Chapter 3
*⚖️TUHUMA!.*⚖️
🥰*MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️*
*PAGE3️⃣*
Miƙa masa bandir ɗin kuɗin da ta ɗauko ta yi, ya amsa fuskar shi ɗauke da farin ciki yace "Mamy Nagode sosai Allah ƙara lafiya da nisan kwana."
Ita ma tana murmushi tace "Amen ɗan gidan Mamy."
Tashi ya yi yace "Mamy zan koma."
Kallon shi ta tsaya tana yi kamar mai tunanin wani abu, sai kuma ta riƙe hannun sa tace "Mu je na raka ka motar."
Tun da suka fita ta hango yadda ya yi parking ɗin motar, ta fara masa nasiha akan me yasa ba zai daina hakan ba, ya daina ganganci da rayuwar shi.
Murmushi ya yi kawai yana jin ƙaunar Mamyn har cikin ran shi, Allah ya sani duk duniya bayan Momcyn sa ba ya jin akwai wata halitta da ya ke darajawa bayan ita.
Yana ƙoƙarin buɗe motar ya shiga kenan, suka ji Muryar Hamida a bayan su.
A guje ta Ƙaraso tana haki tace "Ya Sa'id Hajiya kaka na kiran ka."
Hannu yasa ya dafe kan shi yace "Kashh." Ya ɗago ya watsawa Hamida harara yace "Ya akai ta san na zo gidan nan?, ki koma ki ce mata ba ki ganin ba.
Da sauri Hamida ta ja baya tana ɗaga hannu tace "Wallahi ba ni bace na faɗa mata, ina shiga ta ce ba je na kira ka."
Mamy ce tace "Kai da baka shiga ka gaida Hajiya Kakar ba, ka ke ƙoƙarin tafiya?."
Ɓata fuska ya yi ya kalli Hamida da ta tsaya tana kallon shi, cikin tsawa yace "Ɓace min a nan ki je ki ce na tafi."
Jiki na rawa Hamida ta juya, tana takaicin aiken da Hajiya kaka ta mata wajen shi, ita da take addu'ar ya tafi ya bar gidan, ita kuma wannan jarababbiyar tsohuwar ta wani ce a kira shi.
"Kin ga Hamida ki ce mata gashi nan zuwa."
Mamy ta faɗi hakan daidai lokacin da Hamida ta juya za ta tafi.
"Haba Mamy ya za ki ce mata haka? Ke ma fa kin san halin tsohuwar na..."
Bata bari ya ƙarasa maganar ba, ta ɗaga masa hannu tace "Ka wuce ka je ka gaida ta kawai, bana son ka ƙara magana."
Yana wani ciccijewa shi a lallai an masa dole ne, ya banka murfin motar da ƙarfi, ya juya ya nufi babban ginin nan da ke ƙarshe Mamy na biye da shi a bayan sa.
Daga cikin farlon Hajiya Habiba ce tsaye jikin window, tana ganin duk abinda ke faruwa tun daga shigar Sa'id sashin Hajiya Bilkisu, har zuwan Hamida da wuce sashin ta da suka yi tare.
Wani irin abu ne ya caki zuciyar ta, ganin yadda Hajiya Bilkisu ke neman ƙwace mata ɗa ido da ido, in ba munafurci ba me ye haɗin ta da Sa'id, ta yi jarabar ta yi faɗan duk da ta raba Sa'id da Hajiya Bilkisu abin ya ci tura, tun yana ƙarami Allah ya haɗa jinin sa da Hajiya Bilkisu, ta rasa ya zata raba wannan alaƙar ta su, dan abin ya fara bata tsoro ganin yanzu Sa'id ya daina damuwa da fushin ta.
Dafa tan da ta ji anyi ne, yasa ya juyo a firgice.
Ganin wadda ke tsaye yasa ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya tace "Har kin bani tsoro wallahi."
Babbar mace ce mai jiki tsaye, shekarun ta za su iya haura na Hajiya Habiba kaɗan, dan fuskar ta tafi ta Hajiya Habiba tsufa, sanye take cikin wani dandatsetsen leshi na alfarma.
