SO DA HAWAYE!

11&12

by @mrsalkali01

***


*Assalamu Alaikum, masoyana.*

*Bayan na kammala posting na "Free Pages" na jiya, na samu korafe korafe, ƙwarai daga wasu masoyana, a kan cewa ya kamata in ƙara wasu shafukan domin jin daɗinku.*

*Saboda darajarku da kuma ƙoƙarin masoyana, na yanke shawarar ƙara muku waɗannaan shafin a matsayin kyauta ta musamman. Ga shi nan don ku more, fatana ku biyo ni har zuwa ƙarshen wannan tafiya.*

*Nagode da soyayyarku!*



💫SO DA HAWAYE 💫 

✍️Mrs Alkali.

*Page 11-12*


Cikin sanyin AC da daddadan ƙamshin turaren wutar da ya cika dakin, Hajia Zeenat ta mike, ta kamo hannun Nazir wanda jikinsa yake ta karkarwa. Ganin zuciyar sa ta shiga tsaka mai wuya yasa Ta jagorance shi zuwa babban dakin kwananta, wanda ya sha ado da fitulun dake bayar da haske mai kaloli daban-daban (dim lights).

Nazir ya tsinci kansa a wata duniya da bai taba mafarki ba. Hajia Zeenat, wadda ta kware a harkar kissa irin ta manyan mata, ta fara jansa da wasu kalaman dake narkar da natsuwar sa. A hankali Ta cire masa dukkan wata fargaba, tana nuna masa cewa shi din "Zaki" ne a idonta.

"Nazir, ka duba kanka a madubi," ta rada masa a kunne yayin da take tsaye a bayansa, hannayenta suna yawo a kirjinsa. "Wannan kyan da kake da shi, bai kamata ya lalace a banza ba. Ni zan koya maka yadda ake rayuwa, zan koya maka yadda ake dandana dadin duniya."

Nan take ta fara sarrafa shi da kwarewarta. Nazir, wanda bai taba sanin mace ba a rayuwarsa, ya ji kansa ya fara juyawa. Natsuwar sa ta fice, hankalinsa ya gushe, ya mance da wata Huda, ya mance da addini, ya mance da dukkan wani kishin kansa. Kissa da salon da Hajia Zeenat ta yi amfani da su sun gigita masa lissafi, ya tsinci kansa yana mika wuya ga kowace bukatar ta.

Daren ya kasance daren "Nisadi" ga Hajia Zeenat, amma ga Nazir, daren batan basira ne. Ta sarrafa shi yadda take so, ta mayar da shi tamkar jariri a hannunta. 

Yayin da Nazir yake cikin wannan yanayin na gigita, a can asibiti Huda tana rungume da hoton sa dake wallpaper n wayarta, tana kuka tana tunanin ko lafiya ya kashe mata waya, tana addu'ar Allah ya karemata shi a duk in da yake.


#TheLossOfInnocence #HajiaZeenatSeduction #NazirInTheDark #MoneyTrap #TheBetrayalOfTrust #FedralLowCostToJekaDaFari#SoDaHawaye


Washe gari Nazir ya buɗe idanunsa, hasken rana dake ratsawa ta cikin labulen ya gauraye da fuskarsa. Nan take abubuwan da suka faru a daren jiya suka fara dawo masa ɗaya bayan ɗaya. Ya kalli kansa, ya kalli gadon, sannan ya kalli Hajia Zeenat dake kwance gefensa tana baccin dad'i. Wani irin nauyi ya danne masa ƙirji; ya san ya tafka babban kuskure, ya san ya ci amanar kansa, ya ci amanar addininsa, kuma ya ci amanar Huda.

A hankali Ya tashi ya zauna a gefen gadon, ya dafe kansa yana jin wata irin nadama tana ratsa shi. “Me na aikata? Me zan gaya wa Allah? Ta yaya zan iya kallon Huda da ido na?” ya tambayi kansa a fili cikin muryar raɗa.

Motsin da ya yi ne ya tada Hajia Zeenat. Ta buɗe idonta, ta ga yadda Nazir yake cikin damuwa. Ta yi murmushin kissa, ta matso ta baya ta ɗora hannunta a kafaɗarsa, ta hura masa iska a kunne.

