SO DA HAWAYE!

9&10

by @mrsalkali01




đź’«SO DA HAWAYE đź’« 

✍️Mrs Alkali.

*LAST FREE PAGE Page 9-10*


Ina jin Nazir ya yi saurin sallama da ni, gabana ya fadi. Ban taba ganin inda ya gaggauta kashe kiranmu ba sai yau. Bayan ya kashe kiran nawa, ya kalli allon wayarsa ya ga sunan Hajia Zeenat yana yawo. Ya dan ja dogon numfashi, ya gyara murya sannan ya dauka.

"Hajiya, barka da dare," ya fada cikin rawar murya.

Daga daya bangaren, Hajia Zeenat ta saki wata 'yar dariya mai cike da kissa da kasaita. "Nazir, har na fara fushi. Ka tafi ka bar ni ba tare da ka min bankwana na musamman ba. Ko har ka manta da batun kwangilar miliyan hamsin din nan ne?"

Nazir ya dan yi sanyi, ya fara nokewa. "A'a Hajiya, akwai wasu harkoki ne suka taso min a gida, shi yasa na wuce batare da na miki sallama ba."

Hajia Zeenat, gogaggiyar mace, ce ta fahimci lagon sa. "Kada ka damu, na san harkar gida tana bukatar kuÉ—i, kuma ai na san ko ma me kake yi yanzu kuÉ—in da na baka sun sanya ka farin ciki. Amma Nazir, wannan kuÉ—in sunyi kad'an. Akwai wasu miliyoyi guda biyar da nake son tura maka a daren nan idan har za ka iya zuwa gida na gobe mu karkashe maganar business dinmu."

Miliyan biyar? Nazir ya ji kansa ya dauki zafi. Duk da yana kokarin nuna shi mutumin kirki ne mai son rufin asiri, amma jin yawan wadannan kud'ad'en ya sa ya fara sakin jikinsa da ita.

"Miliyan biyar kuma Hajiya?" Nazir ya tambaya, muryarsa ta kara lafawa, ta d'an yi sanyi.

Hajia Zeenat ta cigaba da jansa da hira, tana sanya masa hoton rayuwar alfarma, tana nuna masa cewa idan ya bi ta, ba zai sake sanin zafin talauci ba. "Kwarai kuwa, kuma daki na musamman na tanada maka a katafaren gidana dake cikin unguwar Federal low cost, domin ka huta yayin da muke gudanar da aikin nan."

A hankali, Nazir ya saki jiki, suka fara hira sosai, har ma ya manta da cewa HĂĽda tana jiran shi. 


#TheSugarMummyCall #BetrayalInTheMaking #MoneyVsLoyalty #NazirFallingDown #HajiaZeenatIntrigue #TheBigMistake #SoDaHawaye

Ina kwance a daki ina tunanin kalaman soyayyar da muka yi da Nazir, ban sani ba ashe a daidai lokacin shi kuma duniyarsa ta sauya.

Bayan sun dade suna hira da Hajia Zeenat, tana nuna masa cewa shi din na musamman ne a wajenta, can sai ta ce masa, "Nazir, duba wayarka yanzu, na tura maka wani abu wanda zai sa ka yi barci cikin kwanciyar hankali. Wannan kawai don na nuna maka cewa ni mace ce mai cika alkawari."

Nazir bai gama rufe baki ba, sai ga Karan sako (Alert) ya shigo wayarsa. Ya zaro ido, numfashinsa ya dauke na dan lokaci lokacin da ya ga adadin kudin: N5,000,000.00.

Miliyan biyar rigis! A lokaci guda! Jikin Nazir ya fara rawa, zufa ta wanke masa goshi duk da sanyin dare. Ya kasa yarda da abin da idonsa yake gani. A rayuwarsa, bai taba mafarkin mallakar ko miliyan daya ba lokaci guda, balle biyar.

