5
*BAYAN AURE*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 5.
Sarac Stars R Pen...✍️
Hamida ta wayi gari cikin ciwon kai dan bata samu bacci mai kyau ba, idaunta sun koɗe har wata 'yar rama tayi a fuska. Bayan tayi wanka ta sake mayar da kayan jikin dan babu wanda zata saka, duk da Suhaima ta bata duguwar rigar atamfa amma sai ta ƙi amsa tace ta gode, ta nuna mata tana jin kunyar haka kuma dan ta mayar da kayan jikinta ba wata damuwa bane, Suhaima ta jinjina sauƙi irin na Hamida sai kawai ta fita, ba jimawa ta kawo mata lafiyyyen waina da miya da ya ji ƙashi, wannan karan bata cutar da kanta ba ta ci guda uku da ruwan tea mai kauri, ga kuma kunun gyaɗa data sha kaɗan, sai taji natsuwa sosai a tare da ita dama har da yunwa ke damunta, sai ga Rashida ta shigo tana yi mata tsiya.
Amaryanmu ki saki jiki ki karya sosai fa nan gidanku ne, ki dai na fulako.
Anty ai naci sosai.
Ke ni ƙanwarki ce ba anty ba, dan Yaya Habib shi ne babba sai ni sannan Suhaima sai Hassan da Husaini.
Anty duk da haka ai kin girme mini bazan iya kiran sunanki ba.
To sai ki ce mini maman Walid, sunan ɗana na farko kenan.
To shi kenan.
Hamida ta faɗa cikin sun ne kai tana murmushi, ita ma Rashida tayi murmushi kuma taji daɗin yadda ta girmamata, hakan ya tabbatar mata da Hamida ta samu wadataccen tarbiyya, ta ɗauki abunda tazo ɗauka tace ta fito falo ta zauna kar kaɗaici yayi mata yawa.
Laaa da kwanciya zan yi, dan akwai sauran bacci a kaina.
Kuma hakane, to ki kwanta abin ki.
Cewar Rashida kafin ta fice daga ɗakin, ta koma falo ta zauna tana basu labarin yadda suka yi da Hamida, umma tace cikin murmushi.
Ai tun sadda ya kawo ta ta gaishe ni kafin aurensu na karanci yarinyar ɗiyar mutunci ce, duk da an kawo mana sukarta na 'yar tallace amma tasha bamban da sauran, akwai natsuwa da girmama mutane, shiyasa na ƙara aminta da aure, nace ita ce daidai auren Hafiz nasan ba zata bada matsala ba.
Wlh kuwa ga zahiri mun gani dan da wata ce aka samu matsala jiya da ƙila tana gidansu ana niman tayar da rikici, dan kin san mutane wasu ba zasu yarda da cewar rashin lafiya ne yasa Laila rufe gidan ta tafi ba.
Cewar Suhaima, nan dai suka cigaba da hira har Hafiz ya shigo da sallama suka amsa ya ƙaraso ciki ya samu guri ya zauna, ya gaishe da Umma kafin sauran ƙannensa suka gaishe shi ya amsa sai ya cigaba da cewa.
Ina Hamida.?
Yanzu ta gama Karyawa ta kwanta.
OK, umma yanzu zan wuce gidansu Laila kar 'yan uwanta Hamida su zo su tadda bama nan.
Gaskiya kam ai mutanen sun nuna dattako duk da an ce rashin lafiya ne amma kuma sun nuna girma da arziki, da wasu ne ba rashin lafiya ba ko meye kansu kawai suka sani, ƙarshe abun sai ya zama rikici suce kishi ne kawai.
A cikinsu ma ba za a rasa masu zargin haka ba, shiyasa nake so koda sun zo anjima su samu Hamida a ɗakinta hakan zai kore dukkan wani shakku.
Gaskiya dai bari na shirya muje dan naga wannan 'yar tawa sai anyi lelen kishinta.
Cewar Umma tana yunƙurawa, a lokacin wayar Hafiz ya ɗauki ruri ya ciro daga aljihunsa sai yaga Laila ce, da sauri ya ɗauka ya kara a kunne yana ambaton.
Da girman kujerarki ranki ya daɗe Lailatul khairi.
