ALIYU HAYDAR

Chapter 8

by @nieemartullah

Qarfe biyu da minti hamsin suka sauka a Nnamdi Azikwe airport suna fitowa taxi suka shiga wanda zai kai su gidan mamy dake unguwar maitama,bayan mai taxi ya aje su suka gaisa da mai gadi yana musu sannu da zuwa suka wuce cikin gidan a main entrance din suka tsaya zannur ya danna bell ya koma gefe bayan kamar minti biyu mai aiki ta bude qofar ganin sune yasa ta koma gefe tana gaishe su tare da yi musu sannu da zuwa amsa mata suka yi suka shiga cikin parlour basu tarar da kowa ba hakan yasa HAYDAR ya kalli mai aikin da har ta kusa shiga kitchen yace ta ce ma mamy tana da baqi toh tace masa ta fara haurawa sama a parlour ta same ta tana zaune tana kallon news a TV tsugunnawa tayi tace barka da hutawa mamy dama baqi kika yi da mamaki take kallon ta tace baqi kuma Zahra'u eh Alhaji qarami ne da abokin shi mamaki ne kwance kan fuskar ta amma sai tace kice masu ina nan su karaso nan ta koma ta sanar masu da saqon mamy bayan ta sanar masu ta koma ta cigaba da aikin ta su kuma suka wuce parlour sama,da mamaki take ta kallon su har suka qaraso cikin parlour ta juya ta kalli zannur tace tace usman yaushe kuka zo garin murmushi yayi yana zama a gefen qafarta yace daga airport muke mamy yanxu muka sauka ikon Allah shima HAYDAR gefen qafarta ya zauna duk suka gaishe ta da ladabi ta amsa tana musu sannu da hanya bari na kira jiddarh ta kawo maku abinci jiddarh jiddarh daga can cikin dakinta tace mamy ina zuwa sai gata ta fito idonta ne ya sauka akan HAYDAR dake zaune gefen mamy bama ta lura da zannur ba ta buga tsalle ta qaraso inda yake ta taba shi tace wallahi mamy bro ne sai kuma ta marairaice tace kuma shine baka fada man zaka zo ba jiya fa har chatting sai da muka yi da daddare dan murmushi yayi mai kyau yace to ba gani kin ganni ba zannur ne daga gefe yace eh lallai kulun mamy tunda na zama cinnaka ai dole baza ki ganni ba dariya tasa tace Allah ya usman ban ganka ba sannun ku da zuwa toh sarkin surutu sai ki qyale su haka Kije ki kawo masu abinci miqewa tayi da sauri har tana tuntube zata fadi dariya zannur yayi yace anya kulu kina da rabon hankali kuwa mamy ma murmushi tayi tace banga alama ba,bayan minti goma sai gata sun dawo ita da Zahra'u tana riqe da tray din da ta dora abinci akai ita kuma Zahra'u na riqe da na drinks wucewa tayi ta aje masu a dining sannan ta dawo tace yaya ga abincin can na aje sannu zannur yayi mata sannan suka wuce suka zauna flasks din farko tuwon shinkafa ne miyar taushe dayan kuma masa ce sai na qarshe da ke dauke da funkasau kowanne a cikin su yayi serving kanshi da abinda yake so suka fara cin abinci................................

Jay ce zaune a dakinta tana aikin da ta kasa yi jiya files din dake gefen ta take dubawa bata ga file din da take nema ba room slippers dinta ta saka ta wuce dakin mom tana shiga ta tarar da mom na gyara wardrobe din ta juyowa tayi ta kalleta sannan ta cigaba da abinda take qarasa shigowa tayi ta gaida mom sannan tace mom ranar Tuesday da zan fita ban bar wani file a dakin ki ba juyowa tayi tana kallon ta gaba daya tace A'a baki bar file ba kin dai shigo da su a hannun ki,tsaya wa tayi tana tunani can kuma tace ya ilahi ina tunanin na barshi a asibiti bari na shirya naje na duba tace mata sai kin dawo fita tayi daga dakin ta wuce nata dakin a gurguje ta shirya cikin wata light blue din two piece abaya rolling veil din abayar tayi ta dauki wayar ta da kuma mukullin motar ta tunda sunyi sallama da mom yasa bata koma ba tayi wucewar ta ta kunna motar ta bar gidan.......................

