HADIN KADDARA

Chapter 1

by @aishanalado88

🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

                    By

            AyshaNalado


Young talented writers Ass.

YOTA ID NO/15

Kirkirarren labari ne👌

Ina godiya ga Ubangiji daya bani ikon fara sakar mu ku wannan labarin a yau ranar Litinin 13 ga watan Afrilu shekarar dubu biyu da ashirin da shida miladiyya, yadda ya bani ikon farawa lafiya ina rokon yasa na gama lafiya cikin amincin ya ba ni ikon rubuta abin da zai amfani al'umma.


Wannan labarin kacokam ɗin sa  sadaukarwa ne ga 'yar uwata Ruƙayyatu (Aunty ummi)

SAKON GODIYA ga shuwagabannin kungiyata YOTA da mambobinta baki ɗaya, ina rokon Allah ya kara hada kanmu mu zama tsintsiya madauri guda.


GODIYA TA MUSAMMAN   ga Ayshercool, Amanar cool, Nusy bee, da kawata Oum Nihal bisa jajircewarku da taimakon da kuka bani ta ɓangarori daban-daban kafin fitar wannan labari Ubangiji ya biya ku da gidan aljannah.


Page 1

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.


Dare mahutar bawa inji masu iya magana, tabbas haka yake amma ni a gareni wannan daren da na riski kaina a ciki yau,  na rasa da mai zan kirashi, kai tsaye zan iya kiran shi da daren baƙin ciki a sauƙaƙe, amma tabbas lamarin yafi gaban haka. Dare ne dana shirya rabuwa ko kuma na ce tserewa daga gaban iyaye na mutane mafi soyuwa a gareni, idanuna sun rufe ruf, zuciyata cike take da kudirin *Daukar fansa*
 Tsakar dare ne Sakaliya ko ina ya dauki shiru gabas, yamma, kudu da arewa, ko wani bawa a daidai wannan lokacin yana gida dan hutawa, mafi rinjeyen mutane haƙarƙarinsu na a ƙasa suna barci dan huce gajiyar rana,   jaruman bayin Allah suna tsaye a gaban mai duka, yayin da wasun su ke aikata akasin hakan. Na kasance ɗaya daga cikin waɗan da ke a ido biyu a cikin wannan dare, kwance muke a kan katifarmu nida ‘yar uwata ɗaya kwalin ƙwal a duniya *Maryoji* Jajayen  idanuna a bushe suke  ƙamas babu alamar wani abu mai kama da barci zai ziyarce ni,duk da kasancewar sa gwanin iya sata, a hankalina na kai hannuna na dafe saitin zuciyata da nake ji kamar za ta kama da wuta tsabar yadda take yi min 'kuna, wani irin zafi na ke ji a cikinta tare da wani irin tuƙuƙin bakin ciki, so na ke yi hawaye su zubo daga idanuna ko zan samu sauƙin abin da nake ji a cikin zuciya ta amma Ina! Abin ya gagara, lallai zubar hawaye ma rahama ce ga bawa. Juyi  nayi tare da kai hannu na dafe marana da nake jin shi yana min ciwo. kamar wacce aka kunnawa majigi haka abin da ya faru a yammacin yau ya shiga dawomin tar a kwakwalwata. Tuno yadda yara harda ma wasu manyan marasa kamun kai, suka ringa jifan Baffanmu suna ja mishi riga tare da yi mishi ihu kamar wani ɓarowa yasa  zumbur na mike zaune, tuno yadda baffanmu ya shigo gida a ɗazu da yamma jikin shi butu butu, yara sun jefe shi sun watsa mai ƙasa har sun jimai ciwo goshin shi na tsartuwar jina yasa naji ƙuna da rad'ad'in da zuciya ta kemin ya ninku ninkin ba ninkin, lokacin kuwa da zuciyata ta haskomin , su Talatuwa da su Innan Zainu da kande da sauran matan kauyenmu sun rufa akan innarmu suna mata tijara suna zagin ta har da masu dungure mata goshi, take na ji wani irin kuka ya taho min daga can 'kasan zuciyata, da sauri na kai hannu na dafe bakina saboda kar sautin kukana ya tashi Maryo wacce da'ker ta samu barci b'arawo ya yi awon gaba da ita, kuka na shiga risga bil hakki, kuka mai cike da kaico da ba'kin ciki, nadama tare da danasani, duk wannan cin mutumcin da wulakancin da tozarcin da ake yiwa iyayena ni ce sila,ni ce na janyo musu, iyayena basu cancanci