4
*BAYAN AURE*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 4.
Sarac Stars R Pen...✍️
A waje Hafiz yayi parking ya fito ya bar Musa a mota ya wuce cikin gidan da sauri. Ya buɗe ƙaramar ƙofa ya shiga, Jamil ya ƙaraso wajensa da sauri ya bashi hannu yana cewa.
Ni fa zan gudu dan madam sai kirana take yi, dan haka Allah ya bamu alkhairi.
Ok, Musa yana waje ka rage masa hanya.
Wlh ka sauke shi dan bana so na ƙara minti ashirin ban isa gida ba, mun gama haɗa naka auren ba zan yarda nawa ya samu tangarɗa ba.
Shegen kaya, ka dai zama mijin tace.
Haba dai ai ban kaika ba, saboda abunda matarka ta shuka maka yau kasan ba zan taɓa ɗauka ba dole sai ta girbe shi.
Cewar Jamil yana dariya, Hafiz ma dariya yayi yana girgiza kai, haka Jamil ya wuce gurin motarsa ya shiga maigadi ya buɗe masa gate, Hafiz kuma da sassarfa ya ƙarasa gurin Hamida ya tsaya.
Allah ya huci ran gimbiya amarya, kiyi haƙuri akan yadda abubuwa suka faru.
Zuciyata ai dole na karɓi uzuri dan rashin lafiya ya wuce gaban wasa. Ya mai jikin.?
To godiya nake, kuma jiki da sauƙi, yanzu muje gidan umma na sauke ki ko.
To tace masa sai ya wuce tabi bayansa suka fita maigadi ya rufe gate ɗin dan Hafiz ya sanar da shi ba zasu dawo ba sai da safe. Ya buɗe mota gidan baya ta shiga ta zauna ya rufe, kafin ya koma mazaunin driver ya kunna suka wuce gidan umma, haka suka yi tafiyar kamar na kurame dan Musa kwantar da kai yayi kamar mai bacci. Lokacin da suka isa tudun Wada Hamida taji Kamar tace ya sauke ta a gidansu amma babu hali, tana gani suka wuce Layinsu suka wuce kinkinau wanda a nan gidan ummansu yake. Bayan sun isa yayi parking a ƙofar gate ya fito yace mata itama ta fito, kafin suka nufin ƙofa ya shiga bugawa, da yake babu maigadi shiyasa aka samu jinkirin buɗe musu, suka ji murya Husaini yana cewa a hankali.
Nan ne.? waye.?
Hafiz ne ka buɗe.
Jin muryarsa yasa Husaini ya isa ƙofar da sauri ya buɗe cikin mamaki yana cewa.
Babban yaya lafiya cikin daren nan.? ashe ba kai kaɗai bane, ya tabbata anty Laila bata bada key ɗin ba, ɗazun su Suhaima suka dawo da labarin...
Zaka matsa mana mu shiga ne ko sai ka gama ƙarar da zancenka, faɗi ba a tambaye ka ba.
Sorry Yayanmu.
Husaini ya faɗa yana shafa kansa sai ya matsa suka shiga ciki ya rufe gate kafin yabi bayansu. Da suka shiga falo sun tadda umma da su Suhaima duk suna zaune, da alama hira suke yi kuma a lokacin ana maganar sha biyu na dare.
Hafizu lafiya.? Ke ɗiyar albarka ƙara so ciki, gaskiya Laila bata kyauta ba ai wannan shirme tayi, taya zata rufe gida ta yi tafiyarta.
Kai umma an ce miki Khalil ne fa ba lafiya.
Cewar Suhaima cikin ankarar da Umma dan kar ta yi suɓul da baka, Umma ta ce.
Ai duk da da haka ko megadi sai ta barwa key ko kuma ta bar ƙofar a buɗe tunda tasan baƙi zasu zo. Suhaima kaita ɗakinku ki zo ki ɗibar mata abinci dan na tabbatar ba zata rasa jin yunwa ba, in ta kammala sai ta kwanta ta huta.