"Nazir, me yake damunka? Kada ka ce mini har yanzu kana tunanin wannan unguwar taku da ka fito?" Ta faɗa cikin muryar lallashi.

Nazir ya juyo ya kalleta, idanunsa sun yi jawur. "Hajiya, ban kyauta ba. Wannan ba tarbiyya ta bace. Na san na yi kuskure..."

Kafin ya ƙarasa, ta sa yatsanta a leɓensa ta dakatar da shi. "Wannan ba kuskure bane, Nazir. Wannan shi ne asalin 'Wayewa'. Mutanen da kake gani suna taƙama a cikin garin nan, ta nan suka biyo. Karka bari tsoro ya hana ka zama attajiri. Ka duba wayarka; na riga na sa an tura maka ƙarin miliyan biyar na biyu a yanzun nan."

Nazir ya zaro ido, ya duba wayarsa, nan take ya ga sakon banki. Gaba ɗaya miliyan goma ke nan!

"Kuma ba wannan ba," ta ci gaba da jansa, "Idan har ka yarda za mu wuce Abuja gobe, akwai wani katafaren gida da nake son rubuta shi da sunanka. Za ka zama mai gida, Nazir. Za ka daina tsoron kowa. Me GOMBE zai baka banda talauci da wahala?"

Nazir ya duba wayar, ya kalli Hajia Zeenat, sannan ya tuna irin kudaden da yake bukata don biki. 

"Abuja kuma Hajiya?" ya tambaya, muryarsa ta fara sanyi sabida fargaba.

"Kwarai kuwa. Abuja ce asalin inda za ka san kai wane ne. Nazir, ni fa na riga na fara sonka, kuma zan mayar da kai wanda kowa zai yi sha'awar sa."

Haka Hajia Zeenat ta ci gaba da shafa masa fentin duniya, tana kore masa duk wani tunani na rashin kyauta tawa, har Nazir ya mance da nauyin zunubin da ya tafka, ya fara mafarkin zama hamshakin mai kuɗi a Abuja.


Subhanallahi 🥹 Allah kayima tsari da aikata zinah da fad'awa mummunan ƘADDARA.


#GoldCuffs #ThePriceOfSin #AbujaCalling #NazirsDownwardSpiral #HajiaZeenatSeduction #BetrayalOfSoul #WealthVsFaith #SoDaHawaye

Huda tana zaune a dakin hutu na asibitin Specialist Hospital Gombe, kanta a sunkuye, tana tunanin dalilin da ya sa Nazir ya kashe mata waya a daren jiya. Tana cikin wannan fargabar, sai ga kiran sa ya shigo. Ta dauka da sauri, muryarta cike da rawar jiki.

"Nazir! Don Allah me ya faru? Na kira ka jiya ka kashe wayar, daga baya kuma ka kashe ta baki daya. Hankalina ya tashi sosai!"

Nazir ya daure fuska, ya danyi tari na karya don ya nuna cewa yana cikin aiki ko damuwa. "Huda, kiyi hakuri. Jiya na shiga wasu manyan tarurruka ne da mutanen da zasu ba mu wannan kuɗin ginin kongilar. Wajen akwai tsauraran sharud'a, shi yasa aka sa mu kashe wayoyinmu."

"Amma Nazir, har yanzu kana can baka dawo gida ba?" Huda ta tambaya, tana kokarin gano gaskiyar maganar a cikin muryarsa, dan bai saba mata karyaba.

Nazir ya kalli Hajia Zeenat, wadda take masa kallon 'idan ka kuskura ka fadi gaskiya ka koka' da kanka. Ya hadiye miyau, sannan ya cigaba da karyar sa. "Huda, wani sabon al'amari ya taso. Wadannan mutanen sun ce lallai sai na bi su zuwa Abuja a yau. Akwai wasu takardu da zan sanya wa hannu wadanda zasu bamu damar mallakar wani katafaren fili da za a gina mana gidanmu wanda zamu tare bayan bikin mu. Abuja zan wuce yanzu haka, kuma kuɗin da zan dawo da su, ko ke kanki zaki yi mamaki."