"Hajiya... wannan kudin sun yi yawa," ya fada muryarsa tana karkarwa.

Hajia Zeenat ta saki wata 'yar dariya mai cike da mulki da kissa. "Ga wanda bai san darajarka ba ne kuÉ—in suke da yawa, amma a wajena wannan kuÉ—in ba komai ba ne. Sai dai ka sani Nazir, ba na zuba jari a inda ba zan ci riba ba. Ina jiran ka a gidana gobe, akwai sauran abubuwan da nake son mallaka maka."

Nazir ya kasa cewa komai sai godiya. A wannan daren, Nazir bai yi barci ba. Ya dinga kallon wannan lambar a wayarsa, yana lissafin yadda zai je gidan ta gobe, ya bar ni da batun shirye-shiryen biki. 


#TheFiveMillionAlert #TheGoldenHandcuffs #NazirInTheTrap #SugarMummyPower #WealthOverLove #HudasHeartbreakLoading #SoDaHawaye


Bayan na idar da sallar asuba, na zauna a kan sallaya na daɗe ina addu'o'i. A raina, babu kowa sai Nazir. İna hango ranar da zan zama matarsa, ranar da zamu shiga sabuwar rayuwa. Da na fito tsakar gida, ko Ummanmu da Baba Ladi sai da suka lura da canjin da fuska ta ta yi; wani irin haske da annashuwa ne yake malala a kowace gaɓa ta jikina.

"Huda, yau kuma wane irin farin ciki ne haka? In ji ummanmu da alama tana zolaya ta ne.

Na rufe fuska cikin jin kunya, "Haba Umman mu, kawai dai ina jin daÉ—i ne."

Daga nan Na shiga wanka, na fito na shirya tsaf cikin unifom ɗina na aikin jinya (Nurse). Farar riga da wando tsaf, sannan na ɗaura farin ɗan kwali na sanya farin baby hijab dina. Madubi na kalla, na ga yadda kyan fuskata ya ƙara fitowa, ba don kwalliya ba, sai don kwanciyar hankali, ko break fast ban tsaya nayi ba nayiwa su Umman mu sallama.

Na fito daga gidanmu da sauri don in nufi wurin aikina, wato Specialist Hospital Gombe. A hanya, duk wanda na gani, murmushi nake masa. Ina jin kamar kowa ya san cewa nan da wata É—aya zan zama matar Nazir.

Ina tafiya ina tunanin kalaman Nazir na daren jiya, ina ƙara gode masa a zuciyata yadda ya yi fadi-tashin nemo mana kuɗin da zamu gina rayuwar mu.

Ina isa asibiti, na sa hannu a kan Register, na fara zagaye a Ward ɗinmu. Zuciyata fari ƙal.


#NurseHuda #SpecialistHospitalGombe #BrideToBe #MorningVibes #LoveAndWork #GombeNurse #SoDaHawaye


*******


A gidan Fatima, iskar soyayya ce take kadawa mai cike da ƙamshin kulawa. Tun bayan kwanaki hudu da Nurse Huda, taje ta dubata, Fatima ta kara samun sauki, amma hakan bai sa Ustaz Abdulmajeed ya rage nuna mata tattali da kulawa ba.

Yau ma kamar kullum, Abdulmajeed ne ya kammala dukkan aikin gidan. Ya shigo dakin kansa tsaye, sanye da farar jallabiya mai kamshi, fuskarsa dauke da wani kyakkyawan murmushi wanda ya sanya Fatima jin cewa ita ce mace mafi sa'a a duniya.

Ya zauna a gefen gadon, ya sanya hannunsa ya shafa kanta cikin sanyi, muryarsa can kasa yace, "Zuciyata, ya kike jin jikin naki yau? Fatan zafin ya ragu sosai?"

Fatima ta sunkuyar da kai cikin jin kunya, tace "Na gode Ustaz, jiki ya yi kyau sosai. Ai dama kai ne ka wahala..."

