Chapter 2
🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Young Talented Writers Ass.
page 2
*Bayan wasu shekaru....*...
Tsaye take a gaban dressing mirror tana makeup, ta dangwala wancen ta shafa wancen fuskar nan ta ɗauki hoda da jambaki bajau. Matashiyar budurwa ce wacce ba za ta gaza shekara 20 zuwa da biyu ba. Daga bayanta A'ishatu ta tsaya cikin yanayin damuwa ta ce "Oh Allah Salmah mu je mana yamma na ƙarayi fa, kuma sarai kin san idan 5:30 ya yi Ammi ba za ta barmu mu fita ba ko?” Ba tare da ta juyo ba, ta na ci gaba da abinda take yi cikin sauri sauri take faɗin "Sorry Sister dan Allah ki yi hakuri 2 minute, eyeliner kawai ya rage min." Gyara tsayuwa ta yi tana bin bayanta da kallo, a zuciyarta tana mamakin shegen son kwalliyar Salmah, kamar wacce Aljanin kwalliya ya aura, sam bata iya zama da fuska a bushe sabanin ita da ko kwalli da man leɓe, wata rana sai Ammi ta fatattake ta take sakawa. Turo ƙofar ɗakin a ka yi, Salman ya shigo babu ko sallama, a dan fusace ya ce "Zo mu wuce sister, mu bar ‘yar rainin hankalin nan, ita ba kyau ba sai shegen iyayi, ace kullum idan za mu fita sai ta ɓata mata, da wannan fente fenten nata na banza." Ya ƙarashe maganar tare da kama hannun Aysha ya shiga jan ta su tafi, ita kuma ta ɗan tirje. Juyowa Salmah ta yi ta auna mai wata uwar harara da manyan fararen idanunta da ta ƙara ƙawatasu da ƙwale-ƙwalen kwalliyarta “To almunafunfun, ba za ta bi ka ba, sai ta jira ni ɗin, idan ka matsu ka yi tafiyarka, sai mu sa driver ya kai mu." Ta karaso itama ta kama d'aya hannun Aysha ta riƙe, tsaki ya ja ya yi ƙwafa, tare da cewa."Banza mummunan kawai.” Zaburowa ta yi kamar za ta kai mishi duka, a tsiwace tace "Salman ka kiyaye ni." Mari ya kai mata, da sauri ta saki hannun Aysha ta dunƙule ta kare fuskarta, ya sake yin ƙwafa, ya ɗauke hannunshi ba tare da ya isa jikinta ba, yana auna mata hararar tare da faɗin “'Yar banza ga tsoro ga mugun aiki." Jin bai sauke mata yatsun nashi ba kamar yadda ta zata, yasa ta ɗago tana ci gaba da hararan shi tace "Me yasa ka fasa, ai da ka mareni ka gani.” “Mitsssw! Aikin banza kawai.” ta furta bayan ta ja dogon tsaki. Zai yi magana, Aysha ta dakatar da shi a da cewa "Dan Allah Salman ya isa haka, wai yaushe za ku girma ne saboda Allah? Ku kenan kullum cikin tashin hankali sai kace ba 'yan uwa da suka fito cikin mahaifa ɗaya ba. Ku ba yara ƙanana ba balle ace ba ku da hankali, wlh lamarin ku ya fara isana, ni mu tafi yamma na ƙara yi.” Yadda ta yi maganar a ɗan zafafe yasa Salman bai sake tankawa ba sai ya yi ƙwafa ya girgiza kai yana kallon Salmah dake banka mai harara ya ja hannun Aysha suka fice daga ɗakin, Salmah ta rufa musu baya tana ‘yan kungunai.
