IMAM ZAID

Page 7

by @pendingamarya223

IMAM ZAID 🔬🥼





Pending Amarya ce🎭




JAJIRTATTU WRITERS ASSO………………✍️



The Odogwu Writer ✍️ 

Chapter2: THE HEIR HAS ARRIVED 🙌



An Empty barrel makes the loudest noise 🙌🏻🎭



IMAM ZAID 🔬🥼🧪

Paid book ne.
At a low fee za ku samu 500 naira kacal.

***😢

Opay Farida Aliyu Ibrahim 
shaidar biya via what’s app🙌🏻
***


Pending Amarya 007
Not edited 


So be patient. Indeed, the promise of Allah is truth 🥰🗣️




Ba ta sake masa magana ba ta gama shiryawa, suka wuce compound da Jamal da Sabila ke tsaye a jikin motar Jalal kirar _Range Rover Classic_ Wanda ko a wancan time din kudinsa ya kai almost 500k, dan wannan motar a wancan time din is a very luxurious car is not for y’ay’an Malam Shehu.(😂🙌🏻Yawwa)…….




Gida ne madaidaici mai kyau daidai da na rufa asirin wancan lokacin, duk da gidan is familiar to me buh renovation dinsa da akai ya wuce misali.

Mata biyu ne a madaidaicin tsakar gidan daya na jajjage yayin da dayar ke iza wuta a mangal wani dan karamin yaro na kusa da ita.

“Yaya Rukayya kin ga malam shiru har yanzu bai dawo daga kasuwa ba gashi yamma ta fara yi.”

Wadda ke iza wutan ta fada tare da kallon Yaya Rukayya.

“Kinsan yanzu watan Ramadan ya fara gabatowa akwai masu siyan kayan sallah tun yanzu kila mutane ne suka masa yawa.”
Ko gama rufe baki Rukayya ba ta yi ba Malam ya shigo hannunsa rike da ledoji.

Gabadaya gidan sun daina duk wasu tashin hankali da suke yi a tsakaninsu, zaman hadin kai suke sosai.

“Ikon Allah, ku ne ke hira haka?.” Malam ya fada tare da mikawa Suwaiba ledar hannunsa tare da daukan karamin yaron da ba zai wuce shekaru uku ba.

“Ahmad din Baba.” Malam ya karashe fada tare da saba shi a kafadansa.
Daure fuskarta Rukayya ta yi tamau dan ta tsani ta ga Malam ya dauki dan Suwaiba a rayuwarta.

“Ni fa wani albishir na zo muku da shi.” Malam ya fada tare da gyara ma Ahmad zama a kafadarsa.

“Wani kalar albishir kenan Malam?.” Rukayya ta tambayesa.
“Na siya mana sabon gida, sannan wannan umarah har da ku a cikin ma su zuwa da yardar Allah.”

Bakinsu duk su biyun yaki rufuwa dan farinciki.

Asalinsu🙌🏻🥰


Abubakar Shafi’u Madaki (Malam), ya kasance dan garin katsina ne amma ba ki dayansu shi da iyayensa mazauna garin Kano ne.

Kannensa uku biyu mata daya tal namiji, matansa biyu Suwaiba da Rukayya, Rukayya ta kasance yar uwarsa ce maana cousin dinsa, ita kuma Suwaiba yar gidan Kawar mahaifiyyarsa ce Hajjo.


Allah ya yi masa rufin asiri a Yanzun daidai gwargwado, dan sa daya Ahmad Wanda Suwaiba ce ta haifa masa.
Ita kuma Rukayya in dai ta haifa mutuwa suke shiyasa gabadaya ta tsani ta ga Mijinta na hidimtawa dan nasa.

cikin shekara dayar da ta wuce ne ya siyar da filinsa sannan matarsa Suwaiba ta damka masa set din Daham dinta Wanda hakan ya zama silar budewar arzikinsa.
Wannan kenan.


******


“Wallahi Sakinat ki tashi tsaye a kan mijinki, ke kin ga kalar kayan da ta saka da ita da danta masu tsada da kanwarta sannan suka bar gidan nan?, ke kin ga motar da ya siya ma dan nasu wai idan za’ayi fita da shi a dinga hawarta?, wallahi mu ne dai kike da shi da zasu fada miki gaskiya idan ba mu ba babu Wanda zai fada miki.” In ji cewar Shema’u.

Fashewa da kuka Sakinat ta yi sannan ta dago a hankali ta ce “Toh ni yanzu Shema ya zan yi?.”
“Ya za ki yi ya na wajen ki Sakinat, ke ko irin kissar nan ta kishiyoyi ba ki iya ba?, ko an fada miki a haka Fatimar ke zaune?.” Habashiyya ta fada tare da kallon idanun Sakinat.
“Toh a ya take zaune?.”
“Haba Sakinat, ay wallahi malamai take bi ba komai ba, wani namiji ne zai miki kalar wannan muguwar soyayyar, tun aurenki da shi ki ki haihuwa sai bayan shekara 10 sha….. Kuma Kina tunanin a haka ta bar shi?.” 

