SARTSE A ZUCI...!

SARTSE A ZUCI....! Chapter 20

by @ayshadansabo

*SARTSE A ZUCI...!💔* *Arewabook@ayshadansabo*

*Paid book ****

©️ _Ayshat Ɗansabo Lemu_ ✍🏻

*Chapter 20*

Ƙarfe huɗu na yamma jirgin dasu Yaya Zayd suka bi zuwa Port Harcourt ya sauka a airport ɗin,kuma already sun samu driver ɗin office ɗinsu yazo ɗaukarsu don haka basu ɓata lokaci ba ya ɗaukesu zuwa gidan da Zayd ɗin ke zaune.Tunda suka shiga Unguwar Old GRA Hameedah ta yaba ta kuma san cewa bada ƙananun kuɗi ya kama hayar gidan ba,domin tun daga farkon shiga Street ɗin za ka fahimci cewa na masu rufin asiri ne babu yadda za ai ƙaramin ma'aikaci ya iya kama haya a Unguwar.Tunda suka isa bakin gate ɗin gidan Hameedah taji gabanta ya yanke ya faɗi,zuciyarta ta shiga rawar da bata san dalilin faruwar hakan ba.Abdallah dai yana rungume a hannun Yaya Zayd yana faman gwalanniyarsa irin na Yara domin idanunsa biyu lokacin,time ɗin da driver ya sauka ya buɗe gidan tare da zuge ƙaramin gate ɗin ya shigar da motar sai Yaya Hameedah ta miƙa hannu ta amshi Abdallah daga hannun Ya Zayd ɗin.Shi da driver ɗin ne suka fita suka fara kwasan manyan Luggages ɗin da suka taho dasu suna kaiwa bakin ƙofar shiga falon suna ajewa,kuma suna kammalawa Yaya Zayd ya sallami driver ɗin ya tafi abinsa.Hameedah sai ta shiga ƙarewa gidan kallo tana yaba tsarinsa da irin shuke-shuken da suka lulluɓe jikin ginin ta waje suka sanya gidan yayi wani irin lullumi,yanayin yadda aka ƙawata parking space ɗin da motar Yaya Zayd ɗin ne kaɗai ke wajen ba ƙaramin birgeta yayi ba.Tun zuwansa garin da kwana biyu Habu driver ya kawo masa motar tasa daya barta a KD,Kulu dai na biye da bayanta suka nufi ƙofar shiga cikin falon bayan Yaya Zayd ɗin ya buɗe ya basu hanya.A cikin falon suka yada zango kafin Zayd ɗin yayi kiran Hameedah suka shige cikin wani corridor ɗin da ya fitar dasu zuwa kitchen,daga can kuma ya sake kutsawa da ita ta wata ƙofa daya fitar dasu backyard inda aka tanadi wani single room mai ɗauke da toilet a ciki.Babu komi a cikin ɗakin sai katifa madaidiciya da aka siya aka aje sabo dal,dama kuma ya siya ne sabida irin wannan ranar da za su ɗakko yar aiki su taho da ita.Kuma ɗakin babu laifi da girmansa domin za a aje katifu manya guda biyu ta yadda ƴan aiki uku ma za su rayu a ciki babu takura,don haka suna shiga ya sanar da ita cewa nan Kulu mai rainon Abdallah za ta zauna.Yaya Hameedah suna komawa ciki ta sanya Kulu ɗaukar jakar kayanta tayi mata jagora zuwa ɗakin tare da nuna mata toilet,tana komawa ɓangarensu ta tadda Abdallah riƙe a hannunsa yana masa wasa.Kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kanta tana sanar da Yaya Zayd ɗin cewa ta gaji wanka take son yi ta gabatar da sallar la'asar dake kansu,don haka yana nuna mata hanyar da bedrooms ɗin guda biyu suke bata ko jira ya taso ba ta nufi corridor ɗin ta shige ciki.Kuma direct ƙofar dake hannun hagunta ta nufa domin jikinta ya bata cewa nan ne bedroom ɗin da yake amfani dashi sabida ƙamshinsa data fara jiyowa tun daga wajen ƙofar shiga,kuma tana murɗa ƙofar ta buɗe ta sanya kanta ciki wannan dai ni'imtaccen ƙamshin nasa shi ya fara yi mata sallama.