Kafin ta karasa, ya dora yatsansa a laburanta don yin shiru. "Babu maganar wahala tsakanina da ke. Ke fa sanyin idaniyata ce." Ya miko hannu ya dauko wani kwano mai dauke da yankakken kankana da ya sha sanyi, ya soka cokali ya kai mata baki. "Bude baki masoyiyata, wannan zai kara miki dad'i a jiki."

Yayin da yake bata abincin nan, idanunsa cike suke da wani irin shauƙi. Duk da cewa yana jin buƙatar matarsa tana nukurkusar sa, amma tausayi da kaunar da yake mata sun fi komai karfi a tare da shi. Ya matso kusa da ita, ya sumbaci goshinta cikin wani salo da ya sa Fatima taji wani dad'i ya ratsa ta.

"Fatima," ya kira sunanta cikin sanyi, "Ina son ki sani cewa ina miki son da koda kwanaki dubu zasu wuce baki warke ba, zan kasance mai miki hidima ba tare da na gaji ba. Kece aljihun sirrina, kuma kece farin cikina."

Fatima ta kalle shi, hawayen dad'i suka cika mata ido. Ga wani tausayin sa da yake ratsa zuciyar ta.


#UstazRomanticSide #FatimasWorld #LoveInTheSunnah #PureDevotion #HusbandGoals #SoftMoments #SoDaHawaye

Misalin ƙarfe 11 00pm Daren ya yi tsit, ƙamshin turaren wuta ya gauraye da sanyin d'akin. Fatima ta matso kusa da Abdulmajeed, ta dora kanta a ƙirjin sa, tana shakar dumin jikinsa. Cikin muryar lallashi tace, "Mijina, na san kafi kowa hakuri, amma yau ba zan bar ka ka cigaba da cutuwa ba. Ina son in kasance taka a wannan daren."

Abdulmajeed ya dube ta da mamaki da kuma tsantsar kauna, koda yake yana tsoron kar ya kara ji mata mata ciwo, amma kwarjinin soyayyar Fatima ya riga ya ci karfinsa. Nan take ya fara sarrafa ta cikin wani salo na kwarewa a hankali. Fatima ta ji wani zafi a kasanta saboda raunin dake wajen, amma yadda Abdulmajeed yake rarrashinta yana fada mata kalamai na addini, ya sanya radadin ya ragu.

"Zuciyata, ki yi hakuri," ya fada yana rada mata a kunne, "Kowace azaba da kika ji a sanadin biyan bukatar mijinki, Allah yana rubuta miki lada. Manzon Allah (SAW) ya nuna mana cewa biyan bukatar juna sadaka ce." Wadannan kalaman suka sanya Fatima jin wani sanyi, ta saki jiki ta biye masa, suka raya darensu cikin shauƙi da amincin da ya dace da ma'aurata.

Bayan komai ya lafa, Abdulmajeed bai kyale ta ba. Ya cigaba da rungume ta, yana shafa kanta tare da sanya mata albarka. Ya fara karanta mata hadisai dake nuna falalar biyayyar mace ga mijinta, da kuma yadda Mala'iku suke mata addu'ar alhairi idan ta faranta wa mijinta rai.

Daga nan, Abdulmajeed ya dauke ta cak zuwa bathroom tamkar jaririya. Duk da Fatima tana jin kunya, ya yi k'okarin kawar da ita. A can, ya nuna mata cewa wanka tare yana daya daga cikin sunnar Ma'aikin Allah (SAW) da yake kara dankon soyayya. Ya taya ta wanka cikin tsantsar kulawa, sannan ya fito da ita.

Bayan sun fito, ya zaunar da ita ya shafa mata mai da kansa, sannan shima ya shafa. Bai barta ta sanya sutura mai nauyi ba, ya ja ta zuwa gado, ya lullube su da bargo guda daya, inda fatar jikinsu take gauraye da juna, batare da sun saka komai a jikin su ba, (Body Contact). Ya rungume ta tsam a ƙirjin sa, ya karanta musu addu'o'in bacci, yana mata fatan alhairi. A haka bacci mai dadi ya kwashe su, suna cikin rantsattsen shaukin juna.


