ADNAN (The Artist)

Chapter 4

by @khairatup01

ADNAN(The Artist)
A 2026 Novel
Ummulkhair Sani Panisau 
(Khairat)
Ummulkhair Sani Panisau 

                    04

Nan suka yi zaune zugum suna jiran a kira su don su ga Adnan. Daga ƙarshe ma likitan cewa ya yi su tafi gida su dawo washegari.
*

"Malam ni fa na gaji da abubuwan da yarinyar nan take yi a gidan nan nema take yi ma ta wuce rawa da makaɗi haba ta hana yara sakat da zaman lafiya in ka ji gidan nan babu hanyaniya to bata nan ne ɗazu don Iskanci baka ga wulaƙancin da ta yiwa su Taheer ba haka fa ta dinga saka su gudu a titi suna bin ta kamar bata san su ba." Umma ta faɗa tana gungunai.
Baba ya gyara zaman sa yace "Ki ƙara haƙuri Bilkisu na san kina ƙoƙari da hallayen ta kuma ina gani Allah ne zai biya ki ba kowa ba shi ɗa ai na kowa ne sirri ne wanda daga ni sai ke ne muka san shi sai mahaliccin mu idan kika fara gazawa tun yanzu ai akwai matsala ni yaya zan yi?"

"Haƙuri na ne ya fara gazawa na soma gajiya ne abin ya fara kai ni intiha.Yarinya sai ka ce yayen aljannu."

Sai da ya yi Murmushi kafin yace "Ki yi haƙuri. Abinda haƙuri bai bayar ba rashin sa ba zai ba da ba. In dai Lamrat ce zan yi mata magana zan ja mata kunne tana cikin kalar yaran da faɗa baya mata komai kuma baya hana ta yin abinda tayi niyya. In kina son ki ci galaba a kan ta to tilas ne ki bi da ita da wasa a nan ne za ki samu yadda kike so amma ke faɗan nan ya riga ya zama jikin ki ba ki lura cewa yanzu yaran na duk sun yi wayo sun yi hankali fadan ma ya daina ɗaɗasu da ƙasa? Saboda sun gaji."
"Sai a kyale yara su yi yadda suke so fisabilillahi?"
"A'a amma yadda kike yi ne za ki sauya ki ja su a jiki kina musu nasiha shi ne zai sa ki samu kan su ba kya ganin abokiyar zaman ki?"
Sai ta sha mur ta juya tace "Dole sai an ɓatawa mutum rai a cikin dare sai da safe in ka gama ka kashe kyandir ɗin bacci zan yi."
Ya bi bayan ta da kallo yana murmushi a hankali yace "Mata halin su sai su."
*
 
"Ba amfani kenan aikin sa na baku? Meye amfanin barin sa da kuka yi da rai ni da na aika ku don ku hallaka shi? Ku saurare ni da kyau sai kun biya ni kuɗi na ba zan ɗau asara ba ga rashin dukiya ga rashin biyan buƙata a haka ne aka ce kune best killers a gari? Na raina ku Wallahi."
"Matsala aka samu wasu ne suka zo wurin bamu shirya ba amma ka ƙara bamu dama don mu wanke kan mu an ce yana asibiti bai san inda kan sa yake ba zamu iya zuwa mu ƙarasa shi a can."
"Baku da hankali ashe? Ku yi masa me a asibiti? Ko kun manta da cewa yanzu kowa ya san an kai mai hari ko an gaya muku naɗe hannuwa a ƙirji za su yi suna kallo ku je kuyi knocking a buɗe muku ku shiga kuce kun zo kashe shi? Are you guys stupid or what?"
Suka yi shiru. Ɗaya daga cikinsu da yake ta cijewa  ya fusata yace "Kai Oga Wallahi ka ci darajar a amma fa ka fara wuce gona da iri ya za ayi ka zo kana mana ihu kamar ba ka san su waye mu ba kar fa ka ja kafin mu far mai kai mu fara da kai?"  Ya faɗa cikin muryar yan daba ta asali.
Tuni ya shiga cikin taitayinsa ganin da manyan makamai a hannayen su suna kallon shi da mici-micin idanuwansu bakuna su baƙiƙirin suna zazzare musu idanuwa.
"Yanzu kana da ƙorafi ko kuma a ka gane ai?" Ya faɗa yana buɗawa yana wasa da wuƙa a iska.
"Na fahimta bani da sauran ƙorafi kuna iya tafiya na sallame ku."
Daya ya fashe da dariya yace "Ka ce da baka ji? Ko ka yi tunanin mu ɗin ƙananun kai ne? To hattara maza bisa kan ka."
"Na gane! Na gane ku je sai da safe."
"Ah! Ai ba ka bamu na mai ba."
Ya buɗe baki zai yi magana ɗaya yace "Kamar yaya me za ka ce ko ba za ka bayar ba ne?"
"Zan....zan bayar mana nawa zan baku."
"Ehuhuhu hayya maza hayya maza ni ne gugar takobi,sarkin  bugun gaba Allah Wallahi idan ka ji ƙarar ƙafata ka san bala'i ya sauka."

