SARTSE A ZUCI...!

SARTSE A ZUCI....! Chapter 21

by @ayshadansabo

*SARTSE A ZUCI...!💔* *Arewabook@ayshadansabo*

*Paid book ****

©️ _Ayshat Ɗansabo Lemu_ ✍🏻

*Chapter 21*

Kwanakin da suka biyo baya duka a jihar Port Harcourt ɗin Hameedah ta dage tana iyakar bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta faranta ran Yaya Zayd ɗin,soyayya da tarairaya sosai yake nuna mata domin sake haƙurƙurtar da zuciyarta.Maryama tayi nacin kiran ta aiko masa saƙon ban haƙuri akan irin shariyar da yake nuna mata har a wajen aiki amma Zayd yayi biris da ita ya kuma yi blocking duka line's ɗinta da take aiko masa saƙonni dasu,da gaske so yake ya nisancesu daga ita har Najwan data aiko masa saƙon cewa aurenta saura wata guda.Kuma a lokacin da saƙon ya riskesa sai yaji tamkar ya fita farin ciki da jin hakan,ita kuma Maryama ta kasa haƙuri domin tunda ta ɗanɗani zumarsa ya gama gigita tunaninta ya sake jefa zazzafar ƙauna da sha'awar sake son kasancewa dashi kota wani hali.Hakan yasa a wani yammaci da ya kama ranar Friday ta shawo wanka ta sake biyoshi har gida ba tare da ta san cewa ya ɗakko matarsa ya dawo da ita kusa dashi ba,koda ta isa gidan nasa kuma sabon mai gadin daya ɗauka ne ya fara tsareta da tambayoyi domin sharaɗin aikinsa ne duk wanda yazo gidan kada ya buɗe masa gate ya shiga saida izininsa tunda yasan cewa Hameedah bata san kowa a garin ba,don haka data matsa sai kawai yayi kiran layin Zayd ya sanar dashi cewa yana da baƙuwa gata a wajen gate ɗin gidan.A lokacin suna zaune tare da Hameedah tana manne a jikinsa tana shayar da Abdallah shi kuma yana wasa da gashin kanta daya sha gyara domin a jiya ya kaita wani saloon akai mata gyaran kai har ma dana jiki,tunda Tunde ya sanar dashi cewa yana da baƙuwa sunan Maryama ya haska a cikin kansa domin itace kaɗai yasan cewa tasan gidansa a kaf ƴan office ɗinsu da za su iya nemansa kosu nemi zuwa gidansa.Don haka zuciyarsa a ɓace ya baiwa mai gadi Umurnin cewa kada ta shigo,kuma ga tsananin mamakinsa yana sauke wayar Hameedah ta ɗaga kanta tare da tsaresa da idanunta dake da tasiri a kansa ta tambayeshi wace ce baƙuwar da yake bada umurnin kada a barta ta shigo?Yaya Zayd ɗin bai iya ɓoye mata komi ba domin yasan ta riga taji komi a cikin wayar sabida kusancinsu da juna,sai kawai ta sanar da ita cewa Maryama ce.Kuma abinda bai taɓa kawowa zai faru bane ya faru domin nan take Hameedah tace dashi ya kira mai gadin yace masa a barta ta shigo,kuma daga yanayin kallon da take masa da yadda ta saki fuskarta sai ya kasa gane a wani yanayi zuciyarta ke ciki.Lokacin da Maryama ta shigo ta iso har bakin ƙofar falon nasu ta danna door bell Hameedah ce da kanta taje ta buɗe mata ta kuma bata hanya domin ta shiga daga ciki,Maryama na shiga cikin falon ta hango Zayd hakimce a cikin kujera yana riƙe da ɗansa Abdallah a hannunsa.Cikin tsananin mamaki da shiga ruɗu Maryama ke ƙarewa kyawun Hameedah kallo tana raina kanta da haɗuwarta domin hatta shigar dake jikin Hameedah a lokacin ba ƙaramin kaɗa zuciyarta yayi ba,domin tana sanye cikin English wear's ne masu azabar tsada da suka fidda surarta matuƙa da gaske.Kuma daga yanayin azababben ƙamshin dake fita a jikin Hameedah dake dukan hancinta,da kuma sauyin ƙamshin data ji a cikin falon baki ɗaya sai taji ta sake rasa