Chapter 1
*🪴TUSHEN MU ƊAYA 🪴
*PAGE 1️⃣*
_*🥰MAMAN 'DAN ALBARKA CE🥰✍️✍️*_
*Bismillahirrahamanir rahim*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Ya Allah yadda kabani ikon fara rubuta wannan littafin lafiya, Allah kabani ikon kammala shi cikin aminci da koshin lafiya. Ya Allah ka ba ni ikon rubuta abin da zai amfani al'ummar musulmai baki ɗaya. Allah kaba ni ikon isar da saƙon da nake son isarwa kasa ya fadakar. Ya Allah Ka tsaftacemin alqalamina.*
_*WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE NA MAIDA SHI FREE DAN FARIN CIKIN KU, IN NAGA KUNA COMMENT YADDA YA KAMATA ZAN CIGABA FA POSTING ƊIN SA HAR KARSHE.*_
_*IN NAGA SAƁANIN HAKA KUMA ZAI KOMA PAID ƊIN SA.😃*_
*_SANNAN BA LALLAI NA CIGABA DA POSTING ƊIN SA A GROUP BA, DAN HAKA DUK ME SON CIGABA DA_* *_KARANTAWA TAYI HANZARIN YIN FOLLOWING ƊIN CHANNEL ƊINA GA LINK ƊIN NAN A ƘASA_*
👇
Follow the TASKAR MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️ channel on WhatsApp: ***
*FARKON LABARI*
"Haba Menah nace ki yi Haƙuri dan Allah."
Ahmad ya faɗa cikin lallashi fuskar shi cike da tausayi.
Shiru nayi bance komai ba sai cigaba da nayi da kukan da nake, babu shiri kukan da nake ya tsaya ganin an shigo ɗakin. Da sauri na ɗago kaina da ke tsananin ciwo, hawaye na zuba a idanuna na kalli wadda tashi go.
Cikin sauri na sunkuyar da kaina, ganin yadda take ta faman huci tana ƙare min kallo sama da ƙasa.
Gabana ne naji yayi wata faɗuwa duk da bansan da wacca ta zo ba, dama na tsammaci shigowar tata sai dai banyi zaton zuwan nata da wuri haka ba.
Cikin masifar dake cinta, ta fara magana da karfi tana tafa hannu tace "Ah lallai samun guri nan kika zo kika zauna kenan? Ni ina can na shanya baki ina jiran ki ki zo kimin aiki, ke ashe kina ɗaki kin sa min ɗa a gaba kin hana shi fita ke kuma baki fito ba saboda baƙin munafurci."
Ta kai ƙarshen maganar tata tare da sa hannu ta ɗage labulen ɗakin, ta jefa shi kan k'yauren tare da faɗin"Jarabar ki tasa ko labule ba za ki iya ɗagawa kisha iska."
Ni dai kaina sunkuye har lokacin, dama ga kukan da nake saboda ciwon kan dake damuna, ga kuma Hajjo data shigo zata ƙara min wani tashin hankalin.
Ahmad ne yayi ƙarfin halin magana cikin ladabi yace "Hajjo kanta ne ya ke ciwo, shi yasa ta zauna kiyi haƙuri ta ɗan samu sauƙi, zata fito ta ƙarasa aikin."
"Laila'hailallahu yanzu dama saboda aikin dana sata take kuka?." Ta kalle ni tare da nuna ni da yatsa ta cigaba da magana "Ke yanzu Aminatu dan nace ki fito kiyi wanke-wanke shine kika zo kika sa shi a gaba kina kukan munafurci, kamar wadda aka ce ga ranar mutuwar ta salon ace na cika takura miki, to wai ciwon kan ma ki ke wa kuka sai kace ba mace ba? Wallahi kin ji kunya halin ki."
Ta juya ta kalli Ahmad dake gefena, wanda yayi shiru tun bayan maganar farkon da ya yi. Ransa na ciwo akan irin abinda Hajjo take musu shi da matar sa, saboda ɓacin rai idanunsa gaba ɗaya sun kaɗa sunyi jawur.
"Kai kuma na dawo gare ka Ahmad, ka nuna min ni ba kowa bace gare ka ina matsayin Uwar ka ace ka fifita matar ka a kaina, wato ka zama sallamamme tunda gashi ka ƙi nuna mata ina da matsayi a gunka ka barni sai ɓaɓatu nake Ni kaɗai."
