da ita. 

Idan kina buƙatar wani abu ki faɗa yanzu sai na siyo miki, kuma idan kin gaji da zama ga mota nan ki shiga ciki ki kwanta zamu jira Hafiz ne suna hanya, yace shi ne zai kai ki gidan umma dan kar ki zauna ke kaɗai saboda asibiti zai koma ya kwana. 

To babu damuwa Allah ya kawo su lafiya, kuma bana buƙatar komai. 

Cewar Hamida a sanyaye kanta a sunkuye dan bata ɗago kai ba, Jamil ya ce ok ya juya cike da tausayinta, ace a daren farkon aurenta yazo da irin wannan ƙalubale, sauƙin abun ma babu wanda ya fahimci da gangan Laila ta aikata haka, saboda da sun san meke faruwa da ba wannan maganar ake yi ba sai hakan ya haifar da babban rikici. 

****

LAILA. 

Koda Zahida ta isa ɗakinsu ta samu Laila akan gado tayi ɗai-ɗai abunta tana ta game da wayarta, data ji shigowar Zahida ta miƙe ta zauna tana cewa. 

Hafiz ne.? Amma ya wuce ko.?

A'a basu tafi ba dan yanzu dana hau sama na hango su a jikin motarsa suna magana. 

Rabu da shi ɗan wahala kawai, ai wlh yau sai sunyi kwanan baƙin ciki shi da amaryarsa. 

Amma anty ba kya tunanin yasa a ɓalle ƙofar. 

What.? Wlh daya kunnawa kansa wata sabuwar fitinar, ba zai yi haka ba nafi tunanin zasu kwana a hotel, koma dai miye nayi abunda naji sanyi a raina, dan wlh zuciyata fes. 

Ta ƙare maganar cikin dariya, Zahira ta yi murmushi. 

Waya ga ango na kwanan hotel, kuma yadda muka gajiyar da shi babu abunda zai iya sai dai barci, Deeni fa cewa yayi a hargitse yake. 

Ta ƙare maganar tana dariya, Laila ma ta shiga kyalkyale dariya har da riƙe ciki, can kuma sai dariyar ya rikiɗe ya komai kuka, ta shiga yinsa da ƙarfi kamar wacce aka aikowa saƙon mutuwa, Zahida ta tsaya cak tana kallonta cike da matsananin mamaki da tsoro. Haka Laila ta cigaba da fidda amon kuka mai cike da baƙin ciki, bata taɓa zaton haka zata ji zafin ƙara auren Hafiz ba, da farko ta zata abu ne mai sauƙi kamar yadda mutane suke cewa ta jure ba wani abu bane, amma kuma yanzu ta tabbatar da cewa abu ne babba da ba ko wace mace take iya jurewa ba, ita sai yanzu taga wautarta data yarje masa har aka kawo wannan gaɓar, yanzu bata ganin laifin mata masu yi wa mazansu asiri su mallake su, babu zancen ƙara aure, amma kuma ita bata taɓa yarda da malamai ba dan gani take duk 'yan daffara ne kuma hasali ma mahaifiyar su macece mai tsantsenin irin wannan shirkan, su riƙaƙƙun 'yan boko ne dan hatta mamansu lecturer ce, sunfi ƙarfi a abunda ya shafi boko dan ko addini wajiban da suka hau kansu suke yi, sannan kuma kaf danginsu dake nan cikin birni babu wacce aka yi wa kishiya saboda mazansu duk 'yan boko ne sun fi ganewa mace ɗaya basa son damuwa, shiyasa wannan ƙarin auren yayi wa danginta zafi sosai, dan akanta za a fara kafa tarihin anyiwa mace matashiya kamarta kishiya a zuri'arsu.