Kallon Hajiya Habiba ta yi tare da barin wajen ta nufi ɗaya daga cikin kujerun farlon ta zauna tana faɗin "Ai dole na ba ki tsoro, tunda kin ɗorawa kan ki wahala, haka kawai a banza kin kasa maganin abinda ki na da iko a kan shi."
Ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsaki.
Dawowa Hajiya Habiba ta yi kusa da ita, ta zauna a kujerar dake gefen ta tare da zabga tagumi, fuskarta ɗauke da damuwa tace "Ya zan yi da Sa'id Hajiya larai, na yi na yi na raba shi da Hajiya Bilkisu abin ya ci tura, wallahi a kullum na gansu tare ba ki ji yadda nake jin zuciya ta ba."
Taɓe baki Hajiya larai ta yi tace "Na faɗa mi ki tun wuri ko ɗauki mataki kin ƙi, kina ganin maganar fatar ba ki zata sa Sa'id ya yi abinda ki ke so ne?."
Girgiza kai Hajiya Habiba ta yi tace "Na faɗa mi ki ba zan iya kauce hanya ba wajen karkato da hankalin yaron nan kaina, bana son na sa Malamai a cikin harkar nan ko kaɗan."
"Ai kuwa ba ki shirya ba, ai muddin kina son Sa'id ya ji maganar ki, sai kin sa an musu farraƙu da Bilkisu, yadda zai tattara hankalin sa a kan ki ta yadda sai ya fiku tsanar ta.
Cewar Hajiya Larai kenan cikin faɗa.
Dafa kafaɗar ta Hajiya Habiba ta yi tace "Ai akan na aikata hakan, gwara na masa barazana zan tsine masa, na san dole ya bi magana ta."
Dariya Hajiya Larai ta fashe da ita tace "Aikuwa kina da aiki a gaban ki." Ta tashi tsaye ta cigaba da magana "Ke kan ki kin san Sa'id ba ya shakkar ki yanzu, wata barazanar tsinuwar ki babu abinda za ta masa."
Cike da baƙin ciki Hajiya Habiba ke faɗin 'Wallahi wallahi na tsani Bilki da ƴaƴan ta Larai, bana ƙaunar Bilkisu har zuciyata."
Wani kallo Hajiya Larai ta ke bin Hajiya Habiba da shi, sai da ta bari ta gama magana tace "Duk irin tsanar da ki ka wa Bilkisu a bayana ki ke Habiba, Ni nan zan faɗa mi ki in har za'a bani dama na kashe wani a duniyar nan, to wallahi Bilkisu da ƴaƴanta sune farko, amma na san yadda nake bi da salon da nake tafiyar da ita, shi yasa Ni ƙiyayyar da nake mata bata fito fili ba, amma a ƙasa ni nasan tuggun da nake shuka mata, ina daf da cika burina na wargaza rayuwar ta da ta ƴan iskan yaran ta."
Hajiya Habiba na ƙoƙarin magana, suka ji sallamar Salama ta shigo farlon, hakan yasa dole suka yi shiru suka shiga wata maganar.
*Hajiya Larai kenan, ita ma tana ɗaya daga cikin matan gidan, mijinta wa ne a wajen mijin Hajiya Habiba.*
A bakin ƙofar shiga sashin Hajiya Mamy ta kalli Sa'id tace "A haka za ka shiga wajen Hajiyar da zamammrmen wando." Ta kai ƙarshen maganar tare da nuna jikin shi da hannun ta.
Kallon jikin shi ya yi ya ɓata rai yace "Mamy ba abinda kayan suka yi fa."
"Ko ba komai ka ja wandon sama, ka riga da kasan halin Hajiya Kaka."
Babu musu ya ja wandon suka shiga farlon. Ya subhanallahi aljannar duniya kenan, wani irin ƙaton farlo ne wanda aka ƙawata da wasu luntsuma-luntsuman kujeru na alfarma, tun daga farkon shiga farlon an malala wani lallausan carpet mai shegen kyau.