Hmmmm ni bana son wani daɗin baki ba dai ka zama ango ba ai magana ta ƙare, dama na kira ka ne nace maka na aiko da drivern gidanmu da key ya kawo maka, sannan anjima inna kimtsa zan dawo.
OK nagode Allah ya huce ran gimbiyar Hafiz.
Sai ƙit ta kashe wayar bata jira cigaban zancensa ba, ya sauke wayar yana sakin murmushi.
Yaya ta sauko kenan.?
Cewar Suhaima, sai duk suka tsureshi da ido suna jiran amsarsa, Hafiz ya nisa yace.
Eh gashi ta aiko da key ɗin a kawo min, bari ma na kira driver ya kawo nan gidan sai na jira shi.
To Alhamdulillahi bari na koma na zauna na miƙe ƙafa, kaga da aka bita a yadda take so ba gashi komai ya daidaita ba, da ace an nima yin rikici da ita da shi kenan shaiɗan ya samu wajen zama, Allah kaɗai yasan me zai faru, shiyasa aka ce da haƙuri da rashinsa tazarar su kaɗan ne.
Cewar Umma ta koma ta zauna a Cushing, nan suka cigaba da maganar Hafiz kuma ya kira driver yace ya kawo masa key ɗin nan gidan Umma, ya sauke wayar yana cewa.
Umma wlh abinda Laila tayi ya ɓata mini rai sosai, amma kuma na duba yadda ta kwantar da hankalinta tun farkon maganar auren nan shiyasa nayi mata uzuri ban ja maganar ya kaimu ga faɗa ba, kuma gashi dai anyi an gama Hamida da danginta basu fahimci komai ba.
Allah dai ya kyauta yasa ta yarda su zauna lafiya, dan ga dukkan alamu yadda ta nuna halin kishinta ba lallai a zauna lafiya ba, ni harta fara sure mini wlh.
Cewar Suhaima cikin ɓata fuska, Rashida ta galla mata harara.
Zaifi ki yi wa mutane shuru ki bari waɗanda suka san ya zafin kishi yake su bada amsa, ai na Anty Laila ma da sauƙi akan wasu matan, mu bi su da kyakkyawar addu'a kawai da fatan alkhairi.
Da kyau 'yar albarka dama nasan kinfi wannan mai kan kifin hankali, kuma yadda na tsara tafiyar gidana bana zaton za a samu saɓani, dan ban bawa Hamida fuskar ta raina mini mata ba.
Cewar Hafiz, Umma tace.
Ai haka shi ne dai-dai ko wacce a bata haƙƙinta.
Haka suka cigaba da hira har driver ya kawo key, su Rashida suka miƙe suka shirya, Suhaima kuma ta taso Hamida daga baccin data fara suka fito Umma ta yi musu rakiya zuwa gate tana shiwa Hamida da albarka, har suka shiga mota kafin ta juya gida su kuma suka wuce a motar Hafiz zuwa gidansa.
Ko da suka ƙarasa sun tadda 'yan uwan Hamida sunyi cirko-cirko kusan su sha shida a bakin gate mai gadi ya hana su shiga, Hafiz ya yi mamakin ganinsu a wannan lokacin wanda ƙarfe tara ne na safe da mintuna, su kuma sunyi sammako dan su samu damar bawa idonsu a abinci na ganin kyawun gidan kafin sauran mutane su zo anjima, maigadi ya buɗe gate Hafiz ya shiga yayi parking suka fito, 'yan uwan Hamida suka ƙaraso ciki sai washe baki suke yi suna gaisawa da su Rashida, Hafiz ma sun gaisa da shi sai ya wuce ya buɗe musu ƙofa suka shiga, a ransa yana cewa.
Ohhh Allah ka haɗa mu da mutane marasa hankali, tabbas sai na ɗauki mataki dan bazan yarda da zarya ba, ai talauci ba hauka bane, sai kace a kansu aka fara auren mai kuɗi.
