SARTSE A ZUCI...!

SARTSE A ZUCI...! Chapter 19

by @ayshadansabo

*SARTSE A ZUCI...!💔* Arewabook@ayshadansabo

Paid book ***

©️ Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

Chapter 19

Wannan kiran da Yaya Zayd yayi shine silar katse hirar da Amal da Yaya Hameedah suka faro,kuma tun daga wannan ranar basu sake samun damar da sukai doguwar hira ba domin hidimar biki ne aka shiga yi ka'in da na'in.Ranar Wednesday mutanen Maiduguri su Anty Falmata suka iso Zaria,Anty Yagana ita sai Thursday ta iso aka cigaba da hidima waɗanda za su halarci Gombe wajen kamun Amarya da za ayi Friday da yamma suka fara shirin wucewa Gombe.Cikin waɗanda za su wuce Gombe har da Amal dasu Yaya Sakeenan Gwaggo Abu da Gwaggo Abun kanta tare da Anty Salma ƙanwar Umma Asiya,Yaya Hameedah taso zuwa amma Ya Zayd yace ba za ai masa doguwar tafiyar Mota da Yaro ya takura ba.Hakanan tana ji tana gani su Amal suka kama hanya da safiyar ranar Friday ɗin,ba za su dawo ba sai an ɗaura aure a washegari sai su taho da Amarya kamar yadda aka tsara.Sosai suka samu kyakykyawar tarba daga Iyayen Amarya da danginta,domin ba ƙaramin karramasu aka yi ba tun daga kan masaukin da aka ajesu har zuwa kan cima.Kamun kuma ya ƙayatar sosai Amarya da Ango sun sha kyau abin sha'awa,Amal tasha ado tayi kyau tamkar ka sace ka gudu.Sosai ta hargitsa hazo manyan samari masu ji da kansu sukai ta bibiyarta tana sanar dasu cewa wani ya rigasu,wasu kuma ko damar da za ta tankasu ma basu samu ba domin gabaki ɗaya ta murza kambun miskilancinta.A can gida Zaria kuwa haka kawai Hameedah tunda ta nemi wayoyin Yaya Zayd a round 9pm na dare taji a kashe hankalinta ya tashi,domin sun rabu akan cewa da zarar ya isa Gombe zai kirata sai gashi dare yayi bata ji kiransa ba.Rabonta dashi tun da sukai waya da safe ya sanar da ita cewa jirgin 2pm zai bi zuwa Gombe,kuma tun a cikin wayar dama taji muryarsa wani iri alamun yana cikin damuwa amma kuma data tambayeshi sai ya sanar da ita cewa babu komi kawai ya tashi baya jin daɗin jikinsa ne.Sai dai abinda bata sani ba shine tun a daren alhamis komi ya faru,komin daya zama silar sake buɗe wata shafin ƙaddararsa na yin tarayya da wata mace bayan Najwa har suka haɗa shimfiɗa da ita.Kuma hakan ya faru ne ranar alhamis da yamma lokacin da Maryama ta shiryo masa lafiyayyen abinci da lemun coconut milk da ya taɓa sanar da ita cewa yana so a cikin hirar da sukanyi ta chat idan yana jin bata lokacinsa,ko kaɗan baisan za ta ziyarci gidansa ba domin baima taɓa sanin ta bibiyeshi har ta sanya an gano mata Unguwar da yake zama da gidan nasa ba.A ranar sam bata je office bama domin a bakin wani ɗan office ɗinsu yaji ana zancen cewa bata da lafiya,amma kuma komawarsa gida daga office ta kirashi tana sanar masa cewa gata a bakin gate ta kawo masa abincin data shirya na musamman dominsa.Ya sha ji ƴan office ɗinsu suna yabon iya girkinta domin tana yawan yin abin breakfast mai yawa ta je musu dashi ayi ta zuba santi,amma shi tun zuwansa garin bata taɓa yin hakan ba shiyasa ma data faɗi cewa gata a bakin gate abin ya bashi mamaki.Kuma a cikin mamakin ya tashi ya fita wajen gate ɗin,idanunsa suka sauka akan motar dake fake a bakin gate ɗin ita kuma tana daga cikin motar alamun da kanta tayo driving ba driver ɗin gidansu daya saba kaita office idan ta tashi yaje ya ɗauke ta bane ya kawota.Da tsananin mamaki sosai Zayd ya buɗe mata gate ta shiga da motarta kafin yayi mata jagora zuwa madaidaicin tsararren falon gidan nasa,falo ne da aka ƙawata shi da kayan more rayuwa so simple and Unique.