Page 4
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
GABA KURA
AISHA HANWA
PAGE 4
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Da kyar aka bari ta je gida wanka, shi ma can d'in ba gama tunda abincin da za ta ci ya cika mata cikinta gagararta yake yi. A daddafe ta samu ta kai arba'in aka tattarata aka maida ta d'akinta.
Haka rayuwa ta yi ta tafiya kullum ba sauyi, haihuwa kuma shiru kamar an aiki bawa garinsu; nan fa dangin Munzali da shi kanshi suka sako ta a gaba da gorin haihuwa, abu ƙalilan zata yi ace dan bata san zafin 'Ya'ya bane shi yasa.
Jamila har ta haihu danta namiji na nan ga cikin na biyu tana ja. Rana tsaka Munzali ya tada ballin shi aure zai kara dan ya gaji da zama da juya, ganga-ganga aka tashi da biki Ita dai nata ido. Aka yi aka gama ba tare da tasan wace ce amaryar ba, sai daga baya ta santa ashe yar kusa da gidan ne hasalima suna da danganta a tsakaninsu.
Tun da amarya ta tare bata sake saka Munzali a idanuwanta ba sai dai Muryar shi zata ji a d'akin amarya ko wulk'itawar shi idan za shi bayi;ta d'auki na mujiya ta zuba musu ganin sarakuwar su ta san komai.
A haka sai da Amarya tayi wata shida sannan ya fara shiga d'akinta shi ma ba dan ya biya mata buk'ata ya dawo ba domin tun da ya dawo ko kallo bata ishe shi ba, jiki da jini watarana har zama take yi ta ci kukanta ta koshi bata da wanda zata fad'awa gani take yi idan ta fad'i irin wannan maganar za'a yi mata kallon jarababbiya.
Bata k'ara tabbatar da
abun na Munzali babu Allah a ciki ba sai ranar da hak'urinta ya k'are ta runtse idanu ta neme shi, bud'en bakin shi sai ya ce 'shi fa ya gaji da yankawa kare ciyawa' mace kullum ana abu d'aya amma ba sakamako ga shi sa'ade Amarya har ta samu ciki Ita kuwa tana nan jiya iyau".
Ranta ya b'aci ta ce "Amma sanin kanka ne ni d'in ba juya ba ce ko?, da abun da na haifa ta yi tsawon rai da yanzu ba wannan maganar ake yi ba". Shi kenan ya ce ina wuta ya saka ta cin mutunci sai wanda ya manta daga k'arshe ya ce shi fa dama fad'a mata ne bai yi ba amma ya gama yanke hukuncin rabuwa da ita zai yi sun gama gano ita din da farar k'afa ta shigo gidan, tarayyar su bata da amfani sai ma ci baya da aka samu komai ya taba baya albarka shi yasa suka je wurin Malam kalla a yi mishi istihara, inda Malam yace taurarin su ne bai zo d'aya ba dole ya rabu da ita idan yana so ya yi arziki".
Kukan da take yi ne ya d'auke jin abinda ya fi karfin kunnenta "Yanzu to mene kake jira da baka sallame ni ba?". K'askantaccen kallo ya yi mata kafin ya ce "Ai da yake ƙwaƙwalwar taki dusa ce shi yasa kika kasa fahimta ballantana ki kama gabanki tsakaninki da Allah wata nawa kenan rabon da ki ganni na tako kafafuwana kofar d'akinki? kora da hali na yi ta yi miki amma kin kasa ganewa kika ci gaba da zama ba sai in kyale ki ba.
Cikin kuka ta ce "To yanzu ka bani shaida sai gobe da safe in tafi gida da k'arfina", ko baki ce ba tunda yanzu na gano ki yarinya ai dama dole ki bar gidana ato!" Ya juya gefen damar shi ya zato takarda a aljihun shi ya jefo mata yana cewa "Ga shi nan dan Allah gobe ki shirya da wuri ki tafi domin na k'osa ki matsa a kusa dani ko arzik'ina zai dawo", Ya juya ya kwanta yana 'yan surutan shi.