"Ka kula Alhaji daga yau mu ya'yansa ne amma ba da jini ba ta aminci da rantsuwa." 
Ba shiri ya shiga ya dauko rafar kuɗi ya basu. Suka tafi.
*
Washegari da ciwon kai ya tashi ƙoƙarin kama kansa yake yi amma sai ya ji kan na sa ya ji kamar an ɗaure masa hannaye. Sunan Allah ya ambata "Ya Rahman" sannan ya koma ya kwanta ba zai iya misalta kwatankwacin irin ciwon da kan sa ke yi masa ba amma tabbas yana jin raɗaɗi sosai. A hankali komai ya dawo masa na dalilin zuwan shi gadon asibiti amma bai san waya cece shi ba. Juyawar da zai yi ya ga an buɗe ƙofar ɗakin an shigo. Nas ce a hannun ta da wani plate da kayan wanke ciwo a kai. 
Tana ganin idanuwansa a buɗe tace masa "Ka farka?" Bai samu zarafin yi mata magana ba ta juya ta fita jim kaɗan sai ga shi ta dawo da Dr a bayansa su Mami ne.
Likita ya duba shi sake yi masa tambayoyi dan ya tabbatar da lafiyar ƙwaƙwalwar sa ya ba shi amsa yana murmushi yace "Alhamdu Lillahi babu wata matsala dama tsorona ko kan ka ya bugu sosai." Ya yi masa murmushi kawai.
Mami ta zauna a kan wata kujera da ke gefen shi tace "Sannu Adnan ,sannu ka ji yaya jikin na ka?"
"Da sauki Mami." Ya amsa mata a hankali.
Ta sa hannu ta shafa kan a hankali tace "Amma ka tabbata baya maka zafi?"
"A'a ba sosai ba kaɗan-kaɗan kawai."
"Shi kenan me kake so ka ci?"
"Bana jin yunwa."
"A'a ai mara lafiya sai da abinci ko ka manta za ka sha magani?" 
Bai bata amsa ba,Abba ya katse su. "To uwar iya nima ki matsa na gan shi ko? Kamar kin fi kowa son shi kin wani kanainaye shi duka." Ya faɗa da masifa. Mami dai ta matsa don ba kasafai ta fiya son kula shi ba.
"Yaya kake ji?"
"Am ok Abba."
"To shi kenan sannu ka ji Allah Ya kiyaye gaba Ya tsare amma an auna arziƙi Adnan."
Ya kalli Sahib. Sahib yace masa "Sannu Blaze ya jikin?"
"Da sauƙi. Su waye suka cece ni?"
"Wata baiwar Allah ce tace ma za ta zo ta sake duba ka."
"Allah Ya saka mata da alkairi. " Nas ta shiga ciki ta ce duk su fita haka a bar mara lafiyan ya huta. Duk suka fita daga ɗakin ko mutum ɗaya ba a bari ba.
*

"Yaya Khadija,da gaske har yanzu baki yadda cewa yaran nan sun rasu ba? "

"Idan har sun rasu me yasa ban samu gawar su kamar yadda muka ga ta   Alhaji ba? Su me yasa ba mu gan su ba? Zuciyata ta kasa yarda da hakan ba zan cire rai ba in sha Allahu zan gan su a gaba."