Ita kuma ƴar gwal ɗin taka, ka sata gaba kana kallo tana kukan munafurci kamar wadda na daka."
Ganin bai yi magana ba yasa ta fashe da kuka, tasa bakin zanin ta ta shiga fyace majina tana magana cikin kuka Oh
ni Hajjo yau naga abin da ya ishe ni bai ishi Allah ba. Yanzu Ahmad har ka isa ka wulaƙanta ni, kana ji ina magana ka share ni kai lallai sai ka nuna min ka zama shanyayye, kuma mijin hajiya."
Sai da ta dakata da kukan nata tukun ta cigaba da magana "To Wallahi ƙarya kake ka maida ni uwar banza, ni da haihuwa wasu da mora a banza, yoh yaushe kayi auren ma duka da zaka nunawa matarka bani da wata daraja da ƙima a idonka.
Yarinya daga cewa kiyi wanke-wanke sai ciwon kai, bayannan ciwon kai takewa kuka don baƙin makirci, kai kuma ka kasa gane gulma ce ka fito ka gwada mata darajata a matsayina na mahaifiyarka."
Tayi ƙwafa tare da buga zanin ta tace "Ayi dai mugani in tusa zata hura wuta, kuma wallahi kun ji na rantse ko zaki mutu ke za kiyi aikin nan."
Kuka kawai nake ina jin zuciyata namin zafi kamar zata fashe, ban yi zato ba naji ta fusgi hannu na da ƙarfi tace "Munafuka tashi mu wuce dan tsabar iskanci kowa gidannan ya gama aikin sa ya wanke kwanukansa tsaf ya adana, Ni ina nan ba'a min ba saboda kin maida ni shashasha, yanzu ƙarfe tara 9am ace mutum bai yi ayyukan safen saba.
Na gama fuskantar ki, so kike ki maida ni ƙazamar ƙarfi da yaji."
Sai da taga na miƙe tukun ta saki hannuna, ta tsaya tana gyara ɗaurin zanin ta, ta nuna min hanya tace"Wuce muje munafukar banza da wofi kawai."
Zuwa lokacin hawaye ne kawai yake zuba a idona. Bansan me Hajjo ta ke so dani ba a rayuwa, wannan wace irin rayuwar ƙasƙanci ce. Tun da nake ban taɓa tunanin zanyi rayuwa irin wannan a gidan aure na ba. Gaba ɗaya na shagala da tunani ban fita ba kamar yadda ta tsaya tana jira na.
Ganin haka kawai sai Hajjo ta zuba min, ido dani da Ahmad da shima alamar tunanin ya faɗa.
Gaba daya Ahmad ya rasa yadda zaiyi da halin mahaifiyar tasa, tunda yayi aure ta canza kullum fitowa take da ɗabi'un da bai santa da suba su, sam bai taɓa tunanin cewa mahaifiyar sa zata iya aikata masa haka ba.Tun ranar da yayi aure gaba ɗaya ta hana masa kwanciyar hankali shida iyalinsa, bai san me take so ba bayan duk sharaɗin data gindaya masa yabi ya mata abin data ke so, Madadin ta barshi ya samu zaman lafiya, kullum sabon salon tashin hankali take ƙara fitowa dashi.
Ƙarar marin da ta saukewa Aminatu ne, ya dawo da Ahmad daga duniyar tunanin da ya tafi.
Cikin masifa Hajjo ta fara magana "Wallahi kinyi tsararo, Ace ni Hajjo ina miki magana ki tsaya kiyi banza dani. Wuce muje kafin na aikata miki abinda baki yi zato ba. wato rainin da kika min har ya kai ina magana kiyi banza dani , yoh ko ubanki yayi kaɗan nayi magana ya min haka nace uban ki Salisu yayi min ƙanƙanta inyi da shi bare ke, wuce muje kafin na bugeki."
Ta Kai ƙarshe maganar tare da ƙara kawo min hannu, kamar zata dake ni.
Tun Marin data sauke min na farko, gaba ɗaya wutar kaina sai da ta ɗauke.
Na kasa komai hannu na dafe da kumatu na, na ɗago ina kallonta.
A rayuwata na manta rabon da a mare ni ko a taɓa lafiyar jikina.l,
A hankali na juya na kai kallona ga Ahmad.
Sai naga kanshi sunkuye ina iya hango yadda idanun sa suka kaɗa suka yi jawur saboda ɓacin rai.
