Chapter 4
⚖TUHUMA!️⚖️
🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍
️ PAGE4️⃣
Koda ta fita daga wanka, kayan data tarar akan gado su ta ɗauka tana dubawa, fuskarta sam babu walwala ganin ba kalar kayan da take so bane, riga da sket ne na wani lallausan leshi, an masa wani irin ɗinki mai ɗaukar hankali, ga wani stone da aka jera daga wajen wuyan rigar zuwa hannun, duk da ita ba ma'abociyar sa riga da sket bace, amma sai da ɗinkin ya burgeta.
Bayan tasa kayan ta daɗe a gaban madubi tana kallon kanta, ganin yadda kayan suka mata wani irin kyau, sun zauna a jikin ta sun yi cif-cif kamar a jikin ta aka ɗin ka.
Tana tsaka da ɗaura ɗankwali ne ta ji ƙarar motoci, da alamun baƙin sun sauka kenan, ƙirjin ta ne ta ji ya wani irin bugawa, zuciyarta cike da fargaba tana tunanin waye zai zo? wanne irin hali ne da shi, uwa uba ya suffar shi za ta kasance?.
Ji ta yi zuciyarta ta kasa daurewa, sai ta tashi a hankali ta je jikin window ta ɗaga labulen tare da leƙawa, sai dai bata hango komai sai bayan baƙin suna shiga sashin Dadyn ta, wanda ke haɗe da farlon baƙi.
Ta dai ga mata guda biyu, sai maza su biyu da Dadyn ta na uku, Barister Auwal dama ta riga da ta san shi, na gaban ne take tunanin shine wanda ya zo ganin ta.
A hankali ta saki labulen ta koma ta zauna a bakin gado tana sauke numfashi, nan ta shiga tunani a zuciyar ta, yanzu haka za ta tunkari wani namiji ba Anwar ba da sunan soyayya?, shin zuciyarta za ta iya amincewa da soyayyar shi, ko kuwa shi zai yarda ya so ta?.
Tana cikin tunanin ta ji an turo ƙofar bedroom ɗin an shigo, Mom ɗin ta ce tsaye ita ma ta ci kwalliya sai walwali take. Takowa ta fara yi cikin ɗakin ta kalli Hafsat tace "Sun Ƙaraso sai ki fito ki je ki gaishe su."
Sunkuyar da kai Hafsat ta yi tana wasa da yatsun hannun ta tace "Mom yanzu dole sai na je na gaida su?."
Wani kallo Mom ɗin ta watsa mata cikin gatse tace "A'a ni zan je na gaida su tunda saboda ni suka zo."
Ta gane gatse Mom ɗin ta mata, dan haka sai ta tashi tsaye ta nufi bakin ƙofar fita.
"Au haka za ki je musu babu mayafi?."
Ta ji Muryar Mom ɗin na ta ta ratsa kunnen ta.
Bisa dole ta juyo ta wuce wadrobe ɓangaren mayafai, sai da ta zaɓi wanda ya yi daidai da kayan jikin ta, ganin ƙaramin mayafi ne yasa Mom ɗin ce mata ta ajiye ta biyo ta.
Bedroom ɗin Mom ɗin suka shiga, ta yi mamaki ganin Mom ta ɗauko mata ɗaya daga cikin sabbin mayafan ta, irin nasu na manya matan aure, mayafin sabo ne fil ta buɗe shi a leda ta miƙa mata tace "Amshi."
Tana son ta yi magana, amma yanayin fuskar Mom ɗin da ta gani babu wasa yasa ta haɗiye maganar ta ta, sai ta yafa mayafin a kafaɗar ta ya ɗan zamo kaɗan.
Kallon ta Mom ta yi ganin tana shirin fita a haka sai ta jawo hannun ta baya, da kanta ta cire mayafin ta ɗora mata shi a saman kanta ta gyara zaman shi sosai, sannan tace "Wuce mu je."