Ya wuce sama abinsa ransa ba daɗi, addu'a ya shiga yi karsu ɓata masa gida da ƙazanta. Su kuma suka yada zango a falo Hamida kuma Sumaiha ta rakata ɗakinta da yake a nan ƙasa ciki ɗaya, iya kayan gadonta ne a ciki, gado da wardrobe sai kayan kitchen da suke a buhun masara guda biyu da aka ɗaura, ta zauna a gefen gado tana sauke numfashi tare da cire mayafi daga saman kanta, Suhaima ta kunna mata fanka sai ta fita, madadin 'yan uwanta su shigo su zauna tare da ita sai suka yi zamansu a falo suka fara kallon wani film ɗin india a tv, Suhaima kuma ta haura sama wajen Hafiz tana ce masa ya za su yi da baƙin da suka zo dole ayi musu girki, yace ta shiga kitchen akwai kayan abinci su ɗiba yadda zai isa amma kar a yi girkin komai a kitchen ɗin su fita tsakar gida suyi, akwai murhun gawayi da suka aje tunna hidimar sallah da Umma ta saka shi ya siyo wa Laila, sannan ta saka ido kar a yi musu ɓarna, tace masa to kafin ya fito, nan ta kira Rashida ta faɗa mata abunda Yayansu yace sai suka haɗu su biyu suka fara kiciniyar yin girkin abincin rana na tarban baɓi.
Zuwa ƙarfe biyu gida ya cika ya tumbatsa da dangin Hamida yadda kasan a ranar ake taron bikinta, Allah yasa su Suhaima kamar sun san za a taru suka dafa shinkafa rabin buhu har da kaji biyu suka ɗauka a freezer suka gyara, haka dangin amarya suka yi badago da abinci suka ƙoshi, wasu ma har guzirinsa suka yi a leda zasu tafi da shi gida, sannan sun sha ruwan gora da drinks wanda suka ƙara shaida Hamida ta shigo cikin daula, sai suka fara yiwa kansu fatan Allah yasa su a danshinta.
*****
HAFSA.
Zaune take a tsakar gida tana daka yajin siyarwa, wanda take ɗaura na ƙullin 'yan ɗari ga mutanen unguwa, sai kuma wanda take sakawa a roba tana parkaging ɗinsu tana siyar dasu a online tare da garin ɗanwake, garin daddawa, garin kuka da kuma kuɓewa busasshe, duk tana manna musu sticker wanda ta saka aka yi mata da sunan Hafsy mai awara, sannan aka jera abubuwan da take sayarwa a ciki tare da number wayarta da Adrshinta, dalilin da yasa ake kiranta da Hafsy mai Awara saboda da shi ne ta fara sayarwa a online, in ta dafa shi ta siyar da shi a ɗanye tayi parkaging ta aikawa waɗanda suka yi oder in kuma soyayye mutum yake so nan ma zata soya ta aikawa mutum, daga baya ne da daina saboda lalacewar wutar layinsu basa samun wuta mai kyau kamar da, sannan masuyin Awaran sun fara yawa, shiyasa ta koma yin yaji da garin ɗanwake da sauran. Daka take sosai amma tayi zurfi a cikin tunanin littafin Mijin Aro da take saurare a YouTube wanda Pinkishlady ta karanta, sallamar Bilal shi ne ya katse ta, ta bishi da kallo cikin natsuwa tana amsa sallamarsa, ya risina yace.
Mama sannu da gida.
Yauwa Bilal, amma lafiya naga idonka sunyi ja kamar kayi kuka me ya faru?
Abu ne ya faɗa mini.
Subhanallahi to Allah ya kiyaye gaba sai kaje ka kwana kafin lokacin islamiyya ya ƙarasa, Abbanku yana shago ne ko ya fita.?
Yana nan.
Bilal ya bata amsa a taƙaice sai ya wuce ɗakinsu, ya cire riga ya hau katifarsu ya zauna ya jingina da bango ya saka fuskarsa a tsakanin ƙafarsa ya fara hawaye ba tare da nishin kuka ba. Ɓangaren Hafsa kuwa aikinta ta cigaba da yi harta gama kafin ta kwashe su ta adana a ɗakinta, sai ta dawo ta ɗauki turmi ta mayar da shi kitchen dake nan tsakar gida, sannan ta dawo ta matsar da kujerar data tashi ta ɗauko tsintsiya ta fara shara, tana tsaka da wannan aikin sai ga sallamar wani yaro ya shigo gidan riƙe da leda a hannunsa, ya gaisheta ta amsa sai yace.
Wai Hafsa tana nan.?