A hankali na ɗaga ƙafafuna da suka min nauyina fita a ɗakin,
Ta gaban Hajjo na wuce wadda ta tsaya bakin ƙofar tana jiran fitowa ta.
Tana ganin na wuce tabi bayana, muna tafe tana zagi na tare da aibata ni.
Kasancewar akwai ƴar tazara tsakanin Lungun ɗakina zuwa ƙofar ɗakinta hakan yasa ta rigani isa.
Ina zuwa na tarar ta shige ɗaki, a hankali na kai kallona gurin kayan wanke-wanken masu uban yawa sai kace gidan biki.
Roba na ɗauka na ɗi bi ruwan ɗauraya na duba cikin kwanukan, sai naga babu kilin a cikin. Ƙofar ɗakin Hajjo naje na tsaya daga bakin ƙofa nace "Hajjo banga klin ɗin ba."
Kamar jira take na dire ta fara sababi, ke ina naki da ba zaki ɗauko ki yi amfani da shi ba, ko ke kika siya Marowaciyar banza da wofi, in zaki ɗauko ki ɗauko in ba zaki yi ba ni sai na tashi naje wajen wanda ke siyan klin ɗin, inji koshi yace inya siyi abu karki mana amfani dashi.?"
Juyawa nayi jikina a sanyaye, na koma lunguna na ɗauko klin ɗin banbari Ahmad yasan da dawowata ba, gudun kar ya tambaye ni ko yatsayar dani.
Ina komawa na fara wanke-wanken.
Jin motsin buɗe ƙofa yasa na juya, na kalli inda naji motsin.
Ɗanladi ne ya fito daga ɗakin dake kusa da zaure. Cikin takaici na kalle shi daga shi sai ɗan gajeran wando wanda ko cinyar sa bai gama rufewa ba.
Sai da ya kalle ni tukun yayi miƙa, idanun sa a kaina cikin kallon da ya saba min wanda bana so, bansan me yasa kullum muka haɗu ya ke bina da kallon ba,
In da sam ni bana jin daɗin hakan da ya ke min.
Babu zato naji motsin mutum kusa dani, ina juyawa naga Ɗanladi ne, butar dake kusa dani yasa hannu ya ɗauka.
Cikin mamaki nake binsa da kallo, ganin ba butar kaɗai bace a tsakar gidan, amma sai ta kusa da ƙafata zai ɗauka.
Ban ɗaki ya shige, na bishi da kallo cikin takaici. Yau sati na biyu kenan a gidan amma halayen mutanen gidan sun fara bani tsoro.
Banga abin dana tsare musu ba, haka kawai sun tsangwame ni kowa da halin da ya ke nuna min. kauda kaina nayi cikin jin takaicin halayyarsu ta rashin kunya, da rashin ganin girman ɗan adam inda na gama fahimtar da gudummawar mahaifiyar su a cikin hakan. Sam bata ɗora su akan kyakykyawar hanya ba, Nasan cewa a girme Ɗanladi ya girme ni, amma duk da haka ina ganin kodan matsayina na matar yayan su, yaci ace ya martaba ni.
Sai dai sam babu wannan a tare dasu dukan su, babu me min kallon arziƙi bare gaisuwa ta haɗa mu.
Kullum burinsu su ganni cikin ƙunci.
Koda ya fito daga banɗakin, sai da ya zo daidai in da nake ya ajiye butar a inda ya ɗauka, kamar wanda zai faɗomin haka yayi.
Sai kuma ya miƙe yana tafiya cikin rashin kunya.
Ban ko ɗago na lalle shi ba, na cigaba da aikin gabana ina Allah-Alllah na gama na bar wajen.
Umar autan Hajjo na gani ya zo ya fara birkita kwanukan da ban wanke ba, wata roba ya binciko ya miƙo min ba tare da ya damu da kwanukan da ya zubar ba yace "Wannan robar zaki wanke min kuma ni gaskiya ki ɗaurayeta sosai, dan jiya ina cin abinci ina jin warin Klin alamar ba'a ɗauraye kwanukan da kyau ba.
Kallon shi kawai nayi, ina jin wani abu ya tsaya min a wuya, yaro ƙaramin irin Umar wanda dududu a haife da zai fi sa'an ƙanwata ta huɗu ba, shine yake sani abu kamar wata ƴar aikin sa.
Kai na yarda wani abin in yafi ƙarfin mutum bashi da yadda zai yi sai addu'ar neman sauk'i wajen Allah.
