PAGE 51-55
by @swrites22
A gurguje suka hau sama suka sake shiryawa cikin wani sequins material pink colour dinkin fitted gown komai iri daya banbancin kawai seena heel tasa ita kuma najwa plat shoe.
Suna fitowa Adnan yace inye kaga yan biyun nina sai kace wanda za muje gasar kyau, najwa tace to ya Adnan so kake mu fita harbatse² damu a dinga nuna mu da baki ana mana dariya , dariya yayi yace kunga muje karmu bata lokaci.
Seena na gaba wajen Mai zaman banza ta sake sai zuba surutu suke ita da Adnan najwa na taya su har suka isa wani babban wajen shan ice cream.
Adnan ya kalli seena tare da fadin "madam wanna wajen fa da yayanah ya dace kuzo harara ta galla masa ta wucewar ta ta barsu a baya , dariya yasa yace to ki jiramu mana ki Kayi gaba sai kinje kin bata kisa a tisa keyata ana tambayar ina na kai yar mutane, ko juyowa bata yi ba balle su sa ran zata tsaya din.
najwa ce ta matso kusa dashi tana fadin " ya Adnan ko kasan gwaramar da aka tafka dazu kuwa ?
" Ta mai Kenan " ya tambaya da neman Karin bayani
" hmmm lalle kuwa anyi ba Kai fada su kayi dazu ita da emir har ya mareta zaro Ido yayi yace
" whattt Mari kaman ya ?
" Kamar yadda kaji kuwa wai kawai d...... daga farko har karshe ta zayyane masa abinda ya faru tana mai kallon kofar shiga wajen
"ya Adnan dan Allah shiii karka nuna wa seenah ka san zancen plz .
Shuru yayi sai kuma can ta tsinkayo muryar sa na fadin "amma najwa bakya ganin daddy yayi kuskure wajen hada emir da seena anya abin nan za'aji ta dadi kuwa seenah seems innocent, and Emir appears kindhearted, but I'm puzzled by his behavior toward her da har zai mata hakan kamar dai akwai wani abu a kasa gsky.
" hmmmm ya adnan mu dai namu ey... shuru tayi saboda hango seenah da suka yi dan tuni sun shiga wurin joining dinta suka yi suma suka fara sayan abubuwan daya kawosu .
sosai suka yi shopping din kayan zaqi kamar ba gobe najwa ce tace " kunga mu zauna musha ice cream din a nan din kawai seenah tayi saurin cewa
" a a dai ki bari muje gida nan mutane sunyi yawa we won't feel comfortable Adnan yace haka ne fa idan mukaje gida sai ma kunfi jin dadi .
"shikenan toh muje din tunda kunce ba haka ba.
Suna Shiga mota Adnan ya kalli seenah yana fadin " sai ina kuma ? ummm ya Adnan inaga muje gidan aunty Faty da sauri najwa ma tace eh ya Adnan muje can, " to ya zaayi da kayan naku .
seenah tace abu dan sauki ba sai a barsua motar ba
"Tho ai ice cream din zaiyi melting
Najwa tace ai dama bada sanyin zamu sha ba
Okay dama asarar kudi Kuka sani tho ni dai idan na kaiku na ajje zan dan je wani waje tukunna a tare suka amsa da eh ba damuwa .
Ko da sukaje a tsaitsaye ya gaisa da aunty Fatyn ya musu sallama akan zaije ya dawo.
Aunty Faty tace kaman kuwa kunsan yanzu nake zancen Ku a zuciyata, najwa tace "sai kuma gamu munzo ko .
"whl ai tun jiya nake cewa Zan Kira nina inji ko zata barku kuzo ku tayani aiki yau birthdayn Adil Amma ina ta tunani ba lalle ta yarda kuzo Ku kwana ba daman nasan wanna umman ba barin su nafisa zatayi ba bare kuma daddy ya bar matar dan gaban goshin sa emir saisa ma ban kira ba sai kuma gashi Allah ya kawo ku a daidai.
najwa tace " toh ai aunty Faty ya sadam din ma yana gari jiya ma ya dawo .