Bedroom ne a farko in ka shigo, daga gefen shi akwai wata matattakala wadda zata kai ka sama, sai wasu ƙofofi guda biyu da alama ɗayan kitchen ne, ɗayan kuma wani bedroom ɗin ne daban.
Wani irin sanyin AC da ya gauraya da sassanya ƙamshin turare ne kawai ke tashi, sai wasu irin jibga-jibgan tuntu irin na sarautar nan da aka ajiye a tsakiyar farlon, wata kyakykyawar dattijuwa ce fara mai zubi da Fulani, kishingiɗe a tsakiyar farlon, ta ɗora hannun ta ɗaya a kan tuntun, idanun ta akan ƙatuwar tvin bangon da ta cinye rabin bangon, tana kallon wani shiri na addini a Sunnah TV .
Daga wajen ƙafar ta kuma wata mace ce zaune, a ƙalla zata kai shekara arba'in da biyar, ta ɗora ƙafar tsohuwar a cinyar ta tana yanke mata farce.
Sallama suka ji, hakan yasa matar dake yanke mata farcen Ɗagowa ta amsa sallamar.
Ita kam ba tare da ta juyo ta ga waɗan da suka shigo ba, ta amsa ƙasa ƙasa ta cigaba da kallon da take.
Takowa Sa'id ya cigaba da yi ciki, a ranshi yana takaicin halin kakar tashi, kai tsaye ya nufi kujerar dake setin inda take kalla ya zauna.
Yana kallon Mamy na hararar shi ya share, ya yi kamar bai gani ba dan yasan abinda take nufi.
Ita kam Mamy wucewa ta yi ta tsugunna daga gefen Hajiyar, cikin ladabi tace "Hajiya Barka da hutawa."
Cikin isa da ƙasaita tsohuwar ta ɗago ta kalli Mamy, ba tare da ta yi magana ba ta ɗaga mata hannu haɗi da jinjina kanta.
"Kai ishashshe ban isa ka gaishe ni ne ba, ka zo ka sani a gaba kana faman hura hanci."
Ta faɗi hakan tana kallon Sa'id.
Kauda kan shi ya yi ba tare da ya ce komai ba, ya ƙi ko kallon Mamy dan ba ya son ta sa shi ya yi abin da bai yi niya ba.
Ya yin da shirun na shi ya ɓata ran Hajiya kaka, kallon ta ta maida kan Hajiya Bilkisu cikin nuna fushin ta tace "Bilkisu yanzu dai ta tabbata maganar ki kaɗai Sa'id ya ke ji a gidan nan? Kina zaune ina masa magana ya maida ni ƴar iska ko?."
Ƙasa da kai Mamy ta yi cikin girmamawa tace "Ki yi haƙuri Hajiya kaka, ina iya bakin ƙoƙarina dan ganin na dawo da shi kan hanya, a yi masa afuwa dan Allah."
Taɓe baki Hajiya kaka ta yi tace "Ai mun godewa Allah da yasa kina iya tsawatar masa ya ji, duk gidan nan wa ye ya isa ya yi hakan in ba ke ba bilki, ke dai Allah ya saka Miki da alkhairi da ba ki biye mugun halin uwar shi ba."
Wani kallo Sa'id ya watsa mata jin ta kira Momcy da mai mugun hali, a rayuwar shi baya ƙaunar ya ji an aibata Momcyn shi, duk da shi kan shi yasan bata da halin Ƙwarai.
Amma Hausawa su ka ce, uwa uwa ce ko ya ya take.
Ganin yadda ya ke wani cika yana batsewa yasa Hajiya kaka tashi zaune, ta ɗauke ƙafar ta daga cinyar mai yanke mata farcen, kallon Sa'id take tare da ƙanƙance idanun ta dake cike da masifa tace "Ni ka ke wa kumbure-kumbure Sa'idu? To ka tashi ka fice min a farlo tunda ba ubanka Hadi ya gina min ba, wannan ɗin gumin Abubakar assadiƙu ne."