Ɗakin ta fara ƙarewa kallo tana mamakin yadda ya bar kayansa a watse a saman bed,wasu a saman sofa da alamu wanɗanda ya cire ranar da zai wuce Gombe ne bai sakasu a cikin laundry ba,kai tsaye ta nufi bakin bed ɗin tana yaba tsaruwar komi dake cikin ɗakin baccin nasa da colour ɗinsa ya zama white da sirkin silver.Sannu a hankali ta fara ɗaga kayan dake zube a saman sofa da nufin kwasa takai zuwa wajen data hangi laundry basket ɗin dake aje daga hanyar shiga toilet,ta ɗaga riga guda tana shirin kai hannunta kan wandon dake ƙasan rigar idanunta sukai mummunar ganin daya tayar da hankalinta har ta ji ƙafafunta sun fara ɗaukar rawa.Condom ta gani wanda alamu suka gama nuna anyi amfani dashi an manta ne ba a kawar ba,hantar cikinta yayi masifar kaɗawa wani abu mai nauyi ya taho ya danne ƙirjinta.Cikin rawar hannu ta zubda kayan dake hannunta ta duƙa ta ɗauki condom ɗin cike da ƙyanƙyamin tana sake jin ƙirjinta na sake mata nauyi,hawaye take son su zubo mata amma idanunta sun kafe sai turiri kawai take ji na tasowa daga tsakiyar zuciyarta yana mamaye ƙirjinta.Da ƙyar bakinta ya iya buɗewa ya furta kalmar,"Innallilahi wa'inna'ilaihirraju'un!" Kuma a daidai lokacin Yaya Zayd ɗin ya turo ƙofar ɗakin ya shigo yana rungume da Abdallah a hannunsa,ganinta a tsaye a gaban sofa ɗin ya bashi mamaki domin ya ɗauka cewa tuni ta shiga wankan.Tamkar wanda aka baiwa umurni sai idanunsa suka sauka akan hannunta dake sanƙare,kuma take zuciyarsa tayi masifar bugawa sakamakon abinda ya gani riƙe a hannunta.Jin shigowarsa cikin ɗakin ya sanya Hameedah ɗaga kanta ta zube masa manyan idanunta da suka gama hargitsewa,cikin rawar murya tayi masa nuni da condom ɗin dake riƙe a hannunta tana tambayarshi mene ne wannan? Yadda tayi tambayar cikin rawar murya da sarƙewar harshe ba ƙaramin sake hargitsa zuciyarsa tayi ba,tausayinta da wani irin kunya suka lulluɓeshi yana jin duk ya gama muzanta a gabanta.Kuma tun daga kallo ɗaya da tayi ma ƙwayar idanunsa ta gano cewa bashi da amsar da zai iya bata a nan kusa,sai kawai ta saki condom ɗin ta nufi ƙofar data tabbatar cewa nan ne toilet ta murza ta faɗa ciki tare da rufo ƙofar da ƙarfin gaske har saida ta sanya Abdallah ya firgita ya fara kuka.Itama sai kawai ta jingina bayanta da jikin ƙofar wani irin azababben kukan da take ta fatan yazo ya ƙwace mata,kuka take sosai wanda sautinsa ke fita yana ratsa kunnuwar Yaya Zayd dake zaune a saman sofa yana jijjiga Abdallah dake kuka sosai.Gabaki ɗaya ya rasa nutsuwarsa har baisan ma ta ina zai fara rarrashin Hameedah ba bare har ya kare kansa a gurinta,me zai ce mata ta yarda cewa ba shine ya gayyato Maryama gidansa har komi ya faru ba? Da wani idanu zai kalleta ya sanar da ita cewa Maryama ita tazo har gida tayi masa fyaɗe? Yo fyaɗe mana tunda itace ta sanya masa desire tablet a cikin lemunta har ta rinjayesa suka aikata wannan aika-aikar data