" toh kin ji ba ai kaman nasani kice da na kira dana sami rabo na dan watakil cewa zaiyi ba Mai fitar masa da mata .
" Kai aunty Faty dan Yana nan kuma sai ya hanata fita .
" ke kuwa najwa in banda abinki Yana da mata kamar seenah sai ya dinga barin ta sakaka a gari ai irin su killace su ake.
sai a lokacin seena tace kefa aunty Fatyn nan sai ana magana ta hankali saiki kawo shirme ni har kinma ban haushi whl, pillow ta dauka ta wurgeta da shi tana fadin "ahh lalle ma yarinyar nan wato hirar mijin naki ne take baki haushi toh gsky ce dai sai an fada
mikewa tayi tana dariya tace Allah kuwa maganar taki ce ta kayan takaici ni wani aiki ne ya rage yanzun mu tayaki girgiza kai kawai tayi da fadin
" Zama kiyi bayani ne yarinya , abinda ba kuzo da wuri ba saida na gama aiki na cakes dinne kawai banyi decorating ba .
Najwa tace wai ina birthday boy din ne tunda muka shigo banji motsin sa ba .
"Yana wajen nanyn sa tana shiryashi yanzu muje mu karasa sauran abubuwan kunga magrip ta gabato gwara muyi mu kammala .
Veils dinsu suka cire suka ajje sannan suka shige kitchen din , cake biyu ne hakan yasa najwa Jan kujera tana fadin "ni bari na tayaku da hira, seena tace ai dama nan kika fi karfi Amma ana zuwa bangaren kitchen kice kin gaji.
kallonta aunty Faty tayi "aaa lalle yarinyar nan kin samu dama wato haka nina tasa maki ido kike zuba san jiki yadda kikeso ko shagwabe fuska tayi to aunty Faty nice autar ta fah.
"auto Mata ke baki san duk kyan mace da ji da kanta in bata a kitchen fanko ce saisa masu iya magana ke cewa girki adon mace , "hmmmm rabu da ita aunty faty bata da wayo ai bata san dabarun kama miji a hannu ba riqe baki najwa tayi tace "odahalfffff kece gabana ko spirit dinki sai kuma tayi dariya lalle kice idan yayana ya shigo hannu sai buzunsa dan Allah a dan sassauta masa kinji sis
bata fuska tayi kaman zatayi kuka tace aunty faty kin ganta ko .
" kema kika kulata tsokanar ki kawai take sonyi rabu da ita muci gaba da abinda ke gaban mu .
Cikin lokaci kankani suka gama decorating cake din sosai design din seenah ya birgesu har saida aunty faty ta kasa hakuri tayi magana " hala ni kam seenah nina ta saki makarantan da ake koyon decorating din cakes ne, dariya tayi tana fadin " a a wallahi kawai ni inason girki ne daga Kan abinci har su snacks especially irin su decorating cake ko kuma shirya abinci kinsan iya shirya abinci ma wani abu ne domin ko da abincin bai cika dadi ba yadda aka tsara zaman sa cikin plate din zai dauki hankalin Mai kallon zuwa ga cin sa , " gaskiya kin birgeni kuma kinyi kokari sosai, amma ya kamata ace yanzun ai kunada wayar kanku ku ma najwa tayi saurin chafewa da cewa " whl aunty faty abin dake cimin tuwo a kwarya kenan ace kamarmu wai bamu da waya dan Allah kisa baki daddy ya sayo mana waya.
" in sha allah ai ko dan seenah ma , yanzu shikenan in zatayi magana da mijin ta sai ace saita wayar Nina , ficewa daga kitchen din tayi tana jan dan karamin tsaki najwa tace kya sani dai ana so ana kaiwa kasuwa .
Fitowa sukayi daga kitchen din aunty faty tace seenah tashi muje muyi sallah sai muzo mu karasa sauran abubuwan .
"ai aunty faty je kiyi sallarki kawai mukam red car tayi parking najwa ta fada tana yin hanyar corridor dinda zai kaita bedrooms .
balloons ta dauko ta mikawa seenan tana fadin "ku hura wa'anna keda najwa ni barin je inyi sallah nayi wanka kafin Ku gama , najwa ce ta dawo parlourn dauke da yaron wanda ba zai wuce 4years ba, aunty faty tace yauwa zo ki taya ta ku gama kafin na fito .
