IMAM ZAID

9

by @pendingamarya223

IMAM ZAID 🔬🥼





Pending Amarya ce🎭




JAJIRTATTU WRITERS ASSO………………✍️



The Odogwu Writer ✍️ 

Chapter3: THE PROMISE 🥺🙌



An Empty barrel makes the loudest noise 🙌🏻🎭



IMAM ZAID 🔬🥼🧪

Paid book ne.
At a low fee za ku samu 500 naira kacal.

***😢

Opay Farida Aliyu Ibrahim 
shaidar biya via what’s app🙌🏻
***



️


Pending Amarya 009
Not edited 




And do not lose hope in the mercy of Allah. Indeed, none loses hope in the mercy of Allah except the disbelieving people.❤️💕😢



 Jin kamar za a bude kofa hakan ya sanya Sakinat saurin barin dakin jikinta na kyarma.
Koda ta fito ganin gilmawar mutum kawai ta yi , ba ta dauki abin serious ba ta wuce ta shige cikin bathroom dinta tare da fara taran ruwan, ganin wani koren abu a ciki kamar garsa kuka ma hakan bai hanata wankan ba.

Ta na futowa kam ta fara shirin baccinta ita ma dan Allah na gani wani kalar sarawa kanta yake, a haka dai ta daure ta yi kwanciyyarta tare da tofe kanta da addua…..




Washegari da safe ma, Imamu ne ya fara tashi daga bacci, dan mahaifiyyarsa ta riga da ta saba masa da tashin asuba, ganin ba ta zo tashin sa bane hakan ya sanya shi zarcewa bedroom dinta tare da tashinta.

Bai tsaya jiranta ba ya shiga toilet din tare da zuba mata ruwa a buta sannan ya wuce masallaci.
A compound suka hadu da Papansa da Uncle dinsa, hannunsa cikin nasu suka shige masjid din estate din dake cike da family members.

Sai kusan 6 sannan suka fito daga masallacin, yana biye da su har suka je suka gaida Dadah, da kannen mahaifinsu (Iklima da Yaya Abu, to avoid confusion ), sannan ya bi uncle din nasa yaje gaida Amminsa sannan ya wuce bangaren Maminsa.

Zaune take kan abin sallahr hannunta rike da carbi, ta ma rasa ina ke mata dadi, karasa shigowa cikin dakin ya yi tare da rungumeta a zaunen da take a kan sallayar, shafa kansa ta yi tare da shafe adduan a kansa sannan ta dago shi suka nufi dakinsa tare da hada masa ruwan wanka.

“Mami dan Allah ki min wankan.” Ya fada tare da bata fuskarsa. Kallonsa Mamin ta yi da kyau tare da fadin “Wai kai ba ka san ka girma bane?, you will be 11yrs old next month and you’re telling me na maka wanka, haka ka ga Zayn yake yi?.”
“Mami daga yau fa ba za ki sake min wanka ba har abada, Mami ni dai dan Allah kiyi min, idan na yi baya fita.” Ya karashe maganar kamar zai yi kuka.
“Wuce muje toh.” Ta fada tare da fara masa wankan.
Bayan ta masa ma shiryashi ta yi a uniform dinsa sannan ya wuce zuwa side din Ammi.

“Nyeee Doctor, har ka shigo?.” Inji cewar Ammi dake sama Zayn button.
Murmushi kawai ya yi mai sanyi tare da kallon Ammin da cikin jikinta ita ma ya dan fito.

“Ammi Good morning again.” 
“How was your night Son.?”
“Alhamdulillah Ammi, dan Allah Ammi ki gaya ma Mami zanje wajen AMMUH hutun second term dinnan.”
“Kai fa ka gaya min ba’a shiga tsakaninka da ita?, yanzu naje na same ta ay na maka shishigi.”
“Ammi nine fa?.”
“Ba na son surutu Zaid, kama dan uwanka ku tafi dinning ku fara breakfast kafin kowa ya fito ace sai anyi tare.”
Zayn shi dai bai yi magana ba in banda kumbure kumburen da yake, dan shi sam yau baya son zuwa school dinnan.

A haka dai ta korasu dinning room, suna gamawa suka wuce school da su da sauran yaran gidan Uncle Jamal ya kaisu.

Ko da ya dawo ma kara shirya shi ta yi ya wuce islamiyya.

Shirye take cikin wani atamfa holland Wanda muke masa lakani da off color, babban mayafi ta daura a Shigar nata sannan ta dauki jakarta ta nufi side din Ammi.
Zaune take ta na aikin ninke kayan Zayn da ta wanke dazun. 
“Aunty!, sannu da zuwa.” Ammi ta fada tare da gyara ma yayarta wajen zama.
“Yawwa beloved, ya gida ya iyali?.”
“Alhamdulillah Timmy, Ina zuwa haka aunty?.”
“Wallahi gidan Yaya Shattimah nake son naje.”
“Kai Aunty shi ne ba ki fada min ba na tambaya?.” 
“Wallahi nima sai yanzu zuwan ya zo min, shi ne  nake son na yi sauri naje na dawo kafin danki ya dawo ya ga bana gidan.” 
“Ai kam nima bin ki zan yi, ay an dade ba’aje ba.” Daga haka ta nufi dakinta tare da shiryawa suka fita.
 