bar masa tabonsa har gashi Hameedah tayi nasarar ganin gamsasshen shaidar da bazai taɓa iya kare kansa a wajenta har ta yarda dashi ba.Gabaki ɗaya ya manta da condom ɗin a cikin ɗakin baccinsa tun a daren daya cire ya shiga yin wankan tsarki,kuma tsananin ƙunci da damuwar da aukuwar lamarin daya farun ne ya mantar dashi har ya bar garin ba tare da daya kawar dashi ya fita dashi ya yarba.Jin sautin kukan Abdallah dake ƙaruwa yana tayar da hankalinsa ya dawo dashi cikin nutsuwarsa har ya iya miƙewa ya taka zuwa bakin toilet ɗin yayi tsaye kunnuwarsa na sake jiyo masa sautin kukan Hameedah dake sake ratsa kunnuwarsa,cikin murya mai cike da rarrashi yake roƙonta ta buɗe masa ƙofar ta amshi Abdallah ta bashi nono tunda bata fara wankan ba amma tayi biris dashi ta cigaba da rera kukanta zuciyarta cike da tarin baƙin ciki da nadamar zuwanta garin Port Harcourt ɗin.Jin irin kukan da Yaron keyi bilhakki ya karya zuciyarta tayi saurin buɗe ƙofar tayo waje,bata iya kallon fuskar Yaya Zayd ɗin ba domin ji tayi a lokacin bata ƙaunar kallon fuskarsa.Hannu kawai ta miƙa masa alamun ya bata Abdallah lokacin data kai bakin sofa ta zauna tana jan ajiyar zuciya,sai ya taka ahankali ya isa wajenta ya miƙa mata Yaron yana jin zuciyarsa na sake karyewa da tsananin tausayinta.Shayar da Yaron ta fara hawaye na cigaba da wanke fuskarta,Yaya Zayd ya durƙusa a gabanta tare da ƙoƙarin kai hannu ya riƙo nata amma sai tayi gaggawar matsawa tana jin wani irin kuka na sarƙeta.Cikin muryar kukan take roƙonsa daya fice ya bar mata ɗakin bata son ganinsa,kalaman suka dira a cikin kunnuwarsa tamkar saukar tsawa a saman dutse.Yanayin yadda tayi maganar cikin ɗaga sautin muryarta abu ne da bata taɓa yi masa hakan ba,hakan ya bashi tabbacin cewa a yau ya kaita bango kuma daga yadda ta rintse idanunta ya bashi tabbacin cewa da gaske bata son ganinsa a gabanta yanzu.Sai ya tashi jiki a saluɓe zuciyarsa a hargitse ya fito daga bedroom ɗin yana jin nadamar abubuwan da yake aikatawa suna lulluɓeshi,tsanar Maryama na samun gurbi a cikin zuciyarsa domin ya ɗauki duka laifin ya ɗaura a kanta domin da bata kawo masa ziyara ta yaudareshi yaci girkinta ba da bata samu damar data yaudareshi har ya faɗa tarkonta ba.Cikin falon ya koma ya zube bisa doguwar kujera yana ji duniyarsa baki ɗaya na juya masa,sosai tausayin Hameedah ke keta jinin jikinsa domin bai san da wani abu ta rageshi data cancanci ɗanɗanar baƙin cikin da take shiga a samakon bibiyar matansa ba.Dukkanin irin kulawa da soyayyar da take bashi suka dawo masa yana aunasu a ma'auni na adalci,yana tuna cewa duk wannan ƙaddarar da take bibiyarsa akan Najwa da Maryama duk cikinsu baiji mai taste ɗin data kama ƙafar Hameedah ba.Hannuwansa duka biyu ya kai ya dafe kansa dake masa matsanancin ciwo,tunawa da yayi shima akwai bashin sallar la'asar dake kansa ya sanya ya miƙe ya nufi ɗaya bedroom ɗin daya kai mata luggage ɗinta ciki ya wuce toilet ya ɗaura alwala ya fito.Ita kuma ɓangaren Hameedah tana gama shayar da Abdallah ta