Zama sukayi suka shiga hura balloons a mijin aunty fatyn ya shigo da sallama wasu yan Mata biyu na biye dashi dayar baza tafi 15yrs ba dayar kuma 17 ko 18 Kana ganinsu kasan kannensa ne saboda kamar da suke .
gaishesa sukayi ya amsa da fara'a Yana fadin " yau kuma manyan baki ne damu Kenan najwa sai yau aka tuna damu ko ?
" Ah ah ya Ibrahim whl ba haka bane kasan lamarin school yau ma dai mun fito shine mukace bari muzo mu gaishe ku .
"gasky kam kun kyauta shi zuminci ai sai an daure dan ma yanzu akwai waya ana gaisawa in ba haka ba kafin a hadu sai a jima abubuwan da yawa ya karashe yana daukan Adil dake ta miko masa hannu alamar ya dauke shi, ina auntyn taku ne ?
" tana wanka najwa ta bashi amsa.
"ohk juyawa yayi wajen kannen nasa yace yusra ku zauna kafin ta fito nima barin shiga daga ciki in shirya.
Hira ce ta barke a tsakanin surayya dasu seenah ita dai yusra latse² ta take a waya sai in sunyi abin dariya ta dara har su aunty Fatyn suka shigo parlourn cikin shiga ta alfarma ita da mijin nata dake dauke da Adil din a hannu , su yusra ne suka shiga gaisheta ta amsa tana kallon su najwa tace " ya baku jera komai ba kuma ai sai Ku tashi, mikewa sukayi harda surayya seenah na fadin kefa muke jira ki fito hajiyata .
Dauko cakes din da snacks sukayi suka kawo Kan centre table dinda suka daddaura balloons a jiki suka jera .
Tashi sukayi suka karasa jikin table din su najwa na tafi da wakar happy birthday su yusra kuma na video, Adnan ne ya shigo da sallama " Ku tsaya² a jirani ya fada Yana shigowa da dan gudu dariya ya Ibrahim yayi "wato Kai dai Adnan baza Ka fasa halin nan naka bako, dariya shima Adnan din yayi yace "to ai naga ana kokarin yi bani ne to yanzu dai a yanka girgiza Kai aunty faty tayi tace "Allah ya shiryeka ya amsa da ameen yana dariya .
matsawa seenah tayi kusa dashi tace "ya Adnan ban wayarka kallon ta yayi tare da fadin "Mai zakiyi da waya ta , dan rage murya tayi "dan Allah ni Ka bani video zanyi sharp² ciro wayar yayi daga aljihunsa ya Mika Mata Yana fadin sauran ki min shige² kuma dan kika bata min waya whl sai mijinki ya biya , " eh naji dai.
Sosai sukayi pictures da videos gaba dayan su, sannan aka zauna ciye², seena tace yusra dan turomin pics din wajen ki mana ?
"ohk bani number taki ?
"bani da waya but bayin baki number yayana sai ki tuyamin ta ciki kallon ta tayi tana yar dariya ta mika Mata hannu alamar ta bata wayar .
Mika Mata tayi tana dan hararar ta kasa² tace "what's funny ganin tana neman manna Mata hauka.
dariya sosai yusran tayi sannan tace "I'm sorry dear but your accent is hilarious and fun to listen to shuru seenan tayi ita kuma ta fara saka number ta a wayar adnan tayi flashing sannan tayi saving da sunan da taji su seenan na fada ta shiga WhatsApp tai mata sending sannan ta mika Mata wayar , "thank you ta fada tana tashi daga kujerar da yusran ke Kai "my pleasure Kanwata har tayi gaba ta juyo ta sake kallon ta jin sunan data kirata dashi, murmushi yusran tai Mata ganin karta gwaleta ya sata yi Mata murmushin back dukda ta dan bata haushi dariyar data Mata da farko .
Sai wajen 9:30pm sukayi wa su aunty fatiman sallama suka tafi shima dan Nina ta damu da Kira ne akan su dawo gida dare yayi hakan yasa suka tashi badan sunso ba .