#HolyRomance #SunnahLove #UstazAndFatima #SpiritualConnection #HusbandGoals #NightOfLove #SoDaHawaye


Washe garin Hasken safiya ya gauraye da sanyin ɗakin, amma dumin da suke ciki ya fi komai daɗi a gare su. Abdulmajeed yana rungume da ita, yana shafa bayanta a hankali yayin da take lumshe idanu tana jin bugun zuciyarsa a nata. Ya sunkuyo da kansa dai-dai kunnen ta, muryarsa ta fito can ƙasa, ƙasa-ƙasa mai cike da shauƙi, ya ce:

"Humairatun Nafsy, har yanzu baccin bai ishe ki ba? Ko dumin jikin nawa ne ya miki daÉ—i kike son ki hana ni fita neman abinci?"

Fatima ta yi murmushi, ta ƙara tura kanta cikin ƙirjinsa tana jin ƙamshin fatarsa. "Mijina, sunan nan yana sanya ni jin wani iri a raina. Ka bar ni in ji dumin nan, domin na san idan ka fita, kewa za ta zama abokiyar zamana."

A tare Suka tashi cikin tsantsar nishaɗi. Bayan sun fito daga wanka, Abdulmajeed ya tsaya yana kallon yadda Fatima take ƙoƙarin jawo masa had'edden Jallabiyarsa ta alfarma. Ya matso ta bayanta, ya sa hannunsa ya zagayo da su ta kunkuminta, ya ɗora habarsa a kafaɗarta, yana da'n goga mata gemun sa dake da d'an damshin ruwan wankan.

"Bari in taya ki, Humairatun Nafsy," ya faɗa yana sumbatar wuyanta a hankali. Shi ya zura rigar, sannan ita kuma ta tsaya tana gyara masa maɓallan wuyan rigar. Jallabiyar ta zauna a jikinsa tamkar an halicce ta dominsa ne, kwarjininsa ya ninka na kowace rana, haka ta kammala shirya shi tsaff, bayan sunyi break fast ne.

Fatima ta ɗauko wani daddaɗan turaren "Oud" ta fesa masa. Kafin ya fita, Abdulmajeed ya kamo fuskar Fatima da hannayensa biyu, ya kalle ta cikin ƙwayar idon da yake narkar da ita.

"Zan tafi gaida su Abba , amma ki sani, ko taku É—aya na yi daga gidan nan, ruhina yana tare da ke. Ki kasance cikin addu'a, Humairatun Nafsy. Ke ce sanyin idaniyata, kuma ke ce cikar farin cikina."

Ya sumbaci goshinta cikin wani irin salo mai cike da daraja, sannan ya juya ya fice daga ɗakin yana mata wani kallo na ban-kwana. Fatima ta tsaya turus a tsakar ɗakin, tana jin tamkar numfashinta ya bi shi. Ta koma kan gado ta faɗa, ta jawo matashin da ya kwanta a kai, ta shaki ƙamshin turaren da ya bari, tana maimaita sunan "Humairatun Nafsy" a ranta cikin tsantsar farin ciki.


#HumairatunNafsy #SoulConnection #UstazLoveLanguage #MorningRomance #PureIntimacy #IslamicMarriage #JallabiyyaVibes #SoDaHawaye

Ustaz Abdulmajeed ya faka motarsa a cikin katafaren gidan iyayensa dake unguwar GRA, Dan unguwar tasun d'aya ce, sai dai akoi d'an rata a tsakanin su. Isar sa keda wuya, ma'aikatan gidan suka fara kwasan , gaisuwa, yana amsawa cikin nutsuwa da takunsa na kasaita. Ya shiga babban falon gidan inda ya iske mahaifinsa, Alhaji Ibrahim, yana duba wasu takardu, yayin da mahaifiyarsa, Hajia Amina, take zaune tana kallon labarai.