"Yaya Khadija ba zan miki musu ba amma dai ina rokon Allah Ya bayyana miki su in har suna nan da ran su idan kuma ba su da rai Allah Ya baki dangana."

"Amin A'isha amin."

"Yanzu asibitin zamu je kafin mu tafi gun Yaya Asabe ɗin?"

"Eh muje sai mu wuce daga can. Dr ya fita ko?"

"Eh ya fita da sassafe ko ni note ɗin shi na gani."

"Oh halin dai na nan."

"Ke da kika sani." Suka fita suna dariya. Imran ya fito cikin shadda kamar ba saurayin da ya dinga yawo a cikin suit ba jiya. 
"Yaya Khadija yaron nan fa ɗan latsi ne ko ina sai ya bi ki wai?"
"Asalin cingum ake gaya miki ai na rasa irin shi ya fi sauran ƙulafuci."
"Ai shi kenan sai ki aurar da shi ki huta ke ma."
"Wa zai aure shi wannan ɗan rainin wayo ko fara'a fa baya yi."
"Me nufin ki? Kina ganin yaro bafulatani mai kyau ga gashi kamar na larabawa curly kike cewa wa zai so shi sa wasa."
A'isha tayi dariya ta na kallon shi har ya iso gabansu yace "Ya na ji kamar gulma ta ake yi?"
Dariyar suka kuma yi sannan A'isha tace "Gulmar ka nayi na ce ka yi kwantai ba mai son ka akai sanarwa a masssalaci ni na bayar da kai sadaka."
Ya kama haɓa kamar mace har yana komawa da baya kaɗan sannan yace " Kuma ni guda handsome guy za a kai masallaci a bayar sadaka."
"Kwarai ma kuwa kana wasa ne?"
"Innallillhi wa inna illahir rajii'un na shiga uku Hajiya kina ji ko?"Hajiya tayi dariya tace "Wallahi ban san ranar da za ki girma ba A'isha ke ɗan naki ma baki bar shi ba kai Allah Ya shirye ki."
"Hajiya a gama maganar nan yanzu Wallahi Tallahi tsab Aunty Aisha zata kai hotona masallaci..."
Me zasu yi in ba dariya ba. 
"Kin gani ai na gaya miki da sauran shi."
"Na yarda ai yanzu."
"Hajiya kika yarda da me?"
"Imran shiga mu wuce ka kyale wannan matar."
Suka shiga baya ya shiga gefe direba ya shiga ɓarin tuƙi suka ɗauki hanya suna raha gwanin burgewa.
IDI ARABA
LAGOS 