nutsuwarta.Sannan halin ko inkulan da Zayd Abdallah ya nuna mata sai ya sake susuta zuciyarta,domin nunawa yayi tamkar ma bai santa ba.Hameedar ce ta zauna suka gaisa ba tare da itama kanta ta nuna mata tasan ita wace ce ba take tambayar Maryaman wajen wa tazo? Kuma duk rashin kunya da bariki da buɗewar idanu irin na Maryama sai taji kwarjinin Hameedah ya daki zuciyarta har ta rasa yadda za a yi ta iya sanar da Hameedah cewa wajen mijinta tazo.Sai ta mayar da dubanta ga inda Zayd ke zaune riƙe da Abdallah wanda kyawunsa da kalar skin ɗinsa ya gama tafiya da zuciyar Maryama,ta shiga tambayar kanta cewa dama ya haihu yana da ɗa? Domin bai taɓa bata dama sunyi hirar matarsa ba bare har ya sanar da ita cewa ya haihu.Ganin yadda ta rasa nutsuwarta ya sanya Hameedah haɗiye ɗacin kishin dake sake turnuƙe zuciyarta ta fara zazzagawa Maryama nasiha akan taji tsoron Allah ta rabu mata da mijinta,daga Maryama har Zayd kalaman Hameedah suka daki zuciyarsu lokacin da take faɗin,"Kiji tsoron Allah Maryam kisani cewa idan kin cigaba da bibiyar Zayd kuna aikata saɓon Allah ba za a taɓa raba zunubinku tare da ni ba,domin nina san ban rageshi da komi ba,illar da za ku yi mini kawai shine ku ƙuntata zuciyata da rayuwata baki ɗaya ta yadda ko ance zan iya kamuwa da hawan jini bazan yi musu ba,domin duk yadda kike jin kina sonsa kina ƙaunarsa da kuma sha'awarsa na fiki jin hakan domin ni da soyayyarsa na rayu a cikin zuciyata kuma da ita a zare numfashina,don haka idan baki rabu dashi ba tabbas za ki ƙuntata mini don haka ina roƙonki ki rabu dashi idan kuma aurenki zai yi bazan hana ba,Zayd kana sonta za ka iya aurenta?" Wannan tambayar da tayi ne yayi masifar tashin kan Zayd da Maryama har suka ji saukar sautin a cikin kunnuwarsu tamkar saukar tsawar dake neman tarwatsa kwanyarsu baki ɗaya.Zayd ya dubi fuskar Hameedah yana hango zallar soyyarsa da kishinsa da bazai misaltu ba a cikin ƙwayar idanunta,wani irin tausayinta ya lulluɓe zuciyarsa har baisan time ɗin daya tashi daga mazauninsa ya isa nata ya sanya hannunsa guda ya rungumota ya haɗa da Abdallah dake ɗaya hannunsa ya rungumesu baki ɗayansu yana ji tamkar ya tsaga ƙirjinsa ya sanyasu ciki.Kuma Yaya Zayd ɗin bai kaiga iya buɗe bakinsa yace komi ba suka jiyo muryar Maryama daga can bakin ƙofar fita tana musu sallama,sai suka ɗaga kawunansu tare da aje ganinsu akan bayanta Hameedah ta ɗaga sautin muryarta wajen faɗin,"Ki sauka lafiya Maryam,idan har nayi magana da mijina ya sanar dani cewa zai iya aurenki zanyi maraba dake a cikin rayuwarmu,amma don Allah ki daina bibiyarsa ta haramtacciyar hanya."Waɗannan kalaman sune na ƙarshe da kunnuwar Maryama suka saurara daga bakin Hameedah suka kuma kimsa wani irin firgici da ruɗani a cikin duniyarta baki ɗaya,domin ji tayi kamar bata taɓa jin tausayin wata halitta kamar yadda tausayin Hameedah ya lulluɓe zuciyarta ba.Har ta isa bakin gate ta fice ta shiga motarta ta tayar kalaman Hameedah take bita tana kuma hango sanyi da magiya a saman fuskarta da muryarta baki ɗaya,jikinta yayi sanyi ƙalau tana ayyana da itace a matsayin Hameedah wata mace ta biyo mijinta har gidan aurensa bata san wani kalar mataki za ta iya ɗauka a kansu ba.Haka ta tashi motar tana baiwa kanta shawarar taji roƙon da Hameedah tayi mata ta rabu mata