Wanke robar nayi na bashi, na tattara sauran daya zubar na wanke, na kai kayan can kan wani ɗan tebur ɗin katako da take ɗora kwanika na aje nasa tsintsiya na sharce ruwan.
Har ma nufi hanyar barin wajen da niyar komawa ɓangarena.
Naga an bankaɗo labulen ɗakin Hajjo ce ta fito cikin isa da gadara tace "Ke dakata ina za ki?."
"Jikina ne ya hau rawa, Allah ya sani ina matuƙar tsoron Hajjo, dan sam bata sakar min fuska ko kaɗan, nan da nan gabana ya hau faɗuwa, na shiga addu'ar Allah yasa ba wani aikin zata haɗa ni dashi ba.
Sai da ta ƙaraso kusa dani tukun tace "Kinga dawowa za ki yi ki jik'a min tumatir ɗin, kafin kije ki kwanta barcin jarabar da kika saba, in ba lalaci ba ace kina mace kin maida barcin safe aikin yi, sai kace farillah."
Sunkuyar da kaina nayi nace "Ina tumatir ɗin?."
Sai da taja tsaki tukun ta shiga ɗaki ta ɗauko ƙullin tumatir ɗin a bak'ar leda, amsa nayi na nufi bakin murhun Allah ya taimake ni akwai ruwan zafi a tukunya na juye a ciki.
Ina jimamin hali irin na Hajjo na shegen mammak'on jaraba, ba ƙaramin kuɗin cefane take amsa wajen Ahmad ba amma abin takaici bata iya yin cefane me kyau, kullum sai dai ta sai bushashshen tumatir. A cewarta miyarshi tafi afki, sai dai kaga miyar baƙik'k'irin dama ba wani man kirki ake zuba mata ba.
A ɗan zaman da nayi da Hajjo na fahimci Hajjo irin matan nan ne masu shegen mammak'o da son abin duniya, ga yar banzar rowar tsiya.
Ko abinci tayi in dai kaga tayi kyautar shi, to lallai baƙi tayi shima kuma sai baƙin da suka amsa sunan su, dan in ta raina hankalin ki ko kin zo wajen ta haka za tayi fuska ko a gaban ki ta gama abincin, sai tace a kai tukunyar ɗaki har sai baƙuwar ta tafi za'a raba abincin ranar.
In kuma irin yara ɗin nan suka zo gaida ta kamar ranar juma'a, a gabansu zata raba in kaga ta basu a kwano to sai Umar ko Salaha sun ci sun rage.
In basu rage ba sai ta zuba a wani ɗan kwano ta rarraba musu a hannu, in zasu tafi tace su gaida gida in sunyi Sa'a ta raba musu naira goma-goma.
Hajjo na matuƙar son ƴaƴan ta, bata haɗa su da komai bata son laifinsu, In kana son ka ɓata da Hajjo kaga ɓacin ranta to ka taɓa mata ɗa ko ka kawo ƙarar ƴaƴan ta, komin munin abin da suka yi bazata taɓa tsawatar musu ba.
Sai dai kai ta nuna jin haushin ka a fili, tace haƙuri ake da yara kowa yana da maraji a ɗakin sa.
Hajjo mutum ce me ƙin gaskiya a rayuwar ta, ga sa idon tsiya akan harkar da bata shafe taba da son aibata mutum daga taga yana wani abu na ba daidai ba, ta dinga yaɗawa wane yayi kaza-wane yayi kaza kenan kamar abin kirki.
Gata bata son taga cigaban wani a rayuwar ta, ita Indai ba ita zata samu abuba ba ko Ƴaƴanta to fa kowa karya samu.
Rayuwar gidan wata irin rayuwa ce a waje na, komai a jirkice nake ganin sa, kasancewar duka mutanen gidan duka yare ne.
Gidan irin babban babban gidan nan ne, kai tsaye za'a iya kiran shi da gidan gandu.
Kuma ni da Hajjo ne kawai hausawa sauran duk nupawa ne, gidan irin ginin mutanen da ɗin nan ne wanda ke ɗauke da sashi-sashi kowa da ɓangaren sa.
In ka shigo babban zauren gidan da Ɓangaren Hajjo zaka fara tozali, su biyune da ita da wata mata wadda ake kira da Maman A'isha.
Daga ɓangaren hannun hagu wani ɗan lungu ne, anan ɗakina ya ke inda ni ni kaɗai ce a ɓangaren.