Kamar wanda akawa allura haka Sa'id ya tashi a kujerar, ya kalli Mamyn shi murya a cushe yace "Mamy na tafi."
"Allah ya tsare Sa'id, kar ka daɗe fa ka tuna da alƙawari."
Waje ya nufa ba tare da yace komai ba, yana jin haushi kakar tashi da kullum ya zo gidan sai ta zage shi da mahaifiyar shi.
"Dan jakar uba, da wani kan shi kamar tukubar tsire an wani tattare gashi a tsakiyar ka." Ta juya ta kalli Mamy tace "Ya Miki alƙawarin zai dawo kenan?."
Murmushi Mamy ta yi tace "Eh Hajiya in sha Allahu zai dawo yanzu."
Jinjina kai Hajiya Kaka ta yi tana yatsina fuska tace "Ah lallai zai dawo ai, tunda ke kika ce ai na san zai dawo."
Ita dai Mamy murmushi kawai take yi, ganin ya tafi yasa tace "To Hajiya zan koma ina son duba wasu takardu."
Sai lokacin Hajiya ta saki fuskar ta, kamar ba ita ce ta yi fushi ba tace "In kin koma ki cewa Kubra ta damo min kunun nan mai daɗi."
Da "To." Hajiya Bilkisu ta amsa, ta miƙe ta nufi hanyar fita."
Hajiya Kaka ta ɗaga murya tace "Ki ce ina jiran ta fa."
Da "To." Hajiya Bilkisu ta amsa, tana tunanin halin rikici irin na Hajiya Kaka, ba'a gane gaban ta bare bayan ta, a kowanne lokaci ta so rikincin ta yi take, duk cikin jikokin ta tafi son ƴaƴan Hajiya Bilkisu, dan tana cewa sun fi sauran tarbiyya da nutsuwa.
Sai kuma Sa'id da take wa wani irin so, wanda ya samo asali ne tun yana yaron shi, ta kan ce babu abinda ya baro na tsohon mijin ta, gashi kuma dama sunan mijin nata yaci, hakan yasa take jan shi a jiki take nuna masa so, kafin ya zama abinda ya zama suka fara faɗa tsakanin su.
Amma duk da haka in bata gan shi ba, bata jin daɗi ta dinga tambaya ya zo ko bai zo ba kenan.
*HAFSAT.*
Tun ranar da su ka samu saɓani da Anwar, take cikin tsananin damuwa ta rasa wa za ta faɗawa, ga shi ya toshe duk wata hanya da yasan za ta sa me shi.
Makarantar da take haɗu su yanzu ma ya fi ƙarfin sati ɗaya bai je ba, garejin da ya ke aiki kam ta je yafi a ƙirga amma kullum sai ace mata bai zo ba.
Tun tana ɗaukar abin wasa har hakan ya fara ɗaga mata hankali, ta yi dana sani yafi a ƙirga, da ace ta san haka za ta kasance da ba ta yi gigin bayyana masa gaskiyar ita wace ce ba, da ta barshi sun cigaba da tafiya a matsayin da ya ɗauke ta.
Sai gashi ta yi kuskuren da ba zata taɓa iya goge shi ba, ta rasa duk wata kulawa tattali da ƙauna daga Anwar.
Maganar da Anwar ya fara faɗa mata a ranar da ta sanar da shi iya wace ce ta faɗo mata, "Hafsat matsayin ki da nawa ba ɗaya bane, kin fi ƙarfina ke ɗin tamkar haramtacciya ce a gare ni, babu ta inda auren mu zai yiwu ki manta kin san wani mai suna Anwar a rayuwar ki."
Ta rasa me yasa waɗan nan maganganun ke mata yawo a tsakiyar kanta, ta kasa manta su ta kasa goge su a ƙwaƙwalwar ta.
Tambayoyin da ta ke yiwa kan ta a koda yaushe su ne.