Bayan sun gama cin abinci suka koma parlour suna ta hira da mamy kiran sallah la'asar yasa suka miqe al'wala suka yi suka tafi masallaci bayan sun idar da sallah suka dawo HAYDAR ne yace mamy zamu je mu gaida mom ne ki bamu mukullin motar ki za muyi amfani da shi tace toh bari na dakko maku,daki ta shiga ta dakko ta dawo ta miqa masu tace idan kunje ku gaishe man da ita suka hada baki wurin fadin to zannur ne yace mamy Idan muka dawo zamuyi magana toh shikenan Allah ya dawo da ku lpia suka ce Ameen motar mamy da ke compound suka dauka fita suka yi daga gidan suka hau hanya zuwa wuse,horn suka yi bayan sun qaraso gidan mai gadi ne ya leqo har wurin motar yana ganin wanda ke ciki yace ikon Allah ranka ya dade yau kaine a gidan dan mrmushi yayi yana shafa kanshi yace wallahi kuwa baba yace toh sannu da zuwa bude mashi gate yayi suka shiga bayan sunyi parking ne suka sauka suka wuce entrance din gidan,tsaye suka yi kafin yayi gathering courage ya danna bell sunan nan a tsaye daya daga cikin masu aikin gidan ta bude gefe ta matsa suka shigo ciki bayan sun zauna ne tace bari ta ma fada ma mom tayi baki sama ta wuce ta sanar ma da mom tana da baqi a parlour hijabi ta saka kan kayan jikin ta ta fito tana sakkowa da murmushi sosai akan fuskar ta take kallon su tace zanga annabi in nayi hali na gari yau wa nake gani a gida na sakkowa yayi qasa yana sosa kai yace ina yini mom amsa mashi tayi tana neman gurin zama ta zauna shima zannur zamowa yayi qasa yana gaishe ta amsa mashi tayi shima da murmushi a fuskarta tana tambayar su yaushe suka zo amsa zannur ya bata da yau tace to masha Allah ya ka baro su lateefah Lpian su qlau mom sunce ma suna gaishe ki ina amsawa kallon HAYDAR tayi da ya sunkuyar da kai qasa tayi tace Aliyu ya wurin su safiyyah qasa ya qara yi da kai yace yau na dawo garin ai mom banje gidan ba gidan mamy muka fara zuwa sai nan tace Masha Allah kun kyauta ya kuka baro mamy yace tace tana gaishe ki toh ina amsawa Allah ya muku albarka Idan kaje ka gaishe man da safiyyah hajiya mama ce ta fito daga dakin ta tana ta sababi ita daya tana cewa shikenan an bata yarinya duk anbi an koya mata kukan banxa kina gani fa bilkisu ita da  kanta ta bini har daki babu wanda ya ko rakata amma tana kyalla ido taga wannan ya ta fita sannan ta samin kuka wai ita wurin JAY zata kiji fitina maganar ce ta maqale bayan ta shigo parlour murtsika idon tayi ta bude tace ikon Allah wa nake gani kamar gadanga murmushi yayi yace ni din ne dai hajiya mama ina yini Lpia qlau shima zannur gaida ta yayi ta amsa sannan ta  dora da fadin kaga yanxun nan kuwa wannan ya Jaiyana ta tafi asibiti da tana dakinta tana aiki wai ta manta file zata je dakkowa ayyah babu rabon mu gaisa amma tunda ba yau zan tafi ba wata qila ma gaisa eh toh haka ne miqewa suka yi suka yi ma mom da hajiya mama sallama zasu tafi mom tace ku shiga ku gaisa baban naku yana bangaren shi toh suka ce mata sannan suka wuce part din dad yana nan zaune a parlour suka yi sallama ya amsa musu tare da basu izinin shigowa durqusawa suka yi sannan suka miqa mashi hannu don yin musabaha bayan sun gaishe da shi ne suka nemi gurin zama suka zauna bayan sun dan yi hira ne suka yi masa sallama suka tafi........................