Hafsat kallon kanta ta dinga yi tana jin ta gaba ɗaya a takure, dan bata saba da yafa babban mayafi ba, gani take hakan takura ce a wajen ta.
A farlo suka tarda Baba Salame da Batula, suna aikin haɗa abincin da za'a kaiwa baƙin, suna haɗa ido da Baba Salame ta yi saurin ɗauke idon ta ta cigaba da jera kulolin a wani babban tire, hakan ya bawa Hafsat mamaki, dan inda da ne ta fito cikin kwalliya, haka Baba Salame za ta yi ta koɗa kyanta tana wasa ta, tare da janta da wasa.
Sai gashi yanzu ta yi kamar bata ganta ba, Batula ce ma da ta ganta ta washe baki tare da jinjina mata hannu alamar ta yi kyau, ita ma saboda ta ga Mom ne da haka za ta sata gaba ta yi ya koɗa ta.
Da tunanin yanayin da Baba Salame ta nuna mata suka ƙarasa farlon baƙin, da sallama a bakin su suka shiga, ita dai ƙasa take kallo bare ta san yanayin mutanen dake farlon, amma tana jin dafin idanun su a jikin ta alamar ita suke kallo.
Sakin hannun ta Mom ta yi ta raɗa mata a kunnen "Ki je ki gaishe su."
Sai lokacin ta ɗago kanta ta sauke kallon ta akan mutanen farlon.
Sai ta ga gaba ɗaya ita suke kallo, Barister Auwal ne zaune kusa da Dadyn ta, sai wata babbar mace wankan tarwaɗa mai jiki da alama ita ce matar shi, sai wata budurwa mai ɗan jiki da ta kwantar da kanta akan cinyar matar, bata samu damar ganin fuskarta sosai ba saboda ta ɗan juya kamar mai barci.
Ɗago kan da ta sake yi ne idanun ta suka faɗa cikin nashi, wani irin abu ta ji ya daki zuciyarta ganin yana bin ta da wani mayen kallo kamar tsohon maye, duk da sun haɗa ido hakan bai sa ya janye na shi idanun ba.
Matashin saurayi ne mai kimanin shekara talatin, zaune akan kujerar farlon, dogo ne baƙi kakkaura, yana da ɗan kyan shi daidai gwargwado, sanye ya ke cikin ƙananan kaya waɗan da suka matse jikin shi, duka duka wandon iya gwiwar shi ne, ga wata sarƙa da ke wuyan shi irin wadda gayu masu ji da kan su ke sakawa.
Duk da Hafsat itama ta tashi a ƙasar waje ne, kuma ba ta san yadda ake zuwa wajen surukai ba, amma sai ta ga kamar bai dace ace ya zo da irin wannan shigar gidan su ba.
Ganin bashi da niyar daina kallon ta, sai ta janye nata idon ta Ƙarasa wajen su Dady ba ta manta da gargaɗin Mom ta mata ba, na idan ta je ta tsugunna ta gaishe su, dan haka tana isa wajen ta tsugunna har ƙasa ta gaida Barister Auwal, ya amsa mata cikin fara'a tare da tambayar ta ya karatu.
Daga nan ta Ƙarasa gaban matar shi ta tsugunna har ƙasa ta gaida ta kanta a sunkuye, kallon yarinyar dake kan cinyar ta matar ta yi tace "Ɗaga ni Baby."
Tashi yarinyar ta yi ta na gunguni, ta matsa gefe ita kuma matar ta sa hannu ta ɗago Hafsat daga tsugunnon da ta yi, tana murmushi tace "Ta so ki zauna anan ƴata."
A kunyace Hafsat ta zauna a kusa da ita sai ya zama sun sata a tsakiya, wadda aka kira da Baby a gefe ita ma a gefe, duk lokacin da Hafsat za ta ɗago kanta sai ta tsinci idon gayen nan a kanta, ko kunyar iyayen su dake wajen baya ji.
