Chapter 4
🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Page 4
Bata san iya adadin lokacin da ta ɓata a kwance cikin wannan yanayin ba, zuciyarta na zafi ga wani irin bugu na wuce ƙa'ida da tun da Salmah ta ambaci sunan wanna mutumin mai fuskar Babangida bai sarara mata ba. Hakan ke kara tabbatar mata da cewa tabbas lokaci ya kusa, addu'arta ya karbu, kuma hakar da ta kwashe shekaru tana yi a duhu yana daf daf da ruwa, wanda zai ba ta damar komawa ga farin cikinta wato iyayenta. Rintse ido ta yi tana hasaso fuskar Baffanta, mutum mafi soyuwa a zuciyarta, da Inna, mahaifiyarta wacce su ke yi wa juna wani irin so, wanda zuciya da zuciya kawai ke aiki wajen fallasuwarta, sai kuma Maryo wacce kai tsaye ta bata matsayin rabin jikinta. Murmushinta mai kyau ta saki saboda wani yanayi mai dadi da take tunawa wanda ya shuɗe a baya, sai kuma nan take ta gimtse fuska tana fesar da wani irin wuci mai zafi tare da taune lips ɗinta da karfi, take fuskarta ya bayyana yanayin da zuciyarta ta shiga na tsantsan bakin ciki.
A haka Salmah ta doko sallama tare da shigowa ɗakin, wanda ya dawo da ita hayyacinta, ta buɗe idanunta da suka dan sauya launi, tare da sakar mata murmushin yaƙe, tana miƙewa zaune, Salmah ta ɗan yi jim tana kallonta, kafin kuma ta tako ta ƙaraso cikin ɗakin tana faɗin “Daga shiga toilet sai mu ka ji ki tsit." Dan yamutsa fuska ta yi tana dafe cikinta tace “Cikin nawa ne ban ji daɗin shi ba, shi yasa ban dawo ba." Tace "Ayya sannu ko da na ji dama, bari na duba miki ɗakin Ammi ko akwai flajin sai ki sha." Da sauri ta girgiza mata kai tace "ki bar shi kawai, na ɗan ji dama." Harara Salmah ta watsa mata tace "Ai dama ba son shan magani kike ba nima da gangan na faɗa." "Tunda kinsan da haka meye na wahalar da kanki wajen tambayata.” Ta taɓe baki, tace "ke dai ki ka sani." Ta kai karshen maganar tana shigewa toilet. Bayanta Aysha ta ƙurawa ido, tana tufka da warwara a zuciyarta na yadda za ta bullowa lamarin da ya taso masa bagatatan, ba za ta taɓa wasa da wannan damar ba wanda take da yakinin zai iya kaita ga cimma burin zuciyarta na abinda ta ginata a kai wato ɗaukar fansa, tsawon shekaru ta kwashe tana bulayin neman wannan damar tare da addu'a ba dare ba rana. Minti goma Salmah ta ɗauka a toilet, ta fito ɗaure da tawel da alama ruwa ta watsa, Aysha na kwance tana kallon ta har ta gama shiryawa cikin kayan barci karamar riga da dogon wando masu taushi, ta shimfiɗa pray mat ta kabbara sallar shafa'i da wuturi, har ta yi ƴan addu'o'inta ta shafa, idanunta a kanta kamar zata cinyeta da ido, sai da ta gama ta ninke sallayar ta mayar ma'ajiyar shi, sannan ta ta juyo ta kalle ta ce " yau na shiga uku da wannan mata kallo haka kamar wacece ta warke makanta." Murmushi A'ishatu ta yi tace "Hmmm wlh mamakin ki na dazu na ke yi." Taɓe ba ki ta yi tace "Ɗazun da na yi me kike mamakina, ke dai baki rabo da tsarabe tsarabe." Eshart Tace "Allah ba wasa na ke yi ba ɗazu a green land yadda na ga kin wani ruɗe da zuwan wannan mutumin da naji kuna ta kira da, Mr AA kangiwa, Allah abin ya ɗaure min kai shi ba sahabi ba shi ba ba tabi'i ko tabi'id tabi'ina ba." Wani irin zaro ido Salmah ta yi tace "keee! Kinsan wanene Mr AA kangiwa kuwa?" Ta karshe maganar tana rike haɓa, kallon ta A'ishatu ta yi a zuciyar ta tace "anzo wajen." Miƙewa ta yi zaune ta gyara zama cikin alamar ɗokantuwa da son jin labarin Shi tace "Ina kuwa zan sani Sister." Salmah tace "Haba shiyasa kike wani cewa kaza da kaza akan shi, Allah da kinsan wanene AA kangiwa da sai kin fini ruɗewa, hmm ke ba ki ga yadda kowa ya ruɗe dajin sunan shi kawai ba, kai Mr kan giwa ya haɗu ta ko ina ga kuɗi, gayen ga mulki, ƙasar nan baki ɗaya tasu ce,ga kyau uwa uba kyakkyawar zuciya,wlh ina son guy ɗinnan kamar na zauce ni ko da gaisawa dashi na samu na yi sau daya na more." Ƙur A'ishatu ta ƙurawa bakinta idanu tana kallo, duk wannan lissafin da take yi,ita ba shi take son ji ba, Kawai abin da take son ji shine wanene shi?, Ɗan waye? Cikakken sunan sa? Da kuma matsayin sa a Nigeria? Amma ta ina zata fara jeho mata waɗannan tambayoyin ba tare da ta kawo zargin wani abu a ranta ba.