Zirga zirga kawai take daga nan tayi nan duk ta kasa samun nutsuwa ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a inda take son zuwa  hakan nan dai ta haqura ganin yamma tayi kuma wurin na da nisa sosai amma ta quduri niyyar gobe da sassafe zata je kiran wayar ta da ake ne ya katse mata saqe saqen da take yi daga wa tayi ganin momma ce ke kiran ta kai kunne tace Assalamu Alaiki daga can bangaren momma tace wa'alaikissalam ina yini momma Lpia qlau safiyyah ya gida Lpia qlau Alhamdulillah yanxu muka gama waya da khaleel yake fada man jiya kin je gidan shi eh ai jiya sai maghrib ma na dawo gida toh haka ake so Allah ya maku albarka ya qara hade kanku ameen tace a sanyaye sannan tace don Allah ki cigaba da yi min addu'a kinji tace addu'a kam ana yi safiyyah sai dai a qara amma kar kiji nauyi na ki fada man Idan kina da damuwa saurin girgiza kai tayi tace babu komai momma kawai dai ina buqatar addu'ar ne toh shikenan Allah ya muku albarka kinji sai anjima,ajiye wayar tayi bayan sun gama ta shiga toilet........................

Sai ana ta kiraye kirayen sallar maghrib ta dawo gida,a gajiye ta zauna tana fadin wash mom dake fitowa daga kitchen tace JAY sai yanxu daga dakko file tace mom wallahi zuwa nayi na tarar da marasa lpia da yawa kuma babu doctor ko daya and nurses din suna buqatar helping hand shiyasa na zauna Toh shikenan ki shiga kiyi sallah lokaci yayi,tashi tayi ta wuce sama ta shiga dakin bayan ta idar da sallah ne ta sakko qasa dakin hajiya maama ta shiga ta tarar da ayaanah na bacci gefen hajiya maama dake ta lazimi ta zauna sannan tace mata amma meyasa kika barta tayi baccin yamma tsakani da Allah wannan fitinanniyar yarinyar Idan ban bar ta tayi baccin ba ya zanyi kina sa qafa kika bar gidan nan ta fara kuka wai ita sai ta biki da na gaji da na lallaba qafafu na na fito nan na iske gadanga yazo shi da usman muka gaisa da na dawo ne naga tayi bacci gudun kar ta cigaba da koke koken yasa na kyale ta jinjina kai kawai tayi bata ce komai ba ta koma gefen ayaanah tana tashin ta bayan ta bude ido ne tace oya muje kiyi sallah sai mu sakko ayi dinner ko miqewa tayi ta bi bayanta suka tafi ita dai hajiya maama na nan zaune kan prayer mat ta tabe baki tace gulmammu,bayan ta saka ta tayi sallah ne suka sakko don yin dinner a kan dining suka tarar duk suna zaune su kadai ake jira bayan sun zauna ne mom ta tashi ta zuba  jollof rice da fried plantain Sai ta dakko wani bowl daban ta zuba lamb pepper soup ta ajiye ma dad sannan ta aje mashi glass cup na fresh fruit platter ta qara daukar wani plate din ta zuba tuwon semovita da egusi soup ta aje ma hajiya mama tare da glass cup na chilled zobo,fried plantain ta zuba a wani plate din daban ta dakko bowl ta diban mata greek yogurt parfait ta tura gaban JAY saboda ita bata cin abinci mai nauyi da daddare sai kuma ta qara daukar wani plate shima ta zuba fried rice da plantain sannan ta diba mata greek yogurt parfait itama ta miqa mata sannan tayi serving kanta ita ma tunda suka fara cin abinci ba ka jin komai sai qaran spoons da fork har suka gama bayan duk sun gama JAY ta tattara ta kai kayan kitchen wanda za'a saka a fridge ta saka wanda za'a wanke ta miqa ma su Aunty naja da suke jiran su gama ta fito ita ma ta zauna a parlour aka fara hira hajiya mama ce tace ni ummaru bilki bata fada maka abinda ya faru jiya ba dagowa yayi ya kalleta yace bata fada man komai ba hajiya gyara zama tayi tace ahaf ai dama nasan ba zata fada maka ba labari ta dakko tiryan tiryan tun daga haduwar JAY da Sooraj har zuwa jiya da matar shi tazo tayi masu rashin kirki tana kai wa nan tace toh amma fah Ni tun a jiya nayi wa tufqar hanci don na ce mata duk sanda ya qara dawowa ta ce masa ita anyi mata miji a gida jinjina kai yayi yace nima ina ganin hakan da kika yi shine maslaha in shaa Allah,yawwa toh ai kaga hakan yafi Allah ya muku albarka gaba daya suka ce Ameen yace in shaa Allah hajiya gobe nake son zan koma saboda akwai ayyukan da ban qarasa ba eh ya kamata gaskiya Allah ya tsare ya kare ka yace amen JAY ce tace dad kuma Idan ka tafi sai yaushe zaka dawo toh sai naga yanda abubuwan zasu kasance for now i can't say,toh shikenan Allah ya dawo da kai Lpia yace Ameen...............................