Ƙamshinsa daya gama kama komi nasa har ma da muhallin zamansa shine abu na farko daya fara yi mata sallama,kuma daga irin kallon da Zayd ɗin ke jifanta dashi da yadda ya haɗe face ɗinsa tasan cewa baiyi maraba da ziyarar data kawo masa gidan nasa ba.Ita da Kanta ta sanar dashi cewa driver ɗin gidansu Obi shi ta sanya ya bibiyeshi har ya gano mata inda yake,don haka ya daina mamakin ganin ta kawo kanta gidansa.Zayd Abdallah bai sake tabbatarwa da kansa cewa Maryama shu'uma bace sai time ɗin data cire mayafi ta nemi kitchen da kanta ta samo plate da spoon domin yin serving ɗinsa abincin data kawo masa,kuma inda akai rashin sa a dama da yunwa sosai ya shigo gidan yana shirin idan yayi sallar Magriba ne ya fita yaje ya nemi abinda zaici sai kawai ga kiranta ya shigo.Don haka time ɗin da tayi serving ɗinsa lafiyayyen veggies white rice and stew ɗin sai ya kasa gwasaleta,domin ƙamshin miyar kaɗai da yadda dahuwar rice ɗin yayi ya sanya miyansa tsinkewa.Time ɗin data zuba haɗin salad ɗin da yaji egg and red apple a ciki sai ya sake jin miyansa na sake tsinkewa,cikin tsananin mamakin yadda ta sanyashi a gaba da magiyar ita za ta ciyar dashi ya fara buɗe baki yana amsar abincin data ciko spoon ta kawo bakinsa.Kuma tun daya fara ci daɗin abincin ya ratsa har tsakar kansa bai sake yin gigin ƙin amsa ba har ya tada plate guda data zuba masa,lemun coconut da ruwa sune abu na ƙarshe data bashi ya sha.Kuma tunda ya gama sha baifi da mintuna sha biyar ba sinadarin data saka masa a cikin coconut milk ɗin ya fara aiki a jikinsa,sosai ya fara jin matsananciyar sha'awa na taso masa musamman time ɗin da yaga Maryama ta cire rigar jikinta ta zauna daga ita sai bra da under wear.Bai zai taɓa cewa ga yadda komi ya kasance ba domin shi dai yasan da kansa yakai kansa zuwa gabanta ya fara wasa da ƙirjinta da suka ɗauki hankalinsa tare da sake kunna wutar fitina a cikin zuciyarsa,daga nan ne kuma ya tabbatar cewa ya fara rasa nutsuwarsa tun bayan da Maryama ta fara bidashi da irin salonta da ta fi Najwa iya sarrafa ɗa Namiji.Abu na ƙarshe da zai iya tunawa shine condom ɗin data ciro a cikin jakarta ta saka masa da hannuwanta kafin ita da kanta ta fara sarrafashi,shima kuma cikin ficewar hayyaci da hayaƙin dake tashi a cikin kansa ya fara sarrafata a yunwace domin dama dauriya kawai yake amma yana cike da kewar Hameedah mai tarin yawa a wannan lokacin.Basu samu kansu ba har saida time ɗin sallar magriba ta shige sannan komi ya lafa a tsakaninsu,hankalinsa ya dawo jikinsa har ya fahimci cewa ya sake tafka babban kuskure a rayuwarsa da yayi saken da har Maryama tasan shi a ɗa Namiji.Ita kuma farin ciki da wani irin matsananciyar soyayyarsa ne suka rufe idanunta har tana jin cewa za ta iya yin komi domin mu'amalarsu ta cigaba da ɗorewa tana samun wannan nishaɗin a tare dashi,shi kuma tsananin ɓacin rai da tausayin matarsa Hameedah ne ya fara zuwa kansa har baisan lokacin daya rufeta da masifarsa tare da bata Umurnin barin masa gidansa cikin ƙaraji da zafin zuciya.Maryama cikin rarrashi da ban haƙuri ta gama maida suturar jikinta babu