Chapter 3
by @khairatup01
ADNAN(The Artist)
A 2026 Novel.
Arewapen: khairatup01
Wattpad:Khairi_muhd.
3
Babu kalar iskancin da baya yi amma har yau bai gama mutuwa daga cikin zuciyoyin mutane ba. Na rasa kalar farin jinin yaron nan ya kafa ta tsare ya hana kowa ya yi gaba amma shi yana nan ya yi gaba.
"Na gaya maka a samo sabuwar Muryar da ta fi ta shi a daƙushe shi wannan ne kawai mafitar ka."
"Sau nawa aka kawo sababin fuska amma still yana nan ƙyam? Ko ka manta ne. Sabon lissafi nake so ba wanda ba sani ba."
"A kashe shi!"
Su biyun duka suka juya suka kalle shi cike da mamaki.
"Ya kuke kallona kamar na faɗi wani mugun abu? A kashe shi kowa ma ya huta don idan kuna son blaze ya mutu murus dole ne a kashe Muryar gaba ɗaya."
"No a sake shawara gaskiya ba wani batun kisa ai gara a lahanta shi ya daina muruwa ya fi sauƙi."
"Ƙasim anya kuwa da gaske kana son ka dawo cikin harkar nan? Ina da ja akan kana son ka dawo cikin tafiyar gaskiya."
"Ina so mana Guy. Amma ba ta wannan hanyar ba. Wancan ma da muka gwada ai kana gani bai yiwu ba sai ma rasa rai da aka yi har yau na kasa mantawa bare kuma shi da ya zama sanadi."
"Mtsew! Wallahi kana da rainin hankali Kasim. Ashe ba ɗaukakar kake so ba ka fi son kullum ya maƙale a wuri guda ba ka yi gaba ba kuma baka yi baya ba. To ka sani Adnan sai da ya shirya ya fito idan kuma kana son ka kai shi ƙasa ya zama dole ka bayar da jininsa."
"Zan yi shawara."
"Oh! Har wata shawara ma za ka yi? Ko na tuna maka lokacin ba da jini ya yi ne?"
Sai da ya fesar da iska sannan ya sa hannu ya shafa kan shi ya juya yace"Ina sani amma ban da jinin shi ina da bukatar ya rayu saboda na samu abokin karawa da kyau in ya tafi ai na kashe fafatawar."
"To yanzu ya za ayi?"
"Na san me zan yi. Ka shirya ka je Abuja don Allah akwai aikin da za ka yi min a maitama."
"Aikin me?"
"Aikin da muka saba amma wannan karon kowa da location ɗin da za a kai shi."
"Ba wata damuwa?"
"Babu. An yi taka tsan-tsan wannan karon."
"To na yarda da kai, bana son ayi ta wancan karon ne."
"A'a ba matsala."
"Shi kenan sai anjima."
"Ok,bye."
Suka rabu ya zari karan sigari ya sa ka a baki ya kunna ya shaƙa ya fesar yana kallon taga yace "Adnan akwai maza bisa kan ka in ka san wata baka san wata ba ni ubangidan ka ne ko ka ƙi ko ka so dole ka bi ni." Ya saki wata dariya sannan ya kashe fitilar office ɗin.
*
Har ya saka ƙananun kaya sai kuma ya fasa ya cire ya yar a gefe. Ya buɗe drowersa ya ɗauko wata shadda fara tas da ita ya saka. Ya ɗauki tabaru da agogo ya saka ya fesa turare sannan ya fice daga cikin ɗakin na sa.
Yana saukowa suka ci karo da Ishak shi ma zai hau sama.
"Tabarakallah Yaya Artist ka yi kyau sai ina?"
"Idon matanbayi."
Sai da ya yi dariya sannan yace "Da girman kujerar ka Yallaɓai ko na zo na yi maka rakiya ne?"
"Anya kuwa zan buƙaci rakiyar ka?"
" Don Allah ka bari na raka ka nima ka ga sai na gan ka kana live."
"Ishak awa ɗaya tal zan yi musu a bikin fa na taho ka bari na maka alƙawari akwai wani show da zan yi a Abuja last show da nake so nayi babba zamu je da kai."