da mijinta,wani sashi kuma na zuciyarta na sake ƙawata mata irin daɗi da nishaɗin data ji a lokacin da sukai tarayya da Zayd ɗin.Saita rasa yadda za ta yi ta tsaida zuciyarta waje guda,duk da cewa ɓangaren dake mata faɗan taji tausayin baiwar Allahn da take roƙonta tabar mata mijin aurenta cikin sanyi da magiya bada faɗa ko nuna isar cewa mijinta nata ne ita kaɗai ba.Haka ta dinga saƙa da warwara har ta koma gida tana sake bitar kalaman Hameedah ne a cikin kanta,kuma daga ƙarshe sai taji zuciyarta tafi aminta data ƙyale Zayd ɗin ta fita a harkarsa idan har ba shine ya sake nemanta ba ba za ta sake bibiyarsa ba kamar yadda matarsa ta roƙeta alfarma.A can gidan Zayd Abdallah kuwa sai ya rasa inda zai kai Hameedah da soyayyarta a cikin zuciyarsa bayan tafiyar Maryama,ya cigaba da rungumarta a jikinsa yana jiyo yadda take tambayarsa kozai iya auren Maryama?Hannuwansa kawai ya iya kaiwa ya rufe bakinta kafin bakinsa ya buɗe a hankali yana mai kaishi kusa da kunninta guda ya raɗa mata cewa kada ta sake yi masa wannan tambayar domin bashi da amsar da zai bata sabida bai taɓa ji a cikin zuciyarsa cewa zai iya rayuwa da mace fiye da ɗaya ba.Kuma sai maganar da Hameedah ta faɗi masa bayan ya furta kalamansa sukai masifar girgiza zuciyarsa domin cewa tayi,"Ko baka ƙara aure ina raye ba Yaya Zayd lokaci zai zo da za ka sake rayuwa da wata macen da za ku rayu tare da ita bayan Hameedah tabar muku duniyar,domin ina ji a jikina kamar ni zan rigaka mutuwa." Kalmar mutuwar yayi tsawa a tsakar kansa kalaman kuma sukai masifar tsaya masa a zuci tare da jefa firgici mai yawa a cikin zuciyarsa.Sai ya samu kansa da sake rungumarta yana sanar da ita cewa tare za su mutu ba za ta taɓa tafiya ta barshi ba,murmushin da tayi a lokacin daya furta hakan sai ya tsaye masa a zuci domin a lokacin yaga wani abu daya kasa tantace ko miye ya haska a cikin idanunta.Kuma bai sake cewa komi ba ya lalubi bakinta ya haɗe da nasa domin haka kawai a lokacin yaji baya so ta sake buɗe baki ta faɗi wata kalmar da zai sake tada hankalinsa,kuma daga wannan haɗe bakin ne ya fara bi da ita ta salon da suka kusa mantawa da Abdallah dake jikinsu har saida Yaron yayi kuka sannan Hameedah tayi gaggawar rungumarsa tana ƙoƙarin fito da nono ta bashi sai Yaya Zayd ɗin ya rigata yin hakan.Yaron na gama shan nonon ya jasu zuwa master bedroom ɗinsa suka faɗa duniyar da baya gajiya da nitso a cikinta,sai bakin Magriba suka sami kansu suka yo wanka tare suka gabatar da sallar magribar da shine ya jasu jam'i da kansa.Tun daga wannan ranar Hameedah bata sake jin ɗuriyar Maryama ba bare jin labarinta a bakin Zayd,sai dai zuciyarta na bata cewa basu rabu ba domin a cikin idanun Maryama ta hango soyayyar mijinta da zallar sha'awarsa wanda tasan cewa abu ne mai wahala ta iya ƙyale mata shi.Kuma kamar yadda tayi hasashen hakan ne ya kasance domin Maryama ta kasa haƙura da Yaya Zayd ɗin,sosai ta cigaba da bibiyarsa ta chat tun yana blocking line ɗinta tana sake wasu har ya gaji ya daina.Tana yawan aiko masa da vedios da hotunan tsiraicinta duk don ta sake jan ra'ayinsa amma baya kulata,zai buɗe ya gani amma baya cewa komi saidai idan ta kunna wutar sha'awa a cikin zuciyarsa ya nemi maganinsa a wurin Hameedah.Najwa kuma kamar yadda ta sanar masa aurenta sai gashi