Daga ɓangaren dama kuma hanya ce da zata kai ka har zuwa ainahin cikin gidan, nan ne sauran mutanen gidan suke kowa da ƙofar shi, sai dai ginin babu wani tsayi kana iya hango mutune.
Wani irin zama mutanen gidan suke da junan su, wanda ban taɓa ganin irinsa ba, gulma munafurci hassada rashin son ganin cigaban juna, ƙyashi.
Kai in har baki iya zaman camba ko baki iya kawo labarin gulma ba, tofa kinci baya ba zaki samu masu yin harka dake ba.
Zama ne ya kawo Baba garin har Allah ya haɗa shi da mutanen kirki, suka bashi wajen zama kyauta In da har ta kai sun zama tamkar dangin juna, sai dai fa a ɓoye ta ciki na ciki ne. Kowa da haushin ɗan uwan sa ya ke rayuwa.
Da sallama na shiga ɗakina, nayi ya kai sau uku Ahmad da ya lula duniyar tunani bai ma san ina yi ba. Ganin haka na shiga takawa a hankali na lallaɓa ta bayan shi, na karyi tsintsiya dake ƙasan kujera na ɗan sosa masa ita a kunnensa.
Firgigit ya juyo ya kalle ni yana shafa kunnen na shi, nan na ƙyalƙyale da dariya ina faɗin "Tunanin me kake har ma shigo baka sani ba.?"
Murmushi yayi kawai ba tare da yace komai ba. Hakan yasa na ɗan tsuke fuskata nace "Haka kawai ka zauna kana sana,ar taka ta tunani ko? ya kamata kadaina yawan sa tunani a ranka dan Allah."
Na ƙarasa cikin ɗan karya wuyana.
"Uhmm" kawai yace ya kamo hannayena ya dawo dani gaban sa,
Ya kafe ni da idanun sa waɗanda ke rikita ni a ko yaushe, aikuwa da sauri na sunkuyar da kaina cikin jin kunya.
Dariya ya ɗan yi cikin tausasa murya yace
"Mutum sai tsokanar tsiya, in an kama shi yayi tsuru-tsuru kamar mara gaskiya."
Ƙwace hannu na nayi na rufe fuskata cikin jin kunya, sai ya ɗan matsa ya jawo ni ya zaunar dani kusa dashi har jikin mu na gogar juna.
Ya ɗan leƙa fuskata ya kira sunana a hankali "Menah buɗe fuskar mana."
Ƙara rufe fuskar nayi gaba ɗaya ina jina a takure, har yanzu bana iya sakin jiki gaban Ahmad wata irin kunyar shi nake ji a duk lokacin da muka kaɗai ce haka.
Da ƙyar na ɗago na kalleshi da dara-daran idanuna, yasa hannu ya kama haɓata cikin lallashi yace "Dan Allah kiyi haƙuri abisa abinda Hajjo ta miki, duk halayen da take nuna miki bana jin daɗi, kiyi haƙuri Wallahi bansan yadda zanyi bane da ina da dama dana hana faruwar hakan Menah. Allah ya sani ba ason raina hakan ke faruwa ba kiyi haƙuri kin ji."
Ya ƙarasa hakan Muryar shi gwanin ban tausayi.
Gaba ɗaya wani irin tausayin sa ne ya kama ni, jin zai cigaba da magana yasa nayi saurin sa hannuna na rufe masa baki nace "Dan Allah ka daina bani haƙuri, nima fa Hajjo mahaifiyata ce in ban mata biyayyah ba wazanwa? tana da ikon sani kuma tana da ikon hana ni, bayan nan kaga bani da wasu ƴan uwa garin nan sai ku ni kallon uwa nake wa Hajjo ban taɓa mata wani kallo ba, na ɗauki abin da take min a matsayin kulawa tana ganin ta isa da ni ne shiyasa. Kuma kasan koda ban aure ka ba Hajjo zata iya sani kuma ta hanani na hanu, kaga kenan dan tamin haka aiba komai bane."
Kallona naga yana yi kawai ba tare da ya cire hannun sa daga haɓa ta ba, cikin nuna jimami ya girgiza kai yace "Duk da haka ki yi haƙuri kin ji."
Ina iya hango zallar tausayina a idanun sa.
Gyaɗa masa kai nayi dan ya barni nace "Bari na dan kwanta na huta kaɗan kafin lokacin ɗora abinci."