Huda ta yi shiru. Abuja? Tazarar dake tsakanin su tana kara tsayi, kuma fargabarta tana kara ruruwa a cikin zuciyar ta. "Nazir, baka ganin kamar abubuwan nan suna faruwa ne da sauri? Kwana kayi a wajen su fa, amma yanzu kace zaka wuce Abuja? Bikinmu fa saura kusan sati uku."

"Huda, karki damu!" Nazir ya fada cikin wayar tafi-da-gidanka, yana kokarin nuna isa. "Ai duka kuɗin ne zasu share mana hawayenmu. Idan na dawo daga Abuja, biki ba zai zama abin damuwa ba. Zan dawo miki da mota, kuma zan dawo miki da kuɗin da ba kowa ne a Gombe yake da su ba. Kiyi min addu'a kawai, zan kiraki duk lokacin da na samu dama."

Nazir ya kashe wayar ba tare da ya jira jin abin da zata kara fad'a ba. Ya sauke ajiyar zuciya, yana jin tamkar ya sauke wani babban dutse, amma a zahiri, ya kara dora wa kansa nauyin karya ne batare da ya sani ba.

Hajia Zeenat ta buga masa tafi, tana murmushin nasara. "Yauwa Nazir! Yanzu ka zama namiji. Abuja tana jiran mu, kuma alkawurana suna nan bazan fasa ba."

A asibiti kuma, Huda ta zauna tana kallon wayar kamar mutum mutumi, hawaye d'aya ya diga akan sikirin d'in wayar. Zuciyarta tana gaya mata akwai wani abu da yake shirin faruwa, amma so da amana sun hana ta yarda da zargin dake ranta kai tsaye.


#AbujaLies #TheBetrayal #NazirsDeception #HudasFear #HajiaZeenatControl #MoneyOverLove #GombeToAbuja #SoDaHawaye

Tun sassafe wata haddadi'yar mota kirar Land Cruiser Prado baka wulƙil, mai dauke da bakaken gilashi (tinted), ta zo kofar gidan Hajia Zeenat dake Federal Low Cost. Nazir ya fito sanye da sabbin kaya na alfarma da ita kanta Hajiya Zeenat ta sa aka siyo masa, ya zama kaman ba shi ba.

Tafiyar tasu ta kasance cikin Nishad'i da kide-kiden da suka gigita tunanin Nazir. Hajia Zeenat tana zaune kusa da shi a bayan motar, tana kishingid'e a jikinsa, tana ba shi labarin irin rayuwar da manyan mutane suke yi a Abuja. Duk lokacin da motar ta danyi wani gudu ko ta shiga wani lungu, Hajiya Zeenat kan kara matse shi a jikin ta, tana rura masa wutar sha'awar da take sa shi mancewa da asalin tafiyar tasa.

Suna isa Abuja, Nazir ya zaro ido. Yana ganin gine-gine masu hawa da yawa, ya ga fitilu da manyan tituna kaman na kasashen ketare. Motar ta nufi unguwar Maitama, daya daga cikin unguwannin da sai wane-da-wane yake rayuwa a cikinsu.

Hajia zeenat Ta kalle shi tana murmushin nasara, "Nazir, wannan ita ce Abuja. Kuma nan ne gidanmu yake."

Sun faka a kofar wani katafaren gida wanda ya ninka na Gombe sau goma. Masu gadi suka bude gate din, motar ta shiga cikin wani faffadan compound da aka kawata shi da korayen ciyawa da furanni masu ƙamshi. Nazir ya kasa magana, kawai kallon gidan yake yi.

"Wannan gidan nawa ne Nazir," Hajia Zeenat ta fada tana rike da hannunsa. "Kuma na riga na gaya maka, idan har ka kasance yadda nake so, zan sanya sunanka a daya daga cikin takardun mallakar gidajen nan. Yanzu dai mu shiga ciki, akwai wani party na musamman da wasu kawayena suka shirya domin murnar dawowa ta, kuma kai ne babban bakonmu."

Nazir ya bi ta kaman rakumi da akala. Zuciyarsa tana gaya masa gaskiya, amma idanunsa sun makance da ganin kuɗin da daular Abuja. A daidai wannan lokacin, Huda tana can Gombe tana ta kiran wayarsa, amma wayar tana hannun Hajia Zeenat, wadda ta riga ta sanya ta a "Silent" ta jefa ta cikin jaka.