Mahaifinsu Alhaji Adam Sanga dan asalin southern Kaduna ne daga ƙaramar hukumar Sanga a cikin garin Ninzom, su na da yare da ake kira Gwantu, asalinsu musulmai ne sai dai suna da 'yan uwa aljihun baya, amma hakan bai hana su yin zumunci da juna ba, wannan ne yasa Alhaji Sanga da ya tashi yin gini bayan zaman da yayi a gidan gomnati ya yi gida a can Barnawa kusa da 'yan uwansa musulmai da kiristen. Adam ya haɗu da matarsa Maryam a ABU Zaria lokacin yana ajin ƙarshe na kammala digree ɗinsa ita kuma tana aji na biyu, sunyi soyayya sosai da shaƙuwa kuma ra'ayinsu na son rayuwar boko na Turawa yazo ɗaya, wannan yasa soyayyarsu ta kai su ga matakin yin aure, duk da Maryam 'yar asalin jihar Katsina ce amma mazauna cikin garin Kaduna a unguwar Askolaye, iyayenta sun so ƙin yarda da auren, kasantuwarsa ba asalin Bahaushe ko fulani ba, amma Maryam ta dage akan taji ta gani, bayan kammala bautar ƙasarsa suka yi aure kuma a lokacin ya samu aiki a Abuja ita kuma ta cigaba da zama a Zaria har sai da ta kammala karatun ta kafin ta bishi. Haka ya soma samun transfer daga gurin aiki suka dinga zagaye a cikin jahohin ƙasar har zuwa kudu da arewacin Nigeria, Adam ya soma kama manyan kuɗi shiyasa ya haɗa da kasuwancin citta dan garinsu suna noman citta sosai, a hankali har kasuwancinsa ya miƙa yana fitar da citta ƙasashen waje.

Bayan wasu shekaru suka dawo Kaduna lokacin haihuwarsu uku Saudat ita ce ta farko sai Laila sannan Majeed, duk yaran babu wanda suka sakawa sunan iyayensu a cewarsu an dai na wannan yayin, kuma wasu sun saka a cikin 'yan uwansu dan haka bai zama dole su saka ba. Su Laila sun taso cikin gata dan babansu yana da kuɗi kuma zallar rayuwar boko aka nuna musu duk da suna zuwa islamiyya amma basu bashi ƙarfi sosai ba, a nan Kaduna aka Haifi Zahida sannan Shamsuddeen da ya zama auta. A yanzu babansu yayi retired a aikin gomnati amma yana cikin harkar siyasa dumi-dumi dan abokansa duk 'yan siyasa ne, dan Saudat ma ta auri ɗan abokinsa wanda yake a matsayin deputy governor ɗin jihar Kaduna. Sannan Alhaji Sanga yana da company guda biyu ɗaya a Kano na lipton mai suna Zadeen black tea da kuma madara Zadeen Cremer, sannan anan Kaduna yana da company pure water mai suna Zadeen table water, suna yi harda na manyan gora na dispenser, sannan suna yin yoghurt Zadeen yoghurt, akwai Kuma gidan biredi da yake da shi kusa da gidan ruwa mai suna Zadeen Soft bread, a cikin kankanin lokaci ya shahara domin a jerin mutane talatin na masu kuɗin Kaduna za a saka Alhaji Adam Sanga a ciki, sannan ya gatanta 'ya'yansa sosai shiyasa suke rayuwa babu takura ko kwaɓa sai abunda suke so shi suke yi kuma iyayensu suna mara musu ba.

Shiyasa da iyayenta suka samu labarin Hafiz zai ƙara aure suka ji haushinsa sosai suka taya 'yarsu kishi, mommy har kiransa tayi gidan yazo ta wanke shi tas, dan a gurinta gani take kamar babban zubuni ne ya aika tunda zai saka mata 'ya a cikin damuwa, Hafiz haƙuri ya bata ya miƙe yayi mata sallama ya tafi, ko da ya buƙaci ganin Abba cewa yayi yana meeting sai wani lokaci, haka ya ja 'yan matan ƙafarsa jiki ba kwari ya bar gidan. Hafiz ya shiga damuwa sosai akan irin abunda iyayen Laila suka yi masa, jikinsa yayi sanyi wanda ya saka shi jin ko ya fasa auren, saboda baya so ya samu matsala da su ko kaɗan dan yasan idan har basu goyi bayan auren ba to tabbas aurensa da Laila zai fara rawa, kuma shi bai shirya rabuwa da matarsa ba dan yana matuƙar sonta. A ɓangaren yayar Laila Anty Saudat itama ba ƙaramin tijara tayi masa ba, amma daga ƙarshe ya bata haƙuri ya tabbatar mata saida Laila ta amince da auren kafin ya ce zai yi. Kuma bayan ta haɗu da Laila tayi magana da ita sosai har ta fahimci manufar auren, dan haka sai suka sausauta ƙiyayyarsu ga auren suka shiga kwantarwa Laila da hankali har abubuwa suka zo suka kwaranye aka fahimci juna, sai dai na ciki yana ciki tunda Laila ta su ce, kuma ba zasu so su ganta a cikin damuwa ba a dalilinsa, wannan yasa yake taka tsantsan wajen kauce wa duk wani abu da zai ɓatawa Laila rai.