*Me ne ne alaƙar soyayyar su da sunan mahaifi ta ?*
*Me yasa Anwar ya iya rufe idon shi yace su rabu?.*
*Shin ya manta soyayyar da ya ke mata ne?.*
*Me yasa yace sun haramta ga kuma?.*
*Ta ya za ta gane gaskiya bayan bai bata damar hakan ba?.*
Tana da tarin tambayoyi a ranta, waɗan da take buƙatar mai amsa mata su, amma wa zata tunkara?.
Kai tsaye zuciyar ta bata shawara akan ta yi bincike da kanta, amma ta ya za ta iya bincike bayan babu hanyar hakan.
Tana kwance a kan luntsumemen gadon ta, ta ke wannan tunanin.
Kamar wadda aka mintsina ta zabura ta tashi ta nufi ƙofa, sai da ta tabbatar da ta kulle ƙofar yadda za'a zaci tana ciki, sannan ta nufo farlo, ko da ta fito ta tarda farlon babu kowa shiru.
Lallaɓawa ta yi ta buɗe ƙofar baya, tana tafiya tana waigen bayan ta kamar mai tsoron wani ya ganta.
Kai tsaye ta nufi sashin ma'aikatan gidan(BQ.) Zuciyar ta cike da yaƙinin za ta samu wani abu daga Baba Salame.
Tsohuwar ƴar aikin gidan su.
Da sallama ta shiga ɗan ƙaramin farlon, wanda ke ɗauke da ƙananan kujeru irin na da, sai wata tabarma dake gefe a shimfiɗe.
Daga cikin uwar ɗaka Baba Salame ta amsa sallamar tata.
Tana faɗin "uwar masu gida ke ce tafe?."
Zama Hafsat ta yi akan ɗaya daga cikin kujerun dake farlon, idanun ta akan ƙofar ɗakin Baba Salame
Tace "Ni ce Baba."
Fitowa Baba Salame ta yi hannun ta ɗauke da allura da zare, da alamar tana ɗinkin wani abu ne, tana ganin Hafsat fuskarta ta cika da fara'a tace "Uwar masu gida maraba lale da zuwa, Gashi kuma na aiki Batula yanzu za ta dawo."
Murmushi Hafsat ta yi tace "A'a Baba Ni yau ba wajen Batula na zo ba, wajen ki na zo mu yi hira.
Kama haɓa Baba Salame ta yi tace "To ni na isa uwar masu gida, ai da kin ce na zo da kaina ma da na zo."
Girgiza kai Hafsat ta yi tace "Ni ya kamata na zo Baba, tunda Ni ke da buƙata wajen ki."
Zama Baba Salame ta yi tana faɗin "To Allah yasa dai lafiya ba wani abu ne ya faru ba."
Sai da Hafsat ta kalli bakin ƙofar shigowa, kamar mai tsoron wani ya ji su ta juyo ta kalli Baba Salame tace "Baba dan Allah so nake ki faɗa min, me ne alaƙar dake tsakanin gidan nan da mutanen dake ƙaramin ginin dake kusa damu?."
Da sauri Baba Salame ta miƙe tare da dafe ƙirjin ta, ta zaro ido tana waigen bayan ta tace "Me ya sa ki ka min wannan tambayar?. "
Dafa hannun kujerar Hafsat ta yi, tana nazarin yanayin da Baba Salame ta shiga ba tare da damuwa ba tace "Ka wai ina son sani ne, dan naga duk faɗin unguwar nan gidan su ya fita daban, sannan tunda na taso ban taɓa ganin matar gidan ba, sannan na fuskanci Dady ba ya ƙaunar mutanen ko kaɗan, ina sha'awar sanin tarihin su tunda kin daɗe a gidan nan, na san kin san wani abu dole."
Wani kallon baki da hankali Baba Salame take bin Hafsat da shi, ta shiga gyara ɗaurin zanin jikin ta fuska a haɗe tace "Ban san komai ba Hafsat, dan girman Allah kar ki ƙara zuwa nan da sunan yi min wannan tambayar, in dai ba so ki ke ki jefa rayuwata cikin haɗari ba."
Yanayin yadda Baba Salame ta nuna tsoran ta a fili, abin ya bawa Hafsat mamaki sosai, ta kuma ƙara dasa zargin tabbas akwai wani abu da ya ke tafiya ba daidai ba, sannan dole akwai wani sirri wanda ake ɓoyewa ba'a son ta sani.
