IMAM ZAID

008

by @pendingamarya223

IMAM ZAID 🔬🥼





Pending Amarya ce🎭




JAJIRTATTU WRITERS ASSO………………✍️



The Odogwu Writer ✍️ 

Chapter2: THE HEIR HAS ARRIVED 🙌



An Empty barrel makes the loudest noise 🙌🏻🎭



IMAM ZAID 🔬🥼🧪

Paid book ne.
At a low fee za ku samu 500 naira kacal.

***😢

Opay Farida Aliyu Ibrahim 
shaidar biya via what’s app🙌🏻
***



And your Lord is going to give you, and you will be satisfied.🫩🙌🏻❤️


Pending Amarya 008
Not edited 




Tsaki Sakinat taja tare da fadin “Dan kauye ya yi agogon hannu.” Fattumah ba ta bata amsa ba ta musu sai da safe sannan ta dauke danta ta nufi bangarenta….


Haka rayuwar ta ci gaba mata da dadi babu dadi, Jalal ko da wasa ba shigo mata yake a Yanzun ba, rayuwarta ita dai take a gidan da tilon dan ta guda daya.


After 5 years 🥰🫩


Babu abin da ya canza tsakaninta da Jalal sai ma abin da ya yi tsamari dan yanzu kaff familyn gidan kowa Abun da ke gabansa yake yi, amma Jalal ya kan shigo side din Fattumah ya biya bukatarsa sannan ya dawo wajen Sakinat da ita ma ta haife wancan cikin da suka zo babu lafiya ta na dauke da wani tsohon cikin.

Sanye yake cikin wani black jallabiyya over size fatar jikinsa da duk sai sheki yake ya kara haska sa da shigar sa.

Tafiyarsa yake cikin nutsuwa ya na duba wasu assignment dinsa da ya dawo daga wajen Amminsa ta koya masa. 

Sallama ya yi a hankali tare da shigowa cikin falon ya na mai karasowa wajen da take a zaune kan kujerarta da ta saba zama a yanzun.

Jikinta dauke yake da tsohon ciki, Wanda sosai hakan ya fiddo da manyantan jikinta.

“Mami na dawo, mai kika dafa?.” Ya fadi hakan tare da cire takalmansa da ya shigo da shi har cikin dakin.

“Dan Albarka nah, da takalmi  ka shigo min cikin daki ko?.” Ta yi maganar tare da dauko wani dan karamin bowl da ruwa a flask ta doso wajen da yake da kyar.

Bai ba ta amsar tambayarta ba ya kara mata wani tambayar shi ma “Mami Dadah zogale take kwadawa naje na amsowa princess dina ta ci?.’’ 
“Ka dai ce za ka je ka amso zogale kana son ci babu wata princess da zata so cin wani zogale.”
“Toh Mami yau zamu je general dinning?.”
“Malam daina min surutu na gama wanke maka kafa da wannan tausar duk ka kwaso gajiya, dan na san sai da kaje ka buga ball tun da kai ba magana ta kaje ji ba.” Ta fada tare da saka towel ta na goge kafarsa da ta gama wankewa sannan ta daura shi akan chair ta fara yi masa massage abin da ya fi son Mamin ta dinga masa.

Dadaddare ma shi kadai ne yaje wajen cin abincin ba tare da Maminsa ba, hakan ya sanya shi yin faka faka ya ci abincin ya dawo bangaren Mamin, dan ko kan Papan sa dake ta jansa da hira bai bi ba.


“Mami ba za ki yi min brush ba bacci nake ji.”  Ya fada tare da kashe tvn da cartoon ke ta kai komo a ciki.

“Wai Imam ka tsufa ba ka san ka tsufa ba ?, haka ka ga dan uwanka ya na yi da Amminku idan ban da son jiki kalar naka?, idan na mutu na bar duniya sai na ga Wanda zai maka, ba za ka bar kusa dani kaje ka wanke bakin ka sanya kayan baccin ka ka bar nan ba ko sai na make ka?.”

“Kina make Babana za ki jirayi sammachi.” Jalal da shigowarsa kenan ya fada tare da kallon Fattumah da ta dauke kallonta daga wajen da yake.