A falo suka samu Ammi zaune tana kallon Sunnah Tv, tun daga yanayin yadda taga fuskokin twins ɗin nata, tasan an raba hali, lamarin su yanzun ya daina damun ta, idan suna abin su babu mai shiga domin a nan take za su baka kunya, yi tayi kamar bata ga abun da suke yi ba. Sallama suka yi mata, ta yi musu addu'a tare da kashedin cewa karsu kai magriba, idan ba haka ba sun kashe hanyar gobe, har suna had'a bakin gurin cewa "in sha Allah Ammi ba za mu daɗe ba." Tace "Allah yasa." Har sun kai bakin kofa tace "Amm! A'ishatu." Cikin sanyinta wanda ya zame mata wani ado na musamman ta waigo tare da cewa "Na'am Ammi." "ki kula da kanki, ki kula da waɗannan shashashun da kullum basa girma karki bari su raba hali a cikin jama'a kin ji ko?" Ɗan dariya ta yi tare da cewa "in sha Allah Ammi zan kula sosai." Tace "OK bye kowa yamin tsaraba,da abinda na ke so, zan tantanece cikin yaran Ammi wa yafi sanin abinda Ammi ke so yau.” cike da tsantar kulawa da kauna ta yi maganar, Salmah ta ce "Ni zan lashe game ɗin nan domin nafi kowa sanin abinda Ammina ke so, kuma za ki gani." Salman ya auna mata harara tare da cewa "yen yen yen yen! da dogon bakinta kamar Hajiya Saude na gaba tana binta a baya." Duk dariya suka saka mata, aikam ta ƙulu idan da abin da Salmah ta tsana a duniya ace tana kama da kakarsu mahaifiyar Abbbansu wacce suke kira da Hajiya Saude, dalili kuwa, sam kanwarsu bata ciƙuwa waje guda, duk da kasancewar kuwa a zahirin gaskiya kama suke kamar an tsaga ƙara. Ganin yadda suke mata dariya harda Ammi yasa ta kara ƙuluwa cikin fushi ta bud'e kofar falon ta fice da sauri fuuu! kamar zata tashi sama.
A parking lot suka tadda ita jingine jikin motar Ammi wanda a shine Salman zai ja su, ko kallonsu ba ta yi ba ta buɗe bayan motar ta shige, suma basu ce mata komai ba suka shiga, Salman ya zauna a mazaunin driver Aysha ta zauna a gefensa ya tada motar mai gadi ya wangale masa get yana daga mana hannu tare da yi musu a dawo Lafiya. kallo ɗaya Aysha ta yi wa mai gadin ba tare da ta amsa shi ba ta dauke kanta tare da hade girar sama data ƙasa, saɓanin Salman da Salmah da suka amsa mishi a sake cike da kulawa. A haka suka fice daga gidan, tare da daukir hanyar *kangiwa green land* Bayan sun daidai ta akan babban titi, kallo Aysha salman yayi yace "Sister me yasa baki son mai gadin nan namu ne? Ina lura dake baki amsa gaisuwarsa, kuma ko fara'a kike idan ya yi magana sai ki hade rai, alhali yana da mutunci ni banga aibun shi ba, ko wani abu mara kyau ya taba haɗa ku ne bamu sani ba?" Dan kallonsa ta yi tare da ɗauke kai a hankali cikin yanayin ɓacin ran da ba za ta ce, ga musabbabinsa ba tace "Babu abin da ya taba haɗa ni dashi Salman, bana son sa ne kawai saboda sunan sa *Babangida*." Kasancewar shi gwanin barkwanci sai yayi dariya yace "Me sunan *Babangida* yayi banda rigima irin taki, kya ma dai faɗi gaskiya" Dauke kai tayi ba tare da ta bashi amsa ba a haka suka iso kangiwa green land.