A motar ma hira suka ringayi har suka isa gida ko tsaya debo ledojin basuyi ba suka fara tseren Wanda zai riga wani shiga gidan suka bar Adnan da dakon ledoji😂 .
Duk mutanan gidan suna parlour zaune suna hira , kamar wasu aljanu suka fado parlourn seena na gaba aikuwa najwa ganin seenah ta rigata shiga yasa ta fara kokarin kamota ita kuma tace bata isa ba parlourn suka fara zagayewa suyi dinning su dawo parlour sai dariya suke da alama ma basu lura da akwai mutane a parlourn ba .
Tsawar da sadam ya daka masu yasa su tsayawa cak cike da firgici domin sunji tsawar ne kamar daga sama, "ku mahaukatan inane daza ku shigowa mutane gida babu sallama kuma kun shigo kuna wa mutane ihu a ka, shigowar Adnan dauke da ledojin shopping dinda suka yi yasa shi maida dubansa gareshi Yana fadin " kai kuma daga gidan uban wa ka dauko wa'anna mahaukatan , murmushi Adnan din yayi ba tare da yace komai ba ya karasa cikin parlourn ya ajje ledojin ya zauna tare da fadin "daga gidan Fatima muke.
Tsakiyar parlourn najwa ta dawo tana riqe da kunnenta tace I'm so sorry yayanah ba zamu Kara ba ko kallonta baiyi ba nafisa kuwa tsaki tadan ja kasa² dan tasan in ya jita zai iya mangareta a wajen dan tsaki na daga cikin abinda ya tsana.
Nina tace kinga wuce ki zauna, Kai kuma haka akeyi kawai saika hau ihu zaka firgita min yara ba gaira ba dalili ta dubi najwa ina baby?
"Ta shiga kitchen ta sha ruwa ta fada tana zama kusa da adnan.
Sosai tsawar da sadam yayi ta tsorata seenah dan har saida ta runtse idon ta hakan yasa tayi saurin shigewa kitchen saida taji ta dawo nutsuwar ta sannan ta dauki ruwa ta sha jin kiran Nina ya sata fita daga kitchen din, yayin da ko wane sautin takalmin ta yake daidai da bugun zuciyar sadam har ya ja idanun sa zuwa gareta tun daga kafarta har fuskar ta yake kallo Wanda in ba nutsuwa Kayi ba baza ka taba gane direction din da yake kallo ba.
seenah badai iya tafiya ba saisa take san high heel domin Yana karawa tafiyar tata armashi , maganar ta ta dawo dashi hankalin sa lumshe Idon sa yayi tare da yiwa kansa tambayar da bashi da amsar ta what's wrong with me .
Seenah kuwa cikin murmushi tayi wa daddy da Nina sannu da hutawa sannan ta kalli umma dake aika Mata da harara kasa² wadda ita kadaice ta lura da hakan saboda tunda ta shigo idonta na kanta "hajiya baika da wai haka cikin jin haushin sunan data kirata dashi Wanda ya kasance sadam ne kawai ke Kiran ta da hakan dukda baso take ba dan kawai ba yadda zatayi dashi ne bata amsa ta ba sai kwafa da taja .
Dariya nafisa ta tuntsire da ita cikin shekiyanci tace hajiya baika da waihaka waiii sunan wani abu kacakaura , biting lips seenah ta shigayi dan iya kulewa ta kule dama ga haushin sadam da take ji tashi tayi ta dauki wasu daga cikin ledojin tana fadin naj in zaki shigo ki taho da sauran nina daddy good night.
"ba dai har zaki shiga bacci ba daddy ya fada Yana tsare ta da Ido ganin kamar ranta a bace, murmushi tayi tace " a a daddy zan shiga in huta ne nagaji dayawa mun sha aiki.