muryar salmah ta tsinta tana cewa "kinsan kuwa wanenen Mr AA kangiwa?" Da sauri ta dawo haiyacinta tare da girgiza mata kai, Salmah tace "hmmm zan gaya miki amma ba yau ba dan wlh yanzu barci barci nake ji, kuma gobe inada class din safe." Ta ƙarashe maganar tana sakin hamma tare da fara lumlumshe idanu alamar dai barcin takeji da gaske. Innalillahi! A'ishatu ji tayi kamar Salmah ta ƙwada mata ƙaton sanda a tsakar ka, ji tayi gabanta ya shiga wani irin ɗuka da sauri da sauri, zuciyar ta ce ya shiga bata shawarwari kala kala, ta riga tasan halin Salmah da kafiyar tsiya tunda ta furta ba yanzu ba,to kuwa baza ta faɗa yanzun ba, wata zuciyar tace ki fito fili ki gaya mata wacece ke da kuma abin daya fito dake daga kauyenku har kika faɗa hannun iyayen ta, wata ƙila zata ji ƙarfin taimaka miki, wata zuciyar ce ta ƙwabeta da cewa Ahir ɗinki yar Baffa wannan ganganci ne wai haihuwa da damuna kinfi kowa sanin wacece Salmah bakin ta baya haila, bacin haka kin shirya baiwa wani labarin rayuwarki ne? Idan ma kin shirya ba Salmah ba, domin bata da nutsuwar da zata iya daukar nauyin ruɗanin dake cikin labarinki a kanta, kiyi hakuri kibi komai a hankali, sannu ai bata hana zuwa, kuma in kere na yawo zabo na yawo wata rana za'a jone, indai baki da haƙƙin Babangida to kuwa Allah sai ya saka miki akan zalincin da ya miki. Bata san ta lula dogon tunani ba saida ta tsinci saukar numfashin Salmah a kunnenta alamar tama yi nisa cikin barcin ta, jiki a sanyaye ta miƙe ta faɗa toilet itama, wanka tayi wanda ya zame musu jiki a gidan wankan dare kafin barci sun dauke shi kamar wani farilla wannan kuma tirenin din Ammi ne kasancewar ta mace mai matukar tsabta. Alwala ta d'auro bayan tayi wankan ta fito ɗaure da tawel, kayan barci ta sanya itama ta gabatar da shafa'i da wutiri, ta daɗe tana addu'o'in samun nasara akan abin da tasa gaba kafin ta miƙe ta maida pray mat, ta kashe wutar d'akin sannan ta lallaɓa ta kwanta kusa da Salmah, tare da ja musu bargo. Ƙamas haka take jin idanunta a bushe babu alamar wani abu wai shi barci, tafi awa d'aya a kwance tana saka da warwara, ji tayi daren yayi mata nisa. Sabo fil haka taji tabon da Babangida ya bar mata a zuciya ya dawo, ƙudiri da muradin daukar fansarta yana daɗa ninkuwa, taso koda cikakken sunan wannan mutumin ta sani, duk da bata da tabbacin shine Babangida, amma ai yadda suke da tsananin kamanceceniya bazai rasa nasaba da shi ba, me yuwuwa ɗan uwansa ne na jini, jin barci baida niyar kawo mata ziyara yasa ta mi'ke zaune tare da lalubar wayar ta, Karfe goma sha biyu da ƴan mintoci na dare, data ta kunna take kuma ta shiga tunanin ta ina zata fara, direct Facebook ta shiga wurin searching, ta rubuta *kangiwa* take ya nuna mata sunaye masu ɗauke da kangiwa bila adadi, zuru tayi tana binsu da kallo, ta rasa ma me zatayi, zuciyar ta tace ta bata shawara da cewa ki bisu da ɗaɗɗaya ki duba sunan Babangida kangiwa, hakan ko tayi, har ta gama zageyen ta ta sake babu wani suna mai kama da Babangida a cikin jerin sunayen, bata haƙura ba haka taita research daga wancen manhajar zuwa wancan, amma babu alamar nasara, ta kwashe kusan awa biyu tana abu daya , dare ya tsala sosai tuni barci barawo ya shiga kawo mata farmaki, tana dojewa batasan sanda yayi nasara a kanta ba sai tsinkayar kiran assalatu tayi a kunnenta, lumshe idanun ta da sukai mata mugun nauyi tayi ta buɗe akan fuskar Salmah dake ɗan motsawa, so take ta mike amma jikinta babu kwari, gefen kanta taji ya fara sara mata, tana jin sanda Salmah ta mi'ke tana da karanta addu'ar tashi daga barci, makunnan wuta ta laluba ta kunna wuta take dakin ya gauraye da haske kamar da rana, toilet ta shiga tayi uzirorinta tare da dauro alwala ta ta fito, duk abinda take yi tana jin ta, kin tashi tayi sai da Salmah ta shiga dan bubbuga ƙafar ta tana kiran sunan ta sannan ta buɗe idonta daya mata wani irin nauyi dakyar , suna haɗa idanu ɗan zaro ido Salmah tayi tace "subhanallahi sister Eshart ya naga idanun ki kumbura sunyi ja kamar baki samu isasshen barci ba?." Cikin basarwa tace "ina ganin ciwo suke min." Daga haka ta samu ta yaki zuciyarta ta miƙe dakyer tana layi ta shige toilet, koda ta fito akan pray mata ta samu Salmah hannunta riƙe da dan ƙaramin Qur'ani tana bitar haddanta a zuciya, wani daddumar ta shimfiɗa itama tayi nafila tare da daukar nata Qur'anin itama da nufin yin bitar amma ina ji tayi idanunta na mata wani yaji², a haka har aka ta da sallah a masallacin gidan duk mikewa sukayi suka bi jam'i kasancewar tangararau suke jin kiran sallar kamar a cikin ɗakin nasu akeyi.