*kangiwa green land* fitattace ne kuma sanannen babban shopping mall wanda sunan sa ke amsa kuwwa aciki da wajen birnin Kaduna. Wuri ne da ba ko wane irin mutum kara zuɓe ke iya zuwa domin yin siyayyaba sai wanda yaci ya tada kai da masu gida rana. Wuri ne da yan mata da samari 'yan hutu y'ay'an manya dama y'ay'an y'an uwana talakawa y'an karyan nera ke karakainin zuwa domin shakatawa da kuma siyayya musamman da yammci idan kaje gurin wurin zaka same shi cike da matasa, har ma da manya dama ƙananan yara jefi jefi. Kamar kullum yau ma wurin cike yake taf kowa na harkar gaban shi, a daidai wannan lokacin, Salman ya yi parking a farfajiyar wurin, fitowa su ka yi suka nufi cikin wurin domin yin shopping wanda dama shine abin da ya fito da su daga gida, kowannen su daukar basket yayi suka fara tsintar abin da su ke so tun suna yi a tare har takai ga sun rarrabu kowa yayi nashi ɓangaren. Mintuna 30 bayan rabuwarsu Aysha ta kammala sayayyar duk abin da take bukata harda na Ammi da tace su siyo mata, tunanin ta inda zata fara neman su Salmah ta shiga yi dan a zahirin gaskiya kangiwa green land, babban wajene na bugawa a jarida, kamar daga sama ta jiyo sautin gudu daga bayanta tare da dan hayaniya da sauri ta jiyo, su ɗin ne ke tafe kamar yadda tayi tsammani, tsayawa tayi ta riƙe kugu tana hararar su, wannan lamari na tagwayen Ammi na ci mata tuwo a kwarya, sam basu kula da yanayin da take ciki ba sai ma Salmah dake gaba ta ƙaraso bayanta tare da ƙamƙameta tana cewa "Sister ki boye ni Salman zai dukeni." shiko Salman ƙokarin kai mata cafka yake yi tana dojewa tare da tura Aysha dake kokarin hanashi dukan nata har hankalin wasu daga mutanen wurin ya fara dawowa kansu, suna cikin wannan yanayi kamar daga sama su ka ga an canja hasken wajen ya koma wani irin launin wuta mai kala kala tare da bada wani sauti ɗin! ɗin!! ɗin!!! kafin su gama mamaki su ka ji sufikun dake maƙale a kowani kusurwa na wajen sun d'auki kururuwa da shelar cewa ana ba kowa da kowa umarnin da ya ajiye duk abin da yake yi ya fita an ba kowa five minutes, a tsorace suka shiga tambayar juna mekefaruwa, sai dai cikinsu babu wanda zai iya baiwa wani amsa, tuni firgici ya gama bayyayana ƙarara a fuskar Aysha domin tamkar farar kura take wajen tsoro. Kafin su dawo daga wanna shock ɗin suka tsinkayi muryar wasu manyan y'an mata daga gaban su, cikin farin ciki dayar ke cewa ɗayar "ke Hafsa kamar Mr AA kangiwa ne fa ya kawo ma wurin ziyarar bazata." , cikin zaro ido wacce a ka kira da Hafsa ta ce "kice wlh." "wlh kuwa haka na ji yanzu ana ta fad'a." Ihun murna Hafsa ta saka tare da rungume kawarta cikin wani irin matsanancin farin cike take cewa "finally yau zan ganshi ido da ido wayyo daɗi kashe ni." Sosai Aysha ta cika da mamakin halin da y'an matan nan suka shiga, sai dai bata kai ga jefawa Salman tambayar da ke sakadar zuciyarta ba, taji Salmah da ke kusa da ita ta kurma wani uban ihun murna tana tsalle a rude take cewa "Mr AA kangiwa Innalillahi Salman where is my phone, a she da rabon zan ganshi ido da ido wata rana wayyo ni salamatun Ya Anas yau ina cikin Alheri" Shima Salman ɗin duk a ruɗe yake da farin ciki jin wai Mr AA kangiwa yazo wajen , kan Aysha gaba ɗaya ya gama kullewa, Mr AA kangiwa, Mr AA kangiwa, haka ta yi ta maimaita sunan a