#AbujaLuxury #MaitamaLife #TheGoldenCage #NazirInAbuja #HajiaZeenatsPower #BetrayalInStyle #GombeToAbuja #SoDaHawaye

Kimanin ƙarfe goma na dare, gidan Hajia Zeenat dake Maitama ya cika da manyan motoci masu tsada. Kiɗa mai ƙarfi (loud music) ya gauraye ko'ina, yayin da hasken kalar "Purple" da "Blue" ya mamaye falon gidan da aka tanada don taron.

Hajia Zeenat ta fito sanye da wata shiga ta alfarma da ta nuna tsantsar dukiyarta. Nazir kuma, ta sa an shirya shi cikin wata suit ta alfarma wadda ta fito da kyan fuskarsa da tsawonsa. Ya zama tamkar wani "Model" da aka kawo shi daga ƙasashen waje.

A hankali Yake takowa a gefenta, kawayenta, waɗanda yawancinsu manyan mata ne masu kuɗi da class, suka fara tafa masa.

"Wow! Zeenat, wannan daga ina kika samo shi? Gaskiya wannan ya haɗu," in ji wata ƙawar Hajiya Zeenat mai suna Hajia Baby, tana bin Nazir da wani shu'umin kallo na sha'awa.

Hajia Zeenat ta yi murmushin nasara, ta ƙara ƙanƙame hannun Nazir. "Wannan ai nawa ne ni kaɗai. Daga Gombe na taho muku da shi, na gaya muku ai sai na nemo abin da zai gigita Abuja."

An fara party inda aka riƙa fito da abubuwan sha (drinks) masu tsada da abinci kalar daban-daban. Nazir ya tsinci kansa a tsakiyar mata waɗanda suke ta faman yaba kyan sa, suna taɓa shi cikin salon kissa. Ya rasa inda zai sa kansa; kunya da tsoro su ka fara gushewa a ransa, shauƙin waɗannan kalaman nasu ya fara ratsa shi.

Wata waƙa mai sanyi ta ke tashi, nan take kawayen Zeenat suka fara rawa da samarin da suka taho da su. Zeenat ta janyo Nazir zuwa filin rawar.

"Hajiya, ni fa ban iya rawa ba," Nazir ya faɗa muryarsa na rawa.

"Karka damu, kawai ka rungume ni, ni zan koya maka komai," ta faɗa tana sanya hannayenta a wuyansa.

Nazir ya rungume ta, yana jin yadda waɗannan manyan matan suke kallonsa cike da girmamawa da sha'awa. A daren nan, Nazir ya fara jin cewa shi wani "Babban Mutum" ne. Ya manta da Huda, ya manta da karatun da yake yi, ya manta da asalin inda ya fito. Ya fara amsa sunan "Golden Boy" da kawayen Zeenat suka sa masa a wannan night party.

Yayin da Nazir yake tsakiyar wannan rawar, kansa ya fara juyawa saboda hayakin da abubuwan da ya gani. A daidai wannan lokacin, a Gombe, Huda tana zaune a gaban ummah, idanunta sun kumbura saboda kuka, tana cewa: "Umman mu zuciyata tana gaya mini Nazir yana cikin wani hali. Me ya sa ba zai ɗaga wayata ba?"

Ummah ce ta dubeta cikin hikima irin tasu ta manya tafara lallashin Hüda. ita kanta tana jin tsoron irin wannan ƘAUNA da Hüda keyiwa nazir, dakyar ta samu ta shawo kanta bayan ta bata wasu addu'oin da zata dinga yin su.


#AbujaParty #GoldenBoyNazir #MaitamaNights #HajiaZeenatCircus #TheGoldenCage #BetrayalOfTrust #GombeToAbuja #SoDaHawaye

Bayan an watse daga taron daren, gidan ya yi shiru amma ƙanshin turaren wuta da na barasa har yanzu yana tashi a falon. Nazir ya koma ɗakinsa da aka sauk'e shi, yana jin wani irin shauƙi da bai taɓa ji ba.