To Suhaima ta faɗa ta miƙe, Hamida kuma a lokacin ta samu damar gaishe da su umma suka amsa kafin ta miƙe daga zaune da ta yi a kan carpet tabi bayan Suhaima, Hafiz ya yi hanyar waje yana cewa.
Umma sai da safe zan sauke Musa a gidansa.
To kai ina zaka kwana.? ai gara ka dawo nan ka kwana tare da 'yan biyu.
A'a karki damu zan kwana a hotel.
Amma yarinyar nan bata kyauta ba ina yabonta sallah amma ta kasa alwala, sai bayan aure zata hudo da sabon tsiya kuma, sannan ita aka yi wa gata da karin auren nan fa.
Umma ta faɗa tana biyo bayansa zuwa gate, Hafiz daya buɗe ƙofa ya dan tsaya yana cewa.
Zuwa da safe nasan ta huce In Sha Allah komai zai yi dai-dai, amma dan Allah a rufe maganar nan kar Hamida ta fahimci meke faruwa.
Ai ba zamu bari ta san kamai ba ɗazun ma mantawa nayi, amma kasan me zai faru, da safen kazo ka ɗauke ni muje har gidansu Laila na bata baki komai ya wuce, dole muyi mata uzuri dan mun san halin kishi.
To shi kenan sai na zo da safen In Sha Allah, mu kwana lafiya.
Cewar Hafiz kafin ya fita umma tace Allah yasa kafin ta rufe gate ɗin da kanta ta koma cikin gida, daga haka ta ce su Husaini su wuce su kwanta dan dare yayi saboda bata so a cigaba da wata maganar da zai sa a kawo zancen Laila har Hamida ta gane halin da a ke ciki.
*****
Hamida.
Ta samu kanta a matukar takure, ga kuma tunanin maganar Husaini dana Umma suna juya mata tunani, sai ta fara saka shakku akan rashin lafiyar yaron Laila da Hafiz ya faɗa, shiyasa ko abincin da suka kawo mata dafadukan shinkafa bata iya ci ba sai ruwa da lemun gora ta iya sha, duk da tana jin yunwa amma bata tunanin shinkafar zata wuce mata ta daɗin rai, a wannan lokacin ruwan tea take buƙata sai dai ba tada halin nuna tana so duba da gidan surukai ne, haka ta miƙe jiki a sanyaye ta ɗauro alwala a bayin cikin ɗakin tazo ta gabatar da sallar isha'i ta haɗa da shafa'i da wutiri kafin tayi gajerun addu'o'i ta shafa, sai ta miƙe ta ninke dadduma ta mayar inda ta ganshi da hijab ɗin, sai ta ɗan zuge zip ɗin rigarta ƙasa yadda zata ji daɗin bacci kafin ta hau katifar dake yashe a ƙasa, ta warware ɗankwalin kanta ta yafa ta kwanta tare da rufe fuskarta da shi, ta yafa gyalenta a ƙafarta, a cikin zuciyar ta ta shiga koro addu'ar bacci har ta gama, tana ji Suhaima ta shigo sai tayi kamar bacci ya ɗauke ta, sai taji tana cewa Rashida.
Anty Rashida kin ga harta yi bacci baiwar Allah, kuma nazo da niyyar in bata ɗaya daga cikin doguwar rigana ta saka ta kwanta dan bacci da leshi ba daɗi duk ka takura, wlh ta bani tausayi, ace a daren farkon aurenta ta fara gamuwa da matsalar kishiya. Nifa a wannan abun da Laila tayi duk kirkin da take yi mana sai da naga laifinta tunda ba zan goyi bayan zalunci ba.
Amma umma tace a bar maganar nan ko.
Anty ki bar ni inyi magana abun akwai rainin wayo a ciki, ita tayi abunda take so da gangan an kuma zura mutane akan khalil ba lafiya, kuma wlh sun yarda fa, mu ne dai da muka san cewar haɗa magana kawai yaya yayi dan ya wanke matarsa.
Cewar Suhaima cikin ƙasa da murya, sai dai kuma duk hirarsu a kunnen Hamida wanda zancen lafiyar Khalil ƙalau ya daki zuciyarta, yanzu ta gane maganar Husaini dana Umma inda suka dosa.