Eh gani me za a baka.?
Wata mata ce ta bani wannan ledan yanzu a waje tace na kawo miki wai inji Zinatu.
Zinatu kuma.?
Cewar Hafsa data amsa ledan kayan, yaron kuma ya juya ya wuce abinsa, tsalam sai ga Bilal ya fito daga ɗakinsu ya ƙaraso inda mama take tsaye yana duban ledan hannunta, sai tace tana nuna masa ledan.
Wai Zinatu ta aiko shi.
Ki buɗe muga meke ciki.
Cewar Bilal wanda ya ƙaraso kusa da ita ya tsaya, Hafsa ta aje tsintsiya a ƙasa ta buɗe ɗaurin da aka yi wa ledan, Nan take taci karo da pant da birezia da siket under wear suna ta ƙamshin Turare haɗe da warin zufa, Sai ta saki ledan a ƙasa tana salati, Bilal ya ja guntun tsaki yana cewa.
Wlh mama sai na saka yara sunyiwa matar nan ruwan dutse dan ubanta, har yanzu fa bata daina bibiyar Abbanmu ba, dan ɗazun ta zo shago Abba ya ce na basu guri, shi ne dana ji haushi na kamo hanyar gida, takaici ya saka ni yin kuka dan na rasa meyasa Abba yake zubar mana da mutunci, ya saketa amma kuma sun cigaba da haɗuwa me hakan ke nufi.?
To in banda abun Zinatu Meyasa zata yo mini wannan aiken, me take nufi.?
Tana so ta nuna miki cewar har yanzu tana tare da Abbanmu ne da kuma abunda suke aikatawa.
Innaillahi wa inna ilaihi raji'un.!
Hafsa ta faɗa tana mai duƙawa ta jawo ƙaramar kujera ta zauna dan ƙafafunta suna nimar kayar da ita. Bilal ya ja jikinta zuwa jikin bango ya rungume hannu yana cije baki tare da girgiza kai, Hafsa kuma hawaye ne ya sauko mata a bazata, sai tayi sauri ta goge tana jin bai dace ma ta zubarwa Zinatu da hawaye ba, domin wanda tayi a baya ma ya isa dan lokaci yayi da zata yakice damuwarsu ta samawa kanta farin ciki, sai ta miƙe tana cewa Bilal.
Ɗauki kayan nan ka kaisu bole tunda na fahimci aikenta, Allah ya kyauta.
Mama wlh sai Abba ya dawo yaga kayan nan, saboda ya gane kin san komai, sai muga me zai yi.
Hmmm ba zai yi komai sai naɗe tabarmar kunya da hauka, ni da zai ji shawarata ma daya dawo da Zinatu ɗakinta akan wannan rayuwar gantalin da suke yi, Abbanku sam baya tunanin gobensa da ku daya haifa.
Shi ya sani kuma Allah yana sane da ke zai kawo miki ƙarshen komai. Bari ki gani a ɗakinsa zan zuba masa su.
Ya ƙare maganar yana ɗaukar kayan haɗe da ledan dan yaƙi yarda kayan su taɓa hannunsa, ya shiga falonsu ya wuce ɗakin babansu da yake mallakinsa ya buɗe ƙofar ya shiga ciki ya zuba su a tsakiyar gadonsa ya fito riƙe da ledan ya rufe ƙofar ya dawo ya saka ledan a bola, sai ya ɗauki buta saboda an fara kiran sallar la'asar ya shiga bayin tsakar gida, Hafsa dake zaune duk jiki a mace tana kallonsa har ya shiga bayi kafin ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi tace a ranta.
Allah kana gani, ka kuɓutar dani daga sharrin abunda Saminu yake aikatawa, duk bala'in da zai jawo ya tsaya akansa.
Sai ta miƙe ta ƙarasa sharar kafin ta shiga cikin ɗakin dan tayi alwala tana cike da mamakin Zinatu, ita ce ta nima ya sake ta bata sonsa tafi ƙarfinsa ba zata iya zama da shi ba amma kuma ta cigaba da bibiyaarsa, abun takaici kuma Saminu sam baya taɓa wuce tayin da mace zata yi masa, sai ta yi kwafa tana girgiza kai cike da takaicin halinsa.
Rahma ce.