wuce zuwa toilet ɗin domin yin wanka,time ɗin data fito kayan data cire ta mayar a jikinta ta ɗauki Yaron ta fito domin komawa ɗaya bedroom ɗin ba tare data san cewa Yaya Zayd ɗin na ciki ba.Yunwa take ji sosai amma kuma bata jin cewa ɓacin ran da take ciki zai bari taci wani abu domin gabaki ɗaya zuciyarta a cinkushe take,tana tura ƙofar ta shiga idanunta suka sauka a kansa yana zaune a bakin sofar dake cikin ɗakin bayan idar da sallarsa.Tagumi ya zabge da hannu bibiyu yana wassafa da wasu irin kalamai zai yi amfani ya rarrashi Hameedah ta yafe masa,jin buɗe ƙofar da shigowarta cikin ɗakin ya sanyashi saurin miƙewa ya isa gareta yana ƙoƙarin amsar Abdallah dake bacci.Bata hanashi ɗansa ba ta sakar masa Yaron tana wucewa gaban inda luggage ɗinsu suke ta buɗe guda ta ciri kayan da za ta saka ta mayar ta rufe,akan idanunsa ta sauya kanyan ta ɗauki hijab data ciro a cikin kayanta ta nufi wajen sallayar daya tashi akai ta kabbara nata Sallah.Kuma time ɗin data idar yaso matuƙa ta bashi dama ya fara rarrashinta amma hakan bai samu ba domin kai tsaye ta sanar dashi cewa bata buƙatar jin komi daga garesa,daya matsa sai ta sanya masa kuka tana masa magiyar ya taimaketa ya mayar da ita Zaria ta zauna a kusa dasu Mummy domin bata ga amfanin zuwanta inda yake ba tunda ya aje matan dake biya masa buƙatarsa.Sosai ta haukace masa har yayi mamakin cewa dama Hameedah nada zafi haka? Koda ya fita ya sayo musu abinci da sauran tarkacen kayan ciye-ciye ko kallo basu isheta ba,Kulu kawai ta kwasan mawa nata kason takai mata ɗakinta.Kuma tana dawowa ta ɗauke Abdallah a jikinta suka shige cikin bedroom ɗin data yanke shawarar ya zama mallakinta,duk iya rarrashi da magiyar da Yaya Zayd yaje yana mata akan ta buɗe ƙofar taci abinci Hameedah tayi biris dashi domin da gaske ba za ta iya cin komi ba baƙin ciki da takaicin irin rayuwar da yake da matan bariki ya riga ya cika mata ciki.Tana ji ya gaji da magiyar ya kwaso komi ya kawo mata bakin ƙofar tare da roƙonta ta fito ta ɗauka idan shine bata son gani ya wuce ɗakinsa tayi haƙuri ta buɗe ƙofar taci wani abu kodan Abdallah dake shan nono,bata buɗe ƙofar ba kuma har saida ta tabbatar cewa da gaske ya bar wajen sannan cikin sauri ta buɗe ta kwashe abubuwan cimar daya kawo mata ta shige tare da maida ƙofar ta kulle.Tuni Abdallahi yayi nisa a baccinsa don haka ta zauna tana tsakalan abinda taga za ta iya ci,zuciyarta a cushe rai a jagule haka take faman tura abincin ba tare data ji ɗanɗanon komi a bakinta ba.Sosai take danasanin biyosa garin da bata da kowa daga ita sai shi,kewar gida dana Amal ya cika zuciyarta ta tuna sunyi waya ɗazu amma taƙi bari suyi vedio call sabida bata son Amal taga halin da take ciki domin ta ɗaukarwa kanta alƙawarin ba za ta sake fallasa sirrinta koda a wajen Amal ɗin bane sabida babu abinda hakan zai sake janyo masa face tsana a wajen Amal ɗin.Tasha alwashin birne komi a cikin zuciyarta ta cigaba da haɗiyan baƙin cikin da bata da ranar da zuciyarta za ta saba dashi matuƙar Zayd