Kenan abun dama shirin Laila ne dan ta nuna mini iyakata.
Tace a cikin ranta, nan take ta ƙara jin duk jikinta ya mutu da lamarin, ta shiga yiwa kanta hangen matsala mai cike da tsoro, shiyasa tun farko taso gujewa auren Hafiz amma kuma Hajjo ta dage mata bisa kwaɗaita mata arzikin da zasu warɓa, amma ga dukkan alamu gashi zata sha fama da kishin Laila wanda ita sam bata shigo da niyyar zama irin wannan ba, da kyakkyawar niyya ta shigo gidan Hafiz, burinta ta zauna lafiya dan zaman aure ibada zata yi na haƙiƙa wanda zai kaita zuwa aljanna, bata shigo da wata niyya na rashin zaman lafiya ba ko na son rabasu ba, ko kuma na son Hafiz sai ya fifitata akan Laila. Da yawan 'yan mata da irin wannan niyyar suke shiga gidan aurensu, kuma da ace so samu ne ba kowace mace bace zata so auren mijin wata ba sai dai idan yana cikin ƙaddararta, duk da wasu suna faɗar sun fi son masu mata amma a wajen Hamida wannan ba ya cikin tsarinta, Allah ya ƙaddara masa aurensa ne kawai ba dan ta so ba, kuma soyayyarsa ma ta yi mata jagora wajen sarƙafe zuciyarta na amincewa auren, sai dai gashi ba aje ko ina ba Laila ta soma shimfiɗa mata irin halinta, kuma a irin haka ne mata da dama suke zubar da ƙimarsu na uwargida da Allah ya basu, koda amarya ta shigo da niyyar a zauna lafiya to irin wannan halayya da uwargida ke nunawa na zafin kishi da rashin mutunci to shi ne ke sanya kwaɓarsu ta yi ruwa, me makon su bar amarya ta dama lokacinta wanda ita kanta tasan ba zata taɓa samun dama kamar na uwargida ba, saboda miji ya saba da halayyar matarsa ga hidimar yara, ita baƙuwa ce da komai sai ta bishi a hankali kafin zata san kan mijin, me yake.? meye baya so, duk sai a hankali zata sani, Uwargida kuwa ta sani in kuma ta kwantar da hankalinta sai kuga ta cigaba da damawa a cikin kwanakin amaryar, sai dai wasu matan wannan kumallon shi ne yake sakasu su tafka kuskuren da zai kai su ga danasani, miji ya wulaƙantata ya raina ta, daga nan amarya ma ta raina ta, ta kuma yi amfani da damar uwargida ta kame miji ram da kyautatawa. Ana cewa na watanni ne ango zai gama ririn amarya ya komawa uwargida amma sai a ji shuru ta cigaba da jan ragamar zaren zuciyar ango, a hankali sai girman daya dace uwargida ta samu sai amarya ta amshe, daga nan a riƙa cewa amarya ta asirceshi bayan babu asirin komai sai tsabar kyautatawa tana yi masa duk abunda yake so, a wannan gaɓar ne Uwargida zata zo tana so ta dawo da hankalin miji gareta da kuma martabanta, sai dai kash! ta riga ta rasa shi domin shi mutunci madara ne in ya zube baya kwasuwa, ƙawayenta su zugata ta soma shaye-shayen magungun mata da tushe-tushe a hq ta haukata kanta, dan so take da ƙarfin tsiya sai miji ya dawo hannunta, wata ma in ba a yi sa'a ba sai ta faɗa bin malamai su riƙa dulmiyar da ita suna bata magungunar mallaka da asirin da zai zama sai ita ce kaɗai zata iya juya akalarsa, daga nan buƙata ta biya sai ta hudo da iyayi tsurfa-tsurfa akan miji yafi sonta, wani abun ma da gayya zata yi a gaban amarya dan dai ta nuna mata itace ran gida. Sai dai kuma asiri kwana arba'in ne yake tasiri, da zarar wannan wa'adin ya cika zai fara raguwa musamman in amarya mai ibada ce sai kaga komai ya rushe, shiyasa mata masu yin asiri basa aje komai kullun suna zarya wajen malamai saboda basa haƙura, kullun cikin sabunta asirin suke yi dan kar kwaɓarsu tayi ruwa. Sai dai ga mace mai nasara In ta riƙe Allah lamarin ta baya taɓewa, domin zai zame mata bangon jingina, zai same mata madafar kamawa, domin Allah shi ne kaɗai isasshe. Duk asirin mai asiri in dai kika kama Azkar kika cigaba da kyautatawa miji matsayin ki yana nan daram, ƙimarki tana nan a zuciyarsa, koda an juyar masa da kai wannan abun yana manne a zuciyarsa, kuma addu'a da sadaka shi ne zai cigaba da haƙaiƙaito da zuciyarsa gareki, zaki zama inuwar natsuwarsa, idan yana tare dake zai ji kamar karya rabu dake koda bai fito ya faɗa mini ba, a hankali zai riƙa nuna miki a aikace, ke dai ki kama Sarki Rabbi da baya gyangyaɗi.