Ishak bai so ba amma haka ya haƙura ya ce "Shi kenan Yaya sai ka dawo."
"Na gode my boy.'' ya faɗa yana shafa kan shi Sannan ya karasa fita.
A harabar gidan ya ga motar Yaya Deen ta shigo har ta faka Mami ya fara ganin ta fito daga cikin motar sannan shi Yaya Deen ɗin.
Bai san ya aka yi ba sai ya isa kusa da ita ya kama hannunta yace "Mami sannu da zuwa." Ba iya Mami ba hatta Yaya Deen sai da ya cika da mamakin hakan. Daɗi kamar ya kashe Mami a daren tayi amfani da damar ta sa hannu a kan sa tace "Sai ina Adnan?"
"Mami biki zan je."
"Kai kaɗai."
"A'a ni da Sahib ne."
"Security ɗin fa?"
"Na basu hutu."
"Anya kuwa?"
"Kiyi min addu'a kawai Mami."
"Allah Yana tare da kai Adnan. Ni dai kullum ina gaya maka ka ji tsoron Allah,ka ga ka yi min alƙawari ba za ka sake shan komai ba, ka na dai me Abban ka yake faɗa akan ka ko? Kana ji dai yadda yake faɗe nice ban baka tarbiya ba, ina kallo kana yin abubuwa ni dai ka shiga hankalin ka."
Sai da ya ja numfashi kafin yace "Mami nayi miki alƙawari fa ba zan sake yin komai wanda ba kya so ba."
"Allah Ya yi maka albarka Adnan."
"Amin ,Mami."
Yana kai wa nan ya juya ya shiga cikin motar sa.
A hanya yana tafe yana saƙe-saƙen abubuwa a ransa. Kuskure ɗaya tal ya sauya masa akalar rayuwarsa duk da a lokacin bai san ƙaunar sa da samun cikar burinsa zai yi suka faruwar abubuwa ba...... Birki ya ci a bazata saboda shigowar wata yarinya gabansa. Idanuwanta ya hanga masu cike da tsoro da tashin hankali a cikinsu tana kallon gilashin motar sai dai bata kai ga tsayawa ba kafar ta tayi twisting ta faɗi a ƙasa.
A fusace ya fito daga cikin motar ya kulle ƙofar motar yace "wane irin rashin hankali ne wannan? A duk faɗin titunan garin nan ki rasa titin da za ki kashe kan ki sai a gaban mota ta?"
Bata iya bashi amsa ba saboda yadda take hakki kawai. Hannun sa ya saka ya finciko ta da ƙarfi idanuwansu suka sarƙe da na juna bai ga zahirin fuskarta ba amma ya ga idanuwan ta sak na ta. Bai san lokacin da ya saki hannun na ta ba ya koma da baya da sauri. Ita ma da mamaki take kallon shi. Hasken toci ne ya saka ta yi maza ta tsallaka ɗaya ɓarin ya daina ganin ta.
Bai dawo cikin hayyacin sa ba sai da ya ga maza biyu sun tsaya a gabansa suna tambayar sa."Bawan Allah baka ga wata yarinya ba tayo nan yanzu ba ,ƙanwar mu ce bata jin magana?"
Bai iya basu amsa ba kawai ya ja tsaki ya juya ya koma cikin motar ya kulle. Akan sitiyarin ɗin motar ya saka kan sa ya dinga sauke ajiyar zuciya a jajjere. Sai da ya kai mintuna biyar a haka kafin ya mike ya yi wa motar key ya finciki motar ya yi gaba.
Wasi-wasi yake tayi shin wace wannan mai kalar idanuwan ta? Ba zai manta su ba saboda idanuwan ba irin na normal mutanen da ya saba gani bane like ita kaɗai ce mai wanann piece of eyes ɗin, so bright and sexy. Inda za ayi bikin ya shiga ya yi faking mantawa ya yi da ya fito babu mask a fuskar shi sai da ya ji an fara shi ne, Wallahi shi ne sannan ya farga ya koma ya buɗe motar a karo na biyu ya ɗauko mask ɗin sannan ya ɗauki p-cap ya saka ya shiga ciki.