Tun da ya Bar dinning din ta biyo bayansa har ta ga ya shige cikin side din Fattumah, ganin yadda ya sake mata ne abin ya kara bakanta mata rai sannan ta nufi kofar barin wajen rai a bace ta na huci ba ta kuma zarce wajen kowa ba sai wajen mahaifiyyarta.


After 2 days 

“Kin ga Sakinat Malam fa ya ce aikin ki ba zai ta ba ci ba har sai baya ganinta a cikin gidan nan sannan kuma ba ta cikin hayyacinta, dan kauda tunaninta ne kadai zai sanya shi, jin shi ma babu tunaninta da na danta a cikin kwakwalwarsa, sannan sai yadda kika yi da shi, wannan asirin su yafi na baya Wanda ya fara sakinsa ci , zai ma manta da ya taba wata mata bahaushiyya a doron kasa har sai asirin da za ki binne ya fito sarari sannan ita ma idanunta za su bude, shi ma zai tuno dasu a rayuwarsa.” Mamanta ta fada tare da mika mata wasu ledojin ta fara mata prescribing yadda za ta yi da su, da na abinci, da na binnewa da kuma na sawa a ruwan wanka.


Dadi ne ya rufe Sakinar ba tare da taji wahalar samun ta yadda za ta zuba mata abubuwan ba ta ma mahaifiyyarta godiya sannan ta juya ta nufi bangaren Dadah.

Sai da ta gamawa  Dadar hira sannan ta wuce da tsohon cikinta zuwa part dinta, tana jin wani kalar farinciki na ziyartar ta.

A wajen zuba mata magani a abinci kam ba ta sha wahala ba, dan Jalal da hannunsa ya hada mata abincin, sai da ta faki idanunsa sannan ta zuba mata maganin a ciki.

Bai ga shigowarta kitchen din ba hakan ya san ya shi saurin kwashe tray din ya nufi side dinta.

Ganin har ta fito daga wanka da ta shiga ne hakan ya sanya shi saurin ajiye mata abincin sannan ya fara bata a hankali, tun ba ta saki jikinta da shi ba har ta zo ta saki.
Ya na mata hira jefi jefi har taji bacci ya fara daukanta, gyara mata kwanciyyarta ya yi sannan ya fice daga dakin dan ya san lokacin dawowar Imam daga islamiyya ya kusa zai je dauko sa.

*****


Zaune suke a madaidaicin compound dinsu, Mama  (Rukayya) da yaranta mata suka fara girma na zaune ta daura su a cinya, ita kuma Umma(Suwaiba) na zaune ita ma da dan tsohon ciki ta na yanka ma Ahmad farce.

ko ina na gidan is very neat rayuwar su suke Gwanin shaawa ma shaa Allah.

Yanzu kam gida ne babba mai dauke da dakuna masu kyau ma shaa Allah, kowani daki na dauke da tiles lafiyyayye da katifa, dakuna hudu ne a gidan idan aka cire nasu umma da Abbah.


Sosai yanzu Abban ke tashen kudi.

****


Tun da ya dawo da Imamun daga school da ya fita  daga side din ,  tsaye ta yi a bakin kofar ta na jiran ta kai Imam din dakinsa tun da ya fara bacci, ta na ganin shigarta ta yi wuf ta shige ciki tare da zuba koren maganin a cikin bokitin da take taran ruwa, tun kafin ta fito daga dakin take jin motsin kamar kafar mutum a falonta na waje.

 Jin kamar za a bude kofa hakan ya sanya Sakinat saurin barin dakin jikinta na kyarma.
Koda ta fito ganin gilmawar mutum kawai ta yi , ba ta dauki abin serious ba ta wuce ta shige cikin bathroom dinta tare da fara taran ruwan, ganin wani koren abu a ciki kamar garsa kuka ma hakan bai hanata wankan ba.

Ta na futowa kam ta fara shirin baccinta ita ma dan Allah na gani wani kalar sarawa kanta yake, a haka dai ta daure ta yi kwanciyyarta tare da tofe kanta da addua.





 🥰🙌🏻
Like and share fi sabilillahi ❤️🥰🙏🏻




> IMAM ZAID ONLY ON PENDING AMARYA’S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY 🥰


~///Soft Noorah///~
  

> PENDING AMARYA😘 

> FARIDATOOL NOOR🥰🙌🏻

> THE ODOGWU WRITER ✍️ 


Your favorite troublemaker, Noor 😌