“Toh kenan shirka take yi?, ni kuma ay ba zan taba zama mai shirka ba.” Sakinar ta fada tare da kara kaimin kukanta.

“Toh wallahi ba shirka bane ba tun da ba sijjada kika yi ma wani gardin ba, ay taimakon kanki za ki yi da lafiyarki, ina za ki yi rayuwa a haka Kina matsayin bora?, Haba Sakinat.”

A haka suka yi ta convience nata har ta yarda za ta bisu.

Bangaren Fattumah kam tsakaninta da mutanen gidan sai dai Hi, Hi, Sam har yau ba ta sakin jiki da su, in banda Sabila dake hulda da su.

washegari da sassafe ta shirya cikin wani holland atamfa dinkin Riga da zani, hannunta rike da IMAM ta nufo hanyar da zai sadata da bangaren Dadah.
A tsaitsaye ta gansu a babban falon dake gidan ita da qawayenta, sai goge goge suke kamar Allah ya aiko su, kallo daya ta musu sannan ta dauke kanta tare da gyara kwanciyar danta a kafadar nata, duk wasu maganganu da suke ta fada ba ta dago ta kallesu ba ta yi shigewarta bangaren Dadar.

ko da ta shiga falon Dadar a zaune take ita da Inna Salamatu( mahaifiyyar Shema fa Sakinat mai magana a kan kamfanin da za a bawa Sagir), Ita da Gwaggo Sadiya, (mai cewa ta tsani mutum mai pride a previous page). Da kuma wasu mutane biyu da duk suma facalolinta ne.


Don’t be confused: Gidan dauke yake da families, ba wai wayanda suke uwa daya  uba daya ba, Noo hade yake da cousins din kakanni, gidan dauke yake da families din Swahili, dan ni kaina ban san adadin mutanen dake gidan ba 🤣🥹🙌🏻, muje zuwa.


“Assalamu alaikum.” Ta yi sallama da sassanyar muryarta, tare da durkusawa ta na gaida su gaba daya, Gwaggo Sadiya da Dadah ce kadai suka amsa dan ko kallonta mahaifiyyarsu Sakinat ba ta yi ba.
Jiki a sanyaye ta karasa wajen Dadah tare da mika mata yaron sannan ta fice ta koma bangarenta, a hanya ma haka Sakinat da yan uwanta suka yi ta zaginta da mayya.


After 5 years 🥰

A kwana a tashi ba wuya, IMAM is in primary 2 first term, babu abin da iyayensa suka rage sa da shi, kullum cikin nuna masa soyayya ake, babu kuma abin da ya nema ya rasa, soyayyar da yaron ke yiwa mahaifiyyarsa da ban yake, dan ko mai  yake yi a ka ce ga Mami nan zuwa barinsa yake ya tafi wajen Mami.
Duk girmansa kuwa Sabila ba ta daina goya shi ba, ita ma ta haihu danta is 4 yrs old sunan sa ZAIN.

Kamar kullum bayan an gama shirya shi cikin uniform dinsa, hannunsa na rike da jakar makarantarsa ya fito daga bangaren Maminsa bayan ta gama lallaba shi ba zata samu daman kai shi school din ba saboda ba ta dan jin dadi.


Ransa a bace ya nufi side din Small mum dinsa, ta gama shirya Zain kenan ZAID ya shigo  tare da yin wulli da jakar hannunsa zuwa kan kujera, tare da zama a kan kujerar ya na huci shi ala dole an bata masa rai.


“Wa ya bata ran maza haka?.” Ammi (Sabila) ta tambayesa tare da sakin hannun Zayn ta na mai kamo Zayd, da sai cika yake ya na batsewa.

“Toh yanzu mai aka yiwa IMAMUN MAMI?, wa ya tabawa Mami kai muje mu ce masa ya jirayi sammachi?.” Sabila a ta fada tare da taba kumatunsa.

Hawaye ta gani ya zubo a idanunsa hakan ya sanya ta saurin fadin “Zayn zo kaga Yayanka ya na kuka yau.” Ganin ta Kira Zayn ne hakan ya sanya shi saurin goge hawayensa tare da jan hannun Zayn din suka nufi dakin Jamal.


A tsaye yake ya gama shiryawa cikin manyan kayansa, a hankali yaran suka gaidasa sannan ya kamo hannunsu suka nufi general dinning room.

Har aka gama breakfast din Jalal bai dago ya kalli Fattumah ba ko da wasa, hankalinsa gaba daya ya tarkata shi ne zuwa wajen Sakinat da cikinta ya fito sosai.
Ita dai Fattumah ko kallon su ba ta yi, dan ita abin da yake gabanta take yi kawai.

Bayan an gama breakfast din Jamal ya nufi school da su ZAID da sauran yaran gidan.

