Gaba Kura

Page 14

by @aishayusufhanwa

GABA KURA


AISHA YUSUF HANWA


PAGE 14



Ganin yadda kowa ya
 zuba mata ido jin shiga ukun da take nemawa kanta ya saka ta wayence tana cewa " Mantuwa na yi  mai girma wlh, ga shi Babansu na nan na san kuma Zan sha fad'an shi".  Kamar an daure bakin kowa babu Wanda ya ce mata 'Ta tafasa sauke' ita ta yi kidanta sannan ta yi rawanta.

Ganin an bude musu gate din gidan sun shige ciki ya saka ta barin kallon da take ma wajen gidan ta bisu ta karisa cike sheda.

Gyad'a kanta take yi tana tausayawa Innayo a zuciyarta hango tashin hankalin da za ta shiga idan ta ji labarin irin gidan da Amina ta za ta zauna, domin tabbas sai ta fad'a Mata domin bakin ciki ba zai kashe ta ita kad'ai ba gyara a mutu har liman.

A d'an wani madaidaicin d'akin aka sauke su, saboda cikin babban falon da suka fara shiga ma'aikata ne a ciki suke karisa aikin su, duk da su ba gane ma aikin suka yi ba ganin komai akwai a falon harta da kujeru  masu alfarma ne a falon.

A zuciyar Munari sai ta ji d'an d'ar tuno irin kayan da suka zo da shi na danki, a dai cikin gidan nan ko Yar aikin gidan aka saka Mata sai ta yi tunanin an wulakanta ta ne ganin fasalin gidan.

Har zuciyarta ji take yi kamar ta tashi ta daka tsalle idan ta dubi gidan ta tuna cewa Amina ce za ta zauna a cikin shi sai ta ji duk abincin alfarmar da aka kawo musu ya fice Mata a rai tsabar farin ciki.


Sai da suka ci abincin nan suka take, Dan su Jamila har a leda sai da ta d'ura ta saka a Jakarta cikin su dai babu Wanda ya ce Mata "Dan mene".


 Bayan sun kimtsa suna zaune sai ga yan uwan Angon sun zo, dukkan su manyan ne babu Yara, daya daga cikin su ne bayan sun gama gaisawa ta ce za ta ga d'aya daga cikin su Munari nan da nan Innarta ta ce bari na zo Munari, ganin guggonsu na so ta mik'e kuma ta sani sarai su ban yan arzikin da za'a saki ragamar biki a hannun su bane.

 Gefe suka koma suka ɗan tsaya, sannan wacce za ta yi sa'a da. innar ta su ta fara mata. bayani. "Kamar yadda kuka gani dai Yaron nan ya gama komai na danki a cikin gidan shi ko?" Inna ta gyaɗa mata kai haɗe da cewa "Babu shakka har ma mun fara tunanin a ina zamu saka waɗanda muka zo da su ɗin?".
      "Yauwa yar gari" Matar ta katse ta, Yaron nan ya yi mana bayanin cewa Iyayen Amina ba masu hali bane domin kada mu tsammaci samun wani abun azo a gani a wurin su kin san mu mata da gutsuri tsoma, to Alhamdulillah ba yabon kai ba amma ki bincika a kaf ahalinmu bamu da matsala da mugun halin da za'a tsangwami yarinyar dan kawai iyayenta sun kasance talakawa. Bi'izinillahi yarinyarku bazata taɓa samun matsala daga ɓangarenmu ba. Sannan dalilin kiranki gefe da na yi shi ne kayan nan maganar gaskiya babu gurin ajiye su a gidan nan sai dai ni nadan babu iyayen da za su bugi jiki su yi ma yarinyar su kayan ɗaki a dawo masu da shi su ji daɗi ko ba haka ba?.

 Inna Hauwa da tsoron Allah ya hanata magana take ta kambama sunayensa cikin girmamawa a cikin zuciyarta saboda hango goben yar uwarta za ta fara kyau haƙurinta zai fara mata rana da ta yi ta ce "Haka ne tabbas". Saboda haka mun ware ɗaki ɗaya da zaku zuba abunda ya samu sauran kuma ku yi haƙuri a kuma basu haƙuri suma dan kar su ga kamar an raina musu ne; wallahi babu ko ɗaya domin kun gama mana komai da kuka ɗauki ɗan mutum kuka bamu ai kun gama mana komai yanzu mu je na nuna muku ɗakin da za'ayi jeren". Daga haka suka dawo cikin falon inda suka bar su Munari da guggonsu suna ta yi da Inna Hauwa wai tunda taga gida ta bi ta ruɗe ba dai giringirin ba ta yi mai, Jamila na ƙara jaddada "Dama ance yan Zaria akwai ƙarya idan an bibiya kila ma gonar gadonsu ne ya siyar ya kama gidan nan yake badali da kuɗi sai bayan biki yarinya taci kwal Ubanta" Ita dai Munari babu baka sai kunne sai kuma idan ta ji sun yi masu wani mugun fatan ta nemi tsari da shi a wurin Ubangiji.