zuciyarta kamar mai bitar hadda, tabbas tasan sunan, ba yau ne karan farko data fara jin sa a bakin mutane ba. Shin wanene shi? Wani matsayi gareshi haka da kowa ke rawar 'kafa dajin sunan shi, shiba sahabi ba, shiba wani shahararren malami ba, Hannunta da Salman ya figa da sauri ya jata su ka yi haryar fita daga wurin shine ya katse mata tunani, a guje Salmah da duk ta wani susuce ta rufa musu baya. Rige rigen fitowa suka samu anayi kowa ka gani Kalmar Mr AA kangiwa ke bakin shi, jikin Aysha bai 'kara yin sanyi da lamarin ba sai da taga yadda manyan y'an mata masu ji da kansu y'ay'an masu kuɗi suka ruɗe, da jin zuwan wannan d'an taliki da sunan sa ke amsa kuwwa a kunnayenta, kuma abin mamaki baga yan mata kawai ba harda ma zaratan samari masu ji da kansu dake wurin, fuskar kowa cike da farin ciki tare da zaƙuwa da ɗokin son ganin mamallakin wannan suna, mamaki bai kara kasheta ba sai da suka fito harabar wurin taga cincirundon y'an jarida, gidajen redio dana talabijin babu iyaka ga polisa summa wajen kewanya. Wai ashe ma duk wannan karakainin da a ke yi kan jirgin bai riga ya ƙaraso wajen ba labari kawai aka samu yana hanya shine fa duk wuri ya ruɗe, duk da ba ta san wanene shi da kuma matsayin da yake dashi a wurin mutane ba, tana da tabbacin shi ɗin na musamman ne, haka kurum ta tsinci kanta da son ganin koma wanene wannan mutumin ɗan baiwa mai dubun masoya haka. Salmah ce ta dinga kutsawa dasu gaba gaba inda za su samu su ganshi da kyau, tuni wurin ya kara haɓɓakewa da mutane , da alama ba iya waɗan da ke cikin wurin kawai ba ne ke dakon jiran isowarsa harda wad'an da suka samu labarin zai zo suka taso takanass dan ganin shi. Polisawa sai aikin kakkare mutane su ke yi domin samar mashi da hanya, Aysha dai na tsaye kusa da Salmah da duk ta gama rud'ewa sai wani rawar jiki ta ke yi tana jiran ganin ikon Allah, tsayuwar su kamar da minti ashirin, suka fara jiyo wani irin jiniya mai masifar ƙara, wurin ne ya dauki hayaniya masu ihu nayi masu cewa gashi nan ya iso nayi kowa na fad'in albarkacin bakin shi, Sosai Aysha ta zuba wa hanyar da take da tabbacin tanan nake jiyo 'karar jiniyar ido. Da wani irin mahaukacin gudu wasu zafafan motoci masu mugun tsada suka shiga shigowa wajen a jere, a tare suka shiga yin parking cikin wani salo na gwanancewa, take wurin ya kara daukar sowa da tafi, yanayin shigowar motocin da yanayin parking d'insu ma kawai abin birgewa ne ga mai kallo balle kuma batun kyawu da tsadar motocin, motocine guda goma sha daya reras, gaba dayan su bakake sai guda ɗaya tal na tsakiyar su wanda ya kasancewar fari sol sai daukar ido ya ke yi kwace da diamond a ka ƙera shi. Kusan mintuna biyar suka dauka kafin a hankali murafen bakaken motocin su bud'e a tare a lokaci guda, wasu irin zaratan majiya karfin escort suka shiga fitowa daga cikin motocin sanye da bakaken suit fuskokin su sanye da maka makan space irin no respect d'innan tsit kake ji wuri ya dauki shiru kamar ba shi ba ne yanzu kamar zai fashe da hayaniyar jama'a, d'aya daga cikin escort d'inne ne ya 'karasa gaban farin motar ya bud'e kofar baya tare da matsawa gefe d'aya ya kame kamar gunki, sai da ya share mintuna biyu sannan ya zuro 'kafafunsa dake sanye cikin wasu arnayen ba'ka'ken takalma sawu ciki masu masifar kyau waje, zuru