"Barka da asuba, Abba. Barka da asuba, Ammyy," ya fada yana sunkuyawa har kasa don gaishe su, cike da ladabi.

"Barka dai, Abdulmajeed!" Hajia Amina ta fada fuskarta dauke da fara'a. "Wannan ado haka kaman yau aka daura auren? Gaskiya jallabiyar nan ta yi maka kyau baba na."

Alhaji Ibrahim ya gyara tabarau dake idonsa, shima yana murmushi. "Sannu da zuwa, Ustaz. Ya Yâr tamu Fatima? Fatan tana nan lafiya?"

Abdulmajeed ya dan sosa keya, ya basar da maganar cikin wani irin miskilanci da nuna kamala, kaman ba shi ne ya gama rarrashin "Humairatun Nafsy" a dakin baccinsu ba. "Tana nan lafiya, tana gaishe ku," ya amsa a takaice, yana danyi kaman baya son maganar ta tsawaita don kunyar iyayensa.

Bayan sun dan tattauna, Alhaji Ibrahim ya gyara zama, fuskarsa ta koma ta maganar kasuwanci. "Abdulmajeed, na dade ina son mu tattauna. Kasuwancinmu na shigo da kaya daga waje yana bukatar mutum mai gaskiya da ilimi kaman ka. Ina so ka fara sanya idanu akan wasu rassa na kamfaninmu dake nan kusa."

Abdulmajeed ya jinjina kai, amma sai ya kara gyara murya yace, "Zan duba hakan, Abba. Amma kuma akwai wasu masallatai guda biyu da suka nemi in fara musu karatun Tafsir da sharhin hadisai. Ina so in ba da lokacina wajen hidimar addini shima, Dan haka ina Dan buƙatar lokaci."

Jin haka, Hajia Amina ta fara saka masa albarka. "Masha Allah! Allah ya maka albarka Abdulmajeed. Wannan shi ne babban rabo. Allah ya baka ikon sauke nauyin dake kanka, na duniya da na lahira." Alhaji Ibrahim ma ya biya da "Amin", suna kallon dansu cikin alfahari, ganin yadda ya hada ilimin zamani, na addini, da kuma mutunci.

#ParentalBlessings #UstazMiskilanci #FamilyValues #BusinessAndDeen #HajiaAmina #AlhajiIbrahim #NobleHeritage #SoDaHawaye

Bayan Abdulmajeed ya fito daga gidan iyayensa, yana shirin shiga motarsa, sai ya ji wani irin nauyi a ƙirjinsa. Kewar Humairatun Nafsy ta riga ta mamaye shi. Bai jira ko daƙiƙa guda ba, ya danna kiran wayarta.

A ɗayan ɓangaren kuma, Fatima tana kwance a kan gadon da suka tashi, tana shakar ƙamshin turaren mijinta da ya rage a jikin matashin kai. Ganin kiran sa ya sanya zuciyarta tsalle.

Ta É—aga wayar, muryarta na rawa tace. "Mijina..."

Abdulmajeed ya lumshe idanunsa, ya jingina kansa da jikin kujerar motar, muryarsa ta fito can ƙasa, cikin wani irin salo na mai cike da shauƙi yace.

"Humairatun Nafsy," ya kira sunanta cikin wani irin Nishad'i. "Kin san wani abu kuwa? Bai jira amsarta ba ya Dora da Cewa, Ko da taku É—aya na yi daga gidan nan, nakan ji kamar na bar rabin numfashina a hannunki. Ina nan zaune a gaban mota, amma idanuna ba komai suke gani ba sai murmushinki na safiyar nan."