" okay yar Albarka Allah ya tashemu lpy ta amsa da ameen tana saka takalmin ta najwa tace odahalf Nima gani nan shigowa yanzu
" saikin shigo kawai tace tana yin gaba saida tazo daidai da nafisa tasa takalmin ta ta take mata yatsun kafa cikin tsananin zafi nafisa ta figota saura kadan takai kasa aikuwa saijin Mari tayi Tass ba shiri ta saki seenan ta dago da sauri dan ganin waye ya mareta, ita kuwa seena kujera ta dafe ta Mike tsaye.
Sadam da akan idon sa seenah ta take kafar nafisa yasa shi daka Mata tsawa" keee wai wace irin yarinya ce .
" Mai haka kake yi ne emir daddy ya fada cikin fada, kasa yayi da kansa yace "ya hakuri daddy amma gani nayi hakan bai dace ba ai ba sa'ar ta bace da zata mareta.
" toh Kai baka gani ba ai ita ta fara tsokanar ta Mai ruwan ta da ita kuma yarinyar nan ta tashi zata tafi ta janyota dan neman magana (Dan sufa su daddy ba wanda ya lura cewa seenah taka nafisa tayi), yanzu data fadi fa ai ba karamin ciwo za taji ba , kuma ita nafisan da tana jan girman ta ai da hakan baza ta faru ba duk babban da baiji kunyar hawa jaki ba shima jaki ba zaiji kunyar kayar dashi ba.
Itadai seenah kayanta ta tattara tayi gaba saida tazo daidai kujerar da sadam ke zaune taja wani matsiyacin tsaki " cikin zafin nama shima ya finciko ta da niyyar kifa Mata Mari takalmin ta ya goce ta fado jikin sa tare da sa ihu ta cukuikuye shi jin wata azaba a kafar ta , kamar an kawo wuta an dauke haka sadam yaji wani dif ya kasa motsa ko da dan yatsansa ne sai Ido daya zuba Mata.
tsawa ninah ta daka masa "wai meye hakane emir kalau kake kuwa yaushe Ka koyi mugunta haka whl karka bari musa kafar wando daya da Kai, tashi zo nan baby seenah menene cikin muryar kuka ta sake langwabewa " ninah kafana² ya kayye wayyo shikenan ya kayyani.
cikin masifa itama umma tace "Allah ya Kara bake marar kunya ba ai emir dinne daidai dake maganin mai rawar Kai Kenan... taci gaba da surfa masifar ta .
Tashi daddy yayi dan yasan tunda aka taba yar gaban goshin ta yau sai abinda Allah yayi kuma gwara ya tashi tun kafin ta fadi abinda bazai iya hakuri ba su raba abin kunya a gaban Yara kallon sadam yayi Wanda ya Zama kaman mutum mutumi a wajen yace " wanna shine adalcin daza Kayi a tsakanin kannen naka ko toh hakan yama kyau kaji kaci gaba kaji Allah ya baka saa, amma ina san gaya ma ka kiyayeni akan seenah zan iya saba ma ya karashe da muryar dake nuna tsananin bacin ran da yake ciki.
tashi itama Nina tayi ta kalleshi tare da fadin " idan Ka karya min ya to kaima kashirya karyewa tana gama fada tabi bayan daddy , ninah!!!!! Ya kirata amma ko juyowa bata yi ba maida duban sa yayi ga seenah dake ta sharbar kuka a jikinsa.
cikin fusata yace dan ubanki tashi a jikina kafin na karasa balla kafar
"cikin kukan tace whl baza a tashin ba kuma whl Ka karya min kafa kaima taka kafar baza ta taka ba .
Kallon umma dake ta masifa yayi cike da gajiya da maganganun nata yace wai hajiya Mai hakane wanna abin ai duk kansu ne masu laifi ba mutum daya ba kuma shi daddy da Nina miye nasu a ciki
cikin hasala itama ta koma kansa "Kai dalla yi min shuru sha³ har Kana da bakin magana lusari ma irinka Wanda aka yiwa ''AURAN DOLE littafin mufeedah muazu'' Kana namiji Amma Ka zuba Ido Kayi shuru murmushi yayi yace aure na ba auran dole bane "AURAN HADI by Samira harouna" ne kuma bani da ja da abinda mahaifina yayi dan haka ki daina kunfar baki a kaina kiji da matsalar ki ma.