ta turo masa katin gayyata,a lokacin Hameedah na rarrashinsa ya amince mata zuwa ta halarci bikin Jameelah daya rage saura kwana biyu kacal.Kuma duk iya rarrashi da magiyarta yaƙi amincewa,haka ta gaji ta haƙura tana ji tana ganin aka fara gudanar da shagulan biki Amal na ɗaurawa a status tana gani.Zafi sosai Amal ta sake ɗauka da Yaya Zayd akan hana Hameedah zuwa bikin bestynta Jameelah,domin a cikin wayar da sukai da Hameedah ranar da aka gudanar da Kamu ana gobe biki Hameedah na tuna yadda Amal ke describing baƙin hali irin na Yaya Zayd ɗin.Kuma ranar ɗaura auren Yaya Zayd tafiya ta kamashi zuwa Lagos,ya shirya ya wuce ya barsu daga ita sai Kulu mai aiki da Abdallah.Kwanansa biyu yabi Daddy suka wuce Abuja,domin sunata shirin buɗe babban kamfanin haɗaka da sukai su uku za su dinga shigo da kayan gina-gine kamar yadda Daddy ya saba harkarsa dake mugun kawo masa kuɗi.Kwanansa biyu ya juyo zuwa Port Harcourt ɗin,kuma bayan ya dawo ne yake mata albishir ɗin samun aikin Yaya Sulaiman wanda ya samu aiki a ma'aikatar NNDC dake nan Kaduna.A daren ta kira Yaya Sulaiman tayi masa murna har ya haɗata da Amarya Nadeeya suka gaisa,bayan sun aje wayar ne sai ga kiran Amal voice call tana sanar da Hameedah cewa tahau chat ta turo mata vedio ɗin gidan Amarya Jameelah daya gama tsaruwa domin itama Daddy ne ya ɗauki nauyin siya mata kayan ɗaki na garari ƴan waje da aka siya a kamfanin HAYFAH furniture's dake Kanon Dabo.Sosai Hameedah ta yaba ta kuma kira Amal suka dinga vedio call suna shan hira Amal na kallon babynta Abdallah,kuma a cikin Vedio call ɗin ne Amal ke sanar da Hameedah cewa Aman Kurfi ya sami gurbin karatu a jami'ar Robert Gordon dake Uk ya wuce domin zuwa ƙaro deegree ɗinsa na uku wato PhD kamar yadda yaci buri.Ta sanar da Yaya Hameedah cewa Aman ɗin watanni shida kaɗai zaiyi ya dawo ayi maganar aurensu,domin so yake da anyi bikin ya wuce da ita can ƙasar sai ya kammala karatunsa za su dawo gida 9ja.Hameedah tayi fatan alkhairi tana tambayar Amal cewa amma Daddy yasan da maganar? Amal ɗin ta tabbatar mata da cewa bai sani ba,domin ta fiso ta baiwa Aman dukkanin damar da zai gama kintsawa ya turo wakilansa cikin tsanaki ayi maganar aurensu tunda bawai Daddy ya matsa akan ta fito da miji nan kusa bane.Haka suka rabu Hameedah na roƙon Amal akan ta taho Port Harcourt ko domin masoyinta Abdallah,kuma Amal ɗin ta tabbatar mata da cewa za ta taho zuwa next month idan tayi toneprint sai su dawo bikin Sakeenahn Gwaggo Abu da za ai ƙarshen watan da za a shiga ɗin domin duka wata guda da sati biyu aka saka ranar auren nata.Wani saurayi ta samu ɗan jihar Jigawa amma yana aiki a Abuja ne,don haka can Abujan za su zauna bayan biki.Amal tun bayan da Jameelah tayi aure ta daina jin daɗin zaman gidan,sai ta koma zuwa shago ta yini da ma'aikatanta dake zama wani time ɗin ma tare da Momy sukan je su zauna suna ganin yadda komi ke tafiya akan idanunsu.Kusan koda yaushe Amal suna manne da juna ta vedio call da Aman Kurfi,wanda duk kwanan duniya yake sake alfahari da samun Amal Taheer a matsayin masoyiyarsa.Ya ɗauki dukkanin yarda ya bata na cewa shi kaɗai ne,kuma ba za ta taɓa baiwa wani dama ya shigo cikin rayuwarta ba.Shiyasa hankalinsa kwance ya fara karatun PhD ɗinsa zuciyarsa cike da burin ya dawo 9ja nan da wani