Bayan Murmushi

63

by @zahrabmrs02

63

A can ɗayan ɓangaren, Farhana tana kwance tana jiyo hayaniyar su a sama. Ba ta ji daɗin korar Hanadi ba, amma kuma zuciyarta ta riga ta yi mata nauyi da sharrin da aka wa mahaifiyarta. Ta san cewa wannan tafiyar ta su Yaya Ramla da Hanadi, shi ne farkon ƙarshen zaman lafiya a gidan nan.


A bangaren Farhana, rarrashi ne kawai take yi wa kanta. Fateeha da Precious sun yi kiran duniya zuwa ga Nusaiba, amma layin nata sai ringing yake yi ba a dauka ba. Fateeha ta zauna a gefen gado, idanunta cike da nadama.

"Allah sarki Nusaiba! Farhana, duk tare kuka ganmu da ita, amma Zainab tayi manipulating dinmu har na yarda ita ke miki zagon kasa .Allah ya isa tsakanina da zainab .Mun yi mata babban kuskure farhana ta fada muryar ta a sanyaye


A haka Fateeha ta fara hada kayanta domin komawa Kano, zuciyarta ba dadi. Kafin ta tafi, ta kalli Farhana ta ce, "Idan kin natsu, akwai magana mai mahimmanci da zamu yi. Amma yanzu ki huta."

Precious ma sai wajen yamma ta tafi. Farhana na ganin tafiyarsu, ta kalli Sameena. "Sameena, shirya yaran nan. Zamu tafi Lubge gidan Diddi." Ta ji cewa ba zata iya zama a gidan Asokoro ba yayin da zuciyarta take tafasa.


AK ya dawo gidan da yamma, ya samu gidan ya yi tsit tamkar babu rai. Ya nufi bangaren Farhana amma ya same shi a kulle. Nan take gabansa ya fadi, wani irin tsoro ya ziyarce shi. Allah yasa dai ba barin gidan nan tayi gaba daya ba, ya fada a ransa.

Cikin sauri ya jawo wayarsa ya kira ta. Bugu biyu ta dauka.

"Wifey... ina kike? Kin fita baki fada min ba," ya fada muryarsa na rawa.

Muryar Farhana ta zo masa a sanyaye amma akwai kwarin gwiwa a ciki. "Na tafi gidan Diddi ne. Jibi zamu dawo. Kuma tun yaushe na fara fada maka idan zan fita?"

Kafin ya ba ta amsa, ta kashe wayar. AK ya dafe kansa, ya san cewa lallai Farhana ta kai makura, kuma wannan tafiyar gidan Diddi ba ta hutu bace kawai.


Farhana na isa Lubge, ta samu Diddi tana zaune a falonta. Ganin Farhana da yara a wannan lokacin ya bai wa Diddi mamaki, kuma ganin yanayin fuskar diyarta, ta san akwai damuwa.

Bayan sun gaisa, Farhana ta kasa boye komai. Ta kwashe duk abin da ya faru na dambarwar Zainab (Zee) da Hanadi ta gaya wa Diddi. Ta fada mata yadda Zainab ta rinka amfani da sunan Diddi tana cewa wai tana wa AK asiri.

Diddi ta saki wani nishi, idanunta suka cika da kwalla. " Zainab dai Maryama? Yarinyar da na dauka kamar diyata? Allah ya kyauta. Amma karki damu, Allah ba zai taba barin mai gaskiya ya kaskanta ba."kiyi hakuri ni da tayiwa sharrin na barta da Allah.

Farhana ta lumshe ido tana jin kamshin gidan mahaifiyarta, tana tunanin yadda rayuwarta zata kasance daga nan. Ta riga ta gama yanke shawara a ranta, amma tana jiran lokacin da ya dace ne.


A can Asokoro, AK ya kekashe ƙasa, ya ƙi ɗaukar kiran su Yaya Ramla. Ganin haka ya sa suka kira Mummy, suka kwashe labari suka gaya mata—karya da gaskiya duk suka haɗa suka gaya mata. Mummy ba ta tsaya wata-wata ba ta taho Abuja. Ganin yadda Hanadi ta rame, Mummy ta ji ta ba ta tausayi sosai. Ta kalli Hanadi ta ce, "In dai ni na haifi Abdulkadir, zama Keda shi har abada Hanadi. Karki damu."

Mummy ta kira AK a waya, "Abdulkadir, yanzu zan ƙaraso gidan ka."

"Mummy, Farhana ba ta nan," Nima na fita AK ya ba ta amsa cikin girmamawa amma a sanyaye.