Rik'e take da takardan a hannun tana had'a d'aya da biyu tunaninta d'aya shi ne ta ya ya zata je gida da ita, tun da zo duniya bata taɓa ganin iyayensu mata sun yi yaji ba duk da tijarar mahaifinsu kuwa; hakazalika yayyinta mata dake gidan aure.
Duk yadda aka ce bacci b'arawo ne Ita dai ya gagara satar ta, hakanan ya ganta ya kyale asubar fari ta mik'e ta yi alwala da nafilolin sallah kafin ta gabarta da na farilla, gari na yi shaa alamar ya fara wayewa ta mik'e kafin masu sana'ar kokon cikin gidan su fito ta fice ta bar Munzali na barcin asara.
Ta daɗe a kofar gidan ƙirjinta na dukan tara tara kafin ta yi shahada ta shige, da Baba ta fara cin karo yana kashingiɗe da ƴar radionsa a kunne yana sauraran kanun labaran safiya. Gabansa ta je ta durƙusa gami da zaro takarda ta riƙe a hannu, tun kafin ta ce zata miƙa mishi ya zabura ya wancakalar da radion yana faɗin "Me ye haka ke? Me zan yi da wata takarda ko kin taɓa gani na da takarda da sunan zan yi rubutu da kike miƙo mini ita?" "Baba Munzali ne yace in dawo gida wai ya sake ni", Yadda kasan ta ɗoɗana mishi wuta haka ya zabura ya miƙe.
"Me kika ce? ban ji ba sosai ƙara maimaita mini in ji" cikin in-ina ta ce "Munzali ne ya ce na dawo gida ya sake ni" Da kika yi mishi uban me? na ce da ki ka yi mishi uban me?" Yana yi yana matsowa kamar zai kai mata hannu. Zuwa lokacin duk wani mahaluki na cikin gidan ya hallara a tsaƙar gidan yana ba idansa abinci.
"Cewa ya yi wai Malam Kalla na hayi ya ce wai ina da farar ƙafa tun da ya aure ni komai nashi ya ƙare shi ne ya ce ya sake ni idan yana so arziƙin shi ya dawo".
"Tabɗi jam! cewar Inna cikin son jin gulma tace "To kai Mallam ai zama bai ganka ba kamata ya yi ka nufi wajen Munzali ka ji ainihi batu ba'a yarda da batun ɗan yau" Ta ƙara da faɗin "Gaskiya dai a bincika kar yazo wani mugun halin take musu ya gaji ya yanka mata sikiti Allah dai ya tsayar anan" Tana yi tana kallon Mama dake tsaye a ƙofar ɗakinta a kaikaice.
"Ba'a ƙin ta mutum ina zuwa" har ya kusa kofar gida ya juyo yana nuna ta da yatsa "Wallahi ki kuka da kanki idan na je na ji abun da bai gamshe ni ba" Ya juya ya fice.
A hankali ta miƙe ta nufi ɗakinsu. A zaune ta samu Mama ta zuba tagumi gabanta ruwan koko ne da bata idasa damawa ba.
Ba tare da tace komai ba ta samu lungun ɗakin ta zauna damƙe da takardar dake hannunta.
Suna jin duk waƙoƙen habaicin da Inna ke yi a tsakar gida.
Tura mata ruwan koko Mama ta yi ta ce "Kafa kai ki sha Allah Yana tare dake bi'izinillahi", ba tare da musu ba ta kafa kai ta shanye tas ta ƙara komawa inda ta taso ta ci gaba da tagumin.
Tun daga tsakar gida yake ƙwalla mata kira "Fito nan" A ɗarare ta fito gabanta na dukan tara tara ta durƙusa a gaban shi.
"Malam hala ɗiban albarka take musu ko?", Sai da ya zauna a tabarmarshi sannan ya ce "Ai rashin mutumcin da yaron nan ya mini an daɗe ba'a yi mini irinsa ba, kamar ni zai dubi cikin idanuwa na ya ce mini ya gaji da zama da me ƙashin tsiyar ƴata dan haka idan ma sulhu na zo in san na yi? hhm".
To malam kai wai nan haushi ka ji?, ka san hujjar shi? shi ke zaune da ita fa kasan abunda ya gani?".