Sallamar Batula da Baba Salame ita ta ratso farlon, kamar ko yaushe Batula sanye take cikin hijabi har ƙasa, hannayen su ɗauke da abinci da kayan maƙulashe, a gaban tebur ɗin dake tsakiyar farlon suka jajjera, sannan suka gaida baƙin cikin ladabi suka tashi suka tafi.
Tunda ta shigo idanun Barister Auwal ya sauka akan Batula, sai da suka fita Sannan ya ɗauke idanun shi tare da sauke ajiyar zuciya, matar shi na lura da duk abinda ya ke yi yana juyowa suka haɗa ido da ita, mazewa ya yi ta hanyar jawo goran ruwa ya shiga tsiyayawa a ɗan ƙaramin glass cup ɗin dake gaban shi.
Hafsat kam ta yi shiru tana jin yadda su Dad ɗin ta da Mom ke firar yaushe gamo da
Barister Auwal.
*WANE NE BARISTER AUWAL?.*
Barister Auwal Ali Muhammad, shine asalin sunan shi.
Tsohon aminin Alhaji Mamman Nera ne, tun yarinta tare suka taso, haka karatu tun daga Nursery har zuwa matakin Secondary, daga nan ne kowa ya kama gaban shi, shi Alhaji Mamman Nera bashi da burin cigaba da karatu ya fi son ya yi kasuwanci, ya yin da Barister Auwal ya ke da burin zama babban lauya, dan haka shi ya cigaba da karatun sa shi kuma Alhaji Mamman Nera ya tsunduma harkar kasuwanci ka'in da na'in.
Bayan wasu shekaru kowa ya samu abinda ya ke so, Alhaji Mamman Nera ya zama hamshaƙin ɗan kasuwa, ya yin da Barister Auwal ya cika burin shi na zama lauya, Alhaji Mamman ya riga Barister aure, sai dai Allah bai bawa matar shi rabo da wuri ba, har Barister Auwal ya yi aure matar shi ta haifi ɗa namiji, bayan wasu shekaru sannan matar Alhaji Mamman Nera ta samu ciki, inda kusan tare suka haihu da matar Barister Auwal haihuwar ta ta biyu kenan ita.
Daga nan dukan su babu wadda ta ƙara haihuwa.
Babu daɗewa kuma Barister Auwal ya samu cigaba a aikin shi, aka tura shi ƙasar waje dan yin wani kwas, bayan ya gama kwas ɗin saboda daɗin zaman ƙasar da ya ji, sai ya nemi aiki acan kasancewar shi ƙwararre bai wani sha wahala ba suka bashi aiki, daga nan ya cigaba da rayuwar shi da iyalan shi a can, lokaci bayan lokaci dai ya kan zo Nigeria ya duba ƴan uwa da abokan arziƙi ya koma, bai taɓa zuwa da yaran shi ba sai wannan karon da wa'adin zaman shi a ƙasar ya cika, ya tattara yaran baki ɗaya suka dawo Nigeria.
Dama tun tuni sun riga da sun yi alƙawarin za su haɗa auren ƴaƴan su, hafsat da babban ɗan Barister Auwal mai suna Jamil.
DAWOWA LABARI
Bayan sun ci sun sha ne, Dady ya kalli Barister Auwal yace "Ya kamata mu bari yaran su gana da junan su ko?."
Kowa ya yi na'am da wannan shawarar, dan haka Dady ya ja Barister Auwal suka fita farfajiyar waje suka zauna a kujerun roba, suka cigaba da tattaunawa.
Ita kuma Mom ta ja su Hajiya Sa'a matar barister da Baby suka nufi sashin ta, sai farlon ya rage daga Hafsat sai Jamil.
Baki ɗaya Hafsat jin ta take a takure, babu zato ta ji mutum a kusa da ita ya zauna har jikin shi na gugar nata, da sauri ta yunƙura gaban ta na faɗuwa da niyar tashi tana mamakin hali irin na shi.