Fuuuuu ta tashi ta wuce bangaren ta tana ta masifa kamar ta ari baki .
Hade fuska yayi kamar hadarin gabas ya maida kallon sa ga seenah tare da sake daka Mata tsawa hade da daga hannu kamar zai maketa " tashi a jikina nace ko
sake riqoshi tayi tare da cusa fuskarta a kirjinsa gudun karya mareta tace "nace baza a tashin ba mugu azzalimi kuma Allah saiya sakamin wayyo hajjo kafana, sakin baki yayi Yana kallon ikon Allah Adnan ne ya taso ya matso kusa dasu tare da kama kafar seenan wadda ta gurde, ihu tayi tare da janye kafar da sauri ba shiri sadam ya toshe kunnen sa dan ji yayi har yan cikin kunnen sa saida suka motsa kallon Adnan din yayi yace
" rabu da ita adnan jeka kawai karka damu zanyi maganin ta .
Tashi yayi Yana murmushi ya dauki abubuwan sa ya wuce side din su .
wani kallo ya aikawa su nafisan ba shiri ko wacce ta kama gaban ta ganin haka yasa najwa ma daukan ledojin nasu duka ba tare da tayi magana ba ta sulale tabar parlourn ya rage daga sadam sai seenah.
Kee ? Shuru tayi kamar bada ita yake ba sai kukan ta take a hankali keeee!!!ya sake kiranta shuru har temper sa ta fara hawa seenah ya Kira ta a dan masife.
dagowa tayi ganin parlourn ba kowa yasa ta fara kokarin guduwa tana ci gaba da kukanta , rikota yayi ta juyo a fusace "ni ka sakeni mugu kawai Allah ya isana "faf ya bige Mata baki yana riqo kafar daidai idan sawu inda taji ciwon, wata zabura tayi ta rirriqe hannun sa tana fadin na tuba whl dan Allah Kayi hakuri wayyo nina kafana , sake kafar yayi Yana bin hannuwan nata da kallo da sauri ta sake shi tana kokarin sake tashi daga jikin sa cikin hade rai yayi yace zauna ba musu ta koma ta zauna tana share hawaye .
Shammatar ta yayi kawai ya murda kafar tayi Kara yarfa hannun ta fara tana zaro Ido kamar wadda zata suma saboda wata irin azaba da taji kafar nayi Mata kafin ta saki wani marayan kuka .
Dan karamin tsaki yaja Yana mikewa tareda Ita a jikinsa ya nufi part din Nina.
Har dakin su ya kaita ya sauke ta bakin gado ya juya ya fara tafiya ba tare daya Mata magana ba , najwa ce ta fito daga bathroom alamar wanka tayi kamar Wanda akewa dole yace kije ki shafa Mata menthol , ba tare daya jira amsar taba ya fice a dakin da kallo ta bishi kafin ta maida Idon ta Kan seenah dake kwance tana kuka ta shiga jera Mata sannu kafin ta dauko menthol din tazo ta shafa matan .
Washe gari kuwa garau ta tashi kafar ba wani ciwo sosai sai dan abinda ba'a rasa ba.
Sosai aka fara wasan buya tsakanin seenah da sadam duk Inda tasan zasu hadu bata zuwa wajen ko dinner za'ayi saita tsuro da wani abu tasa akawo Mata daki ko kuma in sun gama taje taci, ko clashing sukayi data ganshi za tayi saurin boyewa haka har sukayi resuming scul taci gaba da al'amuranta tare da maida hankali Kan karatun ta kasancewar wanna exam din third term promotional exam ne dukda kuwa a results din second term ma first position ta dauko najwa kuma third position, sosai daddy yayi farin ciki harya shirya yi musu surprise na gift .
Nina kuwa tana lura da take taken seena dan tasan kwanan zancen saboda tun washe garin abinda ya faru ta tsiri hakan saisa ta sami daddy da maganar shi kuma ya bukaci su zuba masu idon suga iya gudun ruwansu.
Sadam kuwa duk wani motsin seenah akan idon sa yake duk buyar da take idan ta ganshi yana sane da ita kawai ya share tane saboda bashi da lokacin ta.