Yana tafe yana duba wayar sa lambar Sahib yake nema don ya sanar masa da cewa ya iso. Cikin sa'a kuwa wayar Sahib ta riga ta shiga shiga.
"Ya kana ina?"
"Ina ciki fa ka zo ne?"
"Eh!har na ma shigo kai kana ina?"
"Wai kai kaɗai ka shigo?"
"Yes!"
"Ok bari na zo. Bara na gayawa Mc ya yi sanarwar."
"Aa ban son wani commotion na mutane kawai ka zo ka je da ni in na fara waƙar kowa ya nutsuwa yanzu in ka sanar kafin na zo an yamaimaye ni kasan kuma bana son hakan."
"Oh ni Sahib. Allah Ya shirya min kai Adnan."
"Na ji."
Kafin ma ya ƙarasa ciki ya hangi Sahib yana ɗaga masa hannu.
Tare suka shiga ciki salin-alin ya tsaya a kan stage, lokaci guda komai ya yi ɗif Mc ya zage ya buɗe murya cike da annashuwa da girmamawa ya saki sanarwar isowar Adnan Artist Blaze tuni mata suka soma ihun murna suna sambaɗa tafi. Ita kan ta amaryar sai da ta miƙe tsaye tayi yar tsalle ta rasa inda za ta saka ranta don daɗi , ta gama tunanin ba zai zo ba ganin dare ya soma.
Sahib yace a fili "Duk wanda Allah Ya bawa ɗaukaka Ya ba shi kowa ya yi shiru kawai ya kalli ikon Allah."
Adnan kamar yadda ya alƙawar ta awa ɗaya ya yi cike da wakokin sa masu dadi da masoyan sa ke ƙauna after a long time yau ya ji wani abu wanda ya jima bai ji shi ba a ransa game da stage da waƙa. Har ana iya hango murmushi a kan labbansa.
Liƙi kuwa da aka yi masa ba zai iya cewa ga adadin su ba ma.
Amarya saboda farinciki kamar tayi hauka ta kasa ɓoye farincikin ta.
A hankali ya kalle ta lokacin da take ta kwarara masa godiya yace mata "Allah Ya baku zaman lafiya."
Da fara'a tace "Amin Adnan na gode Allah Ya mai da kau gida lafiya."
"Amin, na gode baki sani ba amma saboda bikin ki yau bayan wani dogon lokaci i felt alive."
Ba dai ta gane maganarsa ba amma ta ji daɗin zuwan sa. Ya kalli Sahib yace masa "let's go."
A hanya Sahib yace mai "The Blaze, yau na ji ka a ainihin The Artist...."
"I saw her."
Sahib yace "Wa?"
"The eyes."
"Adnan...."
"Da gaske nake."
"A ina, ta ya?" Ya faɗa a rikice.
Adnan ya sauke numfashi yace "Ban sani ba amma ita ce."
"A'a ba zai yiwu ba ta mutu fa."
"Sahib....idanuwanta daban yake da na saura ita ce."
"Gizo take yi maka Adnan ka taɓa jin inda aka mutu aka binne mutum bayan shekaru ya dawo?"
"Ban sani ba , amma gaskiya idanuwan ta ne na gaya maka fa ban taɓa ganin irin idanuwan ta ba sai kuma yau da na kuma gani hakan ba arashi bane kawai?"
"Adnan, kawai saboda idanuwan ta sai ka ce wai ita ce ,ai idanuwan ba na ta bane ita kadai."
"Sai da nayi bincike a cikin kaso 100 da ƙyar suke haura 2-5% an...."
"Adnan da gaske yau baka sha komai ba?"
Adnan ya buga tsaki sannan yace da shi "Ba don zagi babu kyau ba yau da ka ji yadda ake zagi."
Ya yi dariya ya matsa daga jikin motar yace "Sai mun yi waya drive safe. Amma me yasa baka zo da masu tsaron ka ba kayi dare fa kuma ka san situation ɗin da muke ciki ka zo na sauke ka na wuce."
Sai da ya harare shi sannan yace "Kai ni fa namiji ne ba mace ba ko ka ga na saka awarwaro ne?"