ɗan lokaci ayi maganar aurensa da Amal ɗinsa,ya sha faɗi mata cewa wata guda kaɗai za a saka domin duk wani shirinsa zai kammalasu nan da watanni shida tunda yana da muhallin zama idan sunzo ƙasar, ya sanar da ita cewa gidansu na Kaduna shi ya gada ita Mummysu ta dawo Zaria da zama tana zaune a asalin gidan Abbah daya fara mallaka a Zaria dake Gaskiya Layout.Guest house ɗin Abban dake GRA ma mallakin Aman ɗin ne domin ya sallami ƙannensa mata da suka gaji gidan tare da hakkinsu gidan ya zama mallakinsa shi kaɗai,don haka yace ta zaɓa duk inda take son a fara ajeta idan sunyi aure kafin ya wuce da ita UK ya ƙarisa karatunsa.Koda yaushe cikin tsara yadda rayuwar aurensu zai kasance suke,basu taɓa hango wani abu da zai iya zuwa ya gifta har ya hana aukuwar hakan ba.Ƙaunar junansu kullum ƙaruwa yake basu da burin daya wuce ace Allah ya nuna musu ranar da za su mallaki juna,a cikin hakan aka shiga new month kuma Amal na zuwa Soba tayi toneprint ta dawo ta fara shirin wucewa Port Harcourt zuwa next week.Koda ta sanar da Daddy kuɗin ticket ya bata yayi mata Allah kiyaye hanya,Momy kuma ta tanadarwa Hameedah abubuwan da za a wuce mata dasu kamar yadda Hameedahn ta buƙata.Anty Mamah ta sanya akai mata Dambun kaji aka haɗa da garin ɗanwake akai packing yadda Amal za ta iya wuce mata dashi,ana gobe Amal za ta wuce taje gidan Jameelah sukai sallama da juna.Habu driver shine ya kaita Abuja safiyar da za ta wuce,kuma sai data yi jiran awa guda a cikin airport ɗin kafin jirginsu ya tashi.Tana isa ta tadda Yaya Zayd yazo ɗaukarta shi da Yaya Hameedah,suka rungume juna Amal ta amshi Abdallah tana kissing ɗinsa da raɗa masa cewa tayi missing ɗinsa.Yaya Hameedah sai murmushi take tana kallon Amal cike da murnar zuwanta garin,kadaran-kadaham suka gaisa da Yaya Zayd ɗin Amal na faman jifansa da harara ƙasa-ƙasa tana gulmarsa a cikin zuciyarta cewa yayi ƴar ƙiba,haka itama Hameedah sai Amal taga tayi jiki tayi fresh sosai alamun weather ɗin garin ya amshesu.Baby Abdallah ma sai taga ya sake girma da wayo ga colour ɗin jikinsa daya sake gogewa da yin fresh,koda suka isa ƙaramin gidan da Yaya Zayd ɗin suke ba ƙaramin birge Amal tsarin ginin yayi ba.Bedroom ɗin Hameedah nan ya zama masaukinta tunda dama tun zuwanta basa raba makwanci da Yaya Zayd ɗin,tuni Yaya Hameedah ta shiryawa Amal girkin tarba haɗe da abubuwan sha kala-kala.Bayan tayi wanka ta natsa ne suka baje a cikin falon Hameedah suna kwasar hira,shi kuma Yaya Zayd ya fita ya dawo don haka Amal ta zage sunata hira suna kwasan dariya cike da nishaɗin ganin junansu.Bai shigo gidan ba sai dare ya dawo,kuma hannunsa riƙe da manyan ledoji da yayo sayayyar su ice cream da suya meat ya shigo.Hameedah taji daɗin yadda ya nuna kulawarsa akan zuwan Amal domin tasan yayo sayayyar ne dominta kasancewar yasan Amal da son shan kayan sanyi da kuma cin suya meat,ita kanta Amal ɗin ta nuna farin cikinta kuma babu laifi ya zauna sun ɗan taɓa hira kafin ya shige yayi shirin kwanciya.Amal tace da Yaya Hameedah tayi tafiyarta wajen mijinta tabar mata Abdallah koda ya tashi cikin dare neman nono madara za ta bashi,kuma hakan aka yi ita da kanta tayi masa wanka ta saka masa kayan baccinsa ta goyashi a bayanta domin Hameedah ta sanar da ita cewa yana son goya idan zaiyi bacci......✍🏻