kunya bare tsoron Allah,ta haɗa kwanukanta tas ta bar masa gidansa tana jin kome zai faru ba za ta taɓa rabuwa dash ba mu'amalar bariki tsakaninta dashi kuma yanzu aka fara.Da wannan alwashin ta bar gidansa,shi kuma ta barshi da shiga wanka bayan ya cire condom dake jikinsa yayi jifa dashi a saman sofa.Yana wankan yana juya lamuran da suka faru tamkar a cikin mafarki,sosai yake ji zuciyarsa tayi masa nauyi domin bai taɓa kawo cewa zai kuma mallakawa wata mace gangar jikinsa bayan Najwa ba,sai gashi Maryama tayi amfani da makirci irin na mata ta sanya masa masifar data kunna wutar sha'awar data rinjayeshi har suka kaiga sanin junansu.Tun daga wannan ranar har zuwa wayewar garin da sukai waya da Hameedah yake jin ransa a jagule,zuciyarsa taƙi ta saki daga ƙunci da haushin Maryam daya cika zuciyarsa.Ranar sam bai iya zuwa office ba excuse ya ɗauka a zuwan cewa tafiyar gaggawa ta kamashi,tunda dama niyyarsa daya tashi daga office around 2pm airport zai wuce direct yabi flight ya isa Gombe ya kama masauki kafin washegari a ɗaura aure ya juyo ya dawo Port Harcourt ɗin ba tare da ya waiwayi gida ba.Sai dai kuma wannan ƙaddarar data shiga tsakaninsa da Maryama sai ya canza tunaninsa,domin baya ji zai iya cigaba da barin Hameedah a wata duniya ta daban ba tare da ya ɗakkota ta dawo kusa dashi ba.Amma kuma koda sukai wayar ƙarshe da safe bai sanar da ita shirinsa ba,kuma tunda ya ɗauki hanyar airport ya kashe wayoyinsa duka sabida yadda kiran Maryama ke shigo masa babu ƙaƙƙautawa.Kuma har ya isa Gombe wayarsa guda ɗaya kawai ya kunna ya sanar da Ango Sulaiman cewa ya iso,suna kan hanyar zuwa masaukin da Yaya Sulaiman yayi masa a cikin hotel ɗin da suka sauka ya sake kashe wayarsa ganin cewa Maryama za ta cigaba da damunsa da kira.Tun daga lokacin ne bai sake kunna wayarsa ba har zuwa lokacin da Hameedah ta dinga kira bata sameshi ba,kuma sai zuciyarta ta kasa haƙuri har saida ta yanke shawarar kiran Ango Sulaiman domin taji daga gareshi sabida tana da tabbacin cewa yasan masaukin da Yaya Zayd ɗin ya sauka idan har ma basu tare kenan.Lokacin da kiran ya shiga ya fara ringing har ya buga sau biyu taji Yaya Sulaiman ɗin ya ɗauki wayar yana kiran sunanta,hakan yasa tayi saurin tambayarsa hidimar biki kafin ta jefa masa tambayar data fi cin zuciyarta.Tana jiyo yadda ya saki dariya kaɗan kafin ya sanar da ita cewa Yaya Zayd ɗin na hotel suma yanzu za su ƙarisa can domin basu jima da sauke Amarya a gida ba tunda ba a tashi Kamun da wuri ba,don haka yace mata da zaran ya isa Hotel ɗin zai kirata ya haɗata da Yaya Zayd ɗin.Kuma tunda taji haka sai hankalinta ya kwanta har ta iya kiran Amal bayan sun gama waya da Yaya Sulaiman ɗin tana tambayar Amal ɗin yadda Kamun ya tsaru,Amal ta sanar da ita cewa komi yayi domin ba ƙaramin ƙoƙari Amaren sukai wajen ƙawata wajen har ma da irin cimar da aka ci alamun cewa Yaya Sulaiman ɗin bai kashe dukiya a banza wajen sallamarsu da wadataccen kuɗin daya ishesu har suka tsara komi cikin wadata da birgewa ba.Suna gama waya da Amal Anty Falmata da bata samu zuwa Gombe ba ta kawo mata Abdallah dake kuka ta fara shayar dashi,Yaron nashan Nonon yana saki yana ɓangale mata baki da dariya sai kuma ya koma shan nononsa.Ta zuba masa idanunta ƙaunarsa mai nauyi na sake game jinin jikinta,a haka kiran Yaya Sulaiman