Miƙar dani yayi tsaye yace "Taho muje mu kwanta nima barcin nake ji." Gadon muka haye ya rungume ni ya yana shafa gashin kaina mai yalwar yawa da tsawo, ga gyara na musamman da nake ƙoƙarin yi akoda yaushe cikin amfani da mayukan gyaran gashi masu inganci nake. Shi yasa Ahmad in dai zamu zauna to hannun sa baya zama ya dinga aikin shafa kaina kenan. Na fuskanci Ahmad nason gashi a rayuwar shi, shima yana yawan faɗa min hakan hiyasa bana wasa da gyaran gashi ko kaɗan.
Ahaka barci yayi awon gaba damu, can cikin barci naji kamar ana ƙwank'wasa ƙofar net ɗin ɗakina, a hankali na buɗe idona na kalli fuskar Ahmad ganin shima barcin ya ke cikin dubara na zame daga jikin sa ahankali don gudun kar na tashe shi.
Ɗankwali na na ɗauka na ɗaura nasa hijabina ɗan madaidaici, sannan naje na buɗe ƙofar tare da leƙawa dan ganin waye.
Ɗanladi na gani tsaye, Yana ganina ya wani zuba min ido kamar yadda ya saba yana jifa na da kallon da har yau na rasa na meye.
"Lafiya?." Na faɗa cikin jin haushin sa.
Sai da ya karkata kansa kamar mai son leƙa ɗakin, Sannan yace "Eh lafiyar ce ma ta kawo ni, kin riga da kin san lokacin ɗora girki ya yi shine kika wani shige ɗaki ke me miji. To Hajjo ce tace na kira ki."
Ya faɗa cike rainin hankali.
Kamar nace ya je yace ba zan zo ba saboda haushin da ya bani, sai na daure nace "Kace mata ina zuwa to."
Na juya na kulle ƙofar ina jin takaicin tashi na da yayi, haka kawai mutum bai isa ya huta ba barcin dana kwanta ko minti talatin bai kai ba, shine har an zo ta shi na saboda ba'a ƙaunar na ji daɗi.
Tsintsiya na ɗauka na shiga tattara ɗakin, tunda nasan in na fita ba dawowa zan yi yanzu ba. Ina cikin sharar ɗago kan da zan, sai naga Ahmad zaune ya jingina da fuskar gadon yana kallona, alamu sun nuna ya ji duk abin da ƙanin nasa yace dan yanayin fuskar sa ya nuna rashin jin daɗin.
Fuska nayi danma karya kawo min wata magana, dan nasan yanzu zai fara bani haƙurin nashi.
Ba kuma dan bana san haƙurin bane, sai dan banaso a koda yaushe ya dinga ganin laifin ƴan uwanshi ta dalili na.
Ganin shi nayi kusa dani ba tare da nayi zato ba, ya miƙo min hannu yace "Bani tsintsiyar in share ki je ki yi aikin, kin ji Ƴar aljannah ta Allah ya miki albarka, ya baki masu yi miki kema ya bamu zuri'a ta gari."
Naji daɗin addu'ar shi gare ni, da "Amin" na amsa ina murmushi cikin jin kunya.
Duk yadda na so ya bari na ƙarasa yaƙi dole na bashi, na fita dan gudun nayi wani laifin wajen Hajjo.
Koda naje na tarar harta dora tukunyar, kallo ɗaya tamin ta ɗauke kanta ta cigaba da abinda take.
A sanyaye nace "Hajjo ina shinkafar.?"
Na riga da nasan sai nayi zaman tsintar shinkafa dole.
Nuna min robar dake kusa da ita tayi tace "Gata nan in kinga dama ki zo ki ɗauka."
Ƙarasawa nayi na ɗauki shinkafar na zauna kujera na fara tsincewa.
"Sauran kimin tsintar da ki ka saba ta shegen ha'inci, ba zaki tsaya ki yi abu tsakanin ki da Allah ba. Sai ki tsince shinkafa duk tsakuwa, sai anyi magana ki yi ta raba ido yana shege a rabon gado, daɗin abin ke ake zubawa ta ƙasan."
Bance mata komai ba, sai Umar dake gefe yana rubuta _assignment_ ɗin sa ya ƙyalƙyale da dariya yace "Hajjo kinsan kuma hakan shine maganin wanda baya tsayawa yayi abu da kyau ko?."