Fatima ta rufe fuskarta da É—ayan hannun, tamkar yana gabanta. "Ashe har haka ne mijina? Ni ma kewa ta riga ta fara dukan zuciyata tun lokacin da gangar jikin ka tabar gidan nan."

Abdulmajeed ya yi ajiyar zuciya mai sauti ta yadda za ta ji. "Karki sani a damuwa, amma ina jina tamkar tsuntsun da aka ƙwace wa fukafukinsa. Ina son kalaman nan na Larabci da nake faɗa miki, domin su ne kaɗai suke iya kwatanta irin matsayinki a raina. 'Anti hayati, wa anti kullu shay'in li' (Ke ce rayuwata, kuma ke ce komai a gare ni)'. Ina son in kasance kusa da ke, in ji dumin jikinki da ƙamshin dake sanya ni mantawa da dukkan matsalolin duniya."

A hankali Muryarsa take fita tana nuna tsantsar son da yake mata, wanda ya wuce gaban sha'awa kawai, soyayya ce mai cike da mutunci da daraja. "Ina son ki kasance cikin shiri, domin ina jin yau ma daren namu ne. Bazan daÉ—e ba zan dawo gare ki, tawan."

Fatima ta ji wani dad'i ya ratsa ta, radadin ciwon da take ji ya bi iska ya gushe. "Zan kasance cikin jiranka, sanyin idaniyata. Allah ya dawo min da kai lafiya."

Abdulmajeed ya kashe wayar yana murmushi, ya tada motarsa da wani irin ƙwarin gwiwa, ya nufi hanyar companies din su da Abba ya masa magana akan su.

#PhoneRomance #HumairatunNafsy #UstazConnection #SoulTalk #LoveAndLustre #IslamicRomance #HeartToHeart #SoDaHawaye

Washegari, Nazir ya tashi da wani irin bugun zuciya. Ganin "Alert" É—in miliyan biyar a wayarsa ya sa ya kasa samun natsuwa. Ya bi kwatancen da Hajia Zeenat ta ba shi na katafaren gidanta dake unguwar Federal Low Cost.

Yana isa kofar gidan, ya tsaya turus yana kallon ginin. Gida ne mai bene guda uku, wanda aka ƙawata shi da zallar siminti da fentin da yake sheƙi kaman madubi. Nan take ya tuna gidan su Huda , sai ya ji wani nauyi a ransa, amma ƙyallin arzikin dake gabansa ya shafe dukkan wani tunanin dake cikin ransa.

Yana danna ƙararrawa (doorbell), mai gadi ya buɗe masa tare da gaisuwa ta musamman, dan yasan da zuwan shi ya nuna masa hanyar shiga babban falon gidan. Nazir ya taka kafarsa a kan kafet ɗin da ya nitsar da takalmansa saboda laushi. Falon ya sha kayan alatu; kujeru ne na alfarma waɗanda aka kawo su daga ƙasar waje, sanyin AC ya mamaye ko'ina, ƙamshin turaren wuta na "Arabian Oud" yana tashi.

Cikin ɗan lokaci, Hajia Zeenat ta sauko daga bene. Ta sha kwalliya ta musamman; sanye take da wata doguwar riga ta siliki (silk) wadda ta bi jikinta, fuskarta tana sheƙi da fara'a.

"Maraba da babban baƙo, Nazir," ta faɗa cikin murya mai cike da kissa yayin da take takowa zuwa gare shi. "Na zata tsoro zai hana ka zuwa gidana, amma na ga ka zama jarumi."

Nazir ya kasa magana, sai dai kawai ya tsaya yana kallon yadda gidan yake da kuma yadda ita kanta ta sauya masa a ido. Ta nuna masa wurin zama, nan take aka kawo masa tire cike da kayan marmari da abubuwan sha masu tsada waɗanda bai taɓa gani ba.

"Hajiya, gaskiya gidan nan ya haɗu," Nazir ya faɗa yana sosa ƙeya, duk ya daburce saboda baƙon yanayi.