Zahida ta dafa ƙafaɗar Laila tace cikin sigar rarrashi.

Dan Allah Anty Laila kiyi haƙuri haka kar ki jawowa kanki wani ciwo, haba tuntuni baki yi ɓacin rai ba sai bayan auren, ai aikin gama ya gama fa.

Zahida bana numfashi duhu nake gani, ji nake kamar zan mutu. Na ɗauka abunda na aikata zai sa na ji sanyi a raina na daure kamar yadda ake faɗa amma na kasa! na kasa!! Shi kenan Hafiz ne da auren wata, tabbas na haukace, na shiga uku! Allah ya wadaran soyayyar da nake yi masa da kullun yake saka ni cikin ƙunci tun bayan aurenmu... Wayyo Allah ƙirjina nauyi, nauyi...! 

Ta ƙare maganar cikin matsanancin kuka tare da jawo numfashi da ƙarfi ta duƙa akan guiwarta dafe da ƙirjin, da gudu Zahida ta fito daga ɗakin ta shiga kwalawa momy kira tun daga saman bene, Momy da shigowarta kenan daga ɓangaren Dady ta amsa cikin buɗe murya.

Dan uban ki Zahida wannan wane irin kira ne, me ya faru.? 

Zahida da saukowarta kenan ta ce cikin nishi.

Mom mommy anty Laila ce bata numfashi tana ta kuka.

Momy bata tsaya sake wata magana ba ta bi steps ta hau sama zuwa ɗakin, sun sameta ta kwanta ta rungume da hannunta ta takure a guri ɗaya sai fizgo numfashi take yi, Momy ta ce cikin gigicewa.

Na rante da Allah idan yaron nan yayi sanadinki sai ya ƙare rayuwarsa a kurkuku, kira wayar Abbanku ya zo yanzu Zahida.

A'a momy kar a kira shi zan dawo dai-dai, ku bani ruwan sanyi nasha.

Cewar Laila cikin sanyin murya, da sauri Zahida ta isa ƙaramin fridge da yake ɗakin ta ɗauko ruwan gora ta buɗe ta kawo mata, Laila ta tashi ta zauna ta amsa ta kafa gorar ta shanye tas kafin ta aje gogar ta saki gyatsa, ta ce cikin sakin murmushi.

Hmmm naji sanyi a raina kuma kukan dana yi ya sa ƙullin daya riƙe mini haƙarƙarina tamau ya saki. Momy ki kwantar da hankalinki naji sauƙi, dama kukan nake buƙata kuma nayi na ji sauƙi. Zahida su Hafiz sun wuce ne.?

Eh ba a jima ba naji fitar motarsu.

Ki rashi a waya ki ce yanzu muka dawo bani da lafiya numfashi na yana ɗaukewa.

Angama ranki ya daɗe.

Zahida ta faɗa tana murmushi, momy ta taɓe baki tana cewa.

To me zai miki.? ki rabu da shi yaji da damuwarsa.

Allah momy yadda nake cikin ƙunci a daren nan shima babu shi babu kwanciyar hankali haka itama amaryar, yau zan tabbatar muku da irin tasirin son da Hafiz yake yi mini, shiyasa ban hana shi auren ba domin nasan ni ce duniyarsa.

To Allah ya kyauta, Kuma tunda kin san haka ne karki ƙara tayar mana da hankali a banza.

Cewar momy cikin haɗe fuska, sai ta miƙe ta fice daga ɗakin Laila ta rakata da murmushi sai ta koma ta kwanta. Zahida ta kira Hafiz sai dai wayarsa ya ƙi shiga, wanda a hanya ta mutu ya saka a chagyn mota ya bawa motar wuta dan ya isa gurin Hamida da wuri. 

Anty wayar a kashe, ƙila ba chargy.

Cewar Zahida tana kallonta, sai Laila taja guntun tsaki.

Wlh ba haka naso ba amma ko ba komai na ruɗa kwanyarsa.

Anty ina ganin ki rabu da shi haka, ai kin bashi babban assignment ɗin da zai kwana yana bitarsa. Kawai ki saki komai tunda an riga an ɗaura tunda ƙarin aurensa yana cikin ƙaddararku, sai dai karki yarda ki ɗauki raini daga matarsa.