Ganin Baba Salame na ƙoƙarin shigewa ɗaki, hakan yasa ta kira sunan ta "Baba Salame." Hakan ne yasa ta tsaya ba tare da ta juyo ba.
Miƙewa Hafsat ta yi tsaye, ta Ƙarasa kusa da ita fuskarta cike da damuwa tace "Tabbas na san kin san wani abu, amma kina ƙoƙarin ɓoye min saboda wani dalili, ki taimaka ki sanar min dan Allah."
Juyowa Baba Salame ta yi fuskarta a haɗe, kamar ba Baba Salame mai wasa da dariya ba tace "Hafsat ki daina neman tono sirrin dake ɓoye, ki tsaya a matsayin da ki ke kar ki jawo mana abinda ba za mu iya ɗauka ba daga ni har ke."
Hafsat na ƙoƙarin magana, sai ga Batula ta shigo, Jikar Baba Salame ce, a ƙalla za su iya yin sa'anni da Hafsat.
Sanye take da hijabi har ƙasa, fuskarta cikin niƙaf, baka iya ganin komai sai idanun ta.
Tana ganin Hafsat ta cire niƙaf ɗin fuskarta, Masha Allah kyakykwa ce ta gaske irin kyannan mai ɗaukar hankali, tana murmushi ta ke kallon su ganin su a tsaitsaye tace "Baba ya na ga kin wani coke a tsaye, kamar wadda ke shirin yin dambe?."
Dariyar yaƙe Baba ta yi ta kalli Hafsat tace "Babu komai." Tare da miƙawa Batula hannu tace "Ina aiken da na miki?."
Ƙullin leda Batula ta fito da shi daga hijabin ta, ta miƙawa Baba tana faɗin "Tace a gaishe ki, wai yaushe za ki zo?."
Amsa Baba Salame ta yi tace "Sai ranar da bana aiki in sha Allahu."
Ganin Hafsat bata da niyar tafiya, yasa Baba Salame da zuciyarta ke cike da fargaba, ta kalli Batula da ta zauna suna hira da Hafsat tace "Ki taso mu je ki linke min kayan can Batula."
Bisa dole Batula ta miƙe ta bi bayan Baba Salame.
Hafsat ganin sun barta ita kaɗai, hakan yasa ta tashi ta fita zuciyarta cike da saƙe-saƙe, ita kaɗai ta ke faɗin "Ya zama dole na binciko koma me ne ne."
Kamar yadda ta fito ta ƙofar baya, haka ta koma sashin su cikin sanɗa ta nufi ɗakin ta.
Tana daf da shiga ɗakin ta ne ta tsinkayi Muryar Mom ɗin ta
"Hafsat daga ina ki ke?."
A ɗan firgice ta juyo yanayin ta ya yi nuni da alamun rashin gaskiya tace "Am dama dama na ɗan zagaya baya ne shan iska."
Kamar Mom ɗin za ta ce wani abu, sai ta gyaɗa kai tace "Dama Dadyn ki ne ya bugo waya yace yana ta kiran ki baki ɗauka ba, suna hanya shi da Barister Auwal da iyalan sa.
Ya kamata ace kin je kin shirya kafin su iso."
Tana gama faɗar hakan ta wuce kitchen, ita kuma Hafsat ta shige ɗakin ta zuciyar ta na wani irin bugawa, tun bayan sanar da ita da Mom ɗin ta yi zuwan Barister Auwal.
Ta riga da ta san me zuwan Barister ke nufi, kenan yanzu tana ji tana gani za ta bari Dadyn ta ya haɗa ta aure da wani ba Anwar ba? Anya za ta iya zaman aure da wanda ake shirin haɗa su kuwa? Ya ya yake ya halayen sa ya ke? Duk bata sani ba sai sun iso ta gan shi.
Haka ta wuce toilet ta na wanka zuciyarta cike da saƙe-saƙe kala-kala.
***
🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️