“Aunty bangane abin da kike nufi ba ki ganar dani.” Sabila ta fada idanunta cike taff da kwalla.
“Toh ya zan miki ki gane?, ce miki nayi ni na gaji da auren Jalal gida zan koma ki kular min da ZAID, ko da yaren Swahili na miki magana?.”
“Wani abun ya faru ne Aunty?.” “Kafin ya farun nake son na toshe sa Sabila, kusan sati biyu yanzu na kasa gane kan Jalal, ko abinci na ajiye masa ba ci yake ba, shinfida ma yanzu ba hadawa yake da ni ba, ko sannu da zuwa na masa fada yake min Sabila, idan na basa hakuri shi ma is all thesame, gashi duk rayuwata kinsan na tsani tsawa.” Ta karashe maganar hawaye na zubo mata.

Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya babu wani canji da ta samu a wajen mijinta.

Bangaren su Suwaiba kuwa sun je Saudi, sannan sun koma sabon gida kudi ya dan fara zama a hannunsu daidai da na rufin asiri.


Rukayya ta haifi yan biyu duk mata kuma wayannan sun tsaya Alhamdulillah.

Suwaiba ita ma danta Ahmad private school yake zuwa, shigarsa da ban da na yan unguwar.


“Iklima kenan, wallahi aji tsoronki a doron kasa.”
“Yaya Abu da na miki mai?.” 
“Na ga aikin ki na farraqu da kika yi ma Jalal da matarsa ay dole na ce a ji tsoronki.”

“Ai haba?, Jalal din fada yake da matar tasa?, ta gaban goshi.”

“Ehmana, ke ba ki ma san aikin ya fara ba kenan?.”
“Ni fa babu abin da na musu Yaya Abu, da na gama cika bakina ma Anan ina komawa bangarena bacci na na soma.”

“Za ma ki fadi gaskiya ne Iklima.” Inji fadar Yaya Abu.

A cikin 5 years dinnan abubuwa da dama sun faru, Jalal ya mallaka ma ZAID daya daga cikin companies din Swahili Wanda suka fi ji da shi.

Hakan yaja cece kuce sosai, har hakan yaja Sakinat yin yaji ta bar bangarenta, bayan dawowanta daga yajin recently ne abubuwa suka fara sauyawa tsakaninta da Jalal.

Su Shema da sauran yan group dinsu ma gaba daya sun yi aure amma a cikin gidan suke zaune duba ga suma mazajen cousins nasu ne they’re all Swahili.


Dawowarsu kenan daga school ya yo part din Maminsa, ganin ba ta side din nata ne ya sanya shi nufar side din Ammin nasu.

Ko da yaje side din Ammin bai tarar da Maminsa a can ba hakan ba karamin damuwa ya saka masa ba, conflakes Ammi ta hado musu sannan ta sanar masa da Mamin na wajen Dadah, sannan ya saki ransa tare d nufar bangaren Dadah ba tare da ko kallon conflakes din ya kara yi ba, ya sa kansa ya yi gaba.

Ammi na masa magana ma ko juyowa bai yi ya kalleta ba ya sa kansa ya fice a gidan.

Tun kafin ya shiga side din Dadah ya yi clashing da ita a hanya, wani kalar dadi ne ya mamayesa ba tare da ya san lokacin da murmushi ya fita daga labbansa ba.


IMAM wani kalar yaro ne Wanda ko mai ya yi masa kyau yake sannan kuma kamar babba, hakan ya sanya kowani yaro ke son ya ga ya kusance sa, sannan tun a yanzu da yake yaro abin hannunsa bai tsone masa ido ba.

Rungumo sa ta yi tare da daukansa ta manna shi a kafadarta, sannan ta yi side dinta da shi.

“Dan Mami, ya school din?.”
“Mami Alhamdulillah.”
Daga haka ba ta kara masa magana ba har ta cire masa kaya ta masa wanka tare da zubo masa abinci, ya na gama ci kuwa ta sanya masa uniform din islamiyya Wanda kowa na estate din yake zuwa.

Kalar soyayyar dake tsakaninta da danta babu mai raba shi sai Allah.

Yammachin ranar.

Bayan sun dawo daga islamiyyar ma wanka ta sake masa tare da saka masa boxer da singlet sannan suka nufo wajen dinner din tare,
Zaune suke a waje daya kowa na ta cin abincinsa hankali kwance, zama ta yi sannan ta jawo ma ZAID pepe soup din kifi ta zuba masa sannan ta hau basa a baki.

Ta na basa ya na mata surutu kadan kadan, ta na bashi labari har ya cinye bacci ya daukesa a wajen a kan cinyarta.

Tsaki Sakinat taja tare da fadin “Dan kauye ya yi agogon hannu.” Fattumah ba ta bata amsa ba ta musu sai da safe sannan ta dauke danta ta nufi bangarenta….




 🥰🙌🏻
Like and share fi sabilillahi ❤️🥰🙏🏻




> IMAM ZAID ONLY ON PENDING AMARYA’S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY 🥰


~///Soft Noorah///~
  

> PENDING AMARYA😘 

> FARIDATOOL NOOR🥰🙌🏻

> THE ODOGWU WRITER ✍️ 


Your favorite troublemaker, Noor 😌