Hajia Zeenat ta matso kusa da shi, ta zauna a hannun kujerar da yake kai, ta yadda ƙamshin turarenta ya cika masa hanci. "Duk wannan na ka ne Nazir, idan har za ka iya zama yadda nake so. Miliyan biyar ɗin nan farkon wasa ne. Akwai ƙarin miliyoyi da gidaje idan har za ka biya min buƙatata ta yau."

Ta sanya hannunta ta shafa kafaÉ—arsa, tana yi masa wani kallo wanda ya sanya Nazir jin cewa ya riga ya sayar da ransa.


#TheGoldenTrap #FederalLowCost #HajiaZeenatSeduction #NazirInDilemma #MoneyAndLust #TheBetrayal #ModernLoveScandal #SoDaHawaye


Nazir ya tsinci kansa a cikin wani irin yanayi dake tsakanin tsoro da sha’awa. Hajia Zeenat ta sa aka jera masa abinci na alfarma a kan teburin dake falon. Tana zaune kusa da shi, tana zuba masa kallo mai cike da ma’ana.

"Nazir, ka ci abinci mana," ta faɗa cikin muryar raɗa. "Ina son ka samu ƙarfi, domin daren nan akwai hira mai tsawo da nake son yi da kai game da makomarka."

Nazir ya fara cin abincin, amma duk lomar da ya kai baki, sai ya ji kamar ƙayar kifi tana soka masa makogwaro. Yana cikin wannan halin, wayarsa ta fara ruri a kan teburin. Sunan "Huda Tawa" ya bayyana sarai a saman screen d'in.

Hajia Zeenat ta kalli wayar, sannan ta kalli Nazir. Ta yi murmushin kissa, ta sa hannu ta É—auki wayar kafin ya kai hannu. "Wace ce wannan take son katse mana jin daÉ—inmu?" Ta danna "Reject", sannan ta kashe wayar baki É—aya. "Yau babu wata Huda, yau ni ce kawai taka."

Nazir ya sunkuyar da kai, ya kasa cewa uffan. Miliyan biyar ɗin dake asusunsa sun zama tamkar sarƙar da ta daure masa harshe.


A daidai wannan lokacin, Huda tana asibiti, yau night duty take da shi, ta kira Nazir ta ji "Busy", sannan ta sake kira ta ji a kashe. Gabanta ya faÉ—i, ta rasa dalilin da zai sa ya kashe mata waya a daidai wannan Lokacin. Cikin sanyin jiki, ta cigaba da trying number amma akashe ake fad'a mata.


A bangaren Nazir kuma, bayan Hajia Zeenat ta kashe wayar Nazir, ta matso daf da shi, ta sanya hannunta a kumatunsa. "Nazir, ka daina tunanin wata can. Ni ce zan gina ka. Ni ce zan mayar da kai mutumin da kowa zai dinga sha'awar sa. Amma sharadi guda ne: Za ka daina karɓar kiran kowa idan muna tare, kuma za ka kasance nawa ni kaɗai a daren nan."

Nazir ya kalli tarin dukiya, ya kalli kyawun Hajia Zeenat, ya kuma tuna cewa idan ya bijire, miliyan biyar É—in nan zasu iya zama ajalinsa. Ya lumshe idon sa yana Mai kok'arin yanke hukunci a cikin zuciyar sa.


#LoveVsLust #TheBetrayal #NazirsChoice #HajiaZeenatsGame #HudasHeartbreak #DoubleLife #SoDaHawaye


"Tirkashi! Shin Nazir zai iya sadaukar da Soyayyar Huda da kuma mutuncinsa saboda miliyan biyar da dadin duniyar Hajia Zeenat? Me zai faru idan Huda ta gano cewa a lokacin da take kiran wayarsa yana rungume da wata matar?



Wacece Hajia Zeenat a zahiri? Shin kudin ta na gaskiya ne ko kuwa akwai wata manufa ta