A hankali na ɗago na kalle su, a zato na zata tsawatar masa,
sai naga ita ma ta yi dariya tace "A she ka sa ni Umaririna, kaga yi sauri kagama rubutun ka zo ka kai min kuɗin adashin nan gidan Faɗiime, kace nace har na sati me zuwa dan bana son abini bashi inna ajiye kuɗi nan cinye su zanyi gashi nice da ɗaukar gaba."
Baki ya zumɓuro gaba yace "Haba Hajjo ni in na gama gaskiya gajiya zan yi, ga shi rana tayi kisa a kirawo Shamsu mana yana ƙofar gida babu abin da ya ke yi."
Madadin ta tsawatar masa ko tace sai ya je sai cewa tayi "To shikenan tashi ka kiramin Shamsun."
Kamar ba zai tashi ba, sai da ta ƙara magana ya tashi yana diddira ƙafa cikin gunguni ya tafi.
Ina jin su na cigaba da aikina, har na kammala tsintar shinkafar na wanke na zuba na ɗauki tumatir ɗin dana jiƙa ɗazu na wanke, na haɗa da attaruhun na ɗauko dutsen niƙa irin na da ɗin nan, dan da shi na tarda Hajjo na niƙa kayan miya a cewar ta miyar niƙan hannu tafi afki.
Ina cikin niƙan sai ga Sani ya shigo, ya kalle ni ya kalli Hajjo dake zaune tana ƙulla kayan miyar da take saidawa yace "Hajjo wai yau ma ita kika bawa niƙan kayan miyar nan, bayan kin san ba iyawa tayi ba kullum fa sai ta bar mana naman miya a ciki, mutum yayi ta faman tauna tumatir haka kawai shi ba nama ba, sam basa niƙuwa."
"A'a Sani Wallahi ba iyawa ne ba tayi ba, tsabar mugunta ke hana ta niƙan ya niƙu."
"To Hajjo ki bada akai bayan layi mana a niƙo, ga nera ɗari ni bana son miya ana tauna kayan miya gaskiya."
Sai da ta amshe Naira ɗarin tukun tace " Ni kam miyar hannu tafi min daɗi ga auki, banga ƴar da zata sani kai niƙa injiba haka kawai ina zaman zamana ta sani cacar kuɗi, ta ƙarasa da soke ɗarin tace "Ai wannan sai asai wani abun da ita."
Tsaki yaja yace "Ke fa Hajjo abinda ya ke haɗa ni dake kenan, son kuɗin ki yayi yawa Wallahi,
dana sani ba zan bada kuɗin ba Allah."
Ya wuce ya buɗe ɗakin su ya shige.
Mita ta dinga yi tana banbami sai kace ni nace akai kayan miyar inji.
Kafin in kammala niƙan tuni shinkafar ta tsotse, na sauke na ɗora tukunyar miyar shima manja ita ta tsiyayamin da kanta, ina gama soya miyar ta zo ta maka mata ruwa, wai sai tafi isa Ni kwa nace ikon Allah. Ina mamakin yadda suke zuga ruwa a miyar dage-dage kana cin miya sai kace romo.
Kamar yadda aka saba ina na ɗauki tukunyar abincin gaba ɗaya, na dire a gaban Hajjo na je na harhaɗo kwanikan da ake zuzzuba abincin na jajjera gaban ta, kowa da kwanan da duk yaran ta su shiddan.
Sai na Baba mijinta dana mutanen gida su uku take bawa, kuma duk ranar da basu bata ba bata basu ita ma.
Ganin na koma gefe na tsaya, yasa ta ɗago ta galla min harara cikin tsawa tace "Sai nace ki je ki ɗauko taki kular zaki kawo?."
Juyawa nayi na ɗauko dama ban kaita wajena ba tunda nayi wanke-wanke , dan nasan a ciki za'a zuba min in an gama abinci.
"Miƙo min kujera To tunda sai nace."
Ɗauko mata kujerar nayi na ajiye, nasan ta gani amma sai da nace "Hajjo na gama." Sannan ta taso ta zo ta zauna ta shiga raba abincin.
Gefe na koma na tsaya ina jiran ta gama.
*BAN MUKU ALƘAWARI POSTING KULLUM BA, IYA YADDA KUKA AMSHE SHI IYA YADDA ZAN JI ƘARFIN BAKU.*
*_🥰MAMAN DAN ALBARKA CE_*🥰✍️✍️