vedio call ya shigo mata.Tana receiving fuskar Yaya Zayd ya haska a maimakon na Yaya Sulaiman ɗin,kuma take suka sauke ajiyar zuciya kafin ta riga shi da faɗin cewa tayi missing ɗinsa meyasa zai kashe wayarsa alhali yasan za ta nemeshi domin jin ko ya isa Gambo lafiya?Tana kallon yadda ya kasheta da wannan killer smile ɗin nasa dake narkar da zuciyarta kafin ya fara bata haƙuri da cewa wayoyin ne babu chargy bai jima da cikasu da chargy ba,kuma yana shirin kunnawa ya kirata ne Yaya Sulaiman yazo masa da ƙorafin cewa ya barta cikin tunani jin wayarsa a kashe.Ya gama rattafa mata kalaman idanunsa akan yadda take shayar da Abdallah,wani irin zazzafar sha'awarta ya sake mamaye zuciyarsa domin ba ƙaramin kyau tayi masa a cikin shigar doguwar rigar shan iska mai ƙaramin hannu data saka ba.Yanayin yadda lafiyayyen fatarta ke glowing ta cikin wayar yana haske idanunsa kaɗai abin sha'awa ne bare kuma yadda Abdallah ke shan Nonon yana saki ba ƙaramin kunna wutar fitina yake a cikin zuciyarsa ba,hakan yasa ya sake narke mata yana sanar da ita irin missing ɗinta da yayi.Ta dinga rarrashinsa da kalamai masu sanyi kafin ya sanar da ita cewa gobe ana ɗaura aure zai biyo su Yaya Sulaiman zuwa Zaria ne ya fasa komawa River's ɗin a gobe,kuma koda ta tambayeshi dalili sai yace mata sai yazo zai sanar da ita shi dai kawai ta shirya kominsu domin Kaduna za su ce idan ya ƙariso Zaria komin dare.A haka suka rabu Hameedah na mamakin yadda ya canza ra'ayinsa cikin sauri,kuma sai hakan yayi mata daɗi domin sosai take jin itama tayi kewarsa tana buƙatarshi a kusa da ita.Washegarin ranar kamar yadda ya faɗi tare da Ango da abokanansa suka iso Zaria cikin tawagar motocin da suka ɗakko Amarya da friend's ɗinta da sauran dangi suka iso Zaria,sun shigo Zaria misalin ƙarfe 7pm anata kiran sallar magriba.Ganin sun iso late ya sanya Yaya Zayd haƙura da tafiya Kaduna ya ɗauketa zuwa Gonan Ganye gidansu,Amal sun so zuwa gidan Yaya Hameedah su kwana amma ganin boss ɗin yazo ya tasa ƙeyar matarsa ya sanya suka haƙura suka kwana a ɓangaren Anty Mamah a ɗakin Jameelah.Yaya Zayd da Yaya Hameedah sosai suka raya daren cikin faranta ran junansu domin bashi kaɗai yayi missing ɗinta ba itama tayi nasa,shiyasa ta zage ta bashi farin cikin da yayi missing ta kashe masa ƙishirwarsa da ita kaɗai ke iya kashe masa shi baki ɗaya.Baby Abdallah kuma ya basu haɗin kai domin ko sau ɗaya bai farka shan nono ba tunda ya cika cikinsa da madararsa kafin yayi bacci,saida asuba ya farka ta shayar dashi Yaya Zayd na tsaye a kansu yana kallonsu cike da so da ƙauna.A round 10am na safe ta gama kintsa Abdallah ta miƙashi wajen Babah Gaje ta fara hidimar shirya wa Yaya Zayd abin breakfast,tare suka ciyar da juna yana sanar da ita cewa gobe za su wuce port Harcourt tare domin bazai iya cigaba da zama shi kaɗai ita kuma tana wani waje daban ba.Suna kammala karyawa ya fice yace mata zai je ya sami Daddy ya sanar dashi tare za su wuce da Hameedah zuwa gobe,kuma koda ya sanar da Daddy sai yayi musu Allah ya kiyaye hanya.Koda ya je ɓangaren Momy itama ya sanar da ita cewa da Hameedah zasu wuce Rivers gobe Allah ya kiyaye hanya tayi musu,tadai so ace yabar Hameedah ta gama biki zuwa next week idan za ta bishi ne sai ta bishi daga baya.Lokacin da Hameedah ta sanar da Amal cewa Port Harcourt za su ce