bazai daina neman mata ba,a iya hasashe da tunanin datai tayi tun daga zuwansu garin da kuma abinda idanunta suka gane mata ta kasa gano wani waje data kuskure masa ta hanyar faranta ransa dayi masa dukkanin salon da yake so a shimfiɗa.Wani tunani ya haska a cikin kanta kuma a lokaci guda kuka ya ƙwace mata tana jin yadda zuciyarta ke sake ɗaukar nauyi,hannunta na rawa ta ɗakko wayarta dake kusa da inda ta shimfiɗe Abdallah ta shiga Tafawa Zayd saƙo cike da fata da burin ya bata amsar da za ta gamsar da ita ko za ta gane daga ina matsalar take daya kasa tsare mata kansa.Kuma saƙon na tafiya ta zubawa wayar idanu hawayen da suka kasa tsaya mata na cigaba da wanke fuskarta,takai hannu ta dafe saitin zuciyarta dake wani irin zafi da turiri tana ayyana dama haka Matan da mazansu ke bibiyan mata suke ji ko kuwa ita kaɗaice ke jin hakan?

A ɓangaren Zayd Abdallah kuwa yana kwance yayi rigingine a saman bed ɗinsa yaji ƙaran shigowar saƙo daga wayarsa,tamkar bazai duba ba sai kuma ya janyo wayar domin dubawa.Idanuwansa suka sauka akan sunan Hameedah da yayi saving da My Honey World,cikin sauri ya buɗe saƙon yana karanta kalmomin da suka sake ɗaga hankalinsa da hautsina kwanyarsa." _Yaya Zayd please ka sanar dani bani da taste ne? Don Allah karka ɓoye mini idan har bana gamsar dakai ne ya sanya kake bibiyan mata wallahi zan nemi magani,please karka ɓoye mini komi domin zuciyata ba za ta iya cigaba da ɗaukar wannan baƙin cikin ba please!"_ Waɗannan sune kalaman daya karantasu idanunsa na hasko masa a yanayin da tayi rubutun.Take yaji wasu irin ƙwalla masu zafi sun cika idanunsa,nadamar da bai taɓa jin irinsa akan dukkanin abinda ya aikata ba yake ji.Cikin rawar hannu ya shiga dialling number ɗin Hameedah,kuma cikin sa a ringing biyu ta ɗaga call ɗin yana jiyo shashshekar kukanta.Magiya yayi mata akan ta buɗe masa ƙofar gashinan zuwa,kuma time ɗin daya isa sai ya tadda ta buɗe ɗin tana makuye a jikin ƙofar tana cigaba da kukan dake sake kassara zuciyarsa.Wani irin kyakykyawar runguma yayi mata suka sauke ajiyar zuciya a tare kafin ya ɗauketa zuwa saman bed ɗin ya fara rarrashinta da dukkanin kalaman da sukai saura a cikin bakinsa,bai iya ɓoye mata komi ba ya sanar da ita labarin Maryam da yadda aka yi komi ya faru har kawo yadda ya yankewa kansa shawarar tahowa da ita domin ta sake zame masa garkuwa daga farmakin da Maryam za ta sake kawo masa domin matuƙar tasan yazo da matarsa ba za ta sake karanbanin biyosa gidansa ba bare har ta yaudareshi su sake aikata haramci.Hameedah na kwance a jikinsa tana jin dukkanin bayanan dake sake ɗaga hankalinta,wani irin tsanar Maryama taji yana sake ratsa zuciyarta tana mamakin yadda ƴan mata suke ɓata rayuwarsu.Tabbas a labarin daya bata yayi nasarar rage kaso mai girma na haushinsa da take ji,hakan yasa lokacin daya canza salon rarrashinsa bata hanashi ba ta barshi yayi dukkanin bidirinsa amma bata tayashi da komi ba shi yayi kiɗansa ya kuma yi rawarsa.Haƙƙinsa ne ta bashi kanta ta kuma bashin,domin