wannan ba'kar sakayyar daga gareni ba, sun soni sun nuna mini gata sun bani tarbiya ingantacciya tare da ilmi na boko dana Mahammadiya, iyayena sun kasance mutane masu kima da daraja a cikin wannan dan 'karamin kauye namu, mahaifin shine limamin wannan kauye yayin da mahaifiyata ta kasance mace mai daraja wacce matan kauyen mu ke matukar girmamawa amma cikin abin da baifi rabin awa ba nasa 'kafa nayi fatali da duk wannan d'aukaka da girma da iyayena keda shi a idanun mutunen yankinmu, tunda wannan lamari ya bayyana Innarmu kullum cikin kuka take babu dare babu rana, ta zama wata sususasciya, gashi tun daga ranar har zuya yau d'in nan Kalmar A bata shiga tsakanin mu ba, da idanu kawai take bina wanda hakan yana matu'kar d'aga min hankali. Har gara daga bangaren Baffa, a ranar  yayi min duka,  duka wanda ya asma sunan sa duka, duka irin wanda ake yin shi da niyar daukan ran wanda ake dukan, Allah ne kawai yasa kwanana na gaba da babu abin da zai hana na she'ka barzahu, daga ranar kuma ya d'auki gagarumar gaba dani wanda  ko kallona bayayi balle har takai ga ya amsa gaisuwata,da kad'an da kad'an ya fara kula ni, wata kila tausayi na bashi ganin yadda na lalace  na fita hayyacina a cikin kwanakin da basufi bakwai ba, ranar daya fara jehomin tambaya akan lamarin sai da na saki guntun fitsawa, “Aishatu Wanene shi?” Rana ta farko a tarihin rayutawa da na ji da kunnuwana Baffa ya ambaci sunana gatsau. Innalillahi wainnailaihi rajiun,  hankalinsa bai taɓa tashi irin na wannan lokacin ba,  ji na yi jikina gaba daya ya dauki wani irin yammm! Tamkar wacce minjirya ya kama, kaina ya yi nauyi tamkar an daura mini kullin kaya, Shin me zancen, wata amsa zan bayar, bayan ni karan kaina ban san shi ba, bansan daga duniyar da yake ba hasalima ko cikakken sunan sa ban sani ba, a cikin a bin da baifi wata biyu ba ya shigo yaruwata yayi mata illar da har duniya ta nad'e bazan tab'a manatawa da shi ba, a hankali cikin shehshekar kuka na furta " *Babangida* ka cuce ni ka cuci rayuwata kaci amanata kaci amanar soyayya, na tsaneka tsana mafi muni tsanar da ban taba yiwa wani mahaluki irin shi a duniya ba, meye laifina dan na mi'ka maka dukkan  yardata da soyayyata? A silarka na zama tamkar mujiya a cikin jama'a kowa guduna yakeyi kowa kyamatata yake yi, na zama abin kallo abin nuni a bin zagi da Allah wadai a cikin kauyen mu, hatta a gurun iyayenan ban samu rangwame ba, a gurin mutum d'aya 'kwal nake samun sassauci itace y'ar uwata Maryo. Har gida ake shigowa kallo na, kallo irin na ƙyama, da wukakanci, masu zagi nayi masu tsinuwa nayi. Kuma abin bai tsaya a kaina ba harda iyayena, wad'an da basu ji ba basu  gani ba, Baffanmu bai da dama ya fita waje jama'a zasu yi caa akan shi da zagi da habaice habaice, wasu ma har kofar gida suke suke sallama da shi su ci zarafin sa, innarmu kuwa har cikin gida matan kauyen ke biyota su 'kare mata tijara, zagi ta uwa ta uba kwace itace ta aikata abin bani ba, daidai da Maryoji bata isa ta lai'ka kofar gida ba balle kuma ni uwar gayya. Zazzafan numfashi na sauke tare da sa hannu na share hawayen dake gudu akan dakalin fuskata,  Ya zama dole na nisanci iyayena domin su samu sassauci. Na tabbata ganina yana 'kara kuntata zuciyar su musamman innarmu wacce gaba d'aya wani irin  kallo take bina da shi wanda yafi kama da kallon tsana a duk sanda idanun mu suka had'u, idan bana tare dasu dole zasu manta dani wata rana duk da nasan abu ne mai matu'kar wuya. Lokaci daya naji zuciya ta dake hawaye da ke zubowa daga idanuna ya 'kafe, shawaran da zuciyata ke bani