A daidai kofar gidan taxi driver din ya ajiyesu, sai da suka bashi kudinsa sannan suka nufi cikin gidan.

Gidan an gyara shi sosai, dan sam ba za ka ce gidan Aunty Sharifa bane.
Ta yi murna sosai da ganinsu, Sameer ya girma ya zama saurayi sosai y’ynta baki daya maza ne sai dai akwai ciki ita ma a tattare da ita Wanda bamu san mai zata haifa ba.

“Wallahi Aunty na ce bari dai nazo na gaida ki, kinsan mutuwa ba ta yima mutum sallama, na ce a yayyafi juna.” 
“Wani kalar magana ce wannan kike Timmy, bangane mutuwa bata sallama ba, wani ya fada miki za ki mutu ne?, karki kara yi min kalar wannan zancan.” Aunty Sharifa ta fada a kufule.
“A’a aunty kawai dai incase a kula min da Imam.” Ta fada a sanyaye, ita dai Sabila baki kawai ta saki ta na kallon Yayarta.

“Idan kalar wannan maganar za ki min gwanda ki tashi ki tafi na gode da ziyara.”
“Yi hakuri Aunty.”
Daga haka suka yi ta hira, suna bata labarin yadda Dadah ke ji da su yanzun kamar ba a taba wulakanta su ba, Haka suka yita hira har sai magrib sannan suka wuce gidansu.

Bangaren Imam ZAID kuwa, da ya dawo gidan da bai ga Maminsa ba wucewa ya yi bangaren Ammi a hanya suka yi clash da Zayn da yake fada masa cewa itama Amminsa ba ta nan side dinsu ya tawo ya duba hakannan suka wuce part din Dadah.


Zaune take a kan kujerar royal dake cikin falonta hannunta rike da newspaper din Daily trust ta na karantawa.

Jin muryoyin da ke tashi a falon nata na hirar ball hakan ya sata ajiye newspapers din tare da sakin murmushi ganin her beloved grandchildren a gabanta, wayanda bayan iyayensu su kadai ta mallaka sai kuma lalurorin da Sakinat din ta haifo.

“Dadah Kina basu wuta, wannan atamfar taki ya yi kyau kamar wata yar Africa.” Inji cewar Zayn da ya zauna a kan kujerar kusa da ita.
“Kayan ba su yi kyau ba ay tun da ba mai gidana ne ya yaba min ba.”
“Ashe za ki dade kuwa ba a yaba ki ba, Maminah ba ta nan ne.” ZAID ya fada tare da bude fridge ya dauki wani chocolate guda daya.
“Sai kace ka manta uwarka da bakin hali, ta dai tafi gantalinta amma ba ta zo nan ba.”
“Ai kin ga matsalar ki, shiyasa bana son zuwa side dinki, Zayn tashi mu tafi, dan ni ba zan zauna part dinnan Ana zagin Maminah ba.”
“Kaji min dan kwal uba, idan za ka tafi ka ajiye min chocolate dina tun da ba daga wajen Fatuhn na dauko ba.”
Bai ko kalleta ba ya fincike hannun Zaid suka bar side din Dadah, duk hakurin da take basu haka suka mata biris suka bar part dinta.

Fitowarsu ya yi daidai da dawowarsu Mami, take 99% daga cikin zagin da Dadah ta yi ma Maminsa suka wanye a brain dinsa.


After some hours.

Sanye yake cikin manyan kaya, hannunsa na rike da wani babban trolly Wanda ni kaina bansan me ye a ciki ba, kana ganinsa ka san bai wani dade daga dawowa daga aiki ba.

Ganin shigowarsa gidan hakan ya sanyata saurin tashi da cikinta tare da yi masa nuni da kujerar zama ya zauna.
Fuskarsa dauke da murmushi mai kyau ya ajiye mata trolly din a gabanta tare da kafeta da manyan idanunsa.
“Welcome Jalal.”
“Tnx dear, unzip the trolly and see for yourself.”
Ba ta yi kasa a gwiwa ba ta fara unzipping trollyn, gabadaya trolly din cike yake da gwalagwalai manya manya Wanda gram 10 ya isa ya cire mutum daga talauci na lokaci mai tsayi tun a wancan time din.
She was surprised, bakinta na rawa ta ce “For what….. Jalal?.”
“For our Imam, ki adana masa saboda watarana, komai ba lallai ya cigaba da tafiya har abada smoothly the way it is ba, and kar ki basa sai time din hakan ya yi.” 
Words cannot express how deeply his words touched her, ita ta san soyayyar da Jalal ke mata da danta na da ban ne, duk yadda a ka so a raba su hakan ba zai taba yuyuwa ba.