Suna idarwa ko addu'a bata tsaya anyi da itaba ta mike ta fada kan gado, ragwab! tun cikin sallar taji wani matsanancin ciwon kai ya ziyarceta a lokaci guda tare da wani irin barci mai nauyin gaske, Salmah kam baki ta sake tana binta da kallo, a cikin kwanaki biyu nan lamarin Eshart ya fara ɗaure mata kai yanzu zata ganta normal anjima ta ganta a birkice, bata ce mata komai ba saida ta gama addu'o'in ta, miƙewa tayi taje ta gabanta ta leka fuskarta ta, gani tayi tana sauke numfashi alamar barci yaci karfin ta, a fili tace "oh ni Salamatu meke shirin faruwa ne haka, anya kuwa sister Eshart tana ƙalau." Sake leka fuskarta tayi tare da kai hannu ta ta'ba goshin ta, Aiko ya dau zafi zau ga jijiyan kan sun fiffito da alamar kan na mata ciwo, cikin sauri ta fice a ɗakin don gayama Ammi abinda ke faruwa.
*KANGIWA ESTATE*
Babban estate ne wanda zan iya cewa babu irin shi a ciki da wajen birnin, gidaje ne a cikin shi tsantsara tsantsara masu fasali irin ɗaya sunfi guda ɗari, sai dai wani yafi wani ƙayatuwa da wasu ababen na more rayuwa, hakan ba zai rasa nasaba da yanayin aljihun mabanbantan mutanen da ke zazzaune a cikin rukunin gidajen ba. Dare ne da misalin Karfe 9 wata falleliyar mota mai mugun tsada kirar yayi baka ƙirin sai walwali take yi, tayi horn a bakin makeken get ɗin estate ɗin, da sauri biyu daga cikin sosojin dake gadin get din suka leƙo, ganin falleliyar mota ba bakon abu bane a garesu dan a cikin estate din a kwai manyan yan siyasa da yan ƙasuwa da ma ma'aikan gwamnati masu ji da naira a kwai kuma takawa masu karamin karfi. Doka ce sai sun duba koma wanene ya zo kafin a bude mishi get ya shiga, daya daga cikin su ne yayi knocking din motar, ba'a bude ba sai da aka kwashe kusan mintuna biyu, sannan a hankali glass din gefen direba ya fara zuwa kasa kusan a tare suka leka ciki motar, ganin wanda ke zaune cikin motar yasa jiki na bari suka shiga rige rigen buɗe get din,sai da suka gama buɗewa sarai, sannan motar ta fara tafiya zuwa ciki, duk kamewa sojojin nan su ka yi alamar girmama ga mamallakin wannan motar, tsayawa motar ta yi a daidai wurin su, a hankali ya miƙo hannunshi ya yafito babban cikin su, jiki na rawa ya ƙarasa tare da sara mai, sannan ya duƙa daidai windon. Shi kaɗai ne cikin motar sanye cikin ƙananan kaya kanshi sanye da P cap fuskar shi sanye da wani irin facemask wanda ban taɓa ganin irin shi ba,mai faɗi ne wanda ya rufe fuskarshi sosai har ta ƙasar haɓarsa, idanunsa sanye da wani siririn glass baƙi wanda yayi masifar yi mishi kyau, a hankali cike da tsabar madaran miskilanci, cikin bada order yace "kada kowa ya san na shigo estate." Da sauri ya sake ƙamewa tare da cewa "yes sir." Da wani irin masifafen gudu ya ja motar ya harba kan shimfiɗaɗɗen kwaltar da ta mika zir har karshen estate ɗin.