Ji ta yi ya riƙo hannun ta cikin wata murya irin ta ƴan duniya yace "Calm down baby, I won’t hurt you."
Kiciniyar ƙwatar kan ta Hafsat ta shiga yi, sai dai ya kasa bata damar hakan, sai wani ƙara shige mata ya ke yana rirriƙe ta.
Zuciyar ta wani irin bugawar tsoro tace "Wai me ka ke yi haka? Ka sake ni ni ba ƴar iska bace."
Ƙara riƙe hannun ta ya yi, ya shiga Binta da wani kallo ƙasa ƙasa yace "Ai nima ba ɗan iska bane, ki waye mana."
Hafsat ta shiga tashin hanlslin da bata taɓa tsintar kanta a ciki ba, saboda tunda take a rayuwar ta wani namiji bai taɓa mata makamancin abinda Jamil ya ke mata ba.
Ture shi take iya ƙarfin ta shi kuma yana ƙoƙarin rungumar ta, Allah ne ya bata Sa'a ta kama hannun shi, ta daddage ta gartsa masa cizo.
Wata irin azaba ce ta ratsa Jamil, da sauri ya sake ta yana duba inda ta kafa masa haƙora har ya yi shati, ga uban zafin da ya ke masa abin ka da wanda bai saba da wahala ba.
Ɗago idanun sa da suka canja kala zuwa ja ya ya, ya watsa mata wani kallo tana tsaye ta coge a jikin kujera daga nesa da shi, tana sakin wani numfashi sama-sama har lokacin zuciyar ta bata daina bugawa ba.
Da hannu ya nuna ta yace "Ni kika ciza?." Yana nuna mata inda ta cije shi.
Kama ƙugu Hafsat ta yi cike da tsiwa tace "In ka ƙara kai hannun ka jiki na, abinda yafi cizo ma zan aikata maka wallahi."
Miƙewa ya yi ya nufo inda take gadan-gadan, tana ganin haka ta juya cikin hanzari ta nufi ƙofar farlon, take mata baya ya yi a guje yana faɗin "Ki tsaya ina za ki."
Tun daga nesa ta hango su Dad ɗin ta zazzaune, haka ta wuce su a guje jin har lokacin Jamil bai daina Binta ba.
Cikin mamaki Barister Auwal da Alhaji Mamman Nera suka bi Hafsat da ta wuce a gu je da kallo, miƙewa Alhaji Mamman Nera ya yi yana shirin kiran ta sai ga Jamil shima ya wuce hannun sa ɗaya dafe da ɗaya hannun.
Sunan shi da ya ji Dadyn shi ya kira shi ya dakatar da shi daga bin Hafsat, wadda ta samu nasarar shigewa farlon Mom ɗin ta.
Barister Auwal ne ya ƙarasa wajen shi ya riƙo hannun shi yace "Ya za ka dinga bin ta a guje haka, sai ka je ta faɗi ta ji ciwo."
Yarfa hannu jamil ya shiga yi, fuskar shi a haɗe yace "Dady cizo na fa ta yi." Ya nunawa Barister hannun.
Kallon hannun Barister ya yi ya saki murmushi yace " Ka mata laifi ne shi yasa."
Shi kam Dadyn Hafsat mamaki suka bashi, ganin ko damuwa da rashin tarbiyyar da Jamil ɗin ya aikata bai yi ba, sai ma cewa da ya yi laifi ya mata, ya san wataƙil ya nunawa Hafsat rashin tarbiyya ne ita kuma ta cije shi, bai ji daɗi ba in har haka ce ta kasance.
Amma da ya ke zuciyar shi na son haɗin, kuma baya son ɓata ran aminin nashi, sai shima ya aro murmushi ya yafa a fuskar shi yace "Ka yi haƙuri yarinta ce."
Juyowa Jamil ya yi ya kalli Alhaji Mamman Nera, yana wani ɓata rai.