"Ka kira ta ta dawo yanzu-yanzu!" Mummy ta faɗa a takaice, wanda hakan ya nuna cewa ranta a ɓace yake.

Farhana kuwa, tana kan hanyar dawowa daga Lubge, ta tsaya a wani babban kanti (shopping mall) domin siyan madara da milo na tagwaye. Tana kusa da shelf ɗin kayan abinci, tana duba abubuwa, ashe Sister ɗin Farooq (Lamido) tana kusa da ita, amma Farhana ba ta lura da ita ba.

Lamido (Khalil), wanda tun asuba yake rigima saboda baya jin daɗi, yana zaune cikin kuryar siyayya (trolley) yana ta kiran Farhana.

"Ammi... Ammi..." muryarsa ƙarama mai sanyi tana tashi, yana miƙa mata hannu domin ta ɗauke shi. Farhana tana ta ƙoƙarin sauri ta kammala siyayyar don ta koma gida, ba ta san cewa wannan kiran da ɗanta yake yi, shi ne zai janyo hankalin wadda ba ta yi tsammanin gani ba.sameena na rike da sultana .


"Ammi!" Lamido ya sake kira, da muryar sa ta koyan magana wannan karon da ɗan ƙarfi har sai da Farhana ta juyo ta ɗauke shi tana rarrashinsa. "Yi haƙuri Lamido , mun kusa gamawa mu tafi gida kasha magani."

Matar gefen farhana ta juyo ta kalli farhana muryarta na rawa. "Farhana? Ke ce?"

Eh nice Ina yini ?

Lafiya Lou ,yaranki ne kenan ?naga kuna Kama 

Eh amma ban gane ki ba 

Oh my ,sunana safina yayar farooq Lamido does that ring a bell ?

Dirirricewa farhana tayi ,Tabbas farooq ya taba ce mata kawai yayarsa dake aure a abuja 

Uhmm ki gaishe da mamma sai Anjima Ana jiran farhana tayi saurin barin Wajan .

Bayan fitowar Farhana daga kanti, zuciyarta ba ta daina bugawa ba. Ganin Safina, yayar Farooq, ya sanya ta tuna dukkan alkawuran da suka rushe. Amma kalaman Safina na cewa "zan gaya masa kina gaishe shi duk da baki bukaci hakan ba" ya sanya Farhana jin wani iri, sai kawai ta fice ba tare da ta ce uffan ba, Sameena na biye da ita da yara.

Suna isa gidan Asokoro, Farhana ta iske babban falon ya cika. Su Mummy, su Yaya Ramla, da Hanadi dake gefe tana faman kukan karya. Sameena ta gaishe su cikin hanzari ta wuce bangaren Farhana, amma su Khalil (Lamido) suka nufi wurin AK suna murna, shi ma ya rungume su yana jin dadi a ransa.

Farhana ta samu wuri ta zauna, ta gaishe su sama-sama, muryarta ba dadi. Mummy ta gyara zama, ta fara magana cikin siffar dake nuna lallai ta goyi bayan Hanadi.

"Duk naji abin da ya faru, kuma wannan ba magana bace ta tada hankali. Itama Hanadi ai yaudararta aka yi, kawar Maryam ce ta yaudare ta. Duka-duka nawa hanadin take? Kuma kowa ya san mata ba abin da ba za su iya ba akan kishi. Don haka yanzu kowa ya yafe wa juna a bar maganar nan. Kai Abdulkadir, Hanadi ta koma dakinta, duk rintsi ai 'yar uwarka ce."

Mummy ta juyo kan Farhana da wani irin kallo. "Ke kuma Maryam, ya zame miki izina A Massachusetts ma labari ya same ni cewa da 'yan iskan Turawa masu 'tattoo' kike abota. Show me your friend and I will tell you who you are. Sannan ya zame miki dole ki girmama su Ramla; ranar birthday din 'yan biyu sun zo amma ko gaisuwar kirki baki masu ba."kuma har yanzu biki Kai yaran gidansu ramla ba 


Fadan ya koma kan Farhana gaba daya, tamkar ita ce ta yi laifi. Farhana ta numfasa, ta gyara zaman hijabinta, sannan ta kalli Mummy cikin ido, babu tsoro ko shakka.

"Mummy, duk na ji bayani," Farhana ta fara magana cikin natsuwa. "Amma maganar wai su twins su je gidan su Yaya Ramla, ko za a shekara dari ba zan taba kai su ba. Saboda tunda na haife su, ba wacce ta taba kira ta ji ya yara suke. Ko yanzu da muka shigo falon nan, waye cikinsu ya acknowledge dinsu (ya nuna ya san da su) banda babansu? Idan sun girma, su da kansu zasu kai kansu wurin 'yan uwan babansu su ga dangi, ba zan hana ba, amma ba yanzu ba."