Ba a jima ba, aka turo ƙofar ɗakin. Hajia Zeenat ce ta shigo, tana murmushin nan nata na samun nasara. Ta zauna a gefen gadon, ta ajiye wata leda mai tambarin "Apple" da kuma wani babban envelope mai kauri.

"Nazir, yau ka faranta mini rai. Ka nuna musu cewa ni ba ƙaramar mace ba ce," ta faɗa tana shafa fuskarsa. "Wannan takardar (envelope) kawayena ne suka ce a ba ka, wai 'goro' ne na kyan da kayi. Akwai kusan dubu ɗari biyar a ciki."

Zuciyar Nazir ta buga. Dubu ɗari biyar? Shi da bai taɓa riƙe dubu hamsin ta kansa ba, sai gashi cikin kan'kanin lokaci ya samu kud'ad'e masu yawa?

"Sannan wannan kuma," ta miko masa ledar, "Sabuwar iPhone 17 Pro Max ce. Ba na son ana ganinka da waccan tsohuwar wayar taka, ba ta dace da matsayinka na 'Golden Boy' ba. Ka goge komai na cikinta, ka fara amfani da wannan."

Nazir ya karɓi wayar yana rarraba idanu. Lokacin da ya kunna ta, hoton Huda ne ya fara bayyana a cikin ransa, amma da ya kalli tarin kuɗin da ke gabansa, sai ya ji wani sanyi ya ziyarci zuciyarsa. Ya riga ya fara nitsawa cikin kogin jin daɗi.


Kafin ya farga, Hajia Zeenat ta gyara zama, muryarta ta koma ta natsuwa. "Amma Nazir, akwai wata alfarma da nake so ka yi mini. Gobe akwai wani babban bako na (wani Sanata) da zai zo. Ina so ka zama kai ne zaka riƙa karɓar saƙonni daga hannunsa zuwa gare ni. Akwai wasu 'files' da wasu kananan jakunkuna da zai riƙa ba ka."

"Hajiya, me ke cikin jakunkunan?" Nazir ya tambaya cikin da'n tsoro-tsoro.

Ta yi dariya, "Kada ka damu, kawai wasu takardu ne na kasuwanci da kuma 'samples' na magungunan gargajiya da muke shigo da su daga kasashen waje. Saboda matsayinsa, ba ya son kowa ya ganshi yana ba ni kai tsaye. Kai tunda ba a sanka ba, kai ne mafi kusanci Dani a halin yanzu dole kai zaka na karbo mini sakon."

#TheGoldenTrap #GildedCage #DarkBusiness #AbujaUnderworld #LostInLuxury #TheNaivetyOfNazir #HighStakesDeception


Washegari, tun sassafe Nazir ya tsinci kansa cikin wata sabuwar rayuwa. Tsoron da yake ji a da ya gauraya da wani irin karsashi na karya. Ganin kansa cikin sutura ta alfarma da riƙe da wayar da ya san ko a mafarki bai taba tunanin mallakarta ba, ya sa ya fara jin cewa "ai rayuwar dama haka take."


Hajia Zeenat ta kira shi zuwa falonta na kasa, inda ta mika masa makullin wata mota kirar Mercedes Benz baka. "Nazir, yau ne ranar farko. Zaka je wani babban otal a kusa da babban birnin nan. Akwai wani mutum da zai fito sanye da hular saki, zai baka wata karamar jakar fata (briefcase). Kar ka bude, kar ka tambayi kowa komai. Kawai ka karba ka kawo min."

Nazir ne ya karb'a key motan ya tafi cikin fargaba, amma karshen tafiyar sai ya ga abin da shauƙi. Domin kuwa Mutumin ya mika masa jakar, sannan ya zura masa wasu daloli a aljihu yana cewa, "Kai ma yaron Zeenat ne? Ka hadu, dan haka ka kula." Nazir ya dawo gida zuciyarsa na bugawa, amma ganin yadda Zeenat ta karb'e shi da fara'a, ya sa ya ji lallai shi ma yanzu ya zama "Wani."