kowa yayi ana jiran ya 'karasa fitowa masu yin video irin su Salmah tuni dama suka fara kwasa abinka da zamani na social media, abin watsawa baya kadan to balle baiyanar AA Kangiwa da ranar Allah ai abin kallo ne ga jama'ar Kaduna kai jama'ar Nigeria ma gaba ɗaya, wasu ma live su ke daurawa, sai da ya kuma kwashe wasu mintuna uku kafin ya zuro sauran jikinshi gaba d'aya waje, yadda lokaci d'aya gurin ya d'auko wani irin sowa da tafi sai da Aysha ta firgita, inda kasan wad'an da aka ba umarni a tare kamar irin a fillin ball din nan anci kwallo, yana fitowa escort ɗin shi guda shidda suka layu a bayan shi yayin da sauran ke tsatstsaye a inda suke suna muzurai, ba ta gefen da su Salmah suke ya fuskanta ba ya juyo musu baya, hakan ya yi musu shamaki da ganin zahirin fuskarsa. Tun da Aysha ta sauke idanunta a kan faffadar bayan shi dake sanye cikin wasu irin zafafan suit black masu mugun kyau da masifar tsada, wanda akalla kudin da aka siyen su ya ishi talaka zama karamin attajiri gabanta ya yanke ya yi mummunar faɗuwa haka siddan. Wata tsayuwa yayi irin ta zaratan matasa majiya karfi, ba ta san lokacin da ta furta, "Ya subhanah!." A bayyane ba. A tsaye yake ƙem dogo mai kirar cikakkun maza, sumar kanshi ma kawai abin kallone, gashin baki ne sidik saisayayyen irin tamu ta baƙar fata, sai dai a cike take da kan an yi mata askin zamani irin ta matasa masu aji, ga taushi wanda mutum zai shaida hakan ko a ido, sai sheki take tana daukar ido da gani ba karamin maƙudan kudi yake kashe mata ba. kwarai ta zaku da son ganin fuskar koma wanene wannan mutumin, bata dawo daga duniyar begen shi data lula ba, taga ya fara wata irin tafiya mai cike da ƙasaita da nutsuwa tamkar wani basarake, ya durfafi main entrance na mall ɗin, escort din shi biyu suka rufa mishi baya, yayin da sauran ke tsaye a inda suke kamar an dasa su, ji ta yi bazata iya bari ya shige wurin nan ba tare da ta samu nasaran ganin fuskar shi ba, tunanin ta yadda za ta samu damar ganin fuskar shi ta lalu, ƙur ta kurawa bayan shi idanu kamar zata hango fuskar shi a bayan nashi, Salmah ce ta katse mata tunani da cewa "Oh shirt! Sister Eshart mun tsaya ta bayan shi gashi bamu samu ganin fuskashi da kyau ba, zo mu kutsa ta can mu samu muje ta gaban shi kafin ya shige ciki." Kamar daga sama ta tsinci maganarta jin abin da take cewa yasa ta zabura ta damƙi hannunta da mugun sauri ta ringa janta suna rasta mutane suna kutsawa, burinta bai wuce tayi arba da fuskar shi ba, dai-dai sun iso ta gaban shi yana gaf da shigewa cikin wurin, cak ta tsaya tare da wani irin zaro idanu waje lokacin da idonuna suka yi arba da fuskarsa, fuskar da ko mutuwa tayi ta dawo ba ta jin zata bace a idanunta, a matukar dimauce ta furta *Babangida*
Rikita rikita shin da gaske Babangida Aysha ta gani a matsayin AA kangiwa ko kuwa gizo ya ke yi mata. Shin wai menene haɗin Shatou ɗiyar Baffa da Babangida ne? Yaya haɗuwar ta kasance? Tafiyar mai tsabta ce, nishadi kyauta, za a wasa kwakwale, zuciyoyi sa su yi laushi, dambarwa iya dambarwa let's go ma fiful wannan dai matashiyar marubuciyar ce da ta nishadantar daku da labarin DAMA TA BIYU, sannan ta sake gwangwaje ku da JOY kun dai san hannunta, to wannan tafiyar tasha banban da ta baya kar ku bari a yi babu ku.
Aysha Nalado
***.