Chapter 02
by @teemerheart
Cikin shirin ta na Islamiyya ta fito hannun ta rike da jakan ta.
“ Hajiya kaka ni zan wuce ki min addua”
“ ban gane zaki wuce ba,azumi ki keyi da baza ki ci abinci bah”
“Aaa nifa na koshi ne sae na dawo Kawae zanci”
“ Ban yadda da ba a Ina kika ga ake karatu da yunwa ae shima kanshi karatun baya shiga sae in ciki a cike yake,maza je ki dibi ko kadan ne ciki sae ki tafi.Allah dai ya miki albarka ya baki miji na gari Wanda yake son sosai” a kullum Wannan shi adduan Hajiya kaka da kuma fatan ta Asmirah ta samu miji nagari kuma mai kaunar ta.
Da to ta amsa ta wuce kitchen don cika umarinin hajiya kaka bawai don ranta yana so ba Kawae dae tana gudun fadan Aunty ne don tasan tana kara magana tasan mai zai biyu bayan.
“Hajiya kaka da jikar ta, ni da na dauka rashi son cin abincin Asmirah iya shege ne amma yanzu nake tabba tarwa haka Allah yayi ta ba mai son cin abinci bane”Maman Haidar tafa
Budar bakin Aunty tace kune kuke biye mata ae ita yunwa ba kanwar uban kowa bace da kanta in ta fara ganin biyu biyu zata nemi hanya kitchen.
A gaskiyar magana bawai Aunty bata son Asmirah bane aa sae dai tana yin kawaici ne saboda son da Hajiya kaka take nuna ma Asmirah kar abin yayi yawa yarinyar ta lalace duk dama dai Hajiya kaka tana yin Iya baki kokarin ta wajen bata tarbiya sai dai kun san soyyayar kaka da jika kauna ce ta daban.
Aunty Macece mai saukin Kai sannan kuma tana da riko da addini sosae bata da hayaniya sam maman Haidar da Aunty zulaihat ma sun fita surutu sosae ba laifi.Aunty tana da yara guda uku wanda ta Haifa a gidan da take Aure yanzu ummikulsum,halifa da kuma Adam.Aunty tana Iya kokarin ta wajen kula da Hajiya kaka tun da acikin yan uwan ta mata ita kadai ce take aiki duk yan uwan ta maza Suna da hali amma hakan bai sa da gaza waje kyauta tawa mahaifiyar ta bah sannan ita take biya wa Asmirah school fees ita take daukar nauyin yar ta Wanda hakan yasa Hajiya kaka kusan kullum sai tayi fada ga yan Uwanta sunce zasu dauki nauyin karatun Asmirah amma taki ita kuma tace to Hajiya meye amfanin aikin nawa ke dae Kawae ki ci gaba damın addua.sannan Aunty tana kyauta tawa yan uwan ta maza da mata da Iya abinda Allah ya hore mata.A Gaskiya Aunty jarumar mata ce ba laifi tana yin Iya bakın kokarin ta wanje zumunci sai dai kash babban matsalan su shine matan yayan su maza Suna da girman Kai kowa tana ji da kanta wanna abin yana damun Aunty ba kadan bah.
“Hajiya kaka na gama cin abinci,Aunty sai na dawo.Aunty Yaushe su Haseena dasu Ummi zasu zo mana”
“Sai Anyi Hutu Daughter,Allah ya bada sa’a”Maman Sadeeq ta Fada tana murmushi
Cikin nutsuwa take tafiya har ta isa kofar Islamiyyar su da yake ba wani nisa tsakanin gidan su da makaranta.ta shiga aji ta tarar da Malam Garba wato malamin su na Qur’an yana kar ban hadda,zama tayi ba a dade ba ko a ka zo akan ta ta bada nata haddan sannan yayi musu Kari.Sun fita alwalar sallan la’asar ne Asmirah tace
“Hajara kin San yau ban dauka zan iya bada haddan nan bah”
“Mai yasa keka ce haka “
Hajara ta fada tana duban ta
“Ki bari Kawae kwana biyun nan bacci na nake sha da dare bana wani Karatu sosae”
Rabi ce ta kwashe da Dariya tana fadi
“Na dauka zaki ce mana an bada ke mu fara shirin biki”
“Lalle kam to ni din duka duka nawa nake a sss 2 fa nake tab”
Hajara tace “Sss 2 din fa kinga Kina gamawa sai Aure”
“ Eh mana “Rabi ta Fada tana Dariya
“Kunga malamai in Kun gama surutun na ku ku same ni a aji”
Duk da gatan da Asmirah take samu daga gurin Hajiya kaka hakan bai sa ta lala ce bah sannan kuma tana da wayo sosai ba laifi sai dai fa matsalan ta daya Asmirah bata iya girki bah.
Haka Rayuwa ta ciki gama da tafiya a kwana a tashe ba wuya a gurin Allah.Asmirah ta ci gaba da samu kulawa daga gurin Hajiya kaka da Auntyn ta yanzu haka suna Sss 3 sune masuyin candy bana sai dai babban damuwan Asmirah shine rashin lafiyan Hajiya kaka.Shekaru ba karya bane yanzu Hajiya kaka yau da lafiya gobe babu hawan jini ne yake damun ta su Aunty ne suke zuwa su kula da ita ta sunayin duty duty ne a tsakanin su saboda Asmirah tayi yarinya baza ta Iya kula da ita ba amma duk da haka ita ma tana yin Iya bakin kokarin ta wajen kula da kakar ta.
A Safiyar litinin ne ciwo Hajiya kaka yayi tsanani sosae wanda Haka yasa su Aunty da yaya bukar suka kai ta asibiti a ka basu gado sannan likita yayi mata allurai ta samu bacci.Idan kaga su Aunty sai ka tausaya musu don gaba dayan su hankalin su a tashe yake su yaya Muhammad ma da yaya umar suna hanya yau. Zuwa la’asar Hajiya kaka ta tashi daga bacci Maman Haidar ne da yaya bukar a gurin ta a lokacin Aunty da maman Sadeeq sunje yin sallah.abinda Hajiya kaka ta fara tambaya shine Asmirah yaya bukar ne yace
“Sannu Hajiya yanzu ya kike jin jikin naki”
“Da sauki Alhamdulillah”
“Ina zainabu tako ci abinci don na Santa haka Kawae ma sai da ki cin abinci bale yanzu kuma ga dalili”Hajiya kaka ta sake fada
“Eh Hajiya taci yanzu ma Haka sunje yin sallah ne ita dasu Aunty”maman Haidar ta Bawa Hajiya kaka amsa
Hajiya kaka ta samu tayi sallah a zaune daya ke jikin nata ba wani karfi sosai.
Cikin farin ciki Asmirah ta isa gaban Hajiya kaka”Masha Allah Hajiya kaka ya jikin naki Sannun kin cin abinci “duka ta fada a lokaci daya
“Wanne to zan fara amsa miki yar jikalle”
“Duka mana Hajiya kaka,hankalin gaba daya ya tashi wallahi bana so ki tafi ki barni “ta fada kaman zatayi kuka
“Ikon Allah to ba gashi naji sauki ba,insha Allahu sai naga Auren ki,kiye ta min addua kinji”
“Allah ya Kara miki lafiya Hajiya kaka ta”Asmirah ta fada cikin farin ciki
Da Ameen suka amsa gaba dayan su
Doctor ne yazo ya sake duba ta ya rubuta mata magunguna sannan ya basu sallama saboda Hajiya kaka ta matsa sosae akan su tafi gida.