Idan na bada fuskar rainin kenan, haɗo mini tea ki soya mini kwai da tsire a ciki, sai ki haɗo mini da zadeen bread mai yanka-yanka.

Hooo anty baki wasa da cikinki, yanzu duk da kina cikin damuwa amma sai kin bashi haƙƙinsa.

Dan uban ki idan na kashe kaina saboda shi waye ke da asara in ba ku ba, to damuwa dole ce dan ban isa in raba kaina da ita ba, amma kuma ba na jin zan bari wani ciwon ya kama ni a dalilinsa, dan duk da irin son da nake yi masa a yanzu zan iya yin nesa da shi, ba Lailan da kika sani da bace mai yin makauniyar soyayya.! dan da zan iya dawo da hannun agogo baya tabbas da na sauya ƙaddarar haɗuwata da Hafiz balle azo wannan gaɓar. 

Ta ƙare maganar tana mai sauke ajiyar zuciya, Zahida ta gyaɗa kai alamar gamsuwa sai ta fice daga ɗakin tana murmushi.

*****

Hafiz..

A hanya mai ya ƙare musu sai da suka tura motar da kyar suka samu wani ɗan bumburutu ya saka musu mai suka ƙarasa, shi dai ranar yau ya zame masa baƙar rana daya saka shi cikin kundin tarihinsa, da farko sam bai hango zai fuskanci wata matsala da auren Hamida ba ganin yadda komai ya zo masa cikin sauƙi har kawo ɗaurin aure, ko da yake ance ko wani aure yana zuwa da matsala to nashi sai yau ne ya zo kuma yana tsaka da farin ciki amma komai ya rushe, ko wannan tura motar da suka yi ba ƙaramin ƙara gajiyar da shi yayi ba, ga azabar yunwa yana damunsa, ga kuma matsalar Laila data kunno masa da shi rana tsaka wanda bai yi zato ba, hura iska yayi daga bakinsa ya na furta.

Allah ya tsayar min da wannan matsalolin da suka kunno kai kasa iyakar ƙalubalen da zan fuska kenan a auren nan.

Tsakin da Musa yaja shi ne ya fahimtar da shi maganar a fili yayi, ya kalle shi yana guntun murmushi.

Kayi haƙuri abokina kai ma yau na gama gajiyar da kai sosai, bari na sauke ka a gida.

Muje kawai in ya so Jamil ya ɗauko ni, kaga mun sallameka gabaɗaya ba zancen siyan baki kuma sai mun zo cin girkin amarya.

Musa janye maganar cin girkin amarya nan kar Laila ta ƙullace ku.

Na nawa kuma, ai ni wlh matarka ta gama goge mini hadda ta kuma ƙara hasko mini halin kishin mata, kaga in muma zamu ƙara aure zamu yi saurin ɗaukar mataki kafin su yi mana irin naka, ko da yake wannan maganar Sadiya ba zata ji shi balle tayi mana dariya.

Cewar Musa yana murmushi, Hafiz ɗin ma murmushi yayi suka cigaba cewa.

Kasan meyasa ba zan ɗauki mata akan Laila ba, saboda tun farkon maganar auren ta yi juriya bata kawo mini matsala ba bayan na shawo kanta, nayi mata uzuri domin kishi babu abunda baya sakawa, idan har abunda ta aika zai sa taji sanyi a ranta har su zauna lafiya da Hamida to ni kuma ba zan nuna mata ɓacin rai na ba domin nasan komai zai wuce.

Hakane kayi tunani mai kyau amma a gareka, sai dai in da nine wlh sai ta san tayi haka dan wlh sai na hukuntata, sai dai duk abunda zata yi tayi, aure ne fa ba zaman zina zanyi ba, in banda abun mata da ace mu riƙa niman matan banza a waje ai gwara mu ƙara, sannan yadda mata suka yi yawa in bama ƙara auren ya za a yi dasu.

Haba kai ma kasan lissafinmu da nasu ba zai taɓa zuwa ɗaya ba. Amma fa ni daga Hamida bana tunanin zan ƙara dan bazan iya da hayaniya ba.

Cewar Hafiz haka suka ƙarasa gidan suna hira wanda yasa Hafiz ya samu sassaucin ɓacin rai da damuwar da yake ciki.

Rahma ce