Ta dan yi shiru, sannan ta kalli Hanadi da su Yaya Ramla da wani irin kallo na gatse. "Sannan, tunda an ce laifina ne sanadin haduwar Hanadi da Zainab, to na dauki laifin a kaina. Ina neman afuwar hakan."

Kalaman Farhana sun sauka tamkar ruwan sanyi a kan garwashin wuta. AK ya kalli Farhana, ya ga yadda ta dake, ya ji wani irin alfahari da ita, amma kuma ya san Mummy ba za ta ji dadin wannan martanin ba.


"To mara kunya!" Yaya Ramla ta daka wa Farhana tsawa, tana huci. "Rashin kunya zaki yi wa Mummy? Kuma yara dole su rabe mu wallahi, ko kina so ko ba kya so."

Farhana ta kalli Yaya Ramla cikin natsuwa, "Ba musu zan yi dake ba Yaya Ramla. Ni dai na fada miki, da kaina ba zan taba taka kafa ta na kai su ba."

"Eh, kar ki kawo su! Thank God muna da wasu yaran, gasu Kausar nan sun wadatar da mu," Yaya Ramla ta amsa cikin gadara.

Farhana ta dan yi murmushin takaici, "Eh, dama na san twins ba za su taba samun soyayyar ku ba. Amma inshaAllah zan ba su soyayyar da ba za su nema ta kowa ba a duniya."

AK, wanda ransa ya baci da jin yadda ake maganar yaransa, ya katse Yaya Ramla cikin kakkausar murya. "Gaskiya ni a daina nuna mini bambanci tsakanin yarana! Duk daya suke a wajena. Kuma duk wanda yake sona, dole ya so twins. Duk wanda baya son twins, wallahi baya son Abdulkadir!" Ya ja numfashi, sannan ya kalli Mummy. "Kuma Mummy, I am sorry to say, ba zan iya cigaba da zama da Hanadi ba."


Hayaniyar ta fara yawa, Farhana ta gane cewa zaman falon ba zai haifar da alheri ba, ta fara kokarin barin falon.

"To mara kunya! Mummy ta sallame ki ne da zaki tafi?" Yaya Ramla ta jefo mata magana. Farhana ba ta ce kala ba, ta cigaba da tafiyarta. "Yar masu asiri! Gashi aminiyar ki ta fallasa ku, asiri kuke yi, kin ji kunya!"

Farhana ta kara sauri ta karasa bangarenta (part), ta janyo kofarta ta rufe, tana jin bugun zuciyarta har cikin kunnenta.

A falon kuwa, Mummy ta mike cikin bacin rai. "Abdulkadir, ina da magana da kai!" Ta nufi bene. AK ya bi bayanta 


Mummy ta juyo ta kalli AK cikin ido, muryarta a dashe. "Wacece ni a wajenka?"

"Ke kika haife ni," AK ya ba ta amsa kansa a kasa.

"To ko bayan raina ka rabu da Hanadi, ban yafe maka ba! Ka tuna sirrinka dake hannuna!"

Wani irin daci AK ya ji ya turnuke shi. Ya dago kai, idanunsa sun yi jajur. "Wai Mummy, me yasa kike threatening dina da sirrin nan ne? Har yaushe zaki cigaba da min haka? Lokaci ya yi da duniya zata san meke faruwa! Mummy na gaji... this guilt (wannan nauyin zuciyar) na shekara goma sha biyar ya ishe ni!"

Hawaye ya fara zuba a idon AK, kuka ne na radadin abinda ya dade yana boyewa. Mummy ta zaro ido, ta matso kusa da shi ta rada masa, "Shiii! Keep your voice down! Da sirrin nan zamu lahira ni da kai Abdulkadir. Kar ka kuskura ka bar shi ya fito!"


A daya bangaren kuma, Farhana tana bedroom dinta, tana kuka amma idanunta sun bushe. Ta riga ta gama yanke shawara. "Ba zan cigaba da zama a haka ba. Dole na dauki mataki. Matakin da ba zai yi wa kowa dadi ba. Dole na rayu don yarana, ni kadai suke da shi. Nobody will see me coming."

Farhana ta dauko wayarta, ta fara duba jadawalin jiragen da zasu tafi Massachusetts. Ta san cewa barin gidan Asokoro shi ne kadai mafitarta.