Ya ɗaga hannayen sa biyu ya matsa gefe yace "A'a The grate na manta fa ashe namiji ne."
Ya zuge glass ɗin motar ba tare da ya kuma ce masa komai ba ya yi fice. Sahib ya bi bayan motar da kallo.
*
Yana daf da isa hanyar gida ya ɗauko kwalin sigari zai zari ɗaya sai kwalin ya faɗi ƙasa a ƙoƙarinsa na ɗauko kwalin sai hankalin sa ya kasu gida biyu. Bai kai ga ɗaukowa ba ya ji ƙarar abu tim kamar an yi jifa da abu ko kuma ya taka wani abu haka ya ji. Haka ya sa hankalin sa ya tashi ya taka burki ya tsaya a tsakiyar hanya ya fito waje a hankali ya isa gaban motar sai ya ga wani a kwance a ƙasa har da ma jini take hankalinsa ya tashi ya tsugunna a gaban mutumin cike da fargaba ya sa hannu ya yi ƙoƙarin juyo da shi, yana juyo da shi mutumin ya yi masa murmushi kafin Adnan ya gane cewa shiri ne an maka masa wani abu a tsakar ka ya sa hannayen sa biyu ya dafe kan sa yana ganin biyu-biyu a ƙoƙarinsa na juyawa aka kuma kai masa naushi a fuska bakinsa ya fashe , su uku ne suka yi kan sa da duka ta ko ina tun yana tarewa har ƙarfin sa ya ƙare ya kasa ko da ɗaga yatsan sa ne. Dishi-dishi yake gani sai dai ya gane mutum uku ne saboda muryoyi daban-daban ne yake ji. Biyu suka ɗaga shi sama da ƙarfi yana layi yana son ya kama kai amma ya kasa da ido ɗaya ya ga ɗayan ya zaro wuƙa daga cikin aljihunsa ya nufe shi yana son ya soka mai a ciki. Wata mota ce ta hasko su hakan ya saka suka saki Adnan da sauri ya faɗa ƙasa timmm ya kife da fuska. Suka hau mashine suka yi gaba.
Motoci uku ne suka yi tsaye a tsakiyar titin wata mata ce ta fito da sauri cikin tsadaddun kaya sai walwali take yi saboda gwala-gwalai da suke bisa ƙirjinta da kunne har ma da hannun ta.
A hankali ta tsugunna gaban shi tace "Subahanallahi! Imran zo ku saka shi a mota sun masa rauni."
Wanda ta kira da Imran ya iso da sauri tare da wani a bayansa da bakaken suits a jikinsu suka ɗauke shi suka sa shi a bayan mota. Ta kuma ba da umarnin a taho da motar Adnan ɗin.
*
REDDIGNTON HOSPITAL
LAGOS NIGERIA.
VICTORIA ISLAND
Cikin gaggawa aka karɓi Adnan da fuskar shi ta gama wankewa da jini. Kayan jikin shi ma duk sun ɓaci. Hatta jikin baiwar Allahr da ta taimake shi ya ɓaci.
Imran ya tsaya a gabanta yace "Hajiya ya kamata ki tafi masauki gabaɗaya kin ɓaci da..." Hannu ta ɗaga masa tace "Haba wannan ai ba komai bane ba zan iya zuwa ko ina ba har sai na ga yanayin jikin wannan yaron. Da bamu zo ba shi kenan kashe shi zasu yi ko ƙila ma ɓarayi ne."
Imran yace "Haka ne Hajiya amma ki zauna don Allah."
Wuri ta samu ta zauna. Imran kuwa ya koma wurin ba da rahoto a nan ne ma yake jin ashe matashin mawaƙi ne Adnan Artist cikin ƙanƙanin lokaci masu ɗaukar rahoto suka iso. Cikin wanda suka samu labarin abin har da Sahib tuni ya iso cikin tashin hankali. Ya isa reception suka mai bayanin likita bai fito ba amma ga wanda suka kawo shi nan. Ta nuna su da hannu yayi godiya ya isa kusa da su.
"Sunana Sahib Abokina ne Adnan."