Fitowa ya yi hannunsa dauke da wani text book na basic technology, dan karatun exam yake na second term da za a fara next week, hakan ya sanya shi fitowa ya tambayi Mamin wani spelling da ya shige masa duhu.

The way  he saw his mum and Dad suna hira hakan ba karamin dadi ya yi masa ba, sam ya mance kansa a wajen yadda ya ganta ta na dariya, shi kansa bai san tsawon har wani lokaci ya bata a wajen ba sannan mahaifinsa ya lura  da shi ya Kira shi.
“Imam mai ka tsaya yi a nan wajen shigo mana.” Inji cewar Papa.

Shigowa ya yi tare da zama a kan kujerar kusa da Mami tare da daura kansa a kafadarta.

“Mijin Dadah zo kaje bangaren Auntynka ka amso abin da na siya maka.” Inji cewar Jalal.
“wace Auntyn?.”
“Umma Sakinat, ka amso wani rigar sanyi da na siya maka kaji.”
Da toh ya amsa tare da barin side din Mamin ba dan ransa ya so ba.

Zaune take ta na waya da wayarta kirar Nokia 3310, fuskarta a daure take wayar kamar ta na gaban Wanda take wayar dashi.
“Amma nifa Umma gaskiya na gaji har yanzu shiru fa bata tafi ba.” Sakinat ta fada tare da dan kara bata fuskarta.
 A can bangaren matar ta ce “Sakina ki bari na dawo daga Nasarawar nan na miki alkawarin komawa wajen mutumin nan.”
“Yawwa Umma, sannan ina son idan an kawar da ita shi ma yaron a kawar dashi dan zan bar baya da kura ne.”
“Eh toh kuma hakane, amma dai kin san nace bond din dake tsakanin Jalal da yaran rabawa fa za’a sha wahala Duk da kin cire shakuwar dake tsakaninsu.”
“Ni dai Umma koma mene zan bayar, wallahi ko yaran da na haifa ne a ka ce Ana so zan bada su dan bukata ta biya, dan su yaran ma ban ga amfaninsu  ba, an….”

Ba ta karashe maganar ba ta ga Imam a tsaye ya na kallonta ba ko kiftawa.
“Kai dan ubanka mai kake min anan?.
“Aunty ina wuni.”
“Mai kake anan nace?.”
“Aiko ni aka yi.”
“Wa ya aiko ka?.”
“Papa ne ya ce na zo na amshi rigar sanyin da ya siya min.”
“A ina ya ajiye?.”
“Ce min ya yi na zo na dauka ni bansan a inda ya ajiye ba.”
“Toh kace masa ya zo da kansa ya dauka, tafi ka bar mun waje.”
Har ya fara tafiya ta yi saurin kiran sa tare da fadin “kai!.” Juyowa ya yi fuskarsa a daure tare da kafeta da ido.
“Mai kaji ina fada daka shigo?.”
Shiru ya yi mata bai bata amsa ba ya ci gaba da kallonta.
“Ba kaji mai na fada bane?.
“Ni babu abin da naji Aunty.” Yana fadin hakan bai jira cewar ra ba ya wuce can side Maminsa.

*****

Hira suke sosai kamar ranar suka fara haduwa bayan wasu shekaru masu yawa, shiru ne ya ratsa parlourn na wani lokaci, breaking silence din ta yi tare da fadin.
“Jalal, pls ko bayan raina Kar ka bar jini na ya wulakanta, soyayyar da kake min ka hada shi da Wanda kake ma Imam ka bama Imam na bar masa duniya da lahira, Dan Allah Jalal  ko da raina ko da babu raina Karka bar min dana ya wulakanta, ko da dede da na second daya a kowani hali ka tsinci kanka.” Ta fada tare da kamo hannunsa.

“Wani kalar magana kike haka Fatuh?, Anya kinsan abin da kike fada kuwa?.

“Na sani mana Jalal, ni dai ka rike alkwari na kula da danmu nikuma zan zama mai yin farinciki da hakan, kai ma kasan kalar bridge din da nayi crossing ba saina fada maka ba, pls don’t keep away our promises ko na second daya.” Ta fada kamar za ta yi kuka.

“Naji sai ki adana masa abin da na kawo, or can I sleep here?.”
ya fada fuskarsa dauke da wani kalar ja alamar hawaye ne kwance a cikin idanunsa.

“Kai da gidanka, ay sai inda kayi niya zaka kwana.”
A sanyaye ya shigo dakin jikinsa a mace sannan ya ce “Mami bacci, can I join you ?.”
“Sure Baby we all missed Papa.”
“Yes Mami….
Toh sai yadda hali ya yi a gobe kuma 😂🙌🏻🫩




 🥰🙌🏻
Like and share fi sabilillahi ❤️🥰🙏🏻




> IMAM ZAID ONLY ON PENDING AMARYA’S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY 🥰


~///Soft Noorah///~
  

> PENDING AMARYA😘 

> FARIDATOOL NOOR🥰🙌🏻

> THE ODOGWU WRITER ✍️ 


Your favorite troublemaker, Noor 😌