ne keta amsa kuwwa a cikin kwakwalwata, a fili na furta "kuyi hakuri iyayena ya zama dole na nesance ku, domin ku samu sauki da rangwame akan halin dana jefa ku ciki." Kamar wacce ake controlling da remote  na mi'ke tsaye cikin azama tare da kunna yar tocilana mai batir na nufi jikin bango inda jakukunan mu na makarantar boko ke rataye, nawa na dauko na dawo a hankali na nemi bakin katifar mu na zauna, fefa na falla, na d'auki biro, na saita domin rubuta wasikar da nayi niyya, kamar almara take hannuna ya kama rawa yana karkarwa kwace da gangan nake girgiza shi, kasa rubuta koda Kalmar A nayi a karshe na ajiye biron tare kife kaina na lula duniyar tunani, shin idan nayi haka na yiwa iyayena adalci kuwa, na jefawa kaina tambaya, wani bangare na zuciyata ne ya bani amsa da cewa, “wannan shine cikakken adalcin da zakiyi musu, koba komai idan basa ganin ki a gabansu zasu manta dake koda lokaci zuwa lokaci, kuma ta haka ne kawai zaki samu damar daukar fansa akan wanda ya tagayyara rayuwar ki, ya jefa ki keda iyayen ki a cikin halin kunci da bakin ciki, tuno wanna kudiri nawa na daukar fansa, yasa naji kamar ana ingizani cikin sauri na shiga rubutu a jikin fefan wanda kafin na gama rubutun gaba daya ruwan hawaye ya gama ji'ka fefan, duk wani bayani da suke nema akan lamarin na rubuta musu, tsab na fede musu biri har wutsiya tare da basu hakuri da neman sanyawar albarkar su a karshe na sanar musu da cewa kar suyi wahalar nemana domin baza su same ni ba na shiga duniya neman Babangida domin na dauki fansa akan shi idan da rabon zamu gana wata rana Allah ya kaddara saduwar mu da alkhairi, ina gama wa na  linke shi na ajiye shi a dai-dai inda nake da tabbacin Maryoji zata gani data farka, asusuna na dauka na fasa,  na tattare kud'ad'en dake ciki, daga ni sai riga da zani  sa'kin dake jikina irin namu na fulani da hula, sai ko yan kud'ad'ena dake ri'ke gam a hannun na, na kwashi y'an takalma na na roba a hannu, cikin sand'a na bud'e 'kofar fita daga d'akin mu, har na zura 'kafata d'aya a waje na juyo na kalli y'ar uwata Maryoji dake kwance tana barci ,jinayi hawaye sun ziraro min a fuskata, a hankali na furta sai "wata rana yar uwa Allah ya 'kaddara saduwarmu da alkhairi." da sauri nasa kai na fice daga d'akin, babu kowa a tsakar gida duk mutanen gidan na d'akunan  su, wani baban  mayafin Innata da take yawan amfani dashi na gani rataye akan igiyar shanya, janyo shi nayi  na yafa a jikina,  cikin sand'a na fice daga gidan ba tare da kowa ya ganni ba, har na isa zaure na tura kofar karan da ke a matsayin kofar gidan naji bazan biya wucewa ba tare da na saka Inna da Baffa a idanuna ba, a hankali na juyo na dawo cikin sand'a na isa 'kofar d'akin inna hasken dana d'an hango ya tabbatar da cewa idanun ta biyu, d'an d'aga labulen nayi a hankali na le'ka, tana zaune akan sallaya ta daga hannu sama tana kai kukan ta gurin mai duka hawaye gaba d'aya ya gama wanke fuskar ta, a bayyane take addu'an cikin yaren mu na fillanci wanda shine yaren da tafi ji sosai bisa ga ko wani yare, jin irin addu'an da take yi yasa naji 'kafata na naiman kasa daukar gangar jikina, addu'a takeyi akan Allah ya amshi rayuwarta ta huta da bakin cikin da ni *A'ishatu* na sanya ta a ciki, hankalina naji  ya kara tashi, illahirin  jikina ya dauki rawa,  kuka mai sauti ya subucemin da sauri na saki labulen tare da barin 'kofar dakin, ji nayi bazan iya le'ka Baffa ba, dan shima bansan abin da zan tarar ba, da sauri na fice daga gidan wannan karon ba tare da na sake waigawa ba.

*Mafarin lamari*....


AyshaNalado ✍️