Buɗar bakin shi sai cewa ya yi "Ai ta ci bashi ne kuma sai ta biya, sai na rama cizo na ko min daren daɗewa."
Dariya Barister Auwal kawai ya yi, shima Dadyn sai ya biye masa a hakan suka cigaba da hira.
Daga nan Jamil wucewa mota ya yi ya zauna, zuciyar sa cike da ƙunci yana jin zafin abinda Hafsat ta masa, ya sa a ran shi duk lokacin da ta shiga hannun sa sai ya bata mamaki.
Ita kam Hafsat a guje ta wuce su Mom ɗin ta ta shige bedroom, tana jin suna tambayar ta ko lafiya? Ta share su.
Zama ta yi akan bed ɗin ta tana sauke wani numfashin wahalar gudun da ta yi, ta kai hannun ta ta dafe ƙirjinta da take jin kamar zuciyar ta za ta faso fili.
A hankali ta furta "Wannan wanne irin mutum ne Dady ya kawo min? Na shige su ni Hafsat."
Ta daɗe tana tunani akan halin Jamil, tana ganin shi ɗin ba mijin aure bane, sai dai ta ya za ta gujewa auren shi bayan Dadyn ta yana son haɗin?.
Nan da nan kanta ya sara, ta ji wani irin ciwon kai ya kama ta, dole ta kwanta ta yi lamo akan gadon, ta faɗa tunani akan waye Jamil?.
In da Allah ya taimake ta Mom bata tambaye ta dalilin gudun ba, a haka har baƙin suka shirya tafiya, kiran ta Mom ta yi tace ta zo su yi sallama.
Bandir ɗin ƴan dubu-dubu Barister Auwal ya bata, da farko ƙin amsa ta yi sai da ta ga Yace dole sai ta amsa ta karɓa haɗe da godiya, tana lura da hararar da Baby take auna mata a fakaice, a zuciyar ta tana mamakin hakan ko me ta tare mata take harararta?,sai dai tunda ba ita ce a gaban ta ba sai ta juya tana shirin shiga ciki.
Dadyn ta ne yace "Ba ki je kun yi sallama da Jamil ɗin ba."
Yatsine fuska ta yi cikin sanyin murya tace "Dady mun riga da munyi sallama ai." Kafin su yi magana ta juya cikin hanzarin ta shige ciki.
ANWAR.
Tun ranar da ya gano wace ce Hafsat bai ƙara samun cikakkiyar nutsuwa ba, ya rasa walwalar shi ya rasa kuzarin shi komai yana yi ne kawai, ya yi dana sanin faɗawa soyayya da ita bayan bai san ita ɗin wace ba, ga shi yanzu ta masa babban rauni a zuciyar sa wanda zai yi wahala ya warke yanzu.
Wani irin so ya ke yiwa Hafsat, wanda tunda ya ke bai taɓa jin irin shi ba, kasancewar bai taɓa yin soyayyar ba baki ɗaya.
Yana sane da tana neman shi, shi yasa duk wani waje da yasan za ta same shi ya toshe hanyar, wajen aiki sa dama shine mafarin komai, in ya je ya kan ce in an hango ta a faɗa masa, sai ya ɓoye yace in ta tambaya ace baya nan.
Sai makaranta inda yasan dole su haɗu, to da ya ke kowa da ɓangaren da ya ke karanta, yawanci lokutan da suke zuwa ma ba ɗaya bane, sai dai watarana sukan haɗa lokaci wajen shigowa, in yasan hakan zata faru da wuri ya ke zuwa sai ya shige wani waje inda yasan ba zata gan shi ba, haka in zai tafi gida yake yi, shi yasa in ta zo bata samun shi kwata-kwata, a nata tunanin tana ganin ya daina zuwa ne duka.
WAI SHIN ME CECE ALAƘAR HAFSAT DA ANWAR?.
Mu haɗu a next page in sha Allahu
***
🥰MAMAN ƊAN ALBARKA