"Cika ni Lamrat ki cika ni."
"Ba zan cika ki ba sai kin biyani abincina da kika ɗiba."
"Ba zan biya ba ai na ga kema kina cin namu in muka samu sai ke yau don anyi loma ɗaya kike yi min tijara."
"Tijara kuma? Ai ban ma miki komai ba ke ban ma soma. Uban waye ya ce ki yi loma ɗayar? Ko na saka ki ne? Gayyatar ki na yi ne da za ki zo ki cakumar min ƙirji a dake ka a hana ka kuka?"
"Lamrat na rantse da Allah idan baki sake ni ba sai na tsinka miki mari."
Lamrat tace "Kanbuuu ni za ki mara? Ni kuma sai na tsaya ki mare ni ko saboda ƙanwata ce ta yaye ni ko?"
Baba da ya shigo ya tsaya cak yana kallon bidirin cike da taƙaice yace "Na lura iskancin naku kullum ƙara yawa yake yi. Cika ta ke Lamrat." Ba shiri Lamrat ta cika ta tayi gefe.
"Me ya haɗa faɗa ?"
"Baba kawai ina zaune na sayo wake na da shinkafa ta da awara a gidansu Hussai na zauna sai na ji fitsari sai na shiga cikin banɗaki na yi ina fitowa na gan ta sai loma take kai min."
"Yanzu ke Lamrat ba yar'uwar ki ba ce meye a ciki don ta ci abincin ki? Ke ma fa me bata ce."
"A'a Baba ai a tsarin gidan nan shi ne ka ci na ka na ci nawa."
Baba ya saka salati ya ce "In ji waye? Waye ya zo da wannan mugun halin?"
"Ni ce nan na gaya musu haka saboda na lura wasu na cutar wasu."
"Amma kuwa bilkisu ba ki kyauta ba kuma ba ki yi halin girma ba ta yaya kina uwa za ki ɗora yaran ki a kan raba kansu? A maimakon ki koya musu hadin kai da ƙaunar juna kullum cusa musu munanan ɗabi'u kike yi hana don Allah Bilkisu ta ya in na tafi aiki hankalina ba zai dinga zama a gida ba?"
"Wannan kuma kai ka jiyo. Ba ka gama iyawa da mu ba ka kwaso wata ga shi nan an kwankwaso yara rututu an tara an bar mu da wahala ban da zalama ta maza ma me abun aure kana fama da rayuwa Allah dai Ya kyauta." Ta juya ta koma ciki.
Innarsu Habiba ta koma cikin madafi ba tare da tanka wa Umma ba amma ta sa a ranta in kere na yawo zabo na yawo wata ran za a haɗe ai ba zata biye mata su ɗaga hankalin mijinsu ba a wannan sanyin safiyar ba. Ta hura wuta ta ɗora tukunyar koko.
Baba dai ya samu ya raba faɗan Lamrat da Abida shi ma sai da ya bawa Lamrat ɗin wata tsohuwar Naira ɗari a aljihunsa.
"Na raba faɗan na Lamratu amma ki sa a ranki abin ki na yan'uwan ki ne su ma na su na ki ne bana son kuna raba kan ku."
Ta zumɓuri bakin ta gaba sannan tace "Baba ai su baka ga abubuwan da suke yi mini ba cewa fa suke yi ni babu babata a nan gidan don Allah laifi ne don Babata ta rasu? Su don suna da yan'uwa ni kuma ni kaɗai ce shi ya sa suke ware ni a cikin su."
Ya sa hannu ya shafa kan ta cike da tausayi yace "Allah Yana tare da ke Lamrat amma ke ma ba a ware kike ba..."
Sallama aka yi daga waje ya juya ya fita ba tare da ya ƙarasa maganar sa ba.
Lamrat ta koma wurin kwanon abincin ta zaunawa tayi ta tanƙwashe ƙafafuwan ta  sai aikawa juna harara suke yi ita da Abida. Ita Abidar ma fa ta bata shekaru biyu amma a gidan ba wanda ta kyale har gara ma Sahabi tana tsoron sa.
"Ina aka zo ci ina za a ci in kin gama sai ki tashi ki wanke kwanukan nan a samu a ci abinci in kin gama iyayin da neman bala'in da kika saba." Innarsu Habiba ta faɗa tana hararata haɗe da dangwarar da wata roba a gabanta shaƙe da kofuna da kwanuka yan ƙananu. Sai da Lamrat ta kalli robar sannan ta haɗiyi abincin bakin ta tace "Innarsu Habiba amma jiya ma ni na yi wanke-wanke yau ma sai ace ni zan yi." Ta faɗa cike da tsiwa.