a gobe sai Amal ta sanya kuka tana faɗin cewa za ta yi missing Abdallah ita meyasa zai ce zai wani tafi dasu can wata uwa duniya,Hameedah sai ta saki baki kawai tana kallon Amal domin da dukkanin zuciyarta take kuka tana rungume da Abdallah a jikinta.Ta shiga yi musu vedio tana rarrashin Amal ɗin da cewa ta kwantar da hankalinta Abdallah ai nata ne,da zaran ta yayeshi ma ita za a kawowa shi ta rainesa ta manta cewa ta bata kyautarsa ne.Amal a lokacin sai ta kalli Yaya Hameedah ta sanar da ita cewa ai baƙin halin mijinta da yadda ya tsaneta bazai taɓa yarda ta bata kyautar ɗansa ba,kuma maganganun da Yaya Hameedah tayi mata bayan ta furta kalaman nata sai suka tsaya mata a zuci domin cewa tayi,"Amal ko yana so ko baya so dole ya barki da Abdallah domin jikina na bani haihuwarsa kaɗai nayi amma ba zan rayu dashi ba,kedai kawai kiyi masa kyakykyawar tarbiya ki kuma sanar dashi ina ƙaunarsa."Hameedah ta faɗi kalaman ne cikin raha,amma yadda suka dira a cikin kunnuwar Amal sukai zaman dirshan tare da jefa firgici a cikin zuciyarta abu ne da ba za ta iya misalta shi ba.Kuma kamar yadda suka saba sai da suka yi faɗa da Amal domin masifa ta rufe Yaya Hameedah dashi tace mata ta daina yi mata maganar mutuwa,haka suka rabu Amal na fishi da Yaya Hameedah akan cewa tana faɗar mata da gaba da zancen mutuwa kullum tayi maganar Abdallah.Har bakin mota sukai ma Hameedah rakiya time ɗin da Nuhu driver zai wuce dasu KD,Kulu mai rainon Abdallah kaɗai za su fara wucewa da ita su Babah Gaje sai daga baya Habu driver zai wuce dasu tare da motar Hameedah.Suna tafiya zuwa ƙarfe biyu na rana aka gudanar da walimar tarban Amarya Nadeeya anan cikin gidan Daddy,ƙayataccen walima ne da aka ci aka sha aka ragargaza wa'azi mai ratsa zukata.Kuma zuwa yamma motocin da za su wuce da Amarya gidanta dake Kaduna suka iso,su Amal sune suka fara yin gaba don haka sun riga kowa isa Millenium city Kaduna suka jira isowar Amaren.Yaya Hameedah ma tana jin cewa sun iso ta matsawa Yaya Zayd akan ya kaita taga ɗakin Amarya tunda gobe za su wuce Abuja subi light zuwa Port Harcourt ɗin,don haka suna tare a gidan Amarya dasu Amal har zuwa dare sannan Yaya Zayd yazo ya ɗauketa.Washegari 9am Yaya Hameedah suka wuce Abuja,su kuma su Amal zuwa azuhur suka wuce Zaria aka bar Amarya ita kaɗai domin suma danginta tun sassafe suka kama hanyar Gombe cike da alfahari da inda suka kawo ƴarsu Nadeeya domin kyakykyawar sallama aka musu tun a Zaria kasancewar sunce daga Kaduna za su wuce gida abinsu.Momy da Anty Mamah sunyi rawar gani wajen fitar da Yaya Sulaiman kunya,sosai Yaya Sulaiman ya sake yin alfahari da samun Momy a matsayin Uwa.Iyayen Nadeeya ba ƙaramin kuɗi suka kashe wajen shirya mata ɗakunanta da kayan alfarma ba,gida ya tsaru ko maƙiya sai dai su gani su ƙyale domin komin hassadar mutum dole ya saki cewa an kashe dukiya gida kuma ya ginu ya tsaru matuƙa da gaske.Hameedah sun wuce Port Harcourt zuciyarta cike da kewar su Momy da Amal da zatai,da zaran ta kalli Abdallah sai taji zuciyarta ta sosu da irin kukan da Amal tayi na kewarsa da zatai.Amma kuma da zaran ta tuna cewa sati biyu kacal za su yi su juyo bikin Jameelah sai taji sanyi a cikin zuciyarta,duk da cewa dai basu yi zancen da Yaya Zayd ba bata san ko zai amince ko bazai amince da zuwanta bikin Jameelah ba......✍🏻