Imran ya kalle shi yace "Allah ne Ya kai mu a kan lokaci mutanen nan kashe shi suka so suyi."
A fili ya furta "Innallillhi wa inna illahir rajii'un. Bawan Allah na gode da wannan abu a yadda duniyar nan take sai a ga ana cutar mutum a rasa mai taimaka masa amma ka yi ƙoƙarin taimakawa abokina bani da bakin gode maka Yallaɓai na gode."
"Hajiya za ka yiwa godiya ita ce ta taimaka masa."
Sahib ya isa gaban ta hamshaƙiyar mace fara tas cikin kyan shiga da ado ta cika wurin da kwarjini ta kalle shi sai ya rasa me ma zai ce sai ita ce tayi murmushi tace "Khairan young man. In sha Allah zai samu sauƙi."
"Mun gode Hajiya...."
"Ɗa na kowa ne. Ina fatan ya kasance cikin ƙoshin lafiya."
"Amin Hajiya mun gode."
Jim kaɗan likita ya fito.
Sahib yace "Yaya jikinsa likita?"
"Da sauki. Duk da an ji masa raunuka sosai sannan an buga masa abu mai nauyi a kai zuwa yanzu dai komai da sauki mun wanke ciwukan mun yi dressing sannan mun ba shi magani don rage raɗaɗi duk da haka zamu jira ya farfaɗo sosai sanann muyi monitoring ɗin jikin na sa kafin mu ga cigaban da aka samu."
"Alhamdu Lillahi." Sahib ya faɗa.
Hajiya kuwa ta tashi tsaye tace "Babu wani abun damuwa amma ko likita?"
"A yanzu dai babu sai dai mu jira farfaɗowar shi sannan zamu ga yanayin sa."
"To mun gode. Allah Ya jishe mu alkairi."
Suka amsa da Amin gaba-dayan su.
Likita ya wuce ya bar su a tsaye.
Imran ne ya shigo da waya a hannunsa ya sa ɗaya hannun nasa ya toshe wayar sannan yace mata "Yallaɓai ne a waya."
Ta amshi wayar tasa a kunnen ta.
"Assalamu alaikum."
Daga ɗaya ɓarin ya amsa mata "Wa'alaikum Salam, Hajiya me nake ji daga gun Imran?"
"Ka kwantar da hankalin ka taimako ne fa yaron ya yi sa'an Hamza ba zan iya barin shi ba."
"Amma kin san yanayin garin ko lokaci ne da ake taka tsantsan."
"Na sani Yallaɓai amma ba zan iya wucewa ba da ban tsya ba wataƙila da yanzu ana kukan ya rasu ne. Ƙila mahaifiyar sa tana can tana kuka. Musulmi ɗan'uwan musulmi ne nima a gaba ban san waye zai taimake ni ko nawa ba."
"Wannan sanyin na ki da saurin yarda ya saka ake taka ki Hajiya Khadija."
Tayi dariya sannan tace "Me ya hana ka bacci?"
"Rashin ki a kusa dani mana."
"Haba dai ina ka baro sarautar mata?"
Dariyar ya yi shi ma kafin yace "Bana son tone-tone amma dai tabbas ina cike da Kewar ki sa gayya kika tafi kika bar ni."
"Afuwa Yallaɓai ka tuna A'isha ce fa."
"Na sani shi yasa ai na bar ki."
"Na gode mijina."
"Amma ya kamata yanzu ki wuce ki tafi masauki in yaso da safe in Allah Ya ara mana rai da lafiya sai ki koma ki gan shi don na san ko nace ki tafi kawai ba za ki iya ba."
"Ba zan iya ba gaskiya hakan nan I feel connected to him."
"Haka dai kike kowa kina jin shi a ran ki."
Tayi Murmushi sannan tace "Yanzu zan tafi in na isa zan kira ka."
"Alright sai kin koma ɗin. Shi kuma Allah Ya ba shi lafiya."
"Amin Yallaɓai sai na isa."
"Barka sai anjima."
Ta miƙawa Imran wayar sannan tace "Magana bata zama a bakin ka Imran."