Daga ranar, Nazir ya saki jiki gaba daya. Hajia Zeenat ta san yadda zata yi masa; tana nuna masa soyayya irin wacce mace take nuna wa mijin ta, tana lallaba shi, tana ciyar da shi dad'i, sannan tana biya masa duk wata buƙata tasa ta rayuwa.

Nazir ya daina kallon Hajiya Zeenat a matsayin uwar d'akin sa, yanzu ya fara kallon ta a matsayin mace d'aya tilo da ta san darajarsa. Ya mance da duk wani hani na addini ko na al'ada. Duk lokacin da Huda ta kira shi, sai ya ga kamar tana son maido da shi cikin "talauci da kuncin rayuwa" ne, don haka sai ya daina ma daga wayar, gaba d'aya.


#ThePuppetMaster #GoldenHandcuffs #DeepCover #BetrayalInMotion #AbujaNights #SeducedByLuxury #TheDarkMessenger #SoDaHawaye

Kwanaki sun daina mini lissafi, dare ya koma mini tamkar rana, rana kuma tamkar wutar da take ƙona zuciyata. Tun ranar da Nazir ya tafi, na ji wani sashe na jikina ya tafi tare da shi. A duk lokacin da na ɗauki wayata na kira, muryar nan ta na’ura da take cewa "The number you are calling is switched off" tana zama mini tamkar wuƙar da take sassaƙa zuciyata.

Haka Na daina cin abinci, na daina magana da kowa. Idan Ummah ta kawo mini abinci, kallon kwanon nake yi ina tunanin ko Nazir ya ci abinci a can Abuja? Ko yana cikin koshin lafiya?

Wata rana, na kasa jurewa. Na ɗauki mayafina na nufi gidan su Nazir dake nan bayan layin mu. Kafafuna har rawa suke yi yayin da nake takawa a kan titin da muka saba tafiya tare da shi. Ina son in bincika, ko mahaifiyarsa ta sami labarin sa?

Ina isa, na tarar da mahaifiyarsa (Inna) zaune a tsakar gida tana tsince hatsi. Da ganina, ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Bayan mungaisa tace.

"Huda, har yau dai babu labari ko?" Inna ta tambaya, muryarta na nuna cewa ita ma tana cikin damuwa, amma ba kamar tawa ba.

"Inna, ko sau ɗaya bai kira ku ba ne? Ko ya aiko da saƙo?" Na tambaya, muryata na rawa, hawaye ya fara wanke mini fuska.

"Ya kira sau ɗaya kwanaki, ya ce ya sami aiki a wani company na kongila kuma yana nan lafiya. Amma tun daga lokacin, idan na kira wayarsa ba ta shiga. Ina ganin aikin ne ya yi masa yawa, Huda."

Jin kalmar "company da kongila" ya sanya gabana ya faɗi. Wata irin faduwar gaba ta ziyarce ni wadda ban taba ji ba. Na juya na fito daga gidan jikina na rawa. Na san Nazir; na san idan yana da hali zai neme ni. Idan kuma bai neme ni ba, to lallai akwai wani abu da yake faruwa wanda ya fi ƙarfin sa.

Haka Na koma gida, na shiga ɗakina na kulle ƙofa. Na zube a ƙasa ina kuka mai ban tausayi. "Nazir, me ka fita nema a Abuja da zai sa ka mance da ni?" A nan ne na yanke shawara. Idan duniya zata tashi, to ta tashi, amma ba zan zauna a Gombe ina kallon zuciyata tana kara mutuwa ba. Dole ne in bi sawun Nazir zuwa Abuja, ko da hakan zai zama silar ƙarshen farin cikina.

#HudasDespair #GombeDiaries #SearchForNazir #BrokenSilence #LoveAndAnxiety #TheLongWaiting #Heartache




Toh pha masu karatu nanfa ake yinta ga dai Nazir ya tafi ABUJA karbo GLK da iPhone 17 pro max ga Huda kuma ta yanke hukumcin binsa zuwa ABUJA, shin ya kuke gnin zata kasan ce.

Ga duk me buƙatar cigaba da karanta shi har ƙarshe zai iya sanya kuɗin sa ta ***. Opay sakina Ahmad Musa.
Sai ya turo shaidan biya ta Whatsapp number.



Mrs Alƙali.

***.