Innarsu Habiba tace "Kai yau na ga ikon Allah amma baki da mutunci Lamrat to ban isa in saka ki bane ko kuma iskancin kaina ya waigo?"
Ta miƙe ta zura sillifas ɗin ta sannan tace "Tsakani da Allah wannan ba adalci bane ai a ƙa'ida yau aikin Habiba ne ita tana ɗaka a kwance tana jan munshari kuma ni sai nayi mata aikin ta gaskiya ba zan iya ba." 
"Aikuwa ba za ki ci abincin nan ba sai dai ki nemi mai baki."
"To na ji ba zan ci ba ai kina kallo na yi kyakkyawan kari dai ko? Ga ɗari ta ma da Baba ya bani sai na sayo burodi ko rabi ne na ci ai akan in yi aikin Habiba gara yau na wuni da yunwa Wallahi haba sai kace wata baiwa aka siyo muku." 
"Ba shakka yarinya kin samu wuri amma zan yi maganin ki da ke da uwar taki sai nayi maganin ku Wallahi."
Ita dai Lamrat ta sa kai tayi waje tana yan waƙen ta.
Tana fita ta tsaya a bakin titi nan ta ga yadda masu sana'o'i suke ta hada-hadar su ta kama ƙugun ta tana jijiga jiki kawai zuciyar ta na raya mata ta nemi aikin yi zuwa yanzu ta fara sarewa da lamarin gidan na su mai cike da tarin son kai da ƙurɗa-ƙurɗa.
Ta baya aka dafa ta. Da sauri ta juya ta saki tsaki sannan tace "Amma sau nawa na gaya maka kar ka sake taɓa ni? Wai kai maye ne?"
"Yi haƙuri madam." Ya faɗa yana washe haƙoran sa da suka yi kalar ja saboda ƙazanta.  
"Wallahi ka kuma tabani sai na yi maka abinda ba zaka manta da ni ba ha'an kawai ka zama ɗan iska baka son zaman lafiya dole sai na kula ka."
"Ke don na ce ina son ki zan aure ki? Kaf layin nan ki gaya min waye yake kula ki saboda haukan ki da rawar kan ki."
"Eh ayi zuciya a daina kula ni babu lallai ba dole ban ce a kula ni ba ai dama na fi ƙarfin mazan layin nan tsamaye sai wari ku ka iya ji haƙoran ka jajir kamar basu taɓa ganin ruwa ba wani dagaje_dagaje da kai ba ka iya komai ba. Yo ni in ban auri ɗan boko ba ma ai na faɗi ba nauyi sai na auri mara ilimi irina? Ni ba boko ba islamiyya shi ma mijin haka to ayi yaya da ya'yan? Gaskiya ka daina ma kula ni kar wata ran mijina ɗan gaye ya gan ka ma ya fasa zuwa kusa da ni."
Ya saki baki kawai yana kallon ikon Allah ita kanta tana buƙatar kintsi ga ta nan dai ga ga nan dai ba wani tsabta ba kintsi amma ita ke zagin sa yarinyar da ko sutturar kirki bata da shi. Sai ya ga ma in ya kyale ta ai ta ci galaba a kansa.
"Amma dai kin yi mugun raina min hankali yarinyar nan. Ni ya kamata na ce bana son ki ai kullum cikin tsumma uban wanne ɗan boko ne zai zo ya gan ki a nan ya aure ki kuma? Kina fama da ƙazanta da talauci ana doso ki fa a maimakon ƙamshi wari ake ji Shegiya ni ne za ki yi wa haugoma? Karya kike Wallahi yar nan na ga juya na ga yau kuma zan ga gobe da ikon Allah na fi ƙarfin ki yaga ni Wallahi kiyi ki gama dai mu ne dai irin mu zamu aure ki yarinya."
Lamrat ta yi ciki-ciki da idanuwa tace "Hehe! Warr sannu Allan musuru , to ka zauna ka gani ajina ya fi ƙarfin naka kana kallo za ka ga an zo da zabgegiyar mota an sure ni kai kuma kana nan ka zaba dai a cikin masu suyar ƙosai da awara na nan Araba ka aura ni dai na wuce kan ka yasin." Tana kai wa nan ta yi gaba.
"Uwar bala ke da waye sai mita kike ke kam baki gajiya Lamrat."