Ya saka wayar a cikin aljihunsa sannan yace "Ba ruwana Hajiya. Aunty Aisha ce ya kira tace bamu sauka ba,shi ne ya kira ni yana faɗan ina muka tsaya na gaya masa ga zance ga magana."
Ta ɗan harare shi sannan ta kalli Sahib tace "Zamu wuce gobe idan Allah Ya kaimu zamu dawo. Allah Ya ba shi lafiya kuma ya kamata ka kira mahaifiyar sa don na san yanzu duk inda hankalinta yake ya tashi."
"In sha Allahu Hajiya mun gode da ɗawainiya."
"Shhhh! Bana son irin haka ka kula." Ta faɗa ta kalli Imran tace masa "Ba shi mukullin motar shi da wayar sa." Imran ya miƙa masa mukullin motar Adnan da wayar shi suka juya suka fita.
Ya sa mukullin a aljihun sa sannan ya zaro wayarsa ya kira layin Yaya Deen.
*
"Shamsudeen ka kira min yaron nan mana ni ina ta kiran sa amma bai ɗaga ba duk da ba yau ya saba ba amma dai yau bana jin abin daidai awa ɗaya kawai yace min zai yi ya dawo yanzu ɗaya saura ne fa."
"Ki kwantar da hankalin ki Mami yana lafiya kin san halin kayan ki dai."
"Na sani amma yau abin bai zauna min ba ko waya ta ne ya ɗaga na ji muryar sa sannan ne hankalina zai kwanta."
"Shi kenan zauna na kira miki autan maza."
"Ba fa wasa bane Shamsudeen,an serious."
Sai ya kama kan sa ya soma kiran layin Adnan amma bata shiga. Ta kalla shi tace"Kai ma bai ɗauka ba?"
"Bata shiga bari na kira Sahib ai na san suna tare duk yadda a kai."
"Eh kira shi haka yace tare zasu je. Ni abinda ya sa ma duk na damu bai fita da yaran sa ba yau."
"Mami ba fa yaro bane namiji ne."
"Shamsudeeni ka kira min shi."
Yana ƙoƙarin kiran Sahib sai ga kiran Sahib ya shigo yace "To Hajiya ga Sahib nan na kira ba mamaki ma can zai kwana."
Ya danna wurin amsa wayar sannan yace "Assalamu alaikum! Sahib ina Artist ne ana ta kiransa ya ƙi ɗagawa?"
"Yaya muna asibiti fa."
"Hello Sahib me kace?"
"Muna asibiti an kwantar da Adnan."
"Innallillhi wa inna illahir rajii'un me ya same shi kuma yaushe?"
"Ban sani ba nima labari na samu na fi tunanin ɓarayi ne ko area boys suka yi masa haka."
"Haba Sahib wanne area boys kuma yanzu kuna wanne asibiti?"
"Muna reddignton Hospital."
"Gamu nan zuwa gamu nan."
"Tam sai kun iso."
Suka ajiye waya. Mami tace "Ba lafiya ba ko? Ai na sani jikina ya gaya min ba lafiya ba kuna ta min taurin kai me ya same shi?" Ta ƙarasa faɗa tana kuka.
Ya kama kafaɗunta yace "Yana asibiti an kai mai hari ne......"
Da sauri tace"Hari kuma? Amma dai basu cutar min da ɗa ba ko ? Innallillhi wa inna illahir rajii'un,wayyo Allah na? Adnan."
A bayan mota ya saka ta ya ja motar suka tafi.
Isar su asibitin ke da wuya Mami ta fita da sauri ba ta ma jira Shamsudeen ya gama saita faking ba ta yi waje. A rikice ta shiga cikin asibitin tana shiga ta hangi Sahabi a tsaye yana kai wa da kawowa.
"Sahib." Ta kira sunan shi da ɗan ƙarfi. Koda ya juya sai ya hangi Mummy a tsaye tana kuka da sauri ya matsa inda take ya kamo hannunta amma ita ƙokarin tambayar sa Adnan take yi.
"Mami ki kwantar da hankalin ki don Allah abin ya zo da sauƙi ma ai babu abinda ya same shi Allah Ya taƙaita mana wahala."
