Gaba Kura

Page 7

by @aishayusufhanwa

GABA KURA



AISHA YUSUF HANWA


PAGE 7




A daddafe aka gama taro sunan nan kowa ya watse. Nan fa ta cigaba daga inda ta tsaya.

Tun kafin ta yi arba'in ta fara fita sana'arta,d'an kyan nan da ake yi na jego sai dai ta gani a jikin wasu babu mai taimakonta sai Allah sai kuma Mahaifiyarta.

Dan idan ta surukarta ce da y'an uwanshi to sai dai su mutu daga ita har jaririn nata, idan ana son aga inda kwanjinsu ke motsawa sai idan ta yi yunk'urin hana shi basu abunda suka nema da sunan ajiya to nan fa za su taso takanas a yi mata caaa ba mazan ba baga matan ba ga kuma uwarsu a gefe.

A haka Sani ya yi ta girma har Allah ya sa ya Kai shekara biyu da rabi.

Ta b'angaren Ustaz kuma abun sai dai ace Lahaula wala k'uwwata kawai, ga shi ta yi tayi da su a gwada na asibiti sun ce ba wannan maganar wai ciwon shi asiri ne kishiyar Mamansu ta yi mishi na hausa za'ayi, shi kan shi na hausa sai ayi watanni ba'a amso ba sai fa sun ga ta fara magana asibiti tukuna suke amsowa.

Rayuwa ta yi mata tsanani fiye da zaton mai zato yanzu ma miji mai lafiya ya ka kare da shi balle Wanda ba shi da shi?, Kullum sai dai ya yi zugum a d'aki ba in ba um um, idan ta so su yi hira ba amsa sai dai ya yi ta binta da idanuwa.

Idan abun ya ishe ta, ta zauna ta shaqi kukanta ta koshi sannan ta cigaba da harkokin ta.

Kwatsam ranar ta fita mak'ota siyo kayan cefane ta bar Sani na kwance yana barci Baban shi kuma na zaune a tsakar gida, ta ba shi sallahun Bari da je ta dawo kamar kodayaushe ba amsa ta fice.

Tana dawowa bata gan shi a inda ta bar shi ba sai mamaki ya kamata, sanin yanzu baya fita ko'ina sai ya yi kwana bakwai bai leka kofar gida ba Dan ko gonar ta Hana shi zuwa saboda ko ya yi aikin ba shi ke morar kayan ba, ga shi idan ya tafi ya fara aikin ba ya sanin ya gaji sai yayin da ta bishi ta dawo da shi, kan hana shi zuwan da ta yi ba k'aramin uwar watsi a ka yi ba da y'an uwan shi. 

Sa'an da ta ci kawai yana jin maganar ta shiyasa ma bata Sha wahalar Hana shi ba, shiyasa ganin ba shi abun ya bata mamaki, har ta fara daka ta dakata ta lek'a cikin d'aki babu shi anan ne hankalinta ya Kai kan gadon da ta shinfid'a Sani ta ga wayam.

Gabanta ne ya tattakura ya fad'i.


 Shiga d"akin ta yi sosai ta duba  ko ya tashi ne ya shige lungu ya kana wasan shi domin wata Rana haka yake yi musamman idan ya samu barna, nan ma wayam babu shi.

Nan take jikinta ya d'auki tsima duk da ta San Yara basa bacewa a unguwar nasu amma gudun wahala take mashi domin bai saba fita shi kad'ai ba. Zuciyarta ce ta d'arsa mata cewa duk yadda aka yi Baban shi ne ya d'auke shi suka fita tare.

Hijabinta da ta sagale a igiya ta zara ta k'ullo kofar had'e da kashe wutar da ta rura ta fice zuwa b'angaren Maman shi.

A tsakar gida ta ganta tana kad'in miya, babu alamun akwai mutum a gida baya ga ita dake tsakar gidan.

"Lafiya ke kuma kike ta muzurai?" Ta tambayeta cikin fad'a fad'a tun da har lokacin haushin Hana shi zuwa gonar da tayi bai sake ta ba.

"Uhm dama Baban Sani da Sani ne ban gani ba" 

Shekeke ta kalle ta kafin ta ce "Shi Baban Sani yaro ne da zai b'ata a unguwar ko mene?".

Cikin in Ina ta ce "Dama ganin ya d'an kwana biyu baya fita ne shi yasa na yi tunanin Kada ya zo a samu matsala".

"In Sha Allahu ba Zan ga matsala ba ai na riga da na gane take-takenki kin maida shi mahaukaci shi yasa kike tunanin zai sabauta miki d'a to ki ji ki sani da hankalin shi kuma ki fita idanu na in rufe wallahi".

Ganin fad'an ba karewa zai yi ba ga shi gabanta na ta bugawa alamun akwai matsala ya saka ta ce "Allah Ya baki hakuri Inna", ta juya cikin sauri ta fita Dan Kar ta kuma tsayar da ita.