"Waye kuwa banda wannnan tsuket ɗin an ɓata min rai a gida na fito an kuma ɓata min rai." Mtsew 

"Waye kuma tsuket?"

"Wancan yaron mana Iroro yake kowa ɗan Iskan nan."

"Kai jama'a amma baki da mutunci Wallahi wai yaro kuma tsuket." Ta faɗa tana dariya. Ita ma dariyar tayi sannan tace "Baki ga ƙugunsa ba kamar an san mai shege sai son ya taɓa mutane ɗan cirani ne fa amma ya dage wai yana sona to nayi me da shi don Allah shi kenan ba zan ci gaba ba sai na ƙare a wannan talaucin?"

"To Lamrat ai ƙwarya ta bi ƙwarya kawai kin san dai baki da komai na ilimi ga ki nan dai anan amma kike hangen wani mai kuɗi mai kuɗin ma Adnan?"

"To da yake da Allah na dogara ba ruwana da wannan surutan naku ba."

"Ai shi kenan ni fa aikina na ankarar da ke ne ba na miki dole ba."

"Allahu akbar mai karatu na gaba."

Hannu ta sa ta daddage ta mata dundu a baya.
"Yanzu ina zamu je?"
"Ni fa yau da kika gan ni na shuka tsiya a gidan nan na san ba mai bani sanawa abu guda ne yanzu a raina zan je na nemi wani ɗan aiki ko a shagon Iyabo ne in yi wanke-wanke na samu na dare kin san dai halin matan babanmu."
"Ba kya jin magana Lamrat Wallahi ba ki da haƙuri rashin kunya ta miki yawa na rasa yadda zan yi da ke yanzu jiya me kika yiwa Yaya Taheer ya bi ki shi da Umar a daren nan?"
Sai da ta ɗan taɓe baki sannan tace "Babu abinda na masa fa kawai cin zalin sa ne ya tashi babarsu ta gaya mai ƙarya da gaskiya ya zo wai zai kilen ni kuma na ga ba zan jura ba na gudu."
"Ni dai don Allah ki dinga haƙuri."
"Na ji uwar iya."
"Au haka ma za ki ce da ni?"
"To ki yi haƙuri masoyiya na gode da kulawar ki da ƙaunar ki."
"Yen! Yen! Yen mayaudariyar banza."
Suka yi dariya tare.
A bakin shagon wata beyerabiya suka tsaya tana kasuwancin sai da abinci ne . Ba laifi taɓa da customers sosai saboda ta iya girki yadda ya kamata. Ko da ta ga Lamrat sai ta haɗe rai tace "Me ya kawo ka shagona?"
"Iyabo kawata na zo ne nayi miki wanke-wanke ki biyani."
Sai da ta yanka mata harara kafin tace "Ba zan baka wani aiki ba ka je ka bani wuri a nan. Kai wannan sai an taimaka maka sai ka zo ka yi wa mutum rashin kunya ki tafi."
Lamrat ta haɗe hannayen ta wuri guda tace "Kiyi haƙuri ki tambayi Hussai na yi hankali na daina."
Iyabo tace "Ah! I no dey give you any work ka tafi daga nan."
Lamrat tace "Shi kenan Iyabo na gode." 
Iyabo ta bi bayan ta da harara. 
Duk inda ta je amsar guda ce ba za a bata aiki ba saboda rashin mutuncin ta an sha bata aiki tana guduwa ko in aka biya ta sai ta daina zuwa haka ya sa suka ƙuna.
Hussai ta kalle ta tace "Ki gyara halin ki Lamrat yanzu dai ga ayyuka amma saboda iskancin ki an hana ki."
"Ke ni abin duniya ma duk ya ishe ni na rasa yadda zan yi wai haka nake dama?"
"Ban sani ba."
"Yanzu haka zan wuni na kwana ban ci ba?"
"A'a in na dawo daga gidan da nake aiki ƙila in samo wani abu sai mu ci tare."
"Ƙawalliya ko dai nima gidan aikin zan nema ne na dinga aikin shara da wanke-wanke haka na dinga samun na kashewa?"
"Ai ba a baki aikin ba iya shegen ki."
"Da gaske zan zauna ba zan yi komai ba bana son wannan zaman haka Baba ba sosai yake samu ba muna da yawa mazan kuma dai kina gani ba wani abu suke yi ba sai dai ma a basu."
Hussai ta sa hannu ta dinga taɓa wuya da kan Lamrat. Lamrat ta ture hannun ta tace "Ke! Meye haka za ki dinga min haka?"
"Wai so nake na tabbatar lafiyar ki ƙalau saboda ban taɓa jin nutsuwa da hankali a cikin muryar ki ba Wallahi dama za ki yi hankali?"
"Allah Ya isa!"
Hussai ta sa dariya sosai har tana riƙe ciki.Baƙin ciki kamar ya kashe ta tayi tsaki ta juya za ta bar gun Hussai ta kamo hannun ta tace "Wasa nake miki kiyi haƙuri. Ki zo mu tafi tare gun aikin nawa sai mu ga ko Hajiyar na da wani aikin da za ki iya yi mata ko ba ita ba ko a maƙota ne."
Ta washe haƙoran ta da suka soma dafewa saboda rashin tsabta tace "Muje."