Hamida ta san tare ta gansu dan haka ba zata shiga tsakaninsu ba dan in tayi haka tama so kanta da yawa, taya zata raba abunda Allah ya haɗa tun kafin asan da wanzuwarta, tasan tana son Hafiz sosai kuma tana da zafin kishi wanda yasa tun farkon tsarin rayuwarta babu niyyar auren me mata, dan cewa tayi babu abunda zata yi da namiji second hand, amma sai gashi Allah ya ƙaddara mata auren Hafiz wanda tasan Allah ya yi hakan ne dan ya jaraba Imaninta, kuma ta karɓa da hannu bibbiyu tun sadda maganar aurensu ya fara, ta kuma shiga addu'a akan Allah ya raba ta da zafin kishi ya bata ikon yiwa mijinta biyayya, kuma kamar yadda Hafiz yake jaddada mata zancen matarsa na ta yi mata biyayya wannan yasa ta ɗauketa da muhimmamci wanda ko kaɗan zuciyarta bata kawo mata tunanin ta yi wa Laila rashin kunya ko wani raini ba, tunda taga shi da yake da ita ma yana gudun abunda zai ɓata mata, hakan yasa take ganin ƙima da darajar Laila sosai domin Hafiz ya ɗaga darajarta a idon ta, ba zama ta yarda ta kuskure ba dan kar ace ta zo musu da matsala, ta ɗauki aniyar binta sau da ƙafa in dai hakan zai faranta ran Hafiz, amma kuma yanzu sai taji duk guiwarta tayi sanyi dan ga dukkan alamu Laila ba zata barta ta sha ba, tunda gashi yau kaɗai da ta kasance matar Hafiz ta fara fuskanta ƙalubale, kamata yayi a yanzu tana ɗakinta tare da mijinta amma kuma gashi ta ƙare da kwana a gidan surukai ɗakin ƙannensa. Hawayen da bata so su zubo ne suka fara sauka daga gefen idonta suna sauka kan pillown da take kwance, yadda tayi nisa a tunani bata ji ƙarshen hirarsu Suhaima ba, sai da ta hau katifar ta kwanta a gefenta shi ne taji tana cewa.
Anty Rashida sai da safe ni na kwanta.
Allah ya bamu alkhairi.
Rashida ta bata amsa kafin ta fice zuwa falo dan a can zata kwanta. Da yake babu wasu baƙi a gidan sai su dan Umma bata yi gayyan mutane ba sai dangi na kusa ne suka zo, mutanen Yobe ma sai da aka ɗaura auren kafin ta kira su ɗazun take faɗa musu, saboda bata so ta ɗorawa kowa hidima dan tasan su da zumunci, sai suce sai sun zo ga tsadar rayuwa, na abinci ma yana yiwa mutane wahala, shiyasa bata yi taro sosai ba dan ba baƙin da suka kwana sai 'ya'yanta.
Da safe...
Rahma ce.