"Sahib na gaji da fargabar yau da gobe ta Adnan na gaya masa ni bana son wannan harkar waƙar ya haƙura tunda neman ransa suke yi amma ya ƙi ji uban sa ya kafa ya tsare sai ya yi suna ta wannan hanyar yau na ga bala'i ɗan nawa ake so a sabauta mini?"
"Ki kwantar da hankalin ki Mami komai ya yi farko zai zo ƙarshe."
"Hankalin ba zai taɓa kwantawa ba sai na ga Adnan ya samu natsuwa kullum a fargaba nake in ya fita a shekarar nan sau biyu kenan ana kai masa hari Allah Ya na ƙubutar da shi gobe fa?"
"Khairan in sha Allahu Mami komai ya kusan zuwa ƙarshe da yardar Allah."
Ya Deen ya bata ruwa ta sha kaɗan ya karɓa sannan ya kalli Sahib yace "Ya aka yi haka me ya faru?"
"Ban sani ba nima a labari naji daga local news nayi zaton ma propaganda ce sai da na zo na tabbatar tukunna. Wata baiwar Allah ce ta taimake shi ta kawo shi asibiti."
"Amma Allah Ya saka mata da alkairi tana ina?" Mami ta tambaya.
"Ta tafi amma ta ce za ta dawo da safe in sha Allahu."
"Allah Ya biya mata buƙatun ta na alkairi."
"Amin Ya Allah Mami."
"Amma me likita ya ce?"
"Da sauki ya ce a jira zuwa farfaɗowar shi saboda ya bugu a kai sosai ga yan raunuka haka a jiki dai."
"Bawan Allah Yana ganin jarabawa iri-iri tunda ya afka harkar nan shi kenan nima bani da kwanciyar hankali. Ya Allah ga Adnan ,Allah ka duba min shi ka kiyaye min shi da kiyayewar ka Ya Allah ka yi masa afuwa."
"Amin Mami Amin."
"Ka sanarwa Mahaifinsa?"
"Mami na sha'afa ban sa..."
Daga baya suka ji maganar Abban cike da karaji da faɗa.
"Tuwo ai tuwo ne Amina ba a canja masa suna ni nan dai da kika tsana ni dole ne ambaci sunan Adnan da nawa. Nace dole ne a ambaci sunan sa da Adnan Yusuf Maiturare baki isa ki sauya wannan ba dole ki haƙura ki bi ni."
Mami dai bata tofa ba sarai ta san halin sa. Hakan kuwa ba ƙaramin ƙona masa rai yake yi ba ya yi ta ƙi tanka shi ba sai ta bawa banza ajiyar sa ta nuna masa bata ma san yana yi ba wannan halin ko in kula da take nuna masa shi ne taƙaicina a a rayuwarsa yadda take guma masa haka yake son ya gani in ya guma mata amma sai tayi furunfus nuna bata ma san yana yi ba.
Yanzun ma juyar da kan ta tayi gefe ta ƙi koda kallonsa.
Ammi ce ta shigo ciki da isa ita mai miji a hannu.
"Amma gaskiya Amina ba kya kyautawa. Irin wannan ai ba a bakin bare ya kamata mu ji ba kamata ya yi ki kira ni ko ki kira shi in ni kin raina ni ke ko ba za ki kira mu ba ai kya saka Shamsu ya kira ya sanar mana wato da sai dai mu ji mutuwa ko?"
Sai a lokacin ne Mami tayi magana. Ta sa hannu ta share hawayen fuskar ta sannan tace mata "A kul kar ki sake faɗi ,kar ki sake kira masa mutuwa in sha Allahu sai dai ya binne ki aniyar ki ta bi ki munafuka."
Ammi tace "Ba faɗa na zo ba Amina Wallahi kina bani mamaki wai har yau an tsufa kin kasa zubda makaman yaƙin ki na kishin banza da wofi. Duk kin takurawa kan ki kin hana rayuwar ki sakat kin koyawa yara baƙin hali." Ta faɗa tana kallon Deeni da ya bai wa banza ajiyar ta ita da Abban duka.
Mami ta koma ta zauna ta mata banza saboda ta san wace ce Fatima a rashin mutunci.