haka kawai zuciyarta ke bata shawarar kada ta taɓa hanashi haƙƙinsa na aure komin baƙin ciki da ɓacin ran da zai kimsa a cikin zuciyarta.Tabbas bata gamsu da kalaman daya gama yi mata na cewa ita kaɗaice zumarsa dake iya kashe masa ƙishirwarsa ba,tadai fi gamsuwa da cewa ba dole ne sai mace ta gaza da namiji a wannan fannin yake bibiyan wasu matan ba,wannan wani abu ne da suke ɗaurawa kansu domin taƙi ta yadda cewa hakan ƙaddararsu ce babu son rai a ciki domin Ubangiji ya faɗi dukkanin hanyoyin da maza da mata ya kamata subi wajen nisanta kawunansu daga aikata Zina.Shiyasa zuciyarta ta kasa yi masa uzuri domin idan har abinda yake faɗi a kanta gaskiya ne,to bata ga dalilin da zai saurari wata mace suna aikata fasadi ta waya har su riƙa jan ra'ayinsa da tsarin halittarsu da bata san da me suka fita dashi ba,domin idan nono yake so tana dashi haka ɗuwawun ma bakin gwargwado ta samu domin cikin Abdallah daya buɗata duk ma abinda take ganin ada basu fito sun nuna kansu ba a yanzu sun fito ɗin,domin ta sake cika kuma duk wani shape ɗin jikinta da Ubangiji yayi mata baiwarsa sun gama bayyana to don me bazai iya haƙuri da ita kaɗai ba sai ya bibiyi haramun? Time ɗin daya gama bidirinsa ya kuma sami nutsuwar da ba haka yaso ba domin Hameedah bata tayashi da komi ba duk da tasan cewa ya tsani hakan a tarayyarsu da juna,amma yayi mata uzuri domin ya sani da watace yayi kaɗan ta bashi kanta bayan abinda ta gani da kuma labarin daya bata.Amma Hameedah da yake ƴar halas ce dake sonsa da dukkanin zuciyarta tayi haƙuri ta daure domin ganin ta sauke haƙƙinsa dake kanta,sai ya rungumeta a cikin jikinsa yana sake bata haƙuri tare da yi mata alƙawarin cewa bazai sake aikata Zina da kowacce mace ba In Sha Allah.Hameedah jinsa kawai take amma zuciyarta ta kasa gamsuwa da alƙawuransa,hakan yasa ta rage masa tsawon rarrashinsa ta sanar dashi cewa Allah zai ji tsoro ya daina aikata koma me yake aikatawa domin ba ita yake aikatawa saɓon ba,ita kawai yana jefata cikin baƙin ciki da takaici ne.Farkawar da Abdallah yayi a cikin duhun daren shi yasa Zayd ya raba jikinsa da nata domin bata damar ɗakkosa ta shayar dashi,kuma bayan ta shayar dashi ya koma baccinsa sai shima ya kafa rigimar cewa ta bashi koda kaɗan ne.Kuma bai jira komi ba ya kafa kansa ya barta da mamakin yadda yake iya shan abin ba tare da ƙyanƙyami ba,sosai take sake yaba ƙaunarsa da twins tunda har baya iya ɗaga ƙafa a kansu duk da yasan cewa abin cikin na jaririnsa da yake faɗin bai haɗa ƙaunar da yake masa data kowa a faɗin duniyar ba a yanzu.Zuwa washegari sai komi ya shige tamkar babu ɓacin ran daya gifta a tsakaninsu,Hameedah ta danne zuciyarta ta cigaba da bashi kulawa shi da ɗansa Abdallah.Time ɗin da sukai Vedio call da Amal ne ta dinga sanar da ita irin missing ɗinta da tayi,tace da ita Abdallah kansa yayi missing Mom ɗinsa don haka ta dinga haskawa Amal fuskar Abdallah dake kwance yana wutsilniya da ƙafafunsa yana rera gwalanniyarsa irin ta yara masu cikakken ƙoshin lafiya......✍🏻