Bayan sun dawo gidan mamy ne zannur yace kaga mallam ka tashi ka tafi gidan ka ka wani yima mutane zaune wani banxan kallo yamai sannan yace ai sai kazo ka kaini mamy ce tace ya kamata ka tafi gida Aliyu kaga fa yamma tayi miqewa yayi sai da yaxo dai dai zannur sannan yasa takalmi ya take masa qafa qara yayi yace mamy kin ganshi ko dariya kawai tayi tace ba ruwa na kun fi kusa ya wani tamke fuska kamar bai yi komai ba ya nufi hanyar fita,sai da yaji fitar shi daga gidan baki daya sannan ya dawo gefen mamy ya zauna yace mamy dama maganar HAYDAR ne na gaji da ganin shi cikin damuwa duk da mutum ne shi da ba'a gane yana cikin damuwa ko akasin hakan amma ni ko dariya yayi idan yana cikin damuwa ina gane wa maganar dai kin sani akan matar shi ne kuma ni dama tun lokacin da ya kawo ta na fada maki ai ni hankali na bai kwanta ba amma sai kika ce anyi bincike kuma ba'a sami wani aibu tattare da yarinyar ba kuma yar gidan mutunci ce shiyasa ban qara magana akai ba a lokacin bayan auren abubuwa da yawa sun faru wanda tuna su ma babu abinda zai qara sai bacin rai,shikenan haka zai qare rayuwar shi cikin baqin ciki bai san farin ciki ba kin sani ba haka HAYDAR yake a da ba ko tafiya muka yi wurin aiki da anyi kwana biyu zai ce muje mu gaida mamy amma yanxu sai dai fa ni Idan naga abin yayi yawa nace ya kamata mu zo mu gaishe ki mamy da tun sanda ya fara magana ta kafe shi da ido bata ce komai ba sai da ya gama tace ya kake so nayi ko kana tunanin ina jin dadin ganin shi a haka kullum addu'a nake masa kuma ina da yaqinin Allah zai amsa tausayin ta ya qara ji sosai ya kwantar da murya yace kiyi haquri mamy in shaa Allah komai zai wuce kamar bai faru ba amma ya kamata kiyi ma malam yusuf magana tunda naga Allah ya bashi baiwar sanin maganin karya sihiri tohm shikenan zanyi masa magana in shaa Allah toh mamy bari naje na huta sai anjima,sauka yayi ya tafi bangaren su na gidan inda suke zama kafin suyi aure...............................

Bayan ya sallami mai taxi ya nufo gate din gidan karo na farko kenan a tsawon shekaru shida da yazo shiga gidan shi bai ji gaban shi ya fadi ba hannu ya kai yayi knocking ba'ayi second talatin ba aka bude get yana ganin wanda yake tsaye bakin gate din ya matsa yana fadin barka da dawowa ranka ya dade amsawa yayi yana shigowa a bakin qofar parlour yayi knocking yana tsaye sai ga barira ta bude qofar gaishe shi tayi ya amsa tana ta jero mashi sannu da zuwa ciki ya shiga yana tafiya hanyar part din shi a hanya suka kusa yin karo da safiyyah da sauri ta matsa gefe don for the first in her life taji ya mata kwarjini da har bata san lokacin da tace sannu da zuwa ba shima yayi mamaki amma sai ya fuske yace yawwa part din shi ya wuce direct bai ko waiwayi inda take ba,har safiyyah tayi hanyar dakin ta ko me ta tuna kuma sai kawai tayi hanyar parlour kitchen ta shiga ta tarar da barira na daukar food flask zata kai dining karba tayi bata ko bude taga menene a ciki ba ta dauka tayi hanyar part din shi bayan ta aje ta dawo ta hada drinks shima a wani tray din ta kai ta aje bata jira ya fito ba ta koma dakin ta...............................

Mom ce zaune a bedroom din dad tana hada mashi yan kayayya kin da zai buqata bayan ta gama hada komai ta rufe trolley din ta aje  gefe dad ne ya kalle ta yace thank you my love tace my pleasure yace kin san wani abu there is this thing i want to discuss with you tun ranar da na dawo gidan nan tace ina jin ka yace maganar yarinyar nan ayaanah kallon farko da nayi mata yarintar JAY na tuna saboda sunyi matuqar kama mom tace banda na yadda da JAY kuma nasan bata taba yin nisa da mu dai dai na wata daya ba da zan iya cewa yarinyar nan JAY ce ta haife ta kamar har ta baci ai na fada maka da na ganta ban san lokacin da na suma ba yace ikon Allah sai kallo kuma fa dama ana samun irin haka kiga baka san mutum ba amma kunyi kama tace kuma fah haka ne Allah ya kyauta yace Ameeen...............

Bayan yayi wanka ya canja kaya zuwa jallabiya ya fito ya tarar an jera masa abinci yasan dai yan aiki basa shigowa part din shi bai ko kalli inda abincin yake ba ya wuce masallaci don lokacin ana ta kiraye kiraye sallar maghrib yana nan zaune har aka yi sallar isha'i sannan ya dawo gidan bai tarar da kowa a parlour ba hakan yasa ya wuce part din shi direct abincin da aka aje mashi ya bude flask din farko jollof din cous cous ne wanda yaji liver da vegetables dayan kuma brown spaghetti ne shima sai qamshi yake kallon transparent glass jug jug din da aka saka smoothie yayi sannan ya tabe baki ya miqe ya tafi kitchen coffee ya hada ma kanshi sannan ya dawo ya kunna TV yana kallon kwallo yana sipping coffee din shi..................................

Bayan ta koma dakin ta ta kasa nutsuwa gashi gobe take son yin tafiya amma kwata kwata bata jin zata iya fita Idan bai bar gidan ba hankalin ta ba qaramin tashi yayi ba ta rasa makama ta saqa wanann ta warware har ta gaji don kanta ta shiga bathroom tayi al'wala ta shimfida prayer mat abinda ta dade bata yi ba iya kacinta sallar farilla,bayan ta idar ta daga hannayen ta sama tana fada ma ubangiji damuwar ta ta dakko alqur'ani tana karantawa sai da taji ta sami nutsuwa sannan ta tattara komai ta mayar inda ya kamata bathroom tayi koma tayi wanka bayan ta fito ta shirya sannan ta saka